Showing 108001 words to 111000 words out of 119289 words

Chapter 37 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9437

kaunarsu yake,Ummiya ta karbi kudi Muka fito godiya tayiwa Jawad mun fito zamu tafi sai ga Tahantsi sanye da Uniform nace har zamu tafi tace wlh da nasan zaku Zo bazan je school ba yau amma Fara kin cuceni baki fada min ba,Yaya Jawad Ina yini,ya amsa da fara'a Suka gaisa yace Yan makaranta har mun gaji zamu tafi, Tahantsi tace matarka ce me bakin hali bata fada min ba sai tayi ta wani yanga sabo da tana da Kai ita a dole tayi clean,Jawad Murmushi yayi kawai tunda yasan haka muke caccakar juna,Kallon fara tayi tace lalalalalalala haka Kika Kara haske da kiba karya kike ciki ne dake,ki siyi abin test Fara ki gwada,Najla kunya ta kamani Tahantsi da Kadada ba kunya ce da su ba gaban kowa zasu iya fadar abinda suke so,nace wanne irin ciki Kuma a ruwa na Sha? Tahantsi tace a'a a shayi Kika kurba,Wai Ina Kadada ta ne Yaya nata cikin? Nayi dariya nace ke kinga uban girman cikin Kadada Wai ta daina fita ciki wata hudu Wai baza ta sake fita ba karta haihu a hanya, Tahantsi ta dinga dariya har Jawad,Jawad yace ai sai da naje gidan sannan ta koma school da kyar Wai Farooq din ma ya yarda baza taje ko Ina ba,Ina zuwa Binta sugar ta fada min ai Kuwa na musu fata fata sannan ta koma school,Wai da mayu take haduwa a hanya shi yasa inji farooq,muna ta dariya Jawad yace za a bi shawararki Tahantsi aje ayi test nima ban yarda da Fara ba Maybe ta kurba a shayi din, Tahantsi tace ko a kunu ba a ranta tace ni za a maida yarinya,mun dade Muna surutu data Hantsi har 6pm muna kofar gida sannan zamu tafi nace Wai ya Kika Kare da Gwamma?


Tahantsi tace tana can a jibge a Kauye dana kaita Yan gida Suka yo caaaa kaina Saura kadan su lakada min duka sabo da tsabar haushinmu da suke ji,Ni Kuwa Ina kaita na juyo na gudo gida tana can tana ta faman na siya dinta ga kashin kwankwaso ya goce komai sai an Mata, Rannan da Ummiya taje duk me tallan data shiga gaaaaa kaza tace na siya,yanzu sun Kama jakar Kadada da dan data haifa sun siyar wai za ayiwa Gwamma magani Ni Kuwa an hada da tinkiya ta an siyar nace na yafe musu su karata,Kadada Kuwa tace bata shirya yafewa yanzu ba sai bayan ta haihu,Mukayi Dariya sannan Muka Mata sallama na bata 10k nace idan kinje Ummiya zata nuna Miki kayan da Kadada tace a kawo Miki,to Zan kirata a waya nayi godiya, airport aka wuce damu Muna komawa gida muka iske Safna ta kawo yaran gaba daya kowanne da sabon hadadden Kaya a jikinsa sun Sha wanka har manyan yaran sunzo da kayan shopping Niki niki ta yo musu sai kaunar Safna sukeyi kasancewar Wasa take Yi dasu sai ta shiga cikinsu suyi ta Wasa tare,sai da Jawad ya Mata godiya sosai yaji dadi shima Safna ta bada mamaki babu Wanda ya zaci haka daga gareta.


Bayan kwana Uku da Yamma zaune nake a Palo naci wanka cikin wata Gown me kyau arsh kallo nakeyi sai ga Kadada tayi sallama sanye da uniform nace a'a masu ciki ne a gidan? Dan bakin ciki sai dai ya mutu ba ta shigo ta zauna tace wata Mata a kusa da gidana Kawai tazo Wai ni zata Zo har gida ta nuna tana son Farooq karshe da taga ba Hanya Wai sai tazo rannan Wai ashe mijin naki ma baki ne, Wai Farooq ne baki kiji hassada ai Kuwa jiya na wanke dan Farooq dina fes na hade abina nace muje ka rakani unguwa har gidan ubanta muka je sabo da ta kalleshi sosai,Farooq bai San dalili ba sai data rakoni mota ta ganshi,nace bata San marar mutunci ta tabo ba,Kadada tace ai bata San bani da mutunci ba ni ba Yar arziki bace ka zauna Dani lafiya ma ya ka Kare balle ka tabo ni,ai Kuwa ranar tasan Jinin Gwamma ce,nace kice ta karbi Dan gado? tace buhu buhu ma ai tun a sannan ta gane shayi ruwa ne,a kwalta ta dura Mata buhuna tayi gida da su, nayi dariya nace Kadada masifa Binta sugar jaraba


Wai Ummiya kinji zata sake auren Baba ta koma gidan,Kadada tace Baba dai naki ko wani Baban nace Baba Nawa,Kadada harda dafa kafada ta na zaci kwantar min da hankali zata yi amma sai naji tace kiyi hakuri Fara amma gaskiya Ummiya an Fadi ba nauyi,duk wahalar data Sha a baya nace Kawai yanzu maybe gani take ya canja tunda ya dauke Mata komai Kuma Tahantsi tace a sati sau biyu sau Uku yake zuwa zance Wai har wata kwalliya take ta musamman tayi Masa girke girke,Kadada tace yo ai Tahantsi ta guntsa min a waya tace har fari da rangwada,tagumi na zuba nace ai Ummiya Ni gani nake ai ta wuce aure ma,Kadada tace baki da hankali da nawa Ummiyan ta girmeki su da aka musu auren wuri shekara 13 anyi aure Kuma da wuri ta Haife ki ance babu tausayinta da ba a ji ba lokacin tatsitsiyar kwaila da ita amma da ciki,nace Zan Miki rashin mutunci Kadada uwata ce fa,to ni uwata ce abokan Wasa muke fa cewar Kadada,nace to ai sai ki min Kara,tace Kinga ki kyale baiwar Allah ta koma anaconda ce tayi Kira,nasan Kadada ko Uwarta ce fada zata Yi bare Ummiya shi yasa nayi shuru,Kadada harda masifa haka Kawai Mata tana son saurayinta kice baza ta koma ba ki hakura tayi aurenta,Kinga ni bani abin awon cikin in kin siyo min,Kadada ta Mika Min dan tsinken dake Jakarta muka Shige bedroom,naje nayi fitsarin a murfin dan abu na saka tsinke na gwada abinta ya nuna Ina da ciki,na sake ciro wani na gwada har sau Uku ya bada ina da ciki,Fitowa nayi na nunawa Kadada tace inye anyi ciki to ai shike Nan sai a tafi asibiti gobe a sake tabbatarwa shi yasa nace Miki ki gwada da kanki,Ni Kuwa harda cewa a siyo min farar kasa,Kadada tace baki da hankali ni na tafi gaskiya an kawo min Yar aiki tana nan babbar mace ce me hankali,Nace Farooq ya kyauta baza kici komai ba?tace ae ba abinda Zan ci ni na tafi gaskiya ba son Fitowa nake Yi ba sai dole Kar nazo haihuwa ba shiri ko haka Kawai na hadu da matsafa ko mayu bada ni ba ta fice ta tafi


Sai da Yara Suka dawo daga Islamiyya sannan naje na yiwa su Meenat wanka duk Suka shirya sannan Muka Yi Sallar magriba na zuba musu abinci kowa yaci,Waleed ne kadai nasan baya son jollof ko wacce iri ce,Yanzu ya sakko sosai ya daina min Iskanci sai dai duk da haka baya ji wani banzan hali ne dashi,Nawwara kuwa tunda Jawad yaci ubanta ta shiga hankalinta ita da Asmau sun hakura sun daina mun dawo kamar da sai dai abinda ba a rasa ba dole ne rainon Yara sai kayi hakuri yau a bata maka gobe a faranta maka,Iyayen Yara ma ya Suka Kare bare Kai da baka haife su ba,Allah yasa Safna tana taimaka min ko yaushe ma suna gidanta musamman Weekend ko yaran Umma a kawo su Muna ta zumunci abinmu Safna ta Zama mutuniya ta sosai.


Wanka nayi na cakare cikin kananan Kaya wani dan bum short blue da Yar wata top fara me sharara hannunta dan gajere gaba daya gaban rigar a bude yake da wajen kirji ne Kawai aka Mata wani dan zare na daurewa Wanda ba Kara min kyau nayi ba Kamar wata baturiya,gashina na gyara sosai na Masa dan style jelar tana gadon bayana na zuba kyau Ina zuba kamshi na musamman,Meenat ce ta Fado bedroom din sai ta juya da gudu ganina a haka, Hijab Kato na saka har kasa na fito bayan na gama shiri,Ina Fitowa Naga Jawad a cikin yaran suna ta hira,ashe shine yasa Meenat ta taho da gudu kirana,tana kallo na tace na rantse ban fada ba Aunty ni dai ban gayawa kowa ba ta kalli Jawad ai Yaya ban ce ma naga komai ba ko,Jawad ya kalleni nace bance Miki in zaki shiga ko Ina ki dinga sallama kina knocking ba,sai ance ki shigo Zaki shigo idan Kika sake fadowa daki haka ba sallama ba Knocking sai na zaneki a gidan nan duk kowa ya fiki hankali har su Abeed,Meenat tayi mukus tace to kiyi hakuri ni ban fada ba,kitchen na shiga tace Aunty gashi nan baki sallama ba kema kince ko Ina a dinga sallama,Jawad ne ya rankwasheta yace sai na yanke Miki baki wato baza kiji magana ba ko,sorry yaya,mikewa yayi ya nufi part dinsa a gajiye yake sosai,lemon dana hada na dakko tunda dama abincinsa Ina gamawa na Kai part dinsa,Ina shiga na Iske ya daura towel zai shiga wanka,ajiyewa nayi na karasa inda yake nace Sannu da dawowa yawwa ya furta Yana kallona tare da jawoni jikinsa ya rungumeni,yace muje ki min wanka,nace to na cire hijab dina ya kalleni ya sake kallona sabo da Ina sa kana nan Kaya a part dinsa ban taba saka irin wannan ba gashi ko yaushe Yana ta min order daga waje kamar hauka, yace kinyi kyau me tukunyar zuma Yana ta bina da kallo Yana Jin dadi.


Toilet muka shiga sai kallona yake duk inda na motsa yace ayi sauri ayi wankan nan bazan iya jira ba,ko dai haka Meenat ta kalle min ke? nace ae Mana to ya zanyi Yara makaranta guda dasu haka a guda sai hakuri ,Dariya yayi yace bana son sharri bama aji guda ba makaranta guda,yace tsaya Kawai bari nayi wanka na Ina kallon abata karki bata min kwalliyar kinyi kyau kamar Kar na daina kallonki naja gefe na tsaya cakarere har ya gama wankansa da brush Muka fito abinmu yayi shirinsa da kansa daga shi sai gajeren wando nace Sallar Isha dinfa?sai dana yi a masallaci na shugo fa abinci kawai zanci,tare Muka ci abincin Muka koshi dama ban ci ba sannan muka zube akan bed Yana kwance yayi matashi da cinyata hannayensa Yana ta yawo da su a kirjina nace ban fada maka yace Ina jinki Peace ,My peace,Dariya ya bani har da wani sake narkewa nace kullum sai ka rada min sabon suna,yace ai idan Ina tare dake wani salama da nutsuwa nake samu dole nace Miki my Peace,gemunsa nake shafawa nace ciki ne dani fa dazu Binta sugar ta kawo min abin tsinken pt na fitsari Muka gwada sau Uku ni dai duka yace ciki ne dani da gaske ko karya ne oho,ni dai ana gwadawa ana tabbatarwa ciki ne sai naji Ina sha'awar cin kasa,Jawad ya dinga dariya yace to shike nan ai gaki ga garden me yasa baki je kin ebo kasa a can ba wajen bishiyu sai ki fara cin kasar,Allah da gaske dazu Kuma Ina wanka naji Ina son cin gawayi idan na tuno Sanda Muna girki da Ummiya a gida a kashe gawayi masu kyau kwambala Kwambala sai naji yanzu Kamar na ci,ko na samu na sheki warin wiwi,sabo da kinyi ciki ko cewar Jawad,ya zaci Wasa nake Ni Kuwa a zahiri nafi wata Guda Ina sha'awar cin kasa ko gawayi,ko naji warin Wiwi sai naji dadi hankali na ya kwanta.


Jawad yace Allah yasa Naga kinci kasa ko gawayi nasan halinki sai ki Fadi abu Kamar da Wasa ashe da gaske kikeyi,wiwi Kuwa nasan ba ganinta Zaki Yi ba balle ki shaka ke bari kiji wiwi cutar da dan ciki takeyi ba a so me ciki ta sheki warinta Yana cutar da jaririn dake cikinta karki sake,ko ai ba wiwi ba taba Indai Sigari ce ko wacce iri Ina son kamshin wani dadi Jawad yace gobe sai muje asibiti,ba kace zaka je Office ba kana da aiki,shike nan sabo da aiki bazan yi uzurin iyalina ba sai wajen aiki,to ka koya min mota Mana kaga an huta yace a'a bana son tukinki kije kiyi hatsari ki jawo min Allah ya kiyaye driver ya kaiki ko ni,to school dinfa Zan saka ki sai kin haihu,yanzu har sai na Haihu wata tara nan gaba,da Kika samu ma Zan bari kije ni ba a son raina Zaki makaranta ba wlh Kawai sabo dai da Naga kowa ya daukaki boko shine Zan barki amma da a so nane Islamiyya ta isheki,Nace wlh ban yarda ba akan haka sai nayi yaji haka Kawai Watarana ka Zama shugaban kasa ban San me Allah zaiyi ba shike Nan ka Kara auren me ilimi ta Zama first lady ni an barni a baya ba ilimi,karatuna zanyi kayi min office a wajenka ko Ina ka sani nice next of kin dinka sabo da rayuwar yara,Jawad yayi dariya yace ashe har yau son kudin masifa Yana nan yanzu har fatar min mutuwa kike kici gadona,baki na rufe Masa da sauri nace dan Allah ka daina zancen mutuwa ni wlh Kawai fada nayi badan kudi ba ko wani gado ba, tsakani da Allah nake sonka,Jawad kishiya nake ji kishiya nasan halin maza tam ke Kika San wata kishiya dan Allah ni dai Gwamma tace ya furta,yanzu da ni nace maka Gwamma tace ayi da yanzu kace Ina tsokanarka,Kwantar dani yayi tare da hayewa samana hannayena na sa ta cikinsa na rungume shi ta baya sannan na sake makale shi a jikina na Shiga kissing dinsa sosai Kamar Zan cinye shi na ma fishi zakewa sabo da dama a gwiwa nake ya gama jagula min jiki tun Muna hira, sarrafa juna muke sosai cike da Jin dadi,Yar kunyar nan tuni na watsar da ita yanzu sosai nake tsayawa na zage mu farantawa juna rai duk abinda nasan Yana so babu abinda bana Masa,shima haka yake min bama gajiya da juna,Kalamai da dirty words na sex ba Wanda bana iya fada bare shi dama ba kunya ce da shi ba,sai bayan mun samu nutsuwa yake tambayata Rannan a gidan Ummiya me yasa naga kina Fushi Sanda na dawo? nace Ummiya ce Wai zata koma gidan Baba za a Kara daura musu aure na fada da tausayi,yace ai abin murna ne ke a wajenki,Ummiya ta Sha wahala a baya bana so a sake samun matsala bari dai yau na baka labarin Ummiya da Baba.


Labarin Ummiya














Ina Matukar godiya fans da tayamu da Addua da kuka Yi Alhmdllh.












AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


116-120



NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP








Official


By
AsmaBaffa






SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA








Page naki ne
NAJIDA ALIYU


















Ummiya Kamar yanda ka sani Yar asalin kauyen 'yar Kaya ce gidan Maguzawa Babanta Anaruwa dane ga Dare Wanda Dare Kuma Dan Gwamma ne dake Gwamma ta Tara Yara sai data haifi maza goma cif duk Kuma suna raye da aurensu da yaransu,Ana ruwa auren zumunci aka Masa da Babar Ummiya wato Kyawo,Kyawo sabo da kyawunta aka sa Mata kyawo,yarsu daya tal a duniya Ummiya, Bayan sun haifi Ummiya aka sa Mata suna Hakuri sabo da yanda take da hakuri sosai sai dai akwai kazar kazar itama ba kanwan lasa bace, ta taso cikin gida irin na Maguzawa kowa Yana yabawa da kyan Ummiya,Babanta Anaruwa yace yarsa sai tayi boko sabo da haka Gwamma tace ba a Isa ba ta dinga bala'i da kyar dai ya samu yafi karfin Gwamma ya saka Ummiya a makarantar boko,tana zuwa tana zuwa har ta Fara bin kawaye musulmai na garin tana zuwa Islamiyya a boye,har tayi nisa a karatun boko dana Islam ba a sani ba,har ta Gama primary ta shiga secondary,lokacin Ummiya ta Musulunta a boye take Sallah babu Wanda ya sani,ana haka har ta shiga ss2 lokacin ta Fara fito da akidarta ta musulunci,Gwamma ta daketa yafi a irga sabo da haka a hankali Ummiya ta Fara yiwa iyayenta wa'azi tun suna dukanta har Suka Fara Fahimtar musulunci addine ne me kyau addinin gaskiya ne,sai su tsaya tayi ta musu wa'azi da Nasiha,ta dinga karanta musu tarihin manzon Allah ( s.a.w) tana yi abu Kamar Wasa sai abin ya shiga ran iyayenta Suka ce ta kaisu wajen wani Malam din suna so su Musulunta a boye,haka da murna Ummiya ta raka iyayenta Islamiyyarsu Suka karbi musulunci,Anaruwa Babanta ya koma Usman,Kyawo ta koma Bilkisu,tun zance bai fasu ba har ya watsu kowa ya sani ,Gwamma tunda taji labari sai data Yi yaji ta bar gida ta koma jigawa state gidan Yan uwanta da kyar yayanta Suka lallasheta ta dawo a haka ma cewa tayi baza ta dawo ba sai an Mata dinki kala biyu Suka dinka Mata,tace sai an siya Mata Yogourt sannan ta dawo gida,Ummiya da iyayenta sun Sha wahalar Zama su kadai musulmai a gidan Maguzawa haka suke dukan Ummiya sun tsaneta sai hantara da kyara bata Isa ta shiga cikin dangi ba shi yasa Ummiya bata shaku da kowa ba sai iyayenta.


Tun Ummiya tana shekara 8 Bilal wato Baba yake kaunarta dake shima dan asalin kauyen ne a Nan suke da Iyayensa shima, Dan dangi ne gidansu gidan yawa ne irin masu arzikin Kauye Amma su fulani ne Usul da shanunsu,Bilal Kyakyawan Dan Fulani ne a hankali tun suna Yara suka taso tare da Ummiya, makarantarsu Daya sai dai Baba Yana aji 3 Ummiya tana aji 1, har takai ta kawo Kullum tana gidan su Bilal shima idan yaga bata je ba sai ya tambaya ko ya biyo bayanta ko Ina an San Bilal da Hakuri duk da ta Musulunta amma sunan ya bita, Dangin Bilal haka suka Fara Jin haushi lokacin da Suka girma Wai Yana son Yar Maguzawa wannan abin yasa Suka tsani Ummiya amma ita da Bilal Baba kenan suna son juna,ko yaushe ta Zama kullum tana gidan su Bilal yaran gidan sun Saba da ita sosai tana daukan su,dake zaman Kauye ne duk da sun tsaneta basu fasa mu'amula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login