Showing 45001 words to 48000 words out of 119289 words
Chapter 16 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt
Bai zaci zai ga Jawad haka ba,ajiyar zuciya ya sauke,Jawad ya kalle shi yace matsoraci,Dariya sukayi Asif ya fita ya Kira wayata bugu Daya na daga da sauri,yace Muna asibiti Jawad yayi hatsari amma da Sauki gashi kalau,Nace wanne kalau gani nan kawai Ina da taurin zuciya banyi kuka ba nace Kadada ku Zo mu tafi,Kadada da Tahantsi ba mayafi ba dankwali sai sabon kitsonsu da aka musu na Karin gashi dama suna yin abinsu,hijab na saka har kasa zuciyata tana bugawa,Driver na saka ya kaimu na tafi da Meenat da Ayanah Nima Bamu fadawa Yan Gida ba driver ne ya sani Muna zuwa na shiga da sauri na manta da Sallama ma,Jawad Jin shigowarmu ya bude Ido ya kallemu,haushi na yaji Wai banyi kuka ba,a ransa yace ko kuka tayi shi yasa nace su Kadada sunfi ta mutunci,ya jiki na furta yace ban sani ba da masifa sabo da banyi kuka ba,
Shuru nayi su Kadada Suka ce ya jiki? Ya amsa harda Murmushi,Meenat da Ayanah ya mikawa Hannu,Meenat har ta Fara kuka tana cewa Yaya me ya dameka Dan Allah karka mutu ka barmu irin Daddynmu Umma ce zata Zo ta Duke mu,yace to daina kuka kin ganni lafiya da dare Zan tafi gida ma,Ayanah tace to Yaya kazo mu tafi,yace sai anjima kadan Drip ya Kare,duk sabo da yaran yasa lallai sai an sallameshi a asibitin mukayi Sallar Isha sannan aka sallame shi sai da su Asif Suka rike shi sabo da wahalar da ya Sha haka Muka tafi gida,bayansa waje biyu an saka bandage manya sai kirjinsa shima waje daya,hannayensa biyu Kuwa kashinsa an samu ya goce daya hannun yayi targade sai da aka gyara Masa hannayensa ma bazai iya abin karfi da su ba sai kadan
Likita yace tunda ka matsa sai ka tafi bamu Gama gwajin ba Kai kace kalau kake Kar abarshi ya dinga kwana shi daya sabo da ko ya aka ga matsala ta afku to a dawo da sauri sabo da hatsari Watarana ba a sanin da wata Matsalar sai an dan Yi kwana ki a kula da shi, su Farooq Suka ce ba matsala,sai bayan mun dawo gida sauran yaran da Yan aiki Suka dinga shigowa suna Masa sannu,kannensa suka dinga layi har Suka gama kowa yaje ya kwanta har Ayanah, Meenat tana cikinmu Asif yace Najla da Allah a kula da shi....kafin ya rufe baki Meenat tace Ni Zan dinga kwana da Yaya,Aunty ki kawo min bargo na,Dariya mukayi nace to Meenat ta haye saman bed din tare da kwanciya,Jawad Yana gefen bed a zaune ya jingina da fuskar bed din,Hafeez yace wanka sai dai ayi Masa da towel Kar a taba Masa bandage sabo da sai nan da kwana biyu ko uku za a dinga canja sabo,Allah Kara sauki Suka Masa zasu tafi,Asif ya tsaya kusa da ni a hankali ya furta plus 1million a kula da shi,haushi Asif ya bani wato bazan iya komai ba sai na kudi,duk Suka fita Hafeez Yana cewa matar mu a kula da shi,Jawad yace ka nemi taka wlh aure zan maka da wuri Hafeez Naga so kake ka kauce hanya,Dariya Hafeez yayi tare da ficewa Kawai.
Meenat na kalla wacce tayi bacci tuni daukanta nayi tare da Saba ta a kafada na maidata room dina inda Ayanah ke kwance naje na taso Kadada nace ki kwana a gefen su Meenat please karki danne Yara nasan Kalar kwanciyarki,sannan Kar su tasheki ki zagesu basu Saba da zagi ba karki koya musu,baccinta ta koma, na dauki kayan bacci na har wasu kayan da Zan saka da safe da Kuma sauran abubuwan bukatata sannan na koma sashen Jawad,Yana zaune inda na barshi yanzu Kam ciwon ya fara Masa zafi,gashi da kwailo sai washhhhh yace furtawa Yana cije lips.
Kayana na Adana a ma'ajiyar kayansa gefe daya sannan na karaso gabansa Yana ta cije lips,a kasa gabansa na duka tare da cewa Sannu,harara ya watsa min Yana ta Jin haushina sai da kudi da zanyi komai sannan yayi hatsari banyi kuka ba,da ya mutu ma shike nan babu asarata,Hannayensa na saka da Niyyar cire Masa rigar sa tunda ta asibiti ce ma a jikinsa wancan kayan an jefar dasu a asibitin sabo da sun yage Kuma jini ya Gama da su,hannunsa yasa da Niyyar bige min hannu ya fama gyaran da aka Masa ihu ya saki tare da mikewa tsaye Wai duk azaba ce,ya sake zama Yana nishi,magana nayi nace ka tsaya dan Allah nayi abinda zanyi lalura ce ta jawo,Haka ya kyleni na cire Masa rigar sai boxers dinsa,na ganshi wani Kato nace lallai mutumin Nan Yana da girma na furta a raina,Ruwan dumi na zubo a Bowl da farin towel karami da wani liquid soap kalarsa daban yake na marasa lafiya ne Wanda baza a sheka musu ruwa ba Kamar irin su Dettol yake a ruwan na zuba Yana fitar da kamshin lemon
Nace muje toilet zai fi tunda Zan wanke maka gashi, tashi yayi da kyar ko iya mikar da hannayensa baya yi,kujera na dakko na sa Masa ya zauna,kansa Yana jikin sink,Kamar ana wankewa mace kai a saloon shop haka na Fara wanke Masa gashin da wani shampoo dinsa na maza me kamshi,Ina dirje Masa gashi ya lumshe Ido har na wanke Masa gashinsa tas nasa towel na tsane masa sosai sannan na fara Masa wankan da towel din ina zuwa kusa da ciwonsa zai Yi zullo Yana wayyoooo.....har nazo cinyoyinsa su dake ba rauni ruwa da soap nayi amfani da shi na wanke Masa har zuwa kafafunsa,Ina Yi Yana kallo na nace to Saura private part ban San ya za muyi ba,yace ai ko hannuna zai balle Zan lallaba na wanke da kaina tunda kadan ne Zan iya,nace to idan ka Gama ka Kira ni akwai yin brush sabo da hannunka zai motsa da yawa idan nazo sai na maka,Kai Kawai ya daga min na fita tare da kulle masa kofa,kayana na cire na daura guntun towel dina sai katon hijab na saka na kaiwa su Bintu kayana nace da safe ku wanke a goge sannan na koma,Hijab din na cire Ina jira naji kiransa,Shuru Shuru sai kararsa naji,na tsaya a bakin kofar nace ya akayi yace na gama ashe wai towel zai daura ga hannunsa ya motsa shi da yawa,Shiga nayi na gyara masa daurin sosai sannnan ya zauna Ya rasa inda zai sa hannayensa sabo da azaba,sai da ya huta sannan na matso toothpaste a brush dinsa nace to bude,idonsa ya bude ya kalleni daure da guntun towel ko Ina na jikina mul mul Ina sheki sai kamshi nake,brush din na Fara Masa a nutse Ina bin ko Ina har yace yayi Saura harshe Nan ma nayi Masa har can ciki kusa da makoshi duk an goge, nasa Masa bowl a wuyansa Kar ya bata jikinsa a sink din ya kuskure bakinsa sosai na Masa alwala sannan ya fita da kyar ya zauna a bakin bed,Ni Kuwa wanka nayi nima sannan na wanke toilet din sosai boxers dinsa na wanke na shanya dake bai baci ba ko daya sai da na wanke komai na gyara sannan na fito daure da guntun towel dina ban ma tsane jikina ba duk ruwa,kallo na yake kawai shi mamaki nake bashi yanda nake Abu na ba ruwana da wani Yana wajen Kai tsaye, lotion dinsa me tsada na dakko na Fara shafa Masa sai ya wani lumshe Ido,nace armpit yace manta daban na dakko nace daga hannun kallona yayi sai ya daga na shafa masa da wani turare na armpit a fili nace Dan gayu,Hannu ma Ina zuwa yace ga hand lotion can duk set din body lotion dinsa ne,na shafa Masa na dauki body lotion na shafa Masa a cinyoyinsa da kaurinsa da kafa,sai yace ga na feet can ki dakko na dakko na shafa Masa a feed dinsa sannan na dakko body spray na fesa Masa sama sama,Nace to shi man babu na private part? yace duba wajen Zaki ga men's part cream ki dakko min,na dakko Ina dariya sabo da abin nasa yayi yawa yace juya na juya sannan yayi kokarin shafawa ya kasa ya hakura yace na gama na juyo ya bani na maida saman mirror
Gashinsa na gyara Masa na taje tare da shafa Masa man gashi, kayan bacci Kuwa babu sa riga wando iya gwiya marar nauyi na dakko Masa da towel dinsa na taimaka na saka Masa ta kasan towel din sai da na saka sannan na janye towel din na maida toilet,yace na sa Masa Riga zaiyi Sallah,na saka Masa jallabiyya yayi salloninsa a zaune sannan na cire Masa rigar lokacin ya kwanta kuma da barin da ba rauni Yana facing mirror inda nake tsaye..
Hijab na saka a ciki na shafa Mai sharp sharp Kuma ta cikin hijab din nasa kayan bacci na,Riga me hannun vest da wandonta dogo ko bra ban sa ba haka pant ma ban sa ba turarukana na shafa sannan na haura saman bed na kwanta can karshen gadon nima Kamar inda yake a karshe, tashi nayi na kashe light na rage ac sannan na koma na kwanta na Shige bargo iya ni daya nayi Adduar baccina,yace yunwa fa nake ji,nace na manta wlh ai kamar Naga Farooq ya tsaya an siyo abubuwa,light na kunna Jawad sai kallona yakeyi har yasa naji kunya,ledojin na dakko Naga dayar ledar magunguna ne ashe,sauran ledar na duba naman kaza ne Tasha hadi,sai su Fresh yo da juice tare da fruits daban daban,kitchen din part dinsa na shiga na wanke tare da yanka Masa watermelon na zuba yinibi a gefe,da Apple,sannan zuba Naman shima a plate daban tasha cabbage da kayan hadi,Ina zuwa nace to gashi,tashi yayi ya zauna sannan na dakko katuwar cinyar kaza na Fara bashi a baki Yana ci,Ina so naci Ina tsoro Kar yace na cinye Masa yawuna ya tsinke Nima yunwa nake ji,tana ta kamshi shi yake ci amma ni nake Masa santin nace amma daga gani zata Yi dadi,irin wannan gashin akwai dadi,na Kuma bashi Karo na uku nace dole su samu customers a wajen Nan nasan ma layi ake musu,ai tayi dadi har bargonta ya gasu,na sake bashi nace haka nake son gashi ko Ina ya dau wuta, Tasha maginta har da kayan kamshi,yajin yaji citta,muryarsa naji yace kici Mana kin dameni,dama kadan nake jira ko dana fara ci na fishi ci ma na manta ma da shi sai da naji na fara koshi sannan na tuna da shi naci gaba da bashi Yana ci sau biyu yace ya koshi na dauke ragowar na Kai kitchen na saka a fridge.
yogort na bashi yasha da yawa sannan karshe yace fruits na Fara bashi da yawa ya Sha fruits sannan na kwashe komai na Kai fridge na kawo Masa magungunansa da ruwan roba ya fara sha a nutse Ina bashi daya bayan daya har ya gama nace ana so idan mutum yana shan magani ya dinga shan ruwa da yawa sabo da yafi aiki,yace ke Zaki fada min doctor ne Ni fa asibitin da Kika ganni a ciki nawa ne to Kuma Ina zuwa duba patient lokaci zuwa lokaci,oh na tuna Asif ya fada min.
Ruwan ya shanye gaba daya ya kwanta abinsa,Nima na kwanta can karshen bed bayan na kashe light Ni kadai na lulluba da bargo,wayata na jawo na kamo document din Novel din Dangin Rabi na Fara karantawa,Ina ta dariya tun inayi a hankali har abin ya ci tura,sai bacci ya fara daukansa sai Jawad dariyata ta tashe shi,Tsaki yaja tare da cewa ki tashi ki koma dakinki,novel na canja ko na rage dariyar na Fara karanta Hadin kai,amma shima ganin mahaukacin ya bani dariya nace sorry Jawad wani mahaukaci ne ya bani dariya yace ai kece mahaukaciyar tsaya na karanta ma novel din kaji,bana so ni bacci nake ji,kwanciyar Kai da kafa Muka Yi, yace sai kace wani dan daudu na zauna Jin novel,Wayar na kashe gaba daya nayi Addua na kwanta,shi kuwa har yayi baccin ma
Nima ban San sanda bacci yayi gaba dani ba,cikin dare naji Sanda ya tashi ya Shiga toilet minti kadan ya fito da alama fitsari yayi,kwanciya ya gyara yaci gaba da baccinsa,washe gari da asuba na tashi nayi Sallah sannan na tashe shi da kyar ya iya tashi sabo da cuwon nasa yayi tsami,toilet ya Shiga yayi zamansa bayan yayi bukatunsa zamansa yayi a ciki bai kirani ba Kuma yau hannayensa ji yake bazai iya motsa ko da yatsansa ba,Ina ta jiransa Shuru har Rana ta fito,tashi nayi na Fara knocking Shuru Kawai na Shiga a zaune na ganshi Yana ta baccinsa ya jingina da jikin bango,bacci kayi kuma,Ido ya bude a hankali ya kalleni Kawai,da alama ba abinda yayi,brush na dauko nace to bude,na fara Masa a hankali Yana ta kallon fuskata,Murmushi nayi kawai har na gama na Masa Alwala ya fito,nazo na sa Masa jallabiya yayi sallah na cire Masa ya zauna Yana karatun Qur'ani,toilet din na wanke ko Ina Yana sheki da na saka abubuwan kamshi sai kamshi sannan na cire bedsheet na canja sabo na gyara room din na share nayi mopping na goge su mirror da da su bed etc sabo da yana ciki ban kunna turaren hayaki ba sai Roomfreshner na saka,a toilet Kawai na saka wani turare dake fitar da turiri ba hayaki ba, fita nayi na gyara ko Ina na part dinsa neat sannan na Shiga kitchen na hada Mana kayan Kari faten wake nayi da hanta sai bread ga tea na kawo na ajiye komai lokacin Yana kwance a bed Yana jan carbi,wanka na Shiga nayi na fito daure da guntun towel dina,Ina jikin mirror dinsa Yana Jan carbi ya Kura min Ido har na gama shiryawa cikin doguwar rigar atamfa me aljihu daidai ni sama ta matse kasa ta Bude kadan cif cif ni,turarukana na shafa na gashina na gyara Yana kallon gashina me tsayi,Zama nayi nayi kwalliya sannan nayi dauri na me kyau nayi kyau dankunne na saka da sarka silver sabo da atamfar da silver a jiki
Ina juyowa ya rufe idonsa tuni Kamar me bacci Wai Kar nace ya kalleni,juyowa nayi nace abinci fa? Yace sai anjima okay nace,na fita abina Ina cewa na tafi wajen yara,Ina fita na iske Asmau da Nawwara sunki Shirin school suna kuka,nace lafiya ku Kuma? Kadada tace nice nan na fyallawa shegu Mari Yan Iska yara daga nace baza su school bane ko shiryawa basuyi ba Kawai suka zageni sunci daraja Daya da ba haka ba idan na dinga foli foli da yarinya sai ta kusa gangarawa lahira kamata zasu zaga ni zaku yiwa bur.......ko Fara na girmeta ku sani,nace karya kike wannan Kuma kwana biyu tsakaninmu aka haife lahadi aka haifeki Talata,Kadada tace yo ai kyaleki nayi ke kizo ranar zuwa church Ni na Zo daga baya,kinji kunya musulma an haifeta ranar Lahadi ai baki gwani ba,Dariya nayi nace to naji ai gwara masu zuwa church da ke,koma mene munfi kusa da masu zuwa church a kanku,Tahantsi dama ta bamu shekara uku shi yasa tana jinmu tana dariya Muna ta musu,nace me kuka dafa? tace masu aiki sunyi kowa yaci ai harda farfesu gashi har an gyara ko Ina,su Meenat duk sun tafi school su Asmau ne Suka ki tafiya,na koma wajen su Nawwara na bata rai nace Yau sai kunje school dole kuje ma ku shirya,Basu kulani ba nace wallahi Zan muku dukan tsiya tunda Iskanci kuke ji,tsoro suka ji sun San Zan iya Kuwa tashi Suka Yi Suka barke da kuka sun Sam sum makara yau sai sunci duka a school, Zan iya musu dukan tsiya sum sum Suka tashi na dauki Wayar charger na rakasu bedroom duk sun lalata nace Kuma Kuna dawowa ku tabbatar Kun gyara dakin nan daga yau babu me gyara muku daki, Uniform Suka dakko nace idan baza ku iya sawa ba sai na saka muku,suna Fushi Suka saka Kaya Suka shirya nace kuje ku shiga taxi babu driver da zai sake kaiku ga kudi na Basu kudi har na break,Nawwara ce tace ai mu gwara Yaya ya dinga bamu ba ke ba wa ya sani ko ragewa kike,nace ae na rage bazan baku ba ko zaku kwata ne? Shuru sukayi zasu tafi Asmau ta dawo tace kudin pad Zaki bani,nace period Kika Fara Asmau? Kai ta daga min,nace girma yazo kamarki har kin Fara Kai yaran zamani suna balaga da wuri zamaninmu na da yaushe ake haka Kai yaran zamani oh,Saida Asmau tayi dariya tace to ai kema Yarinya ce,nace kin girmeni ma ai ni kanwarki ce bana yi,ke Kuma fa uban Yan rainin? Nawwara tayi min Shuru naje na dakkowa Asmau pad package biyu nace gashi ai kin iya amfani da shi ko,tace a'a,koya Mata nayi ta karba ta Shiga toilet ta shirya yanda na koya Mata nace yarinya sai aure,Murmushi tayi Suka tafi nace bari nasa driver ya kaiku badan halinku ba,Driver nasa ya kaisu school Allah yasa ma ba a musu komai ba.
Abeed na dauka an Masa Wanka yasha kyau cikin blue jean da maroon t-shirt Kadada tace mufa yau zamu tafi,nace ke dalla matsa wacce tafiya Kuma yau yau hauka ake,na tafi part din Jawad na iskeshi a zaune Yana kallo,yace ya yaran? Nace sun tafi school, abinci na zuba Ina karyawa Abeed Yana saman cinyata Yana ta Wasa da adon rigata dake saman kirjina,muryar Jawad naji yace kanin mijinki ne fa?nace wa? Abeed shine kike bari Yana Wasa da ke,nace dan yaron? ba Namiji bane kanina ne fa ke Wai baki San addini ba,bakya zuwa Islamiyya baki ji illar Kanin Miji ba,ba ruwana ni dan tani ba damuwa ta bace addini nake tuna miki kina aikata haramci karki sa a jefa ni a wuta,nace ai yaro ne bai balaga ba zai iya koma mene yaro Ina ruwansa me ya sani Kai kyaleshi