Showing 30001 words to 33000 words out of 131263 words

Chapter 11 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4628

for your eyes.


Kit! Ya yanke call din, Cikeda zumudi ta Mike ta zaro wani plain lace peach zani da riga, se kuma ta mayar ,ta janyo Abaya ash da silver stones se off white lace da aka saka a edge din hannun da kasan Riga... Rolling tayi da veil din kayan ta fesa turare sannna ta dauki wayarta ta fito anan sukaci Karo da Atika


Uwardakina Kinyi kyau, ina zuwa haka?


Sa ido yanxu zan dawo


Har ta tafi ta isa bakin parlour Se ta tsaya da gaske Ja'afar take wa wannan zumudin ko kuwa? What if idan Junaid ya dawo suka hadu Don ta dan Lura baisan tarrayar su? Tayi kusan 7 minutes kafin zuciyarta tace mata go shi matarsa Ya dauka suka fita, se ke xa'ayi caging a hanaki. Da Wannan ta samu karfin gwiwa ta fita, megadi na zaune Tace dashi


Baba Bari na karba sako


Bata jira me zaice mata ba ta fice, Itakanta bata taba ganin motar ba tana tunanin ya sake mota ne, Tana isa inda yake ya bude mata ta fada Ciki ,tana rufewa ya ja motar with full speed ya bar layin. Da mamaki tace


Yaya Ja'afar what are you doing?


Dariya yayi mata yace


Kin manta a kd kika ki bina kisha ice cream shi zan kaiki kisha yanzu.


Dan Allah don't do this kaga yaya bai sani ba Kada ya dawo bananan.


Bai kara kulata ba itakuma Bata fasa Yi masa magiya ba amma yayi iskar kare da ita, hakan ya tayar mata da hankali.


A gida Junaid da Subay'a sun dawo, yana gama parking megadi ya sanar mishi Sulaim anzo an dauke ta a mota kuma baisan waye ba.


Bakasan waye ba? Ni Kake cewa baka san waye ba?


Ya fada Yana nuna kanshi tareda nuna kanshi wanda hakan seda yasa megadin firgita, hatta Subay'a mamaki tayi yadda ya Daga murya ashe basuga komai ba.


Gidan ubanwa ka barta ta fita? Wayace ka barta ta fita?


Subay'a ta matso zata rike hannunshi ya juya kanta


Don't you dare touch me.


Se taja baya saboda yadda ta tsorata da yanayinshi, Ya dinga masifa wadda tasa baki daya veins din kanshi suka tashi, yayi yayi se kuma yayi shiru ya dinga safa da marwa yana karkada kanshi, baki daya kwakwalwar kanshi ta cushe waye ya fita da ita? Ina kuma taje?


Ganin yanayinsa yasa na aje wayar haka kada nima yar rahoto ya make ni! Lol...... Waye zai bawa Junaid ansa NE? Ya haduwar Sulaim da Junaid zata kasance? Me Ja'afar ke planning yi kadafa yayi!


Shatuuu♥️


[7/1, 8:57 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
11


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣shatuuu095@wattpad


Yaya Ja'afar shi ne soyayyar? Shine son da kake ikirarin kana yimin? Where are you taking me to?


Ta fada mishi muryarta na shaking abu kadan take jira tayi breaking , bai kalleta ba se tukinshi da yake saboda shi ba wani abu yayi niyyar yi mata ba amma abinda ya bata mishi rai yadda take nuna bata yadda dashi ba kwatakwata, Tana nuna zaici wani abu ne daga gareta. Kafin wani Lokaci temper ta Fara building within him hakan yasa yayi wani wawan reverse ji Kake kiiiiiiiii! Ana taka burki Allah ya kiyaye babu wani da yake gaf dashi don da tuni labari yasha banban. Ihu Sulaim ta saki ganin Abinda Ja'afar yayi kafin wani Lokaci baki daya jikinta ya fara rawa kamar wanda aka saka mata mazari.


Mummy! Daddy! Baba! Mami! Yaya Junaid!


Shikenan sunan da take ambata, wani Irin gudu yake fallawa idan ka gani zakayi tunanin kodai yasha ta kada masa karya, kodai titin danshi kadai akayi ko kuma bashi da hankali. Tunda Sulaim take bata taba tsintar kanta cikin madaukakin tashin hankali kamar wannan ba. Jin ya taka burki yasa ta bude idonta Wanda hawaye ya bata su, hannunta tasa da sauri Zata bude ba tareda ta duba ina bane ita kawai tsira take nema. Lock ya danna wanda yasa ta dubeshi da sauri tareda kwalalo masa idanunta da sukayi ja waje.


Is not like zan cinye ki ne, saboda banga abinda zai tayar min da hankali akanki ba, idan I wanted an affair with you ba ta haka zan biyo ba.... Rubbish!


Ya gama fada Yana jan tsaki, cire lock din yayi da sauri ta bude kamar an hankado ta ta fito a guje se taga Baifi 70 meters bane away da gidansu hakan yasa ta nufi gidan da sassarfa sede Tana kama handle din gate din da niyyar rufewa taji gabanta ya fadi saboda idanunta sun sauka akan motar Junaid. Megadi ne ya taso da hanzari yace


Ina kikaje Alhaji Yana ta nemanki?


Gabanta taji ya kuma faduwa jin ya ambaci Alhaji, shi kenan itada Junaid se Allah yau, Bata bashi amsa ba ta wuce ciki kanta a kasa gabanta nata faduwa, a parlon babu kowa ba yadda tayi tunani ba, don haka da sauri ta nufi dakinta Sede ta na daura hannunta Kan handle din taji wannan deep voice din tashi yace


Daga ina kike.


Yadda ta Juyo a kidime seda wayarta ta fadi kasa, dagowa tayi ta dubeshi Yana tsaye Fuskarshi babu annuri ko digo, se ya zame mata tamkar ta zaki hakan yasa ta kasa furta komai se wasa da take da yatsunta


Se na maimaita kenan?


Nida yaya Ja'afar muka fita.


Da izinin wa?


Se tayi shiru Tana son ce masa tayi mishi text Amma babu Wannan halin saboda lokacin da taga da gaske bazai saurareta ba ta turawa Junaid short message, Tana tunanin yadda zatayi taji ya dauke ta da wani gigitaccen mari! Dagowa tayi a rikice ta fito da idanunta waje Cikeda mamaki kafin kuma ta rike gurin saboda zafin da taji, shima se ya tsaya Yana kallonta Cikeda mamakin Abinda yayi, he slapped her? Sulaim? Seriously? Itakam lokacin hawaye sun Fara mata zarya saman kuncinta saboda tsabar zafin da zuciyarta keyi, yana ta jujjuya Hannunsa Wanda yayi Marin dashi, ta shige dakin ta durkushe ta saki wani Irin kuka me taba zuciya! Dafe kanshi yayi saboda yadda yake Sara mishi ya nufi dakinsa ya zube saman gado ya lalubo wayarshi ya fara neman layin Ridwan kamar jira yake a kira ya dauka yana fadin


Angon Sulaimi Baban Ahmad da Muhammad!


Cikin wata Irin murya me Cikeda rauni yace


I slapped her! Marinna nayi ya zanyi?


Cikeda mamaki yace


Wa ka mara? Subay'a


Kanshi ya girgixa Don wannan lokacin yana jin inama ace Subay'a yan mara yana ganin da bai shiga halin da yake ciki yanzu ba. Cikeda nutsuwa ya kwashe komai ya fada masa, ya kara da fadin


For the first time zuciya ta dauke ni na daki abinda take martabawa take ganin mutunci take kuma so sannan take tattali, ya zanyi Ridwan? I'm in a mess Wallahi.


Ajiyar zuciya me nauyin gaske Ridwan ya sauke yace


Aikin gama ya gama ka zartar da hukunci cikin fushi, ba halinka bane Amma kishi ne. Ina ganin ka bata space zuwa safe muga yadda zata tashi.


No! I'm going to Appolgise yanzunnan.


A'a Kada ka sake kamar ba namiji ba, zancen gaskiya Sulaim tayi laifi fa, hukunci kayi mata a matsayinka na brother not suitor, so ka barta.


Da kyar ya shawo kanshi ya amince da hakan saboda yana ganin kamar wannan zai saka ta tsaneshi. Yana aje wayar yaga alamar sako a notification plate dinshi, yana shiga yaga Daga Sulaim ne ta turo masa 3 hours ago


Yaya... Ya Ja'afar yazo zan Yi mishi rakiya Bazan jima ba


That's all the content of it, gaba daya se yaji hankalinsa ya kuma tashi, me yasa zaiyi fushi ya Mari Sulaim? Kansa ya dafe wanda yayi masa nauyi ya kwanta kan gadon, Yana kwancen Subay'a ta shigo cikin kayan baccinta silk very sexy and attractive, Tunda ta shigo take kallonsa Amma baisan ta shigo ba saboda yadda yake deep in his thoughts, kallonshi take tayi zuciyarta tana hana mata abinda take zargi, Kwana biu ta Fara zargin Anya Junaid ba son Sulaim yake ba, ko Abinda yayi dazu abune da bata taba gani ba, amma yadda Lokaci daya ya birkice kamar zautacce shi ne yake daga mata hankali, kada ya kasance tana zaune ayi mata manakisa. Haka ta rungumeshi tare da fara bashi wani sensual and seductive kiss, cikin sanin bukatinshi ta Fara sarrafa shi, kafin wani Lokaci ya bada Kai tareda mantawa da existence din wata mace na iya wannan lokacin .


Baiwar Allah Sulaim ta sha kuka ta godewa Allah se taji gaba daya alhakin komai akan Junaid ta saukeshi, tamkar he caused everything dinnan haka take ji. Tana nan kwance bacci ya dauketa haka tai tayi Marar dadi tana ta ajiyar zuciya. Kafin asuba har ta tashi tayi dukkan abinda zatayi ta shirya tana ta tunanin yadda zata bullowa Junaid, ita bata kawo Ja'afar a ranta don batada lokacinsa se ta gama da wanda zuciyarta ta fi karkata a kai kafin ta dawo kanshi. Idan ta tuna Yaya ya mareta se hawaye ya fara jika mata fuskar hakan yasa kanta Fara mata ciwo sannan idanunta suka dan tashi wanda zai nuna ma kowa kuka tayi. Bakwai daidai dan aike Ahmad ya shigo a guje Tana zaune kan gado ta hada uban tagumi Lokaci daya tayi rama se swollen and sunken eyes kadai kake hanga a fuskarta.


Anty Papa yace kizo Aci abinci!


Tohm..


Ta fada hakan yasa ya kyaleta ya tafi amma har Junaid suka gama cin abinci bata fito ba hakan ya kara tayar masa da hankali ya sake daura dukkan alhakin komai a kanshi, Subay'a ce ta Fara fita itada Ahmad se Junaid ya dauki wayarshi ya kirata amma har ta katse Sulaim batai picking ba, Yana kokarin sake kira ta fito fuskarta babu walwala ko digo, da idanunshi da suka fada ta Fara arba, ya tsareta da ido da wannan sharp gaze din nashi, se taji ya kuma takurata amma haka ta iso gareshi Cikeda dasasshiyar murya Tace


Na fito


Kamar yace ta zauna taci abinci Se ya share ta don yaga kamar a takure take kuma bata sakko ba har lokancin. Ko a motar ko uffan ba tace mishi ba shima bai ce mata ba se lokaci Zua Lokaci yakan kalleta itama satar kallonshi da takeyi da yau ko kallo bai isheta ba. Haka sukai tafiyar so boring ga zukata na wahaluwa. Lucky enough Mami ta kira Junaid da suka gaisa ya bawa sulaim se lokacin ta dan ware sukai magana Harda murmushi.


I'm sorry kui manage yau din se a slow nasan yayi kadan amma better hakan than ace babu baki daya. No one is missing Khulthum NE? Haba kukuwa at least ask about her ko taji dadi.


Shatuuu ♥️
[7/4, 7:08 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*


12


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Duk yadda ka dauki rayuwa to a haka rayuwa take zuwa maka, idan ka dauke ta simple to kullum zaka ganta a saukake amma idan ka matsa ka kuma zafafa to tabbas haka zaka gani. Haka rayuwar take ga Khulthum taki tsayawa inda ya dace ta rungumi yadda rayuwar ta take sede yadda take ganin anayi, yadda wasu Ke yin tasu lifestyle din hakan nan itama take son tayi. Gashi yadda take ganin Sulaim, Aimana da Khairi babu Saar ta a ciki kana kallonsu kasan Daga wanne gida suka fito, komai nasu acan acan to itama tana son meeting up to their level kuma da taemakon Huzaifa dreams dinta basu zama shattered ba. Ya maida ita babbar yarinya yar gayu yar kwalisa, Dama ya lafiyar kura bare tayi zawo, girman kai se ya karu cigaba yaci uban na da.


Ranar ta kasance Thursday, da sassafe ta kammalla komai tayi wanka ta zauna ta tsantsara kwaliyya wadda idan ka kalleta zaka rantse zata je gurin biki ne saboda yadda makeup din ya hau babu karya. Tayi kyau kamar ka saceta. Trolley dinta ta bude ta janyo skirt pencil din wanda ya kamata ga tsaga a kasa har wajen kaurin ta Baki ta saka sannan ta dauki farar top ta daura me long sleeve kafin ta janyo bakar suit coat ta daura akai baka, wig dinta ta dakko ta taje shi sannan ta fixing akanta, se data gama daidaita zamanshi kafin ta kalla large mirror din data kafe a dakin, murmushin jin dadi tayi sannan ta samu farin veil tayi wrapping kanta dashi sannan ta saka wani pointed high heel peep toe shoe fari ta zura a kafarta ta daure da igiyoyin jikinshi. Tayi kyau ko mahassadi ya san haka sede shigar is more of zuwa wani biki ko wani taro not professional Abu. Back pack me kyau Fara da adon black a jiki qaddararsa taga ana yayi ta zura books dinta sannan ta saba a baya ta fito hannunta rikeda wani karamin veil wanda zata yafa saboda yan layi amma tana shiga school se de wani kuma.


Aisha na durkushe gefen murhu tana ta hura wuta da bakinta saboda yadda maficin ya yagalgale Bana tunanin zaifi bakin nata hurawa, idanunta sunyi ja saboda hayaki. Mama kuma na gefe tana ta fada akan bata tashi da wuri ba gashi har Khulthum ta fito abinci bai Gamu ba. Iya wuya Aisha ta Kai saboda idan akwai Abinda ta tsana bai wuce Irin yadda Mama take ba. Zata iya Rantsuwa tun dawowar Khulthum gidannan Bata taba moruwa ba amma komai Mama sede Tace ayi mata komai saboda Khulthum saboda jin dadinta Amma babu Wanda ta raina take wulakantawa kamarsu. Tundaga nan Aisha ta Fara jiyo Sautin takalmin Khulthum, Bowed down Khulthum ta fito bakinta tana taunar chewing gum tace


Mama zan tafi se anjima.


Kallonta Mama tayi ta ciro five hundred daga habar zaninta ta mika mata tace


Baki ci komai ba zaki fita? Sannan yau ki daure kada kikai maghariba a waje yarannan kullum Se yazo, kudin motarki yace a baki


Wannan routine ne Tunda ta Fara zuwa BUK Baifi sau hudu bane kawai Ashir ya tsallake Bata transportation fee ba, amma she never appreciate that effort of his sede kullum cikin ganin gazawarshi take tana ganin me 500 zatayi mata? Kunji fa! Seda ta dubi inda Aisha take tana kallon ta ya mutsa fuska tareda zabga mata harara saboda Tunda sukai wannan damben har yau basu shirya ba harara kawai ke hadasu nothing less and nothing more.


Zanci a waje.


Kanta ta gyada kawai tana son ce mata ta canza skirt amma babu fuska, hakan yasa tace


Zancen Ashiru fa?


Dan murmushi tayi ta cigaba da tafiyarta Tace


Zamui magana dashi.


Daga haka ta fice Seda tazo daidai inda Aisha take tace


A cigaba da girki, jakar gida.


AI kuwa A'isha ta harzuqe tace


Kece jaka Wallahi wayasani ma Maza kike bi ba makaranta ba.


Khulthum ba ta jita ba amma Mama ta jita ranar kuwa seda ta raina kanta.


Motoci na wucewa da hanzari kowa Yana son reaching destination dinsa, Khulthum na tsaye gefen titi Tana ta bin motocin da suke wucewa da kallo a ranta tana tunanin inama ta wawaso zuciyar wani, tunanin hakan yasa ta gyara tsayuwarta tana dan karkada jiki yadda zata jawo hankali, aikuwa babu jimawa wani azababben guy cikin azabbabiyar bakar mota ya parka gefenta tareda wining glass kasa yace


Kyakyawa kamarki Bata cancanci dukan rana ba.


Murmushi me kyau tayi Wanda duk wanda akayiwa se zuciyar shi ta kwaidaitu da burin kasancewa tareda me shi. Lumshe idonsa yayi yace


Idan da kinji yadda tsayuwarki gurinnan take taba ni ina tunanin da ko second Baki kara a waje ba.


Kalamanshi sunyi mata dadi, motarshi me kyau kamar yadda yake me kyau bata wani ja ba tayi wa kanta masauki gefenshi, Tana rufewa yaja suka tafi, shima suit ce jikinsa. Suna tafe Yana bata labari yayinda take amsa mishi da Mhm, a'a ko Eh saboda dole taja class dinta. Seda ta sanar dashi inda zai kaita kuma baiyi kasa a gwiwa ba ya kaita har kofar Faculty ya amshi numbers dinta yayi storing cikin wayarsa sannan ya wuce, Baki daya ta kasa rufe bakinta tana ganin tafi kowacce mace sa'a a Wannan ranar, irin mazan da take so kenan sune taste dinta Amma me zaayi da Ashir wanda kyauta baya iya yin ta dubu Daga 500 shikenan.


Tana nan tsaye Sega Khairi da Aimana sun fito Daga class, inda suke ta nufa tana binsu da kallo, kowacce cikinsu tana cikin abaya yar gaske me Tsada ,khairi tata fara ce tayi rolling Baki itakam Aimana baka tasaka all through se jikin veil dinne akwai Polk dots na fari, fuskarsu babu kwaliyya Daga powder se lip balm akai amma sunyi kyau, a ranta tace kudi kenan da Hutu Shiyasa Baku kwaliyya don kunsan no matter how you look zaku samu miji mu kuwa seda ita.......... Wannan shi ne perceptions din wasu mata not all but many na ganin se kayi kwalliya zaka samu miji, ba haka bane hasalima wani bayason kwaliyya, is not that ki fito kamar jaka a'a but powder, khol da balm a lips is OK, amma too much foundation, powder, concealer da sauransu Yana altering skin integrity saboda dukkansu chemicals ne.


Baza'ayi class bane


Ta Tambayesu lokacinda suka iso inda take, Aimana ta kalleta babu Abinda ta tsana kamar kwaliyyar da Khulthum take, har yau ta kasa banbance meye matsalar Khulthum ne idan ka ganta kamar ta waye amma ko oho. Khairi mutuniyarta tana washe Baki tace


Kinyi kyau matar handsome in a flashy car.


Dariya Khulthum tayi tace


Allah ya karba bakinki yanzu na hadu da wani azababben guy har nan ya kawoni.


Dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login