Showing 21001 words to 24000 words out of 131263 words

Chapter 8 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4626

sau uku sannan Junaid ya gyara murya yace


Ya akai ne?


Bakinta ta turo tace


Tafiyan fa?


Idonshi ya kura mata yace


Zuwa ina kenan?


Kaduna mana, yau fa an tafi mid semester break.


Kanshi ya dauke don kwatakwata bayada niyyar ta tafi wani gurin better ta zauna don shi se yanzu yake ganin Tun tuni me ye dalilin da Tunda su Daddy suka rasu bai dakko ta ba ya bari su Mami suka dauketa. Ganin yayi shiru yasa tace


Yaya flight din fa 6pm zai tashi


Da sauri ya dago Cikeda mamaki yace


Waye yayi miki booking, you didn't even let me know.


Tun last week Ja'afar yayi mata booking ko Mami bata sani ba, to yanxu tasan inhar yasan Ja'afar ne tafiyar sede a fasa,


Mami tayi booking fa,


Junaid baice komai ba ya mike shida Ridwan suka fita, suna fita ta Mike kafafuwanta. Acan Ridwan yace


Ka kyaleta ta tafi, kada kana takura mata idan ba haka ba Abinda muke nema bazamu samu ba.


dafa kanshi Junaid yayi ya sake jinginar da jikinshi a jikin mota yace


I don't want her to go, nafi son kullum ina ganinta by my side.


Kallonshi Ridwan yayi yace


Kada ka zama me son kanka, to me yasa bazaka fada mata ba.


Da sauri Junaid ya dubeshi Yana zaro ido kafin kuma ya fara girgiza kanshi yace


Is not yet time and kasan yanzun haka tare suke da Ja'afar, ni ina tunanin shi yayi booking flight dinnan Don there's no way Mami zatayi batareda sani na ba.


Tabdi! Ja'afar Yana son ta?


Ridwan ya fada Yana kara jinjina abin kafin yace


Abokina ka hakura mana.


Murmushin takaici yayi yace


Da zan iya da tuni na hakura, bazan iya bane na kasa dangana.


To idan bazaka iya hakura ba is better you let her know, yarinyar da alama bazatayi wahalar shawo Kai ba.


Dariya Junaid yayi yace


Ba haka bane, shi ne kawai Abinda mutane Ke gani a tattare da ita amma ni nasan taurin kan Sulaim se addu'a.


Sun dade suna tsaye har Sulaim ta gaji da jiranshi zata kirashi ya turo kofar ya shigo, tashi tayi ta zauna Tana kallonshi, shima kallonta yake har ya zauna inda Ridwan ya tashi yace


Kinyi sallah?


Kanta ta gyada yace


Mu tafi kenan?


Take wani murmushi ya subuce mata, bai kulata ba suka fito Zuwa mota, lokacin awa daya ta rage flight dinsu, kallonshi tayi yadda yake tuki kamar bayaso tace


Yaya zanyi missing flight din fa


Baice da ita komai ba ya cigaba da takunshi itama tayi iskar kare dashi tareda daukar wayarta tana ta danne danne taji muryar shi yace


Zaki dauki abu a gida ne?


Dago kanta tayi tace


A'a na saka a booth Tun safe


Seriously? Kin gaji da ganina ne har haka?


Kawai abinda yaji bakinsa ya furta kenan, lumshe idonsa yayi a ransa Yana fadin you messed up Junaid. Itakam kallonshi tayi tace


A'a Yaya, ina son kawai zuwa ne.


Kanshi ya gyada bai kuma fadar komai ba saboda gudun kwafsawa haka ya kaita airport seda aka gama komai kafin suka rabu, tana ta murna wadda ta kasa boyuwa shi abin har mamaki yake bashi ma.


A airport tana sauka ta fito a departure hall ta hangoshi a tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa, Yana cikin Kaftan coffee da hula a kanshi yayi kyau har ya gaji da kyau, Kada Ku manta Duk yaran Mami Ja'afar Yafi kowa kyau, idanunshi Yana cikin eyeglasses fari tas, sede yana tsaye da wata azabbabiyar kyakyawar Yarinya Irin lousy kyau dinnan wanda abinda zaka fara hangowa kenan, suna tsaye Sunata dariya Irin abinda ake fada yayi dadi, gaba daya se Sulaim taji tamkar karta karasa gurin amma se ta dake ta isa inda suke fuskarta babu walwala ta zagaya Dayan kofar ta bude ba tareda tace komai ba ta shiga ta zauna amma ko bata fada ba kunsan how it feels kaga Abinda kake fadi tashi a kanshi, kake fatan ya zama naka na har abada yake tsaye da wata, abinda taji yace shi ya sake dugunzuma ta


Bari na wuce Kada baby sis tayi ta jira.


Seda ta zagayo inda Sulaim ke Zaune tace


Baby Sis ki kulamin da baby na naga Yana ji dake.


Kamar an buga mata guduma haka taji "Baby sis" like serious, shiru tayi ta sunkuyar da kanta Tana ta battling da hawayen dake son zubo mata se taji ta wulakanta.... Yes wulakanci ne. Shima jiki a sanyaye ya shigo but being the Ja'afar se cewa yayi


Sweetm se ki bani tsoro yadda kika Bata rai dinnan.


Ko kallonshi Batayi ba ta bata rai Haka ya aje wayar shi saman cinyarta ya fara driving sede yadda yake driving kawai will tell you cewar baiji dadi ba. Haka suka tafi shiru kamar anyi rasuwa Duk Surutun Ja'afar kasa magana yayi se can yace


Susu ba fushi zakiyi ba at least let me explain.


Ban tambayeka ba.


Come on Susu why you behaving like this.


Mtsssssssw


Taja tsaki wanda ba Ja'afar ba hatta ni Seda nayi mamaki, yadda take kada kafarta da kuma fuskarta ya nuna bacin rai sosae. A haka bai sake magana ba har aka bude gate din gidan, wani sharp breath tayi inhaling at least she's home. Yana gama parking ta aje masa wayoyinsa ta fice, tana bude parlon Mami ta fito daga kitchen hannunta rike da katon tray, a guje ta nufe ta itama aje tray din tayi ta rungume abarta, wani Irin farin ciki ya dinga shigarsu a hankali Mami tace


Haka unexpected Autar Mami?


Murmushinta tayi daidai shigowar Ja'afar, bai kulasu ba ya wuce inda zai kai shi dakinsu iatakam Mami tabi Zuwa sama rikeda tray din, ganin yanayin ta yasa Mami tace


Auta kamar ranki a bace yake?


Boye fuskata tayi cikin hannunta tace


Babu komai na gaji ne Mami, Ina Baba ?


Yaje massallaci jekiyi wanka kafin ya dawo.


Babu musu tayi dakinta, se lokacin da ta shiga bayi Abinda ya faru daxu ya fara dawo mata, wannan shi ne Karo na uku da suna Irin haka itada Yaya Ja'afar se take ganin kamar ta sake mishi da yawa ne, a haka tayi wanka tana ta tufka da warwara. Seda ta shirya sannan ta dauki wayarta Don duk expecting dinta Junaid ya kirata amma ko message babu hakan yasa ta kirashi, yana zaune kan sofa a parlonshi Ahmad yana ta damunshi akan se sunje siyo chocolate yayinda Subay'a ke dakinta kannenta sunzo, kiran Sulaim ya shigo, kawai murmushi ne ya kwace masa tareda jin sanyi cikin zuciyarshi. Shi kanshi mamakin yadda son Sulaim yayi masa Illa har haka yake, gashi ita bata wani damu dashi ba a yadda take abubuwan ta, a haka dai kiran ya katse. Kamar tana gabanshi tayi pouting lips dinta Wanda har ya zama jikinta tace


He'll not pick shima.


Tana shirin fita taji yayi returning call din, wani murmushi ta saki ta dauki wayar ta kara a kunnenta Sede kafin tayi magana ta Fara tuhumar kanta dalilin da yasa ta kirashi, meye take jinta special saboda yayi returning call dinta.......


Sulaim are you there?


Idan tayi Rantsuwa cewar babu mahalukin da duk duniya ya iya kiran sunanta Irin yadda Junaid ya ke kira Batayi karya ba, Harda gunna, kalkala sufra, madda da komai yake kira, kowanne harafi se ya bashi hakkinsa.....


Mhm


Mhm


Shima ya furta Yana rike wayar sosae, itakam jikinta duk yayi wani yum hakan yasa ta kwanta


Talk to me, ya kika je?


A hankali in a whisper tace


Lapiya lau, Mami na gaisheka


Dan murmushi yayi me sauti har tajiyo shi


Ina amsawa, kije Kici abinci.


Pouting bakinta tayi tace


To Yaushe Xaka zo.


Da sauri ya zaro idanunshi amma yaji dif ta kashe wayar saboda cajinta ya dauke


Shit! Ya furta




Shatuuu ♥️
[6/25, 4:12 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
7
✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣shatuuu095@wattpad


Tana tsaye gefen titi hannunta yana dauke da Leda baka da tambarin Sahad stores, Tana Sanye da skirt da riga na atamfa purple da pattern na mint green, yayi mata kyau, kanta ta yane shi da mint green mini veil, hakan ya bawa surar jikinta fita dukkan wani shape seda ya bayyana. Tana nan tsaye wata flashy car ta wuce, se kuma a hankali akayo reverse ya dawo daidai saitin inda Khulthum ke tsaye yayi wining glass dinshi kasa....Huzaifa ne the rich brat shidin yaron wani senator ne a Zamfara Yana level 4 a engineering cikin BUK , kana kallonshi kaga kwallo wanda duniya take damawa dasu. Murmushi yake tayi yace


Abokaina suna kirana lucky Hu saboda I'm always lucky, luck is always by my side. Gashi mun kara haduwa.


Kallonshi tayi batareda ta canja yanayin fuskarta ba tace


Amma kanada naci


Dariya yayi yace


Wanda ya nace shi zai dace ko ba haka hausawa sukace ba ?


Dauke kanta tayi, shi kuma se ta bashi dariya ita a dole Se ta ja aji ,


Ki shigo bai dace rana tana dukan kyakykyawa kamar ki ba.


Bude gaban motar tayi ta shiga yayinda murmushi ya kwace masa, suna tafe Yana mata hira a haka har ta dan fara warewa, bai tambayeta inda zataje ba itama sanyin AC da daddan freshener yasa ta manta, se ganinsu tayi a kofar More and More, dubanshi tayi tace


Banan zan zo ba.


Irin dariyar shakiyanci yayi yace


Ooops nayi tunanin na dakko ki ne we're on a date, amma dukda haka muje ko abu me sanyi ne kisha.


Ledar ta aje cikin motar sannan suka jero, mutuniyata ta saki fuskarta dama Irin rayuwar da take so kenan, rayuwar jin dadi da yawace yawace kamar yadda take ji take kuma gani idan aka dauke ta gidan yan gayu kunshi.


Tunda suka shiga suka samu guri take ta juye juye hakan ya so bawa Hu dariya amma instead se ya musu placing order. Yana zama wayarta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, se taji kunyar fito da purse dinta saboda yadda ta kode, dauke kanshi yayi hakan ya bata damar daukowa Sede take yanayinta ya canza saboda Ashir ne me kiran, silent ta maida wayar a haka aka kawo musu Burger da chilled Smoov, itadai tasan tana kallon abubuwan a kofar bakeries haka amma bata taba tasting ba, amma haka ta danne ta dinga ci da kadan kadan har suka gama sannan ya bada bill dinsu suka fita, a motar yake ce mata


A level nawa kike ne?


Dagowa tayi tace


Level 1 nake.


Kallonta yayi kafin ya maida titi yace


Shiyasa Naga Baki gama sakin jiki da mutane ba.


Dan dariya tayi a haka har suka iso wani ice cream joint na cold stone yayi musu ordering suka zauna cikin motar suna sha yake mata bayanin kanshi tunda taji yace babanshi senator ne kuma d only heir of them tasan tayi babban kamu. Gaba daya Khulthum ta manta cewar wai ta fito Kai dinki ne seda Hu yace


Baby da me kika fito yi ne.


Bakinta ta rufe tace


Kasan saboda yadda ka shagalta Danni I totally forgot dinki zan kai.


Dariyar shima yayi yace


Lucky Hu!


Bai tambayeta inda take Kai dinki ba se kawai taga sun tafi wani tailoring centre a nan wajen new hospital road, yawancin duk budurwar da yayi nan yake kaita a mata dinki, irin designers dinnan Don haka Khulthum tayi shiru Tana tunanin yadda zata iya kai dinki gurin, Amma ta waske suka shiga gurin, yadda suke da mutanen gurin ya tabbatar mata akwai sabo sosae tsakaninsu within 30 minutes an gama komai Harda billing kuma take ya biya through POS hakan ya kara mishi daraja da martaba idanunta. Suna fitowa ana kirayen sallah maghrib hakan yasa yace


Bari muje na kaiki gida, yau munsha yawo.


Murmushi tayi tace


Gaskiya kam.


Suna tafe Yana mata tambayoyi saboda yadda taga yanada kudi kuma tasan ba wani abu bane yasa ta fada mishi Daga inda take, baiyi mamaki ba saboda ya Lura dukkan guraren da sukaje are new to her, ko da wannan ma zai shawo kanta Tunda akwai son abin duniya tun a yau yayi marking.


Seda yayi mata takeaway me kyau kafin ya nufi inda ya Dakkota lokacin sallar maghrib ta wuce ana shirin sallar ishai.


Nuna min Kwanar da zamu shiga.


Kanta ta girgixa ba dadi ranta tace


Mota bata shiga


Se taga bai wani damu ba hasalima wayar ta ya karba Bayan ya gama jujjuya ta sannan ya saka numbers dinshi yayi saving mata kafin ya kirayi kanshi shima yayi saving a tashi. Daga haka sukai sallama ta fito Tana jin tamkar kada ta fito, kamar yadda kullum take tafiya haka ta cigaba da tafiyarta sede tana zuwa tsakiyar layinsu taji an sha gabanta, idanunta ta dago don ganin wanda yake muradin zagi, se kawai taga Ashir tsaye, yana tayi mata wani Irin kallo me Cikeda tuhuma da zargi. Itama kallonshi take tana karantar mood ensa, Baki daya ranshi a bace yake. Ganin haka yasa ta saki murmushi tace


D kayi ta jirana ko? Wallahi.......


Hannu ya daga mata hakan yasa tayi tsit yace


Waye ya fita dake ya kuma dawo dake a mota? Meye Sanye jikinki haka


Ya fada Yana nuna bingilin mayafin da ta yafa a kanta Wanda iya wuya kadai ya tsaya, wareshi tayi tace


Ni? Akace an fita dani? Wa na sani? Yan unguwa nan munafukai ne.


Se kawai yayi murmushi ganin yadda Lokaci daya take raina masa hankali, bai kuma cewa komai ba ya bata hanya Don ta tafi sede ko an inch ta kasa takawa hakan da ya gani yasa yace


Kije gida Seda safe. Yana fadar haka ya buga Lifan dinsa within an eye blink ya bar gurin, itama cigaba tayi da tafiyarta har ta isa gidan tundaga zaure taji Mama tana cewa A'isha


Kin Dakkowa Khulthum Kwanukan ta ko? Se ta dawo baki wanke ba tazo Tana mana diban albarka.


A'isha dake zaune kofar daki Tana yankan farce da fitila tace


Tai ta zuwa mana ina ruwan wani.


Kafin Mama tayi magana se suka tsinkayi sallamar Khulthum, inda Mama kawai take ta kalla tace


Na dawo Mama.


A... A.... Sannu da zuwa.


Imagine! Wanann ne Karo na farko da Khulthum ta fita takai isha'i a waje, ba tareda sunsan tun asali ina taje ba kuma yanzun babu Wanda zaice Daga ina take.... Akwai sakaci sosae na rasa dalilin da yasa iyaye irinsu Ke sakaci da whereabouts din yaransu, talauci ba hauka bane is a trial and test that are never meant to be easy. Saboda Kai talaka ne Seka bar yaranka sakaka kamar tumakai kada ka manta cewar yara Allah ne ya baku amana and you must account for every deeds da kukai a nan duniya.


As expected zata yi magana kan Kwanukan ta amma ta share ta shige daki ta cire kayanta sannan ta fito tayi wanka, tana fitowa mama tace


Khulthum yaronnan Ashiru yazo nemanki Tun rana.


Juyowa tayi tace


Mun hadu dashi, anyi abinci ne?


Ta tambaya Tana duban inda kitchen din yake,


Eh anyi, a zubo miki ne?


Kanta ta girgixa tace


A'a


Daga haka komawa daki tayi inda ta tarar da A'isha tana kife kwanuka, kamar bazata tanka ma taba se kuma ta kasa kasancewar hakan ba halinta bane tace


A'isha waye ya dauki Kwanukan nan?


Banza Aisha tayi mata hakan kuwa ya harzuqa ta Tace


Ke dan ubanki ba dake nake ba


Inkana son zagi nemi yaran ghetto na fada ina kallonsu, juyowa Aisha tayi tace


Kada ki kuma zagin ubana


Ubanki


Ta bata amsa almost immediately,


Na zageshi akwai abinda zaki iya yi ne?


Dariya Aisha tayi tace


Mutumin da bai bar babarshi ba ai ba abin mamaki bane Don kin zagi ubansu, Sede ki sani wanda kike zagi shidinne Gatanki ba gantallalun danginku ba.


Hey! Khulthum case, dama ance Baki yasan me zai fada amma baisan Meye martani ba. Taji Ciwon abin hakan yasa ta durfafe ta suka fara kokawa, Dama Tun suna yara Khulthum ce Marar karfi, yanzu haka ma Bata canza zani ba, kafin Mama tazo Aisha ta jibgi Khulthum gashi Daga ita se zanin wanka wanda tuni ya nemi nashi gurin.




Da sauri ta yar da wayar tare da fitowa parlour a sukanne, yadda ta bude kofar kadai will tell you Abu take so, gaba daya idanu Baba da Mami suka zuba mata hakan yasa se spirit dinta ya ragu, ta tako a sannu ta zauna daidai kafar Baba Tana gaisuwa, shima da dukkan faraa ya amsa mata yana tambayarta karatu da kuma su Junaid and family,


Duk suna lapiya sunce a gaisheku.


Murmushi yayi ya cigaba da kallonshi se Sulaim tace


Mami ina Wayarki?


Dakina


Daga haka ta koma dakin Mamin ta dakko wayar ta zauna gefen gado ta kuma kiran Junaid, Duk tunaninsa Mami ce amma yana jin muryar Sulaim ya gyara zamanshi tare da sake rike wayar a ranshi yace


This girl will be the death of me!


Are you there?


Ta furta mishi,


Am there Sulaimi, ya kikaje?


Alhamdulillah!


Ta bashi amsa se kuma sukai shiru baki daya hakan yasa sukaji tamkar gaba daya globe ya daina rotating round the universe, tamkar Lokaci ya tsaya ne cak! Seda Junaid yace


Have you eaten?


He always ask that, bata son Meye hadinshi da abinci ba, kanta ta gyada tace


I've eaten, abincin Mami kayi missing.


Dariya ya danyi yace


Nima Wifey ta bani me dadi


Dif taji Abu ya tsirga mata Wifey ta maimaita kafin tace


I've to go zanyi bacci.


Kafin yayi magana ta kashe wayar se taji duk yayi spoiling mood dinta wai Wifey! Ta dade da wayar hannunta tana tuhumar kanta dalilin da zatayi fushi Dan ya ambaci matarshi, to idan bai ambaci Subay'a ba Sulaim zaice. Haka tayi ta reminiscing abin cikin ranta a haka Mami ta iske ta, ta dade a tsaye Tana kallon ta ba tareda Sulaim din tasan da shigowarta ba. Taba ta tayi hakan yasa tayi firgigit tace


Mami.......


Kallon da Mamin tayi mata yasa ta kasa karasa Abinda zata fada se sunkuyar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login