Showing 12001 words to 15000 words out of 119289 words

Chapter 5 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9408

littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24


Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro


*KUDIN WOMEN24 TV VIP*
Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada
Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne


*KUDIN WOMEN24 TV*
*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in


Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv




*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*


1.WOMEN24 TV VIP NOVELS
2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS
3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS
4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS
A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa'in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu


5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE
Kinajin sunan groups innan kinsan meye za'a dungayi a groups in
DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.


Account number.




2065301650
Zubairu Hayat Iman
Uba bank.




Number waya.
09030159301










Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN


Kada kibari gara basannan ta wuceki.








Sadaukarwa ne ga


ZAINAB GARBA BUTALAWA






Page naki ne Yar Aljanna
AIDA MAMAN TASNIM

















Kamar yanda Kika sani Jawad Muhammad Dankoli yake,asalin mahaifinsa Fulanin Zamfara state ne,har yanzu Kuma dangin ubansa a can kauyen suke,Alhaji Muhammad Dankoli su biyu rak iyayensu suka haifa daga Muhammad sai Yayansa Umaru a Kauye suka taso basu yi Ilimin boko ba sai na Addini har suka girma suka Zama samari Muhammad Dankoli shine ya gaji da Zaman Kauye yace gaskiya cirani zai tafi Lagos Iyayensa Kuma sun Amince Masa,wani abokinsa Auwalu shi ya hada shi da uban gidansa Alhaji Mustapha yake Masa yaro a shagonsa da yake siyar da furniture a Lagos ya tafi can ya Zama yaron shago.


A hankali Yana tara kudi sai ya turowa Iyayensa idan Kuwa yazo ganin gida har Yan Uwa yake taimakawa haka a Lagos ya koyi yaren yarabanci da turanci a hankali ya fara bunkasa hakan yasa ya fara tunanin aure,Yayansa Umaru Abba kenan shi Gona da rashin kudi yasa ya kasa ko Neman budurwar ma yace sai yayi kudi.
Ana haka wata balarabiyar kasar Labenon Nafisat tana yawan zuwa Nigeria ita da mamanta Aisha suna zuwa kawo Kaya ciki har da uban gidan Muhammadu wato Mustapha suna sari anan Muhammad yaga Nafisat ya makale shi ita yake so kamar Wasa itama ta Fara kaunarsa mamanta ita kadai ta Haifa Kuma babanta ya rasu duk arzikinsa Nafisat ce ta gaje shi Babanta hamshakin attajiri ne itace ke juya dukiyarsa da kadarorinsa ita da mamanta Aisha wato Kakar Jawad kenan wacce har yanzu tana zuwa gidansa tayi watanni


Aisha ta Amince tunda taga yarta tana son Muhammad dake mutum ne dan Fulani fari irin namu na Yan Nigeria kyakyawan gaske,a haka Nafisat ta dauki Muhammad har garinsu yaje yaga dukkan danginta da asalinsu sannan aka daura aure ya dawo da matarsa Nigeria,gida katafare ta siyawa Muhammad Suka zauna tare cikin soyayya,shekara daya ta haifo danta Namiji kyakyawan gaske shine Jawad,tun daga haihuwa Kuma Muhammad yaji mace daya ta Masa kadan ba a dade ba ya auro wata Mace Yar Zamfara Zulaihat,Zulaihat bata Haihu ba har aka kwashe shekaru takwas lokacin Jawad Yana school me tsada lokacin Kuma Muhammad arzikinsa ya Kara gaba,suna zaune lafiya ya dankara gidansa me kyau Wanda take da part hudu,har Jawad ya cika shekara Sha takwas sannan Zulaihat tace ita sai ya saketa ta auri wani mijin ko tana da rabo,yaki sakinta karshe ta kaishi Kara kotu dole ya hakura ya saketa lokacin kuma yaje kauyensu tare da dansa da balarabiya


Yana zuwa yace da Yayansa Umar ya nemi matar aure shi zai Masa komai da komai har gida sannan zai tafi dashi Lagos shima ya fara Sana'a iyaye da Yan Uwa ana ta tayashi murna,Haka Kuwa ya Gina Masa gida a kauyen lokacin ya auri wata Yar uwarsa Mariya ya barta a Kauye ya tafi Lagos sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa gida lokacin Kuma Muhammad ya auri mace ta Uku me Suna Zaliha bazawara ce bata da kunya sai bakin ciki take da Nafisat Kamar ta kasheta, ita Kuma Mariya ganin itama Taki haihuwa gata harija tace lallai Umaru ya saketa baza ta iya Zama Miji na katsina ita tana daura ba ba yanda ba a Yi ba Taki hakura sai da aka saketa ta auri tsohon saurayinta tun daga haka Umaru bai sake aure ba, a shekarar Kuma Zaliha ta Haifi Danta Hafeez lokacin Muhammad yace sai tayi tsarin Iyali shi baya son Yara ita Kuma tace sai dai ya saketa haka ya saketa tana Yaye Hafeez ta dawo da shi gidan Ubansa Nafeesat tana rainonsa dake ba ruwanta da duniya, ba a fi wata shida ba Muhammad ya sake auro wata yarinya Yar talla zainabu lokacin da Jawad ya gama Secondary yayi sauka karatun Al'qurani ana shirye shiryen turashi London karatu University Muhammad yaga wata Zahrau bayarabiyace amma musulma ya auro,Zainabu ta haifo yaronta Ahmad, Zahrau ta haifo Waleed yace duk suyi family planning Suka ki ji suna samun ciki na biyu ya sake su dukkansu a rana daya,Jawad Yana tafiya da wata daya Umaru ma ya auro wata bazawara marar Imani Hajiya Barira wacce ake bata taba haihuwa ba sai da Alhaji Umaru,Zainabu da Zahrau Kuwa daya mata Suka haifo a gidan iyayensu tun kafin su yaye su Suka dawowa da ubansa yaransa Asmau da Nawwara,daga lokacin Kuma Nafeesat ta samu ciki itama sai ta fara cuta taki ci taki cinyewa hakan yasa mamanta Aisha ta dauki yarta Suka koma garinsu ana duba lafiyarta akace ciwon zuciya ne


A shekarar matar Umaru ta haifo danta Namiji Ayman,Bayan suna Allah ya karbi rayuwar sa, Nafeesat a garinsu a shekarar Yan bindiga Suka je kauyen Iyayen su Muhammad Suka kashe mutane da dama ciki harda Baban Su Muhammad da babarsu Muhammad kamar zai haukace duk shakikan danginsu masu fada aji sun mutu sai su,sunyi kuka da bakin ciki,Nafeesat Kuwa kafin ta rasu ta bar wasiyya dukkan dukiyarta a mallakawa danta Jawad shi yasa Jawad ya Zama shahararren me arzki,duk kyautar da Kaga Yana Yi da taimako sadaka yake yiwa mahaifiyarsa Allah ya Kai ladan kabarinta


Daka Nan Kuma Muhammad yaci gaba da auri sakinsa gashi duk shekara sai yayi aure ya saki wasu har sai dai aka haifa Masa Yara goma Sha biyu cas duk Yan kanana Jawad shine Babba,Lokacin Kuma matar Umaru Umma ta haifo Mata biyu Layla da Nusaiba,bayan shekara biyu ta haifo auta Namiji Rashad daga haka mijinta yace a tsaya haka
Sabo da rayuwar duniya baya son haihuwa da yawa sabo da Kar ya mutu ya bar yaransa a wani hali Kuma baya son wahala Yana ta faman neman kudi suna karewa a yaransa shi bazai iya rike Yara da yawa ba nauyi ya hau Kansa Sam bai so sabo da tsadar rayuwa,shi kuwa Muhammad gida me kyau ya sake ginawa dan Uwansa Umaru ya Kara Masa jari me tsoka ya tsaya da kafafunsa yayin da Jawad ya gama University a London duk da cewa ma Busy man ne Yana juya kadarorin mahaifiyarsa sannan Kuma babban likita ne medical doctor Yana da katafaren hospital a Lagos da kwararrun likitoci Kuma Yana Aiki shima a asibitinsa aikin gomnati ne bazai iya ba kasancewar ayyuka sun Masa yawa baya Zama Bai da time Yana tafiye tafiye akan kasuwancinsa,sai kakarsa dake zuwa daga Labenon idan tazo sai tayi wata shida a gidansa kafin ta koma haka Dangin mahaifiyarsa suna zuwa Yana zuwa shima haka Dangin ubansa Yana zumunci da su sabanin Abba wato Alhaji Umaru tunda Iyayensu suka rasu bai sake lekawa garinsu ba rayuwarsa daga shi sai matarsa da yayansa sai abinda matarsa tace.


Ana haka katsam Alhaji Muhammad ya shirya zai je kauyensu ganin dangi a hanyarsa ta zuwa Zamfara yayi hatsari Allah ya Masa rasuwa motarsa ta kone kurmus,ana cikin zafin mutuwa Abba Umaru yace zai hada yaran kaf ya rike Amma bayan komai ya lafa anyi arba'in yace bazai iya ba,ga wasu yaran duk tsigesu akayi daga nono mutum uku sauran ne bana jego ba,yanzu matar Abba itace take gallaza musu Wanda kamata yayi ace Jawad Yana da aure sabo da a samu me kula da yaran ko da ace akwai Nanny to dole sai da uwa ta gari me kula da lamarinsu kin San Yan aikin yanzu sai lahaula to shi Jawad bai da budurwa bai taba soyayya ba ga Yan Mata suna binsa amma kin San mace ta gari yanzu wahala suke kinji dai labarinsa
Game da halayensa Kinga alama mutumin kirki ne,baya Shan komai baya Neman Mata ga addini,Bai San hayaniya baya son shiga safgar kowa


Nidai Najla nace wayyo Yara sun Shiga tagaigayar rayuwa nima marainiya ce Allah sarki,Asif yaji dadi yaci gaba da cewa Shine ya turo ni ya yaba da hankalin Yar uwarki da nutsuwar ta da tarbiyyar ta.... katse shi nayi nace ni wato baku yaba da tawa tarbiyyar ba ai shikenan kuje ga kanwar tawa nan Zan hada ka da iya, da kalar tausayi na sake langabar da Kai nace wayyo rainon mahaifiya tace haka nake Nima akwai hankali ba ruwana da duniya,Ni Asif ban damu da rayuwar duniya ba masu kudi su daina cewa sai me kudi ga talakawa masu nutsuwa da hankali kaf unguwar nan yabona akeyi idan ka tafi ka tsaya ka tambaya zaka ji yanda suke kirana sunana sun maida shi hakuri sabo da Hakuri na,kasan da sanyin safiya aka haifeni shi yasa nazo duniya da sanyina irin na asuba,Asif yayi dariya yace bari kiji mana,nace to Ina ji Yaya Asif,Asif yace au na Zama yaya? ai ka wuce yaya sai dai ma Daddy Dariya yayi kawai.


Yace to shine Yace zai aureta Nan take Najla ta zaro ido,yace yes deal kudi zai biya ko Nawa ne zai aure ta Kawai aikin ta ta kula da Nanny da tarbiyyar yaran kafin Sanda zata gaji Kawai dai yaran kanana da aka tsige daga nono su Kara wayo dai tana kula da Nanny da komai na yaran gidan kannensa gaba Daya,fashewa nayi da kuka nace Fara tana son kudin Amma Yara goma Sha a wajenta so kake ta tsufa ta ragwargwaje,Kula fa da masu lura da yaran zata yi sai wani Abu in sunyi ba dai dai ba ta gyara musu Zama abinda ta gani ta fadawa Jawad,idan suka San a karkashin matarsa suke dole zasu saitu su koyi biyayya,Najla tace to Allah tana gajiya sai ya saketa,Asif yace Kuma zai sata a makaranta har a university me tsada Zata sa sutura ta ci me kyau ta Sha me kyau, Kawai shanawa zata yi a gidan komai da kowa a karkashin control nata suke...Ashar nake kokarin durawa sabo da murna nace kut...sai na fasa na furta Kut kaiiii Kuma a biyata kudin? Asif yace Fadi ko Nawa za a bata tunda hanya Zaki mana


Cike da tsoro jiki na Yana rawa nace dubu..dubu..dari biyar Ina ganin na fada da yawa,Dariya Asif ya dinga Yi yace million ashirin tayi gabana ne ya Fadi nace me? Million ashirin ai Yana maimaitawa na kwashe takalmana Zan tsere tsoro ya kamani nace to ban yarda ba so kuke ku yanke min Kai kuyi tsafi Dani million ashirin sai kace bankin duniya ne zai bada kudin bada ni ba
Asif yana kiyi tunani Najla please ki taimaka mana ita a Kauye take baza ta gane lissafin ba Ina tuni na fece gida da gudu na kulle kofa,Paper Asif ya zaro tare da rubuta number dinsa ya rubuta ga numberta idan kun shirya ku kirani a wannan number yaro ya bawa yace ya shiga ya bawa Najla yaro ya karba ya Kai Mata lokacin na Shige dakina na dukunkune a cikin bargo sabo da tsoron irin kudin da akace za a bani, Daddy ne ya karba tare da kawo min takardar Yana tambaya kalau kike Kuwa? Nace kalau nake na karba Kawai


Ina haka har Mama ta dawo ta ganni a kwance tace ke Kuma lfy? lafiya Kawai hutawa nakeyi,shine Naga Kamar kina tunani,da sauri nace no ba tunani nake ba,okay Kawai tace ta wuce dakin mijinta,tace Barka da dawowa lokacin yayi wanka Yana shafa Mai,Murmushi ya saki cike da kauna yace tun dazu na dawo,ka dawo lfy ya Hanya?lfy Alhmdllh ya furta Yana binta da kallo yace Naga kin Kara kyau ne da kiba ko duk cikin ne yasa? Mama a kunyace tace bazai wuce hakan ba, I miss you ya furta,a hankali tace me too,wanka tayi taci abinci Suka Shiga soyewa Ni Kuwa Ina ta tunani Kawai na tashi na dauki littafana na fara karatun final Exam na share zancen.


Bangaren Asif kuwa Jawad ne ya kirashi da dare lokacin Yana kwance a hotel bugu daya ya dauka Asif yace ya akayi baka kirani ba ya ake ciki? Asif ya kwashe yanda sukayi da Najla ya fadawa Jawad,ko a jikinsa yace ka bani mamaki Asif wannan Najla din ita ce fa ta Kauye ya zata Raina ma hankali har ka yarda Wai Kai? Asif yace Kaine dai baka gane ba Jawad waccen ai tafi nutsuwa,Jawad dai ya tabe baki yace sai ka dawo ta yiwa kanta ko ajikinsa,Asif yace gobe Zan dawo,better Jawad ya furta tare da kashe wayarsa Yana tunanin wa Kuma zasu nema
Ni Kuwa Sam na kasa sukuni tunani nakeyi har na gama tabbatarwa kaina na yarda da deal din,cikin dare 10pm na Kira number da Asif yace na kira Ina Kira ya daga,a hankali nace Najla ce,Murmushi yayi yace wow to ya gida,sharewa nayi nace dama kira nayi na fada maka munyi shawara ta amince da deal din,murna ta Kama Asif yace gobe kafin na koma zanzo mu tsara yanda komai zai kasance,Waya ta na kashe Kawai sai lokacin na samu nutsuwa na kwanta bacci abina zuciyata cike da tunane tunane


Washe gari bai tafi ba 7:30am ya iso gidan mu na fito sanye da uniform Zan tafi school na ganshi har ya karaso sabo da ya kirani a waya bayan na gaisa shi yace sauri nake zanbi jirgi yanzu a gurguje muna so Maganar ta Zama sirri tsakanin mu uku karki fadawa kowa muma baza mu fadawa kowa ba...da sauri nace hauka nake na fada ai Kawai kuzo a Niyyar auren soyayya zaku yi Kawai,ashe kin gane to zamu zo dashi jibi ya gaisar da iyayenku sai ki Kira Fara tazo daga Kauye Nan gidan,karki manta jibi Saturday zamuzo Kuma iyayenku zamu gaisa sannan sai a a kawo kudi a tsaida rana ba jira bazai Kai wata Daya ba ku fara shiri,ba damuwa na furta, dubu ashirin ya bani yace gashi kiyi break,cike da murna na karbe Nan take nace deal ya hau yanzu naji dai dai aci gaba da gashi sai kunzo Zan fada mata,yace shiga motar na saukeki a school, jeka Kawai Daddy idan ya ganni zai min fada,Asif juyawa yayi ya shiga mota driver yaja suka wuce Ni Kuma na Shiga Napep zuwa school.


Bayan mun zana final exam na tsaya munyi pics daga Nan gida na dawo Kawai,Ina dawowa Mama ce a gidan Kawai Daddy ya fita wurin aiki,wanka nayi naci abinci tuwon shinkafa miyar kubewa danya sannan na zauna gefen Mama Ina so na Mata zancen Jawad Ina tsoro,kallona tayi tace yan makaranta an gama an huta sai aure,haba Mama wanne aure baza ki bari naci gaba ba? Ni wlh nafi so Allah ya kawo Miki mijin aure na gari kiyi aure Wanda Zaki huta Wanda zai yarda kiyi karatu a gidansa,Babanki ma baya son kici gaba da karatu Kinga Kar yazo har Nan yace zai Mana tijara gwara ki rufa min asiri ki tsaida miji,kaji Mama ni Ina da uba ne ni da nake marainiya gani Agola a gidan Daddy wanne Baba Kuma,bata rai Mama tayi tace maza kici gaba da zubarwa da kanki mutunci kina Kiran kanki marainiya banza har yanzu Najla baki da hankali Sam Ni ban taba gani wacce ta Gama school marar hankali irinki ba Sam baki da wayo baki San Ina Kika nufa ba,baki na turo nace ai shike nan Mama ya wuce yanzu dai Albishirinki? Mama tace goro fari kal na samu miji,Nan take Mama ta fara murna tace bana son Wasa, wallahi Mama da gaske Yana mugun so na Allah ya hada jininsa da Nawa nima Ina son....sa na karasa da kyar tare da rufe Ido da tafin hannunwana Wai kunya, Mama tace waye? Guess Mama,I don't like this guessing game Kawai go straight to the point who is he? nace Jawad me bada sadakar kudi Wanda rannan ya biyo Nan Suka siyi fura,Wait Jawad da nake ji a radio station?


Yes Mama Kuma Wai shi a sonsa ma bikin Kar ya wuce 2to 3weeks ya Gama shiryawa,Kin San a Lagos yake kuma Yana so zaiyi tafiya uk dani shi yasa yace bikin da sauri yake so Wai kuyi bincike a Kansa kuma sisi baza mu kashe ba komai shi zaiyi ba komai da zamu siya har bakin mu da mutanenmu duk ya dau nauyin komai,Mama farin ciki ya cika ta tace Alhmdllh babu Wanda yake so yaga nasa a wahala naji Dadi Kuma zamu Yi bincike Zan fadawa Daddy dinki da mahaifinki Inshaallah,ai tunda miji ya fito babu jira Kuma sai Addua Allah yasa hakan shine Alkhairi,Ina wani blushing da kunya nace Ameen Mama,Jibi zasu Zo su gaisarki ki fadawa Daddy,to bari a fadawa mahaifinki idan sunzo sai kije ki rakasu can shima su ganshi su gaisa shima yayi bincikensa,Nace to Mama naga alama wallahi har yanzu kaunar Babana bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login