Showing 33001 words to 36000 words out of 119289 words
Chapter 12 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt
Ina budurwa shanawa nake a gari duk sati sai muje kasuwa da kawayena sau Uku muna abubuwa yanzu Kuwa sai dai nayi girki da aikin yara idona ya kawo kwalla nace wallahi Babanku ni ya haifawa nima ashe Ina can Kano Kuna Lagos ana ta tara min Yara na zaci abinci zanci na koshi na huta tunda ga kudi ga kayan dadi ashe ba haka bane Ina ganin Dan kula da Yara nawa abin yake
Su Hafeez suna ta dariya suka ce Yi hakuri yanzu Aunty tun daga kwana daya tal har kin karaya yaushe aka fara ma me akayi da maza, banga laifinki ba kina yarinya Kuma Amarya har an kawo Miki bataliyar Yara kiyi Hakuri,a raina nace wayyo Hafeez baku sani ba ni na jawa kaina yanzu idan Ummiya taji sai taci ubana karyar da na musu,a fili nayi murmushin yake nace ba damuwa ai haka Allah ya tsara gwara na rike ku ai a raina nace Allah ya Isa Asif tun a iya yini daya na Fara raina kaina ga wata uwar gajiya tun safe ban huta ban huta ba ga hayaniyar Yara ai muna Hira sama sama na koma kasan tiles na kwanta ban San nayi bacci ba ma,su Hafeez harda wani tafiya part din Jawad, Hafeez ya ganshi Yana ta aikinsa da takardu yace Yaya Aunty ta gaji tayi bacci a kasa Muna hira Muka ga tayi bacci kaje ka dakko ta,Jawad yace to goodnight kuje,ko ta kaina bai bi ba har ya gama aikinsa ya taho da su Ayanah Yana zuwa yace ke tashi ki Kai su suyi fitsari ki kwantar da su,Idona na bude na fashe da kuka na Fara burburwa da Shure shure nace ni Allah na gaji dan Allah ka yanke Naira Ashirin a cikin Albashina ka barni nayi bacci,Wai ashirin kacal yace Minus dubu dari to Ina Jin dubu dari zai yanke na mike zumbur na rungume Ayanah Ina Yan Yara anzo bacci inyee inyee to ku taho muje muyi kwanciyar mu,har Muka tafi Jawad yana tsaye a wajen Kamar an dasa shi tunda yake bai taba ganin me son banza Irina ba,Kai ya jinjina ya wuce part dinsa, Yogourt yasha tare da yin Shirin bacci ya kwanta tare da yin adduar bacci ya kwanta.
Tsakar dare Yana bacci ya juya yayi ruf da ciki Nan ya fara mafarkin sex dinsa daya Saba,Yana ta yiwa katifa Yana Nishi da gurnaninsa,lokacin Kuma naji Farida tana ta zazzabi dake su Uku suna bed dina tana ta nishi na fito sabo da na fada Masa ko da magani ya bani a bata.
Ina zuwa bakin kofar bedroom dinsa na dinga Jin gurnani da Nishi sai kace rago,handle na Murda na Shiga gaba daya a saman bed na hango shi ya jefar da blanket a kasa,baki na rufe da hannuna na tsaya a kansa Ina mamaki a hankali nace ohhh wannan kaji kuka irin na rago inama wannan rago ne Allah da a yau sai na jashi na tafi kasuwar Yan awaki da shi na siyar da na samu kudi dan a kalla na siyar da shi dubu tamanin da na samu banza kudi a banza,in sanwa Ummiya dubu biyar a ciki,Kadada Naira Hamsim ladan ganin ido,Daddy dubu daya,Farisa da Hamziyya Naira dari dari, Baba Kuwa ko ficika
Ina lissafina naji yayi wani lakwas yayi shuru,da sauri na dan matsa baya kadan nayi sallama da karfi,nasan lokacin ya farka amma ba lallai Yana hayyacinsa ba nace na shigo ya juyo da sauri ya kalleni fa mun hada Ido amma dake baya ganewa yace tsaya Ina zuwa karki shigo,Ina kallo ya jawo blanket ya rufe jikinsa sannan yace murda handle kofar a bude take,na dinga dariya a raina Ina tsaye a room din kusa da shi yace wani na Murda handle
Masu Sharhi Ina godiya matuka aci gaba da gashi please
AsmaBaffa
08033933642.πJIKAR MAGUZAWA π
31-35
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
ZAINAB GARBA BUTALAWA
KUDIN JIKAR MAGUZAWA 300 NE
MASU BANK TRANSFER 0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK
MASU TURA KATIN MTN
08033933642
'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39
MASU YOUTUBE CHANNEL WASU BASA NEMAN IZINI SUKE MAIDA NOVEL AUDIO KU DINGA NEMAN IZNI DAN ALLAH.
_Ina mata y'an kwalisa ma'abuta gyaran jiki macce Mai gyara daban take ga zuciya mijinta muna da kayan mata da supplement na gyaran jiki kala muna hadin amare da uwargida Dana masu jego muna da set Mai hade da kaza Mai kwai 3 da cicicibe da kifi da galam 3 na tsime da Burkett din gumba 2 da garuruka da zuma wanna set na maccen da ta isa ne muna hadin shi 20k akwai karami set na 15k akwai na 10k akwai na 5k_
_Muna da zuma Bata gindin kishiya ga wadda kishiya ke muzguna mata wanna Zuma In kinyi anfani da ita miji salab zaiji Daya shiyasa indai ba macce cikin matsala take ba bamu Bata ita_
_Muna da magunguna masu jawo hankali maigida da kara martaba dasa alhere ga maruwacin namiji_
_Akwai Zuma kiba da hip sati Daya Kinga result_
_Muna hadin kiba duk ramar ki duk bushewa ki kinka sha shi sai ke ciciko_
_Fanin supplement ma ba'a bar mmn mujaheed abaya ba tana da nagyaran fata da kara haske akwai na gyaran brst na gyaran hip na kiba
Kamar su Lady capsule 4500
Sugar wanita 3500
Glutathione 3500
Vitamin e 3k
Gluta white 3500
Royal jelly 3500
Apetamin 3k_
_Frozen collagen 3500
Da sauran su insha Allah duk Wani supplement Zaki same su ga mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa
Ina wadda sanyi ke Hana ta jindadin gidan miji_
_Y'ar uwa kiyi bayani abaki dai2 da type dinki indai sanyi ki Hana Miki jindadin aure ku budewa GABA ku rashin niima to kedai yima mmn mujaheed bayani zata baki dai2 Dake mun tanade set din maganin sanyi 4500 Wanda zai fatataki sanyi Kuna kashe ne_
_Mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa muna zaune garin kebbi state
08066726866_
_Kayan mu iya kudinka iya shagalin kane_
PAGE NAKU NE
Alhusna
Amina Adamu Usman
Bilkisu Tambari
Maman Murtalah
Umma Khursum
Oum Nuaima
Rukey Muaz
Aisha Sunusi
Mummy Hibbat
Smb collections
Hussaina Abdullahi
Maimuna Umar
Zakiyya Bello
Maryam T Baliya
M.j collections
Maman Nusy
Ruma
ππ
Fuskewa nayi kawai nayi sallama harda bata rai sannan ya amsa nace Farida ce bata da lafiya tana zazzabi in kana da magani ka bani a bata,no asibiti ce dani ba magani ba,akan wannan sai kin tashe ni a bacci Ina bacci na me Dadi kin yanke min shi,a Raina Dariya nayi nace dama Ina so in tambayeka Ashe kana da cutar...? Yanzu naji kana ta gurnani da Zan shigo har naji sai na tuna masu fyarfyadiya nayi,Ido ya tsura min yaga alamar da gaske na ji,yace ae itace Watarana harshena har fashewa yake,Sannu Allah ya bada lafiya bani magani,kin tashi yayi ya nuna min wani first aid box yace zaki ga paracetamol na Yara ki dauka ya juya tare da gyara kwanciyarsa,idan zazzabin bai sauka ba ki sanar dani,to nace nayi waje abina,Ina komawa na tasheta da kyar ta tashi na bata maganin tana ta rawar sanyi,tace ruwa na dakko na Bata ta Sha da yawa,zumbur ta Mike tace amai na kaita toilet da sauri tayi aman ruwan da maganin,bakinta na wanke Mata na gyara toilet din muka fito na Bata maganin again nace to kwanta ta kwanta sannan na lullubeta, su Abeed kuwa suna wajen Bintu Asmau dakinsu da wasu yaran Suma
Haka Muka Yi baccinmu sai da asuba banyi niyyar tashinsu ba amma duk Wanda suka Fara tasawa sai da na tashe su Muka Yi sallah har su Asmau, Ina koya musu azkhar sannan wasu suka koma bacci tunda ba school sunday wasu Kuma Suka fara kukan yunwa,Kawai kitchen na wuce direct na Kira Yan aiki Suka tayani cikin lokaci kalilan na gama shirya breakfast su Bintu na sa suka yiwa dukkan yaran wanka tare da shirya su cikin kana Nan Kaya dama duk kana man Kaya ne da su ban taba ganin wani Atamfa a cikin kayansu ba har manyan su Hafeez ne kawai masu shaddoji da yadika Suma ba wani sakawa suke ba.
Abincin ma masu aiki ne Suka hada musu tea da komai manyan ma Suka zo Suka Yi serving kansu,kafin nayi wanka na shirya masu aiki sun gyara gidan ko Ina sai sheki da kamshi ke tashi,bedroom Dina na gyara kawai na shirya cikin kayan lefena wani lace me tsada na saka fari dinkin Riga da zani buba irin Wanda ake daura zanin akan rigar,Haka na daura naci dauri na nayi kyau sai kace zanje biki Ina Fitowa yaran suka Yi ta gaisheni suna cewa kinyi kyau Aunty,Waleed a hankali yace Yaya Ya auro babbar halitta,wucewa nayi kitchen banyi Niyyar Kai Masa breakfast ba amma dai na hada komai nasa a tire na wuce bangarensa,Ina tafiya Hafeez yace sai naga bana ganin Aunty tana zuwa part din Yaya kamar ba acan take kwana ba,Ahmad Yana kasa da murya yace ka taba gani ai basa zuwa a kan idon Yara sulalewa suke Yi a boye Kar a gani tana zuwa, Hafeez yace yau bazan Yi bacci ba sai na gani da idona tana wucewa taje ko shi yake zuwa
Shi kuwa gogan Ina shiga Naga yasha wanka cikin kana nan kaya ya fito Palo zai fita,yayi kyau sosai da sosai Ina kwana nace, Alhmdllh ya furta kawai yana tafiya ya furta na koshi yayi waje da sauri Yana cewa nayi tafiya ki kula da kowa sai Nan da 2weeks,da sauri na tambaya Ina lekawa compound sabo da sauri yake wacce kasar? Na tambaya, tsayawa yayi har na karasa gabansa da tire na yace min Sweeden ya fada Yana Shiga motarsa kafin ya rufe nace ko tea baza ka Sha ba? na furta da kunkuni,kallona yayi kadan Kamar bazai Yi magana ba yace Ina tea din to? a wata Yar ceramic kettle me kyau na tsiyaya Masa a cup Yana kamshi daukan cup din yayi yace sai me? nace ga chips ga pepper chicken Ina shagwaba,yace bafa birgeni kike Yi ba ganin dama nayi yaja tsaki ya dauki iya tea dinsa a cup zai rufe motar nace ka dawo min da cup dina Kar a batar min ku maza haka kuke duk abinda kuka dauka bakwa dawowa mace da shi spoon dina Kar a batar min, yace iko da kayana Zaki min ke Kika zuba min in zubar ma Mana Ina ruwanki yaja Tsaki tare da furta rufe min mota,hannayensa na kalla cup da waya ce a hannayensa da kafa na tura Masa kofar na rufe driver yaja suka bar gidan mamakina ko Kaya bai dauka ba masu aiki su Haruna na bawa suka cinye bani da aiki masu aiki sun gama komai,yaran na jawo na Fara musu kitso da kayan ado iri iri,kowacce da Kalar nata sun dade rabon da a musu kitso sai uban gashi duk ya lalace,Hafeez ne ya dawo ya kawo min. Sabuwar waya me kyau tekno spark 9 yace Aunty gashi
Nace wow Yayanku ne ya bada ku siyo min? Hafeez yace a'a kudi ya bamu jiya yace yau zaiyi tafiya mu kashe shine Muka Yi Karo Karo Muka siya Miki waya yanzu anci gaba kina ta amfani da karamar Vivo gashi ko dannuwa bata yi,farin ciki ya kamani nace kaii Allah ya muku Albarka nace Kash Hafeez kuyi hakuri an sarkafe ni da sasarin aure amma da sai nayi rawa,Ahmad yace Aunty point of correction igiyar aure dai,Nawa sasari ne a Ina ka taba ganin Amarya irina,layina na saka Suka dan saita min abubuwa na,Hafeez ya duba kaf bani da number Jawad yace Aunty ya Naga baki da number Yaya? Nace na haddace ta a kaina ai number masoyi haddarta akeyi,kiyi saving kin huta Hafeez ya saka number Yaya Jawad yace Aunty me za a saka Honey,Hubby,darling Baby? Nace sa Masa dankalin hausa shi ya dace da shi Yayanku ai sak dankalin hausa,Meenat tayi tafi tace wallahi ba shine ba yayanmu Sugar ne,Ashe Yara suna ji,Farida tace a sa Masa Handsome yaya,nace Kai Hafeez dankali dan hausa karka sake ka canja min suna,Hafeez dai ya saka Sweet potato ya sa min number dinsu Ina ta yiwa Asmau kitso itace ta karshe daga ita an gama su Humaira Yar yarinya ita akwai gashi rarrafe take yi bata son a taba Mata gashi Kuma yau dole sai na Mata ko calaba ce na sa Mata abun ado beats Ina gamawa Asmau na dauko Humaira na matseta a cinyata yanda baza tayi motsi ba,Ina taba gashinta ta Fara ihu amma ko kulata banyi ba sai da na gama tas sannan na sake ta,beats dinne ban saka ba a hakan ma Sai da nasa su Meenat suna Mata Wasa da wayo har na saka Mata duk sai Suka Yi kyau ko wacce Kalar nata daban,wayata Suka dauka bayan na bude snap chat suna ta yin pics harda ni Suka Yi munyi kyau kuwa Hafeez gaba daya ya turawa Jawad ta Whatsapp yaga Yan kannensa chas sun dawo Yan gayu,yaji dadi.
Washe gari da Yamma Abba yazo a motarsa shi kadai,Me aiki ce tazo ta fada min Baban me gidan ya zo Abba Yayan mahaifinsa,Kice ya shigo na yafa mayafi fari Kalar lace dina yaran ma suna bedroom suna Wasa Ni kadai ce a Palo sai hayaniyarsu a daki zaka ji,Abba ne ya shigo da sallama na amsa tare da mikewa tsaye nace sannu da zuwa Abba,kallona yayi sai yau ya taba gani na,nace zauna ya zauna kuwa durkusawa nayi tare da gaida shi ya amsa har da sakin fuska,ruwa da lemuka na kawo masa,anci sa'a Abba da son gaisuwa ko Indai zaka durkusa har kasa ka gaida shi to an gama, lemon ya Sha yace Ina Jawad din ne wajensa nazo,nace laaa Abba yayi tafiya yau Yana Sweeden maybe ma yanzu Yana jirgi,Abba yace ikon Allah to idan kunyi waya kice nazo nemansa ya kirani,kema bari na fada Miki yaran nan Zan dawo na kwashe su ai bai dace kina yarinya a barki da Yara ba haka gani Ina raye da iyalaina mene amfanina,Murmushi nayi nace Abba ba komai wlh Zan rike ai Kuma ya kamata ku huta amma kuyi magana da Jawad abinda yace shike nan yace to shike nan bari na koma,turaruka na kawowa Abba nace gashi Abba kayi amfani da su, bazan taba iya bashi a nawa ba sai a Jawad sababbi naje na kwaso uku nace a raina ko Babana sai yaci sa'a Zan bashi bare wani Abba,Abbo mato da dai Ummiyace sai na bata amma Baba ya min laifi bare wani Abba,yayi godiya ya tafi na Masa Allah ya tsare.
nace in Jawad ya dawo na fada masa
Abba tun a mota yace wannan matar tasa ai Mai hankali ce ban San Haka take ba to ga Kuma Hajiya Barira ta matsa a kwaso Yara ya na iya dole na karbo Mata Yara,Yana komawa gida ya iske Hajiya Barira ta hakimce tana cika tana batsewa,yace Umman yara Yana murmushi,Hmm tace Kawai tace yau bana Jin Zan iya girki Kuma bazan iya cin na Yan aiki ba sabo da haka ka Shiga kitchen ko jullof din shinkafa ka Yi min yanda Watarana kake min ai ka Dade baka min ba dama,Abba yace girki Kuma Umman Yara? ae haka nake so ko baza kayi bane? Abba yace ai ba naki yi bane amma ga Yara da Yan aiki kamata a kitchen,abin kunya ne to idan aka bi ta wani fannin ai sunna ne,to sunna ance dole mace ta tursasa miji? Okay baza kayi bane? Abba hanyar kitchen ya nufa Kawai tace na manta kayi da su Hajiya Mariya da Hajiya Hajara zasu zo yanzu,Abba ya fada kitchen ya fara abinci Umma tace karka cika attaruhu,Su Hajiya Hajara ne Suka zo Abba Yana kitchen Yana fama,Suka ce ya Ina mijin tace Yana ciki Yana Mana girki,tafawa Suka Yi shegiya gaskiya kin kware,Umma ta furta Ni ta Wasa ce Suka sake tafawa,Babbar 'yar Umma Layla ce ta shigo bata Kai su Nawwara ba tunda taga kawayen Umma ta dinga galla musu harara ta wuce ta shiga kitchen taga Abba Yana ta yanka Albasa tace Abba girki da kanka,Umma ce tace sai kayi ko,Albasar da ya yanka ta kwashe ta watsa a dustbin,kafin ya juyo ta dauke ruwan da ya fara zafi ta zubar a sink ta kashe gas din ta rike hannun Abbanta tace muje wallahi yau sai dai ta kwana da yunwa yace ki bari na dafa Mata sabo da a zauna lfy,Fitowa tayi gaban su Umma tare da rike kugu layla ta nuna su da yatsa tace Abba bazai dafa muku abinci ba kartan banza,Umma tace ke kawayena Zaki zaga ashe baki da kunya,yarinya tace ai ba su kadai ba harda ke Umma bazai dafa ba munafukai
Umma dake yarta ce ko fada bata Mata ba tace kuyi hakuri tunda ta zageni ni dana haifeta waye baza ta zaga ba yaran zamani ne sai hakuri dole sai masu aiki ta sa Suka dafa musu abinci sabo da daya Yar tata ma Nusaiba sun kafa sun tsare Babansu bazai Shiga kitchen ba,Umma tace Hajara Ina Kuwa budurwar yarki wacce da ta taba cewa tana son Jawad? Hajara tace wai Safna ai har yanzu tana kaunarsa shi yasa maza da yawa sun fito zasu aure ta Yarinyar Nan taki ita sai Jawad shi kuma bai ma San tana yi ba gashi Yar banza shekarunta talatin da biyar taki aure,sai shegen tara samari na rasa yanda zanyi da yarinya tunda taje kasar waje ta lalace,to kwantar da hankalinki Zan Shige Mata gaba ta auri Jawad kice tazo Ina son ganinta zamu tsara mata yanda zata yi itace zata bibiyeshi kin San maza irin su Jawad sai ana Shige musu ake samu tunda yanzu yayi gida da matarsa ai har gidan zamu na zuwa sai ya so ta,Umma har ranta so take ta kuntatawa Najla Kar ta bari ta samu sukuni ko da Safna bata samu Jawad ya aure ta ba
Maman Safna tace zata Zo Inshaallah,itama dayar tace idan bai so Safna ba ga Bahijja yata