Showing 36001 words to 39000 words out of 131263 words
Chapter 13 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
mishi sending a matsayinshi na exam officer call din Subay'a ya shigo, agogon dake kafe a jikin bangon ya kalla karfe shida har ta gota, picking call din yayi
Dear ka koma gida?
Na koma tun 3pm.
Dama zanje gidan Hajiya ne
Murmushi ya danyi don yasan kiran kenan dole wani gurin Zata biya,
Allah ya kiyaye!
Bai jira amsarta ba ya kashe wayar tare da mikewa Don shirin sallar maghrib. Jallabiya yasa blue black sannan ya dauki farar hula ya saka ya aje wayoyinshi ya fito, Yana Zuwa parlourn Sulaim na fitowa daga dakinta, da dukkan alamu aiki take a kitchen, Tana ganinsa ta tsaya tace
Yaya massallaci?
Kanshi ya gyada mata yace
Eh! Ko zamu tafi tare kiyi acan?
Dan dariya tayi tare da rufe fuskarta tace
Ni?
Shima dariyar yayi Cikeda jin dadi yace
Inasu Muhammad kirasu muje tare.
Komawa daki tayi ta fito dasu dama sunyi Alwala tace
Allah ya kiyaye.
Har ya kai kofa ya juyo yaga tana tsaye inda ya barta tana ta murmushi har wushiryar ta siririya ta bayyana, shima murmushin yayi mata tareda saka hannun shi ya mata alaman Taxo, babu musu ta isa inda yake tsaye tareda barin space kuma har lokancin murmushin take,
Addu'ar me zanyi miki idan nayi sallah.
Dan rolling idonta tayi tace
Naci exams.
Se ya bata fuska yace
Shikenan? Ni kuma fa
Cikin rashin fahimtar inda zancenshi ya dosa tace
Bansan me kake so ba ai.
Kanshi ya gyada yace
Shikenan
Daga haka ya fice abinshi, dariya tayi ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kitchen bayan ta cire Hijabin jikinta dama ba sallah zatayi ba , hakan yasa ta shiga suka karasa girkin itada su Atika dukda yawancin girkin su keyi ita supervising kawai takeyi se murmushi wanda yaki daukewa Daga fuskarta har Atika Tace
Saurayinki kike tunawa ne haka?
Hararar ta Sulaim tayi ta cigaba da aikinta seda suka gama sannan ta koma daki ta janyo wayarta da books dinta se kawai taga message din Ja'afar
_If at all I can turn the clock, I'll never have done what I did, I'm very sorry Susu for that day. Allah shi ne shaida ta I never intended to harm you..... Please sweetm I'm sorry and I love you! Another chance dear_
Iska me zafi ta furzar, tareda kife wayar tayi shiru Tana tunani yadda zatayi, to ya zatayi da Ja'afar hakura zatayi? Ko kuma me? Gashi yadda words din suka fita are so sincere Amma Kwana biyunnan ita kanta hankalinta ya kwanta amma matsawar Ja'afar ya dawo yanzun zai sake dagula mata lissafi. Se taji inama Za'a canza mata Ja'afar da Junaid, Junaid to her yanada komai da take burin samu inama inama.... Kawai se ta kwanta saman tiles din Tana ta juye juye abinta ta rasa yadda zata hada abin.
Yau kam Khulthum ba takai dare Ba, karfe hudu ta isa gida, Tana shiga ta samu se Mama kawai sauran duka basu nan. Seda ta gaida ta kafin ta shige daki tayi wanka ta shirya cikin wata atamfa tazo ta zauna kan daddumar data shimfida. Kallon Mama tayi tace
Mama jarabawa zamu Fara ranar litinin me Zuwa.
With lot of concern Mama tace
Allah ubangiji ya bada sa'a, yasa a dace
Amin Mama, Amira sun tafi makaranta ne?
Eh yanzu nasan suna hanya.
Kanta ta gyada ta Fara revising books dinta, Kwana biu cikin kudi take jin kanta don Huzaifa Yana sakar mata kudi daidai yadda ya dace ga Yusuf da ta hadu dashi yau, Architect ne a wani construction company gashi yana taking private contract wannan yasa yake da kudi shi ne abinda ya fada mata. Kallon Mama tayi tace
Anyi abinci ne?
Kai Mama ta girgixa tace
A'a yace Se ya dawo zai bada kudin cefane.
Allah ya kaimu
Ta fada Tana cigaba da karatunta. Tafi awa tana karatu sannan su A'isha suka dawo, Amira da kananan suka gaisheta, Ta kalli Amira tace
Duba cikin jakar da na fita da ita ki kawo min purse dita.
Tashi tayi ta dakko ta kawo mata,
Amir!
Meye ke kuma zaki ishi mutane?
Harara ta maka masa tace
Siyo mana macaroni uku da nama da kayan miya.
Ta fada Tana mika masa 1500.
Kowa Seda ya kalleta Cikeda mamaki itama kuma tasan haka zata faru amma tasan hakanne kadai zaisa abinda take shirin aikatawa. Mama kam farin ciki sosae ta dinga sawa Khulthum albarka, Aisha ana kawowa ta Fara aikin girki yaran se murna suke yau zasu ci nama wanda aka dade ba a hadu ba. Ana Idar da sallar maghrib Amir ya shigo
Khulthum tashi kije Ashir yana nemanki fa.
Tsaki tayi ta Mike don Tana son bin komai a sannu don Kada ta kwafsa. Bata wani canja kaya ba kamar yadda take duk lokacinda Yazo ta nufi waje, yana tsaye gefen Lifan dinshi wanda a yanzu take ganin shida gurgu basuda maraba. Ko gaisuwa bai samu ba ta tsaya tana jiran taji abinda zai fara fada, shima kallonta yake yana mamakin Khulthum wai wannan Khulthum dinsa ce yarinyar nan Itace idanunta suka bude har haka lallai yarinyar nan shi mamaki take bashi, Ashe mamaki yana gaba
Idan Bakada abin fada zan koma ciki.
Ta fada Tana nufar zaurensu, seda ta shige ciki sannan Amir ya fito ya tarar da Ashir wanda mamaki yake neman kasheshi a tsaye yace
Har kun gama?
Kanshi ya girgixa yace
Kayi min magana da Mama Dan Allah
Lapiya dai?
Kayi mata magana
Haka kawai yace dashi, haka ya wuce ciki ya tarar mama na tsaye kan Khulthum tana tambayarta dalilin da yasa ta dawo
......dama kwana biyu Naga take takenki baki daya tunda kika shiga makaranta halayenki ya canza kin koma wata iri........
Mama wai Ashir yana son magana dake .
Wani harara ta dallawa Khulthum sannan tace
Amira dakko min mayafi na.
Ana miko mata ta nufi gurin shi Khulthum tamkar zatayi bindiga a ranta tace
Lallai Ashir kana ganin wannan ce hanyar bullewa kada ka damu Dani kake magana.
Mama gefe guda ta zauna cikin mutunci da mutunta juna suka gaisa itada Ashir, nan ya fara fadin
Mama kiyi hakuri kila kina wani abun na katse miki aikinki
Babu komai dannan, inajinka
Dama akan Khulthum ne Mama, Dan Allah Inaso ki tambayeta ko akwai abinda nayi mata kwatakwata Kwana biu nan taki dadi kuma ni naga Tunda manya sun shigo ya kamata na sanar dake halinda ake ciki.
Se yayi shiru, itakuma tayi zugum seda ta tabbatar yakai aya tace
Da farko zan baka hakuri, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halunsu ba, Inshaaa Allah zan zauna naji matsalarta idan yaso se asan abinyi. Kadai yi hakuri.
Babu komai Mama kada dai kiyi fushi.
Dan murmushi tayi amma Lokaci guda ya dauke saboda jiyo takun Khulthum da tayi, kamar Aljannah saboda yadda tayi dolling fuskarta, Tana cikin wani royal blue paper lace da farin mayafi iya kafada tayi kyau har ta gaji abinta.
Ke gidan ubanwa zakije?
Mama ta tambaya a fusace, Nikam ina tunanin Wannan ne Karo na farko da Mama ta Fara fito na fito itada Khulthum, shima Ashir kallonta yake Baki daya idanunsa sun Kada sunyi jawur dayake ya haska gurin da wayarshi kirar Tecno hakan ya haska gurin Kake ganin komai daidai. Harara ta watsa mishi idanunta Cikeda tsana Tace
Mama bako Nayi fa
Ubanki Keda bakon kinji ubanki nace Marar mutunci yarinyar nan.
Baki ta turo tareda bubbuga kafarta a kasa, sannan ta ficewarta Mama na kwalla mata kira amma ko Waiwaye!
Turkashi!
Seda Subay'a tayi sallar isha'i sannan ta nufo gida dama kiran Ba wani abu bane wai kawai son ganinsu take. Seda taci abinci cikin yan uwanta kafin ta tuko motar ta hankalinta a kwance don tasan babu Abinda Junaid zaiyi mata Tunda da tace zataje bai musa ba. Tana parking a gefen motarshi ta nufo cikin gidan kafadarta rataye da jaka, se jakar system dinta a hannunta, Tana yin sallama taji Sulaim ta amsa mata karo na farko taji jin muryar Junaid ya fadar mata gaba, sosae gabanta ya tsananta bugawa tamkar wadda tayi bugun marathon haka taji, se kawai ta tsaya a gurin, Sulaim din na Sanye da wani shiny silk material dark purple da pattern na light purple a jiki, dinkin simple gown se mini veil da tayi rolling dashi dan Bata taba zama babu mayafi jikinta saboda wannan tarbiyyar mummy ce hade da Mami, ta rigada ta san akwai aure tsakaninta da Junaid so bata taba zama babu lullubi jikinta that's the rule. Tana dining tana jera plates da spoons yadda kasan Itace matar gidan, shikuma me gayya me aiki yana zaune kan carpet da books din Khulthum din Yana sake highlighting mata abubuwan da suka shige mata duhu, Sede Tunda ta tashi gaba daya yaji ya daina fahimtar Abinda yake karantawa, sukam su Ahmad suna ta wasa abinsu suna jin muryar Mamansu sukai kanta. Shigowa tayi idanunta sun canza kala baki daya taji Anya ba akwai Abinda yake Zaune ba a muhallinsa ba? Anya ba akwai Abinda yayi breaking along the line ba amma ta rasa Meye, taga kwata kwata Junaid baya damuwa da alamuranta kamar da, ko bata nan bai taba damuwa sannan Hana fitar da yake duka ya barta tana tambaya zaice Allah ya kiyaye to abin ya fara damunta, ta Fara zargin kanta da yin sake data bar Sulaim zama mata a gida.
The game is about to start..... Kowa Yana rike da hurdle let's see wanda zai cimma burinsa.
[7/17, 5:39 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU*
15
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Mama kasa fadin komai tayi ga matsanancin bacin rai da yake taso mata, Tamkar an dasa Mama haka ta tsaya ta kasa gaba Kuma ita Bata koma ciki ba, gashi Baki daya kunyar Ashir dinma takeji, mikewa yayi ba tareda ya sake furta komai ba ya wuce abinshi, to me zaice? Duk yadda yayi tunanin saiyawar khulthum ashe tunaninsa ya wuce hakan. Yana fitowa ya same ta tsaye gefen Yusuf se murmushi take tamkar bakinta zai yage, shima hakan ce gareshi Yusuf din, Bai Kara kallon inda suke ba dan surely zuciyarshi zata iya fashewa.
Kice dazun da muka hadu banga komai ba kenan?
Yusuf ya fada Yana sake Kare mata kallo, murmushi tayi tace
A hakan?
Ta fada tana masa wink, dan dariya yayi yace
Kice kada nayi underestimating dinki?
Bata kuma fadar komai ba hakan yasa ya canza topic da fadin
So kina ganin ban takura miki ba idan na turo iyayena, saboda gaskiya ni da gaske nake Kuma aure nake son yi I'm not getting any younger kullum girma Kara kamamu yake.
Gabanta taji ya Fadi,wani irin aure daga zuwanshi, gaskiya itadai she's not ready bata gama fahimtar halayenshi ba kawai se a fara zancen aure ita duk ba wannan ba bata shirya aure ba a wannan lokacin, Bata gama kashe kurar Ashir ba ita Bata San abinda zata tarar a gida ba don tasan dole Mama ranta zai baci.
Kinyi shiru ko Baki shirya ba?
Ya fada yana assessing fuskarta , Dan murmushi ta Kuma saki tace
Haba dai, kasan first semester nake level one so bazai yiwu ace daga fara karatu se aure ba, if you can be a little more patient na shiga level two Ina ganin Babu matsala.
Shima murmushi yayi bayan ya gama saurarnta se yace
Abinda Kika fada is in place, sede Ina ganin aure baya hana karatu kowanne Yana da matsayinshi what matters Shi ne Zan barki ki karasa idan munyi aure.
Wata dariya ta saki, a ranta tace
Lallai Kai har kana tunanin zaka barni ko aa ai ni ba irin wannan matan bace
Amma a fili se tace
A'a bana jinka zaka barni nayi Amma sede hakan Shi ne burina Dana iyayena.
Ganin ta dage yasa yace ya amince amma bawai yakai zuciya ba don ya fahimci auren ne baya gabanta Baki daya Kuma idanunta a bude suke. Sun Dan Kara taba Hira ya ciro katuwar ppaer bag daga back seat dinsa ya Mika mata, se farar leda, karba tayi ta mishi godiya daga haka ta mishi sallama se gida. Ko dar bataji ba don tasan Babu abinda zaayi mata.
A nutse ta shiga cikin gidan Mama na zaune Kan sallaya ta idar da sallar ishai baki daya abin duniya ya iaheta ta rasa yadda zatayi. Kada khulthum ta watsa musu kasa fa a ido? Saboda taga take takenta abinda take niyyar yi kenan. Tana shigowa daki ta nufa tana jin Mama Tana kiranta bata amsa se cewa tayi
Mama kada ki damu indai maganar Ashir ce kada ki saka baki.
Ni kaina nayi tunanin Mama zatace wani abu amma se cewa tayi
Khulthum idan zaka rabu da mutum ba ta haka ake ba, a hankali ake bin komai.
Aisha ce tace
Mama haka kawai Zaki fada? Mama bakwa kyautawa abinda kuke, Ashir Bai canci haka ba wallahi.
Khulthum dake daki ta leko tace
To uwata munafuka ke idan kina sonshi kije Zaki zauna kina gutsiri tsoma.
Aisha batace Mata komai ba ta mike don harhada kwanukan da akai amfani dashi. Mama shiru tayi Don tasan tabbas abinda Aisha ta fada gaskiya ne, is not in place bai dace ta fada haka ba Amma Babu yadda zatayi sede idon kawai.
***
Agogon dake daure kan tsintsiyar hannunshi ta Rolex ya kai duba, Tara na dare ta gota gashi goma daidai ya kamata ya tafi gurin da ya kamata Amma Babu yadda zaiyi wane Shi Gwoggo nasan ganinshi yaki zuwa, hakanan ya ja motar ya nufi asalin gidansu dake cikin unguwar kuntau a Kano. Makeken gida ne na alfarma tun daga gate din zai tabbatar maka da kudi ya zaunawa masu gidan. Bude mishi gate akayi ya shiga ciki yayi parking sannan ya fito Yana amsa gaisuwar masu gadin gidan. Tamkar rana haka yake saboda yadda ko Ina yake a haskake, parlon ya nufa tana zauna kan kujera gabanta an aje mata mug cikeda tea Akan saucer, matar ta manyanta sosae sede yadda take cikin Jin dadi bazai nuna manyanta tata ba. Gefenta daga kasa ya zauna cikeda girmamawa yace
Gwoggo barka da dare
Seda ta gama kallonshi a tsanake ta kurba tea din sannan tace
Barka ka dai Musbahu.
Kanshi ya sunkuyar gabanshi Yana faduwa don baisan abinda yasa take nemanashi ba, itama ta Lura da hakan shiyasa tace
Dama na kiraka naji yadda muka tsaya Akan zancen auren ka, Musbahu wannan karo na nawa ne Ina yi maka magana?
Kanshi a kasa dama jikanshi ya bashi maganar kenan hakan yasa yayi shiru seda tace
Bakaji tambayar tawa ba ko?
Girgiza kanshi yayi yace
Bazan iya irgawa ba.
Good
Ta fada kafin ta sake kurbar tea tace
Mata nawa na kawo maka ka nuna min you're not interested in them, daga kace wannan se kace wancan don haka kayi marking date din yau a matsayin Rana ta karshe da zan Kara daga maka kafa, watanni biyar kawai na baka ka kawo min Mata Shima don na fitarda hakkin ka ne Amma banda haka wallahi da da kaina Zan baka mace.
Kanshi a kasa har lokancin a ranshi Yana fadin to ai akwai Lokaci kenan, shifa bawai aure ne bayaso ba kawai dai bai taba ganin akwai abin burgewa a jikin 'ya mace ba balle har yayi Sha'awar su shi a iya rayuwarsu zai iya counting matan da yayiwa magana dasu a girman shi yanzun hakan zai iya kirga matan da yayi mu'amula dasu shima don dole ne don ita kanta Gwoggo Tasha sawa ayi mishi addu'a don tunaninta ko aljana ce ta aureshi amma shiru babu sauyi.
Inshaaa Allah Gwoggo kafin lokacin zan kawo miki.
Kanta ta gyada tace
Zaka iya tafiya.
Take ya Mike kuwa yayi mata sallama don Dama a takure yake sosae, shikam haka ya tashi cikin tsananin tsoron mahaifiyarshi kuma har yanzun daya girma Bata canza zani ba saboda baya mantawa kafin rasuwar mahaifinshi yana yawan mata fada akan ta daina irin takura mishi.
Musbahu yana fitowa ya sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda sake kallon agogon hannunsa, it's almost time hakan yasa ya figi motar ya fice baki daya daga harabar gidan, a motar ya Kira babban amininshi na hannun dama Kabir Seda suka gaisa sannan ya sanar mishi yadda sukai da Gwoggo,
Ina ganin ya kamata kayi hakuri kawai kayi aure Tunda Naga Gwoggo da full force Taxo
Kabir ya fada, sake dafe steering yayi yace
I thought of that nima, amma ta yaya zan fara neman mace idan naje ya zanyi?
Dariya sosae kabir yayi har ya kusa batawa Musbahu rai, sannan yace
We'll talk about it later, kadai kayi amfani da damar ka ta Daren yau.
Dariya sukai sannan sukai sallama.
***
Cikin tsantsan Subay'a ta karaso parlon yaran sun rike both hands dinta, Tunda ta shigo idanunta Ke kan Sulaim wadda ta cigaba da Abinda take tamkar bata ga shigowar Subayan ba, gefen Junaid ta zauna tareda fadin
Papa na dawo.
Ta fada Tana shafa Fuskarshi, Allah ya taimaka shugabar kishin duk duniya wato Sulaim bata lura ba Don hankalinta yayi nisa kan shirya dining Sede itama a ranta taji babu dadi tana ganin kamar Subay'a din wata barrier ce tsakaninta da Junaid. Shikam Junaid hannunta ya rike tareda nuna mata su Ahmad yace
Barka da dawowa.
Se ya Mike ya nufi dining din, yana zama Subay'a ta taso ta zauna gefenshi tareda janyo plate ta Fara serving dinsa, Sulaim na ganin haka ta zuba nata ta bar gurin Zuwa dakinta, saboda gani tayi Subay'a ta Fara bashi abincin cikin baki tasan matsawar ta zauna a gurin zuciyarta fashewa zatayi, da taje dakinma saka abincin tayi a gaba tana ta kallo Baki daya farin cikin da take ciki ta nemeshi ta rasa, a hankali ta aje spoon din