Showing 27001 words to 30000 words out of 119289 words

Chapter 10 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9409

ya dandana sannan ya mike yabi ta inda ya shigo ya tafi ni dai numfashi na sauke sannan na koma na cinye duk abubuwana Dana dafa nama Kawai na rage na kaishi kitchen na zuba a bowl na saka a fridge na Sha ruwa sosai na koma bedroom dina nayi wanka tare da brush nayi Alwala na fito,Sallar Isha nayi tare da shaf'i da wutr nayi Addua sosai sannan nayi Shirin bacci na kashe light na zauna tsakiyar bed dina Ina Adduar bacci sannan na kwanta sai bacci barawo ban San ya sace ni ba.
Tunda yan biki suka koma suke ta labarin gidana da irin unguwar da nake.


Asuba na yi Jawad ya tashi toilet ya shiga tare da Fara brush sannan ya daura Alwala ya wuce masallaci abinsa ko ta kaina bai bi ba,Allah yasa Nima gwanar tashi ce da asuba tashi nayi tare da goge baki na Nima nayi Alwala na fito bana Jin Kiran Sallah sabo da yanayin unguwar ta daban ce gasu arna sunfi yawa da agogo nayi amfani nayi Sallah tare da azkhar na zauna naci gaba da karatun Qurani har dan haske ya kyallo a saman sallayar na kwanta naci gaba da bacci na sai har 11am ban tashi ba,Jawad ne ya shigo yaga Ina ta bacci yace har 11am mutum na bacci haka ake auren a haka za ayi tarbiyar Yara,tashi na ya fara ke...ke...ke...Shuru sallayar da nake Kai ya shiga jaaaa na farka da kyar cike da shagwaba nace ni ka kyaleni yaushe safiya tayi,Marina yayi na bude idona ba shiri na dawo hayyacina,wuyana na Sosa Ina hamma nace ashe rana ta fito Mika nayi nace kayi min girki? Yunwa nake ji Daddynmu


Baki bude yake kallona yace wait who is your Daddy? Kai Mana na nuna shi da shagwaba,ubanwaye Daddy din naki ashe Zaki mutu,Hannu na miko Masa nace Daddy taimaka min na cafko rigarsa sai yaga Kamar mahaukaciya aka kawo Masa jiya daban yau ya ganni daban,ai sai ya fisge rigarsa ya fice da sauri na tashi Ina kiransa Daddy yunwa Ina kukan shagwaba Jawad sai ya kwashe da gudu yayi part dinsa tare da haura samansa tabbas wannan yasan Aljanu gare ta


Ni Kuwa Dariya ya bani na hau gyara gidan duk da cewar komai neat yake haka na tsaya na Kara gyara part Dina sosai ko Ina ya dau kamshi na daban sannan nayi wanke wanke na gyara kitchen tsaf na fara shirya Karin safe Ina ci gaba da aikina duk inda na gani a gidan shiga nake na sake gyarawa Ina bi ta wani corridor Naga part biyu daya bangaren dama daya hagu,bangaren hagun na Fara shiga shima kasa da sama karshe ya hadu bedroom gasu Nan ga Palo har biyu Kamar dai Nawa sai dai wannan komai brown ne Ina aikin Ina komawa kitchen Ina
Gyara ko ina karshe na dan fita compound wow a nan haduwar take bangaren masu aiki ne Mata da maza daban,sai garden har da pool,ga flowers ko Ina da bishiyu,parking space Kuwa motoci ne dama da hagu iri iri masu tsada


Da sauri na koma part din bangaren dama bayan na kashe gas gudun matsala wannan part din yafi ko wanne haduwa Aljanar duniya tun daga ganin tsarin komai nayi tunanin part din Jawad ne nasan ma ya fita direct samansa na wuce na buda bedroom din farko na hango system dinsa da takardu a gefe,Kallon dakin nayi sosai ya tafi da Imanina da sauri na Shiga gyarawa komai gashi Nan neat tunda shima jiya ya tare a sabon gidan,bayan na kunna abubuwan kamshi na fesa wasu ac na kunna sannan na shiga toilet dinsa gaba daya sai Naga kamar da cikin daji aka kawo ni birni komai ban taba ganin irinsa ba haka na kalkale ko Ina shima na sa Masa nasa Kalar kamshin daban ko Ina ya dau kamshi haka na gyara ko Ina a sama na dawo kasa na gyara komai harda canjawa kujeru style sannan nabi wata kofa ta cikin kitchen dinsa sai na ganni a katon gym room da kayan motsa jiki kala kala fita nayi da sauri nabi kofar wani side sai na hango wurin wani hutawa na musamman ko Ina bishiyu da flowers ga grass carpet yasha wasu kujeru Yan ubansu da table a tsakiya da wata Yar rumfa a samansu a nan na hango Jawad sanye cikin kayan Gym farare yayi Matukar kyau Yana waya,Allah yasa bai ganni ba na koma ciki na wanke abunda nayi mopping da shi na ajiye yanda zasu bushe sannan na koma kitchen naci gaba da soye soye na

Naman nayi warming sannan nayi potato ball na soya doya da kwai na shirya Masa nasa a tire,a gurguje nayi wanka na shirya cikin doguwar rigar atamfa dinkin me collar me dogon hannu ban shafa komai ba sai powder da lipgloss red ban daura dankwali ba Dan siririn mayafi na Dan yafa a kaina nayi acuci da gashi na Ina kamshi sosai na dauki abincinsa na shiga part dinsa a main Palo na ganshi ya hade yanzu cikin kana nan Kaya brown jean da Riga fara me rubutun brown a jiki yayi kyau sosai Kamar a sace shi dangayu kenan
Sallama nayi ya amsa da kyar ya wani dauke Kai Yana amsa waya cike da Izza ni Kuwa sai sannan na Shiga.










Masu Sharhi Kuna birgeni




Zakiyya Bello
Maryam T Baliya
Maimuna Umar
Mummy Muhammad


Ku Kun fi karfin kyautar page wallah.


thanks aci gaba.




















AsmaBaffa
08033933642🌏JIKAR MAGUZAWA🌏




26-30




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA
ZAINAB GARBA BUTALAWA




MASU TRANSFER TA ACCNT


0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK


MASU TURA KATIN MTN
08033933642


'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39




MASU YOUTUBE CHANNEL MAFI YAWA BAKWA NEMAN IZINI AKE MAIDA MIN NOVEL AUDIO,DAN ALLAH KU DINGA NEMAN IZINI,HAKA MASU POSTING A FACEBOOK A DINGA NEMAN IZINI.










MG'S SKINCARE


In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,


Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?


To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,


Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,


Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,


Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg's bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu.










PAGE NAKU NE


Maryam Umar faruq
Maman Muazzam
Khadija Ismail
Nanacool
Hauwancy
Khadija Saleh
Lawiza warra
Hauwerh ZD
A.H.H.N
Asmau B Yusuf
Hauwa j
Mom Husnat
Eekhyn mm
Oum Amatullah
Khadija A Hamza
Fulani gal ce
Hapsat
Maman Humaira & Ikhram










Kafin nayi magana yace idan abinci ne kije da abinki ki daina girki dani idan Ina so zan sanar, rainon kannena na kawo ki kiyi ba raino na ba, rainon naka ma ai sai nayi nawa kake Madara da nama ne Kawai suka ratsaka kake ta girma shi yasa gashi nan har saje ne da Kai kana yaron ka,shegiya Madara tana aiki dama ance mutum ko lokacin gemunsa baiyi ba Indai ta ratsa shi sai kaga ya fito amma da a Kauye kake da yanzu ko ni sai na fika tsayi yanda nake doguwar nan sai ka Zama Dan Wada a kaina,Yar lisuwa ta kamaka na furta Ina tsaye da tire na,Yana jina kamar yayi Dariya yace kici gaba da takura min watarana sai na ballaki ya furta ba Wasa,Knocking Muka ji anyi nace shigo sai ga Asif ya shigo ya kallemu,Murmushi yayi na gaisar da shi ya amsa da sakin Fuska yace Amarya bakya laifi Murmushi nayi kawai,Ina ganin Asif nace Asif ga abinci dama shi na kawowa yace sai anjima nayi masa wani banda wannan,Asif yace wa zai ki girkin Amarya kawo min yanzu nayi maganinsa dama ban karya ba mijin naki yace na zo, ai Kuwa na ajiye a gaban Asif shi kuwa Jawad ko kallonmu baiyi ba Kuma bai ce komai, ficewa nayi na barsu


Ina fita Asif ya fara cin abincin nawa yace Oga dakatar da shi Jawad yayi yace karka dameni kaci abinka haba,kayi ka gama kaje airport ka dakko Farooq zai dawo daga Us yace na sa a dauke shi a kaishi gida surprise zai ma Mamansa,by which time? 1pm,yau baza kaje Office ba? Ae akwai aikin da zanyi a system Zan turawa su Hydar wasu documents, Alright yanzu nasa a dauko Yan aikin gidan nan da su Hafeez...ko baki Asif bai rufe ba yaji motoci sun shigo gidan yace gasu Nan ma,Iso driver ya yiwa yaran zuwa bangaren Jawad dama an kawo kayansu part dina a wani room,Ina Jin ihun Yara da hayaniya, Jikin Jawad su Meenat suke ta fadawa,Yan yaran da ko yaye basu Isa ba suna hannun Nawwara da Asmau,Asif Yana gama cin abincin yace a Kai Mata kwanikan,wata uwar harara Jawad ya watsa masa yace baka da hankali wannan yarinyar ajiye nan tazo ta dauke abinta kudi za a biyata da babu kudi zata Yi auren ne,da sauri Asif ya katse zancen sabo da Kar su Hafeez su gane masu Aiki maza da Mata suna kasa a zaune ciki harda Bintu yace Asif kirata a waya tazo


Asif ne yayi dialing number ta Allah yasa tana hannuna dagawa nayi yace kizo part din mijinki,Harara Jawad ya gallawa Asif, ban dauki lokaci ba na shigo part din Ina sani na zauna a kujerar da Jawad yake kusa da shi ji yake kamar ya kwada min mari na fuske abina tare da harde kafa,Asif sai dariya yake a ransa Yana Jin na birgeshi,Su Hafeez Suka ganni sai Murmushi muke ma juna da su Asmau,na kalli su Meenat da yaran dake hannun Asmau da Nawwara jikina ne yayi sanyi sun bani tausayi sai dai ni Kuma aiki na hangowa kaina nan take nayi surrender naji gaba Daya nayi kuskuren yin auren raino har da boyewa Ummiyata gaskiya,kamar na fashe da kuka haka naji,Jawad Kuwa bai ma kula dani ba yace gasu Nan dukkansu sune kanne na Jini na,ku Hafeez wannan Auntynku ce Banda raini duk abinda tace Indai bai sabawa addini ba kuyi,sannan kema gasu nan amana kece babba kin San komai dai na fada miki,ga masu aiki Mata su uku bana son tarkacen masu aiki da yawa a gidana,sune zasu tayaki rainon Yara da aikin gida duk abinda kike so a tayaki aiki gasu Nan,banda wulakanta Yan aiki Kamar yanda kuke mutum Suma haka suke ba wai Allah ya fi sonku bane ya barku a Haka su suka Zama Yan aiki ba,kaddara ce kowa da irin tasa sabo da haka duk taimakon juna za ayi bana son naji an wulakanta Yan aiki,matan da mazan duk dattijai ne sun haife mu gaba daya kadan su Bintu ne matasa sabo da haka Kar naji labarin an wulakanta kowa,ku Kuma masu aiki ayi Hakuri da Yara,banda tsegumi kowa ya tsaya a matsayinsa,Maza ku uku ne daya zai kula da tsaftar compound,Flowers, pool,da duk komai na tsakar gida ya Zama an same shi Neat,jikin bango su windows etc kai Rabiu Kaine matashi Kaine da wannan aikin Kamar a wancan gidan ka Gane ai? Rabiu yace Inshallah Alhaji ai aikina nane, sai wankin Su Hafeez su Uku sune manya su zaka yiwa a goge musu,sai Baba Hashimu Kai dama kana gate duk da securities zasu na zuwa duk dare da safe zasu tafi,Amma kana gate,Kai Kuma Haruna kaima ba dattijo bane kaine me Kai Yara school ka dakko su,sai sauran aike na gida idan ana bukatar abu zaka siyo da kula da motocin gidan ana kaisu car wash ka dai San aikinka kaima, Inshaallah Alhaji


Jawad yace ke Kuma ki karbi numbers dinsu Duk abinda kike so sai ki Kirasu a waya,ai Kuwa har matan sai da na karbi number sabo da yanzu kowa da Yar wayarsa karama bare su da Jawad ne ke siya musu,ai an nuna muku bangarenku na Mata suna daga ciki naku na maza Yana daga waje sai kuje kowa ya dauki daki daya a zauna lafiya sannan ko me kuke bukata ku sanarwa Aunty gata ya nuna ni,fada min Aunty da yake naji kaina ya Kara fadi na sake harde kafa Ina karkada kafa daya, abinci Kuma Mata masu Aiki a bangarensu da kitchen da komai idan sunyi girki zasu dafa da ku safe Rana dare idan wani Yana son cin wani abu ka fadawa matan masu aiki sai suyi muku idan basu da aiki,duk nasan kun Saba da juna a wancan gidan ma ai haka kukeyi Kuma Kuna zamanku lafiya to a ci gaba a Nan ma,Suka amsa da to,zasu tafi Haruna ya tsaya yace Oga sai ayiwa Zakiyatu magana tana Mana kauron nama sai ta dinga bamu bai fi a tura a hanshi ba, Murmushi Jawad yayi yace to ke Zakiyatu kike ko ki gyara a dinga basu manya,Zakiyatu tace Inshaallah Alhaji suka fice.


Jawad yace su Kuma su Asmau matan suna part dinki,Hafeez ga part dinsu nan kusa da nawa a sasu a hanya tarbiyya ki kula kisa Ido a kansu kiyi aikinki,duk Wanda ya Miki rashin kunya ki zane yaro har su Hafeez Dariya yaran suka Fara yi,sabo da Hafeez mate dina ne ma,wannan Yan yaran sune Suka fi damuna Asmau zasu nuna Miki abinda ake Basu suna Sha ki basu kulawa,Hafeez yace kuzo muje muga gidan nan Suka tafi gaba daya Wai kallon gida,Asif ya fita shima yace naje gida na shirya sai na wuce airport okay ya furta,Ni Kuwa Ina zaune kusa da shi kamshinsa yasa na kasa tashi,yace ke tashi an gama,Ko me ya tuna oho yace biyoni ki karba kudi idan Yara zasu school ki basu kudin break ko in Kuna so zaku siyi wani Abu kuyi amfani da shi,idan Exam dinku ta fito let me know sabo da na saki a school har islamiyya Kuna zuwa da Yara,idan kika bari Suka rainaki ke kika sani ni ba ruwana na cika alkawari,Saura naji anyi ta kakanninki anan gidan duk ashar daya minus dubu dari a kudinki tashi nayi na bi bayansa har cikin bedroom dinsa ya bude wata Yar jaka me dan girma ya bani kudade masu yawa na karba tare da godiya na wuce part dina direct


Ina shiga na Iske yaran a Palo manyan da Yara maza da Mata sun nutsu suna kallon cartoon chanel,Ina shigowa na zauna kusa da Asmau tare da karbar Yarinyar da take hannunta nace ya sunanta? tace Humaira wancen Kuma Abeed duk basu Isa yaye ba aka yaye su,Allah sarki me ake basu? duk gasu can a kitchen na nunawa Nanny ma komai cewar Asmau ,Okay yayi kyau Hafeez kallo na yake sosai Ina juyowa Muka hada Ido nace lafiya dai Hafeez? Murmushi ya saki yace kina da kyau Aunty Yaya ya iya zabe ko a Ina ya samo ki oho,a Ina kuka hadu ne haka? a shopping mall nace Kawai Ina gyarawa Humaira wandonta gashinsu duk wanke shi Kawai ake gasu da gashi ba a musu dan style na kitso, Hafeez na Kira sunansa ya amsa nace Kuna zuwa shopping? Yace ae Mana Indai Yaya ya bamu kudi mana,kasa driver ya kaiku ku siyo Mana snacks da chocolate da biscuits sai kayan kitso da Zan nuna maka ka siyo min,Okay yace,nace Kai da Nawwara da Asmau sai Waleed da Ahmad kuje,a wayata na nuna musu irin abinda zasu siyo nace amma sai Yamma,Meenat tace Aunty yunwa muke ji bamu ci komai ba fa,kwantar da hankalinki Meenat,Ayanah tace Nima haka,Ahmad na kalla nace kayi Shuru baka magana? da sauri yace yunwa ce,Waleed to me za a dafa? Da sauri Suka ce rice and stew mun dade bamu ci ba kullum da Mai da yaji ake bamu,Hafeez yace a hada da hadin salat sun bani tausayi da dariya


Ahmad yace Ni dai da tea me kauri,Asmau tace muma haka nace Indai tea ne kuzo a Fara hada muku kafin a gama girkin ranan,wanda basa iya tafiya su biyu ne kacal Abeed da Humaira Nanny na bawa su nace ta basu abincinsu su kula da su,Su Kuwa ledar cin abinci na shimfida musu na kawo cups da kayan hada tea ga ruwan zafi a flask nasan zai ishe su,
Manyan da kansu suka hada yaran na hadawa su Meenat na kawo musu snacks da ragowar nama da yamballs,Ayanah bata iya Sha da kanta ba ita da Ameera da Meenat,a baki na zauna Ina basu idan na bawa wannan sai na bawa wannan Kamar Ina gidan raino haka nake yi, Ina ta tsokanarsu nace zanga wace bakinta yafi kato ko wacce ta bude nata har su Hafeez Muka Fara dariya,sai ga Jawad ya shigo tsintar mu a haka ba karamin farin ciki yaji ba a ransa a fili Kuwa bai nuna ba mu bamu San ma ya shigo ba muna dai ta Jin kamshinsa a Palo ya gauraye ko Ina Allah bai sa ko mutum daya ya juya ba,hannayensa ya harde tare da jingina a jikin bango Yana kallo


Suna gamawa kowa nace ya kuskure bakinsa da ruwa ya hadiye har Yan yaran na basu na koya musu,nace Asmau kwashe komai ke da Nawwara ku Kai kitchen ku jira nazo na koya muku wanke wanke,wives na dakko na gogewa yaran Fuska ,nace Meenat kece bakya ji Naga alama karki sake na ganki a jikin tv ko kin dauki remote tace to,Su Hafeez na kalla sunki tashi suna ta latsa wayoyinsu nace Kai ku tashi dalla,saman kujera Suka zauna Banda Waleed yaki ko kulani Yana game Wayar na fisge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login