Showing 57001 words to 60000 words out of 119289 words

Chapter 20 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9441

yayi yawo ya dawo ya bude kwano yaci Kaza ya fice,washe gari ma aka yanka zabo aka Masa farfesu ga kudi a aljihu yaro da hauka shi gani yake gata ne duk dadin da yake samu a Gaban Jawad bai Masa ba shi yasa akace a yaran ma akwai marasa tunani sosai


Yau da dare ni kuwa bayan na gama da Yara na musu Assignment Asmau ganin ba Nawwara ta dan sakko kadan har ita na yiwa Assignment na koya musu karatun Islamiyya,sai dai yaran su kwana a wajen masu aiki sabo da ba yanda za ayi a bar yaro su kadai,Meenat da kyar ta yarda ta kwanta can
Wanka nayi da brush nayi Shirin bacci na cikin kayan bacci wando ko gwiwa bai Kai ba da riga Yar karama me siririn hannu wasu masu laushi dark green and orange,Ina Fitowa Allah yasa da hijab dina dogo Hafeez ya shigo yace Aunty dan Allah indomie nace Wai Waleed bai dawo ba? Yace dan Allah ki fadawa Yaya Kar ya dawo da yaron nan ya rabu da su Kawai tunda basu da hankali, nace ai bazai yuwu ba kasan yaro da shirme gwara aje aji idan aka tattabar gidan Suka je shike nan,Okay Aunty Indomie din Dan Allah su Bintu sunyi bacci,to bari in na gama Zan kiraka a waya,sharp sharp na dafa Masa indomie tasha hadi na kirashi a waya ya dauka na kashe komai na wuce part din oga.


Ina Shiga naji Yana ta wayyo ya lulluba Yana ta rawar sanyi Yana nishi,Yana kaina kaina zai fashe ohhhh.....saman bed din na haura nace lafiya yace zazzabi da ciwon Kai Miko min paracetamol,na dakko Masa magani da ruwa hannunsa Yana karkarwa ya Sha ya koma ya kwanta harda cewa na Karo Masa bargo dama shi Yana yawan Yin ciwon Kai musamman idan yaje aiki ,Na sake lulluba Masa bargo na zauna a gefensa can naji yayi shuru Wai har ya sauka zazzabin ya bude bargo ya hada uban zufa harda galla min harara nace me nayi? Haka ake jinyar me zazzabi? Murmushi nayi yace Karo min ac mutum ba tausayi, ac na Karo sosai na kwanta can gefen bed yayi kwanciyarsa,da wuri nayi bacci Yana zaune sai da ya gaji dan Kansa dake na kashe light Kawai ya kwanta,gaf dani ya kwanta ya leka fuskata yaga Ina ta bacci yatsansa yasa a kunnena kadan banyi ko motsi ba,gashi na ya ja kadan Shuru,wuyana ya shafa na dan motsa kadan ya zare hannunsa da sauri ya sake jira,sannan ya jawoni tsakiyar bed kaina na sosa,Ina cire hannun a hankali yace bari a sosa Miki,ya Sosa wajen yaga ban farka ba yace sai kace gawa,girgizani yayi yaga shuru,ya daukeni cak ya maidani kusa da shi sosai yaga ban farka ba,yatsu yasa ya dallar min wuya,a gigice na farka na kalli inda nake nace waye ya kawoni Nan? Kinzo nan sai manne min kike,nace sorry na koma can inda na Saba kwana,sai da ya bari na koma bacci na ya daga kafata daya sama ya jawo ni,na farka yace Asuba tayi,zumbur na mike nayi hanyar toilet Yana kallo Dan mugunta har nayi Alwala nayi Sallah sannan yace ashe 12pm na zaci 5pm ma yanzu, wani takaici ya kamani na koma resting chair na kwanta abina sai bacci,bacci na yana nisa ya dawo ya dauke ni harda min shillo ya kwantar dani ni a bacci naji Kamar an daukeni ban iya tunawa ba sai da nayi bacci ya kwanta a jikina kuka na saki Ina dukansa a hannu wajen ciwonsa,zafi yaji ya koma gefe can inda yake,sai da baccinsa yazo sannan bai San ma yayi bacci ba,harda makara sai dana farka na ganni inda nake kwanciya ina tashi nayi brush da Alwala na fito sannan na tashe shi nace mun makara,tashi yayi shima yayi brush da Alwala dake yanzu kwana Uku Yana yin abinsa da kansa


Kadada Kuwa ranar da Suka dira a Kauye Yan Gida suna ta murna ana ta zuwa Sannu da zuwa Yara har sun waye sun Zama Yan birni,Ashariya ce Kawai ke tashi ba ga yaran baga manyan maza da Mata kowa narkota yake,Kadada tace har nayi Ja haba Kuna cikin bala'i,Tahantsi ana ta kallon gashinta Wai yasha kyau ana ta yabawa,Gwamma tazo tace wannan ai Iskanci kuka koyo,Kadada haushi ya kamata dama Gwamma kakar kowa ce sune tsofaffin gidan,tace Dan Allah kwashi gashin Hammatarki ki Kara gaba Gwamma haba gashi kinyi daura kirji jibi fa gashin hammatarki sai kace anyi adon allurai a jikin banko cako cako, Tahantsi tace baza fa su waye ba,Gwamma ta duro ashariyar tace me kuka kawo Mana Kadada data Hantsi Suka kalli juna Suka ce dama sai da Muka Yi gulmarki a jirgi,Nan fa kowa ya gigice su Tahantsi sun hau jirgi azo a gansu aka yanyamesu a gidan Wai ga bakin jirgi asha kallo ana ta washe baki ana kallon su Kadada Kamar sababbin amare akan Kawai sun hau jirgi sai da aka nutsu su Kadada aka bude tsaraba ko wanne waje garin kwaki gongoni Daya da yankan sabulu Daya da kullun omo,danginsu Kauyen sai da aka aika gida gida tsarabar Lagos,Tanoma aka sa wuka aka yanko Mata sabulu da dan tsayinsa aka hada Mata harda takalmi flat na roba Suka tafi da kansu da daddare za a Kai Mata.


Suna shiga Tanoma ta shararo ashar tace yayi mutanena ah'ah wannan kyau haka,Suka hau tafawa duk magana sai an duro ashar,Tanoma tace kunyi kyau Ina kuka baro min mutuniyar Fara? Ke Fara me farar aniya Fara anci gaba kije kiga Fara yanzu ai yanzu take farar ba da ba,Tanoma aka rike baki da cikinta a gaba,tace ya soyyaya da dan birni? Kadada tace tana can tana cin ubanta tana ta soyuwa har tayi rumus,ai mutuniyar taki anji dadin Namiji mayyar kullum tanacan wajensa Wai kula take da shi ga kudi duk son kudin Fara haka take fal fal fal da kudi Tahantsi ta gwada tana shafe tafin hannunta


Kadada tace zamu tafi ban fada Miki ba nayi katon Goshi,goshina ya girma yayo kwal gaba na samo abokin Jawad,Tanoma tace Kadada Musulmi ne? Kadada tace ae,ai Kuwa su Tashuka baza su yarda ba kin sani karki dakko bacin rai, tab wa ya Isa dani sai in bana sonsa har iyayena sai na bijire musu zaku gani,yo Ni wa nake tsoro ai sai dai kuji kallamar shahada a katuwar speaker ta masallacin garin Nan,bazan Musulunta a gidan Ummiya ba a kauyen Nan Zan Musulunta ranar juma'a sai an sa min speaker a baki kowa yaji a garin nan sannan na zabi suna Fatima daga ranar na koma Fatima Binta Sugar, kowa daga ranar idan bai kirani da Binta Sugar ba a garin nan sai ya gane kurensa ke kin sani kaf garin Nan musulmi sunfi yawa mu dama bamu da yawa, tashi mu tafi Tahantsi me Sunan lokacin Sallar walaha ,Tanoma tace au har Sallar walaha kin sani? Kadada tace ai Muna ji musulmai suna fadan komai Muna gani dole na rike Suka Yi waje,kwana daya zance ya watsa Kauye Kadada ta kusa Musulunta,musulmai a Kauye ana Sallah bayan an idar Liman harda cewa wannan yarinya Kadada da take kaunar musulunci Allah ya karkato da hankalinta Allah ya shiryeta ta karbi kalmar shahada, dama liman yasan Kadada tasha dura Masa ashiriya tafi a irga har gidansa take zuwa ta zazzageshi ta fito musamman lokacin azumin Ramadan Wai ya hanasu bacci da Sallar dare sai taje har gida tayi sallama da shi ta kutuntuma Masa ashariya ta tafi, Haka ladan ma har tare Masa hanya take yi ta antaya Masa zagi


Su Kuma limaman Kauye ga shiga sharo ba shanu har sai an zake ko cuta wani yake a kauyen su Kadada sai sun Kira sunan me cutar wane wane Allah ya bashi lafiya,ko haihuwa akayi sai liman yayiwa jariri Addua a speaker haka za ayi ta jero masu matsala a gari ana musu Addua,barawo idan aka ji an shiga gidan wani sai kowa yaji a masallaci ana addua ko Kuma sai cikin dare kowa na bacci 2pm suzo su kunna karatun Qur'ani,wani idan ya farka shi da bacci shike nan akan haka Kadada take Tawaye,Kafin Kadada ta koma wajen Ummiya har Binta Sugar ya yada gari duk musulmai Ina Binta Sugar


Bayan kwanaki Farooq ya kira Kadada a waya harda gaida shi Ina yini,yace lafiya Alhmdllh Yana dariya kadada tace bafa nason rashin mutunci zamu bata mene na wani dariya na daina gaisheka,yace sorry to afwan,Kadada tace Kai ice ko baka kule kulen Mata naga Kamar idonka a tangare yake Anya kuwa baka dan aeee.....Farooq yace Ina dake ni na isa ba ruwana ni,yawwa yanzu a Ina Muka kwana da aure kazo ko da aurere? Yace ni na isa nazo da wasa,Kadada tace to na kusa komawa Binta Sugar nan gaba idan na gama shawara da zuciyata Zan Musulunta Kai zaka Zo Kauye ka karbi speaker ka musuluntar dani Kuma duk randa ka shirya aure musuluntata sadakin aurenka tunda naji Fara tana ta karanto ko kissar musulunci ko hadisi ko me to dasu zanyi koyi abin ya birgeni naga Kuma Dan kaza kazan da zai ce aure bai dauru ba Farooq yaji Abu Kamar a mafarki shi har ga Allah bai gama tantancewa zai auri Kadada ba yarinya tsagera taje Watarana ta zagi uwarsa,gashi tsoronta yake ji ta Kar taje ta hanshi sukuni,Bayan sun gama waya ya Kira Jawad ya fada Masa Jawad ya dinga dariya yace ka shirya jihadi wallahi lada Babba Farooq, albarkacin musulunci ni gaskiya Ina jinta a Raina amma ba can ba tazo dai tayi ta zama,Jawad yace wallahi a ka'ida gobe zamuje mutum zai Musulunta ayi gaggawa sabo da mutuwa rayuwa ba tabbas,baza ta mutu ba Inshaallah karka kawo Mana zancen mutuwa ana zaune kalau ai tace sai ta gama shawara ya kashe wayarsa Farooq yace daga Wasa yaushe nace Zan aureta ni gaskiya auren dole za ayi min

Wasa Wasa Jawad ya Kai wata guda da yin accident Ina Masa abubuwa da ma kullum ciwo ba sauki Kuma sai yaje office ya dawo gida ya narke idan na daina zuwa tayashi kwana sai ya tsiri zuwa asibiti kullum yace ya tafi asibiti Wai ance yayi bugun ciki cikinsa sai ya dinga ciwo Wai jini ne ya daskare a cikinsa inji karyar Jawwad,,munyi mugun sabawa da juna sabo yawan mu'amula tare ko Ni yanzu bana son na kwana ba shi a gefe duk da ba abinda yake hadamu amma dadin hakan nake ji,ga yaran gaba daya mun shaku,Hafeez ana ta Masa shirye shiryen tafiya turai shi da Ahmad za a hada Kawai duk da Hafeez ya riga Ahmad gamawa sai yace ya jira Ahmad sai su tafi tare,Ni Kuwa batun karatu har an siya mun form Yan Yara duk mun Saba da juna,Tunda nazo gidansa watana uku kenan bai taba barina na fita ba ko bakin gate tunda nabi su Kadada sau daya ya dinga masifa ko nace ya barni naje ko shopping ne shi bazai yarda ba sai dai na rubuta a bayar a siyo,makwafta sunzo min sau nawa yaki bari naje har sun daina zuwa, yau yara kaf Yan manyan yace Hafeez ya tattara su ya kaisu yawo amma Ni banda ni,shiryawa nayi harda yin shigar musulunci ko zai barni nasa hijab na yayi masu kyau har kasa me hannu nasa nikaf, sannan na je part dinsa na iske Yana ta rubuce rubucensa Yana shigarwa Yana fitarwa Yana ta lissafi


Sabo da Ina so a barni nace dan kasuwa dan kasuwa Allah ya Kara ma lfy Allah yasa bugun cikin nan ya warke sai lokacin ya kalleni tunda yaga haka yasan ma dalili bayansa zai Sosa nace tsaya na Sosa ma,harda cewa Yi sauri kaikayi,Dariya nayi na Sosa masa na sarkafo hannayena biyu ta wuyan na kwanta a bayansa duk ba bamu taba haka ba sai yau nace naje dan Allah? Murmushi yayi yace ki dinga kaunar Allah dai ni na San ba banza ba kuje tunda kinyi shigar musulunci haka ake so ki dinga fahimtar Allah kullum ana doraki a Hanya bakya ganewa jiya ko gaishe ni baki yi ba,sabo da murna na jijjiga wuyansa da karfi gefe ya turar dani kije Saura kije ki ta yake baki kina Hafeez Hafeez harda da gwada yake bakin da hakora kina washare baki a gaban kannen Miji dama Ina ciki dake naji Sanda Ahmad ya tsokaneki kin iya girki Aunty, harda Dariya ke ga gwana ta gwanaye me tuwo ba gari jeki dan Allah kafin kisa na fasa barinki kina Abu Kamar zamanin fir'auna Kika Zo raino ko na dakkowa kaina raino,Tafiya nayi Ina dariya nidai tunda an barni shike nan nabi su Hafeez Muka ware,ko 30mnt bamuyi ba ya dinga sambado min Kira naki dagawa ya koma Kiran Hafeez yasan mitar Jawad ya daga yace kai wannan dadewarfa kwana kuke so kuyi ne,Hafeez yace haba Yaya yanzu ma fa ko 3mnt bamuyi ba,Ni kakewa musu ka rainani ko to a fasa ku dawo gida,Hafeez yace to ya kashe wayarsa


Nace dan Allah rabu dashi Muka ci gaba da harkokinmu duk munga kiransa Muka ki dagawa,ya gama kulewa sai wurin 11pm na dare Muka koma gida, ai a compound na ganshi a zaune a wata kujera,nace Kar kowa yayi magana,Ina Fitowa na fito da takalmana a hannu ya bude baki zaiyi magana nace ka godewa Allah da Muka dawo gida a raye,Jawad sai yayi slow yace lafiya nace ai da yanzu mota tayi filla filla da namanmu motar ma Sai da Muka tsaya gyara yaran nan ma takeaway Muka musu Kar a barsu haka yaro bazai ji dadi ba,Sai masifa ta koma Kan Hafeez Zan kwace Motata Zan hanaka driving baka da hankali zaka kashe min kanne,Hafeez Yana ta dariya a ransa ya wuce ciki,na bawa Yara nasu nace Masa muje Ina cewa ai Hafeez yau munga basirarsa shi ya goce abin bai faru ba


Sai da Muka shiga ciki yace anya ba karya kike ba? Nace hmm Kawai na cire hijab dina da Nikaf na kwanta a saman bed nace ga naka take away din yau bazan iya girki ba,dama ni nace ki dafa min abinci ko kinji bakina nace wance Yi min girki,me yasa yanzu ka koyi fada ne da mita? Ke Kika koya min kullum na dakkowa kaina raino,sai da yaci abinda Muka siyo yaje yayi wanka tare da Shirin bacci yace wankan fa? nace dazu fa nayi da magriba sai kace agwagwa Ina laifi kullum Ina Yi sau biyu Watarana sau uku ma,baza ki kwana a dakina ba nace tafi nono fari na mike zanyi gaba.


Yace ni kike cewa tafi nono fari? Kal ma kuwa na fada na fice,harda cewa Iyyeeeeee ae ba laifin glob bane batir ne,Ni na jawa kaina ya mike ya sawa kofarsa key yayi kwanciyarsa ya kasa bacci,sai yaji ya dawo gwauro yace Kai ya naji Kamar lokacin Ina gwauro na,Tsaki yaja yace dole ma nayi bacci na,ya kasa bacci ya tashi yayi nafilar tsakar dare har sai 2am sannan ya iya bacci,Nima bangarena haka dan akwai gajiya a jikina ne da bazan iya bacci ba,Meenat naje na dakko mukayi kwanciyar mu


Ummiya Kuwa Sanda na kirata sai tace Asif yazo ya kawo musu kayan abinci ki Masa godiya nace to,sai tace turo min number dinsa sabo da ya karbi tawa Kar ya kirani nace waye ai ba Dadi nace to nan take na turawa Ummiya
Tana ganin number ta Kira Asif tace ka kawo Kaya ko ka shugo mu gaisa yace wlh lokacin sauri nake kiyi Hakuri,Ummiya tace dan Allah Ina son ganinka a satin nan,yace to zanzo gobe Inshaallah,tunda yaji ana nemansa ai yasan da dalili babba,washe gari da wuri ya sauka a Kano zuwa gidan Ummiya,har Palo ya shiga lokacin Daddy Yana wajen aiki


Bayan sun gaisa ta sake Masa godiya tace dama tambayarka zanyi tsakaninka da Allah,Tsakaninka da Allah,Tsakaninka da Allah,ka dubi girman Allah ka fada min wanne dalili yasa aka auri Najla,Asif yaji wannan magiya ga an hadashi da Allah Indai me Imani ne shi ya Isa ya kasa fadar gaskiya,nan ya kwashe labarin komai ya fadawa Ummiya,karshe sai yace amma wlh da Yan aiki da komai ba abinda ta nema ta rasa Kuma ita da mijinta sun fahimci juna yanzu Allah ne yayi silar haduwarsu haka,Ummiya a ranta Sam bata yarda ba taji haushin yarta data iya zuga mata karya,ramin karya ai kurarre ne zata gane kurenta daga yanzu sai ta daina son kudin masifa,Ummiya tace na rasa wannan son kudi na Najla amma rabu da ita Kawai zanyi maganinta,Asif yace dan Allah kiyi hakuri ki barta yanzu zaman aure sukeyi na gaske,Ummiya tace ka barni da 'yata ba ruwanka duk ba kune kuka ja ba idan kannenku ne zaku bari su aure Haka Yara goma sha duk a wuyanta,Ni nayi bautar auren wahala Allah ya fidda ni sabo da haka ni 'yata baza tayi ba,Asif yace kowa da kaddararsa Umma,bai San Ummiya ta iya ashar ba sai yau ta shararo Masa ita tace rufe min baki,Asif a ransa yace jini ba karya ba zaka ci ubanka Jawad Saura kai,Ummiya tace jeka Alhmdllh naji komai,ya tashi sum sum,Ummiya tace an dauke mu talakawa masu son abin duniya za a Raina Mana hankali da kudi,mu Muna da wadatar zuciya,Najla Kuma sai tasan ta min karya.


Asif tun kafin ya bar unguwar ya kira Jawad ya fada masa komai yace akwai Kura,Jawad yace Kaine babban munafuki da kaje ka fada sirrina,yayiwa Asif kaca kaca harda cewa ya bashi huttun aiki na wata biyar ba shi ba ganin salary.
Asif yace shi yasa ba a so kayi dalilin aure gashinan ta Kare a kaina,duk me dalilin aure Yana cike da shiga irin wannan Nima nabi layi.


Ni dai ban San me ke faruwa ba naga Jawad Yana ta fushi ya shiga ya fita ban taba ganinsa a damuwa haka ba,a kwance na ganshi a saman bed nace Wai lafiya? Yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login