Showing 42001 words to 45000 words out of 131263 words

Chapter 15 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4604




What a nice name baby. I'm Salim


Daidai bude motar da shigowar Junaid idanunshi bai sauka akan kowa ba se akan Salim, wani Irin mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce shi Lokaci guda, bai gama dawowa daga wancan shock din ba gashi yazo ya tarar da wani, shikam wanne irin abu ne yake faruwa dashi daga wannan se wannan kada yarinyar nan ta fasa mishi zuciyarshi.


Sulaim Bata Lura da halin da Junaid yake ciki ba amma gaban ta se faduwa yake, Salim ya juya ta side din da Junaid yake ya bashi hannu tareda fadin


Barka da Rana.


Batareda ya kalleshi ba yace


Barka ka dai.


Daga haka ya sakar mishi hannu ya bawa motar key, tamkar a bye pass haka ya dinga sharara gudu Fuskarshi tamau tamkar bai taba dariya ba, itakuma taki dagowa bare taga yanayinshi. A haka suka isa gida yana parking yace


Get out!


Da sauri ta kalleshi idanunta a waje Tana son tabbatar da Junaid ne ya fadi hakan? Shi dinne yana kallonta da idanunshi yayi jawur wanda ya Kara tsoratar da ita


Are you deaf? Get out of my car stupid kawai.


Maimakon tayi yadda yace se hawaye ya fara zubar mata Daga idanu, ita me tayi mishi, ita tace kada ya kalli gabanshi while driving zai zo ya huce a kanta, shima se ya tsaya Yana kallon ta, gaba daya se yaji duka hankalinshi ya tashi why will he shout at her? Bakin hijab dinta tasa ta goge fuskarta sannan ta bude murfin motar ta fito, stupid kwakwalwar ta ta maimaita mata, se hawaye suka kara sakko mata a kunci. Dama Batayi expecting kowa ba a parlon haka kuwa babu kowa Don haka straight dakinta ta nufa tana shiga ta maida kofar ta rufe sannan ta kifa kanta ta Fara rera sabon kuka, ita ba tsawar da yayi mata bace damuwarta a'a fushin da taga yayi shi ne matsalar ta.


Cikin mota Junaid na zaune yayi clutching fist dinsa kamar wanda yake naushin wani, why zai dinga tufka and wasu suna warware masa? Se yaji zuciyarshi na fadin you're selfish Junaid, Kace kana sonta ne? Tanada magic ne da zata karanta abinda Ke zuciyarka? Wani dogon ajiyar zuciya yaja sannnan ya bude motar ya fito ba tareda ya koma takan Pizza dake Bayan seat ba.


Misalin karfe takwas da rabi na Daren wannan ranar Sulaim ta fito don tasan tabbas an gama abinci kuma tunda tayi masa laifi is better ta fita basai ya tura kiranta ba saboda gaba daya ta dauki alhakin komai ta daura akanta dukda batasan takamaimai Abinda tayi mishi ba amma yadda yayi dazu tasan tabbas ita taja komai.


Gefen Ahmad ta zauna Bata kalli inda suke ba dukda yana ta taba ta amma bata biye mishi ba saboda Junaid baya kan table din kuma yaranshi da matarshi har sun Fara cin abinci hakan ya bata clue din he's not eating. Plate ta janyo ta dauki slice din Pizza daya ta saka sannan ta tsiyaya tea ta Fara sha amma hankalinta sam baya kan abincin don taste din ma Bata jin dadinshi, hankalinta Baki daya yana kofar parlour Junaid. Har kowa ya tashi tana nan Zaune kuma bata cinye slice daya ba. Har Tara da rabi tana nan Zaune Bata san jiran me takeyi ba tadai San ta kasa tashi ta tafi, Baki daya tana jinta a takure Tana jin akwai Abinda is not in place, it doesn't supposed to be.


Yana kwance yayi nisa da aikin da yake cikin system Subay'a ta shigo ta zauna gefen shi tareda kai hannunta saman kanshi tana shafawa a hankali sannan tace


Dinner is set.


Dago kanshi yayi ya kalleta tayi kyau sosae saboda Dama ita ma'abociyar kwalliya ce, hannunta ya rike yace


Inada aiki sosae se Zuwa anjima kawai kije kuci, zan ci nawa


Shikuma ya fadi hakan saboda yana avoiding haduwarsu shi da Sulaim ne amma yunwa yake ji, kanta ta gyada batareda ta ce komai ba ta Mike Don ficewa yace


Dear, kice Sulaim ta fita taci abinci kada ta kwanta haka.


Da sauri Subay'a ta jiyo jin Abinda ya fada, tsira mishi idanu tayi ta koma inda ta tashi ta xauna tace


Junaid meye tsakaninka da yarinyar nan.


Kallonta shima yayi baiji komai ba kuma Abu daya ne zai hanashi ba ta amsa for Sulaim's well-being idan ba haka ba da se ya bata amsa daidai tambayarta.


Me kike cewa?


Ya fada Yana kallonta straight cikin idanu


Kaji abinda na fada ai, Meye tsakaninku kake mata wannan extraordinary kulawar, Junaid sonta kake?


Tsaki kawai yayi ya cigaba da aikinshi dukda tambayar tata tazo mishi a bazata saboda bai taba expecting zata dago shi ba amma akwai Abinda Junaid bai sani ba ko minti daya sukai tareda Sulaim a gurin mutane definitely se an dago su to balle Subay'a wadda Ke tare dasu kullum dukda batada fahimtar abu sosae sannan ba ta cikin mata masu saka ido akan mazajensu. A fusace ta fice shi kuma ya dafe kanshi Yana sauke ajiyar zuciya a gaggauce kamar wanda yayi kuka, ya dade kafin zuciyarshi ta nutsa sannan ya cigaba da aikin da yake daidai da Lokaci daya Sulaim Bata bar zuciyar shi ba, fuskarta kawai yake hangowa tana kallonshi lokacin da yayi mata tsawa, sannan kunnuwanshi nayi mishi amsa kuwwar kukanta kamar an tsikare shi ya Mike bai ma duba time ba ya fito Zuwa parlourn ga mamakinshi tana zaune kan dining din tana ta juya tea din dake cikin mug kana kallonta kasan itadai tana gurin amma tunaninta da hankalinta duka suna wani wajen, har ya zauna batasan yazo gurin ba seda kamshin turaren shi yayi awaking dinta.


Seda ta kwantar da yaranta kafin ta kwanta gefensu ita ba kullum take Kwana dakin miji ba ranar da abin nata ya motsa zataje shima se ya zuba mata ido, wayarta ta janyo ta Fara neman layin Sulma cikin sa'a ta shiga kuwa amma har ta katse Batayi picking ba hakan yasa ta kara kiranta wannan karan tayi picking


Sister Kin duba agogo kuwa goma tayi fa, ina fata lapiya?


Sulma ta tambaya


Inafa lapiya sister?


Me ya faru ni uwar Amna


Dan tsaki Subay'a tayi tace


Ina yarinyar da nake gaya miki tana karatu a gidanmu?


Shiru Sulma tayi tana son tunawa kafin can tace


Yarinyar nan wadda iyayenta suka rike Papa?


Da sauri Subay'a Tace


Ita fa, sister Junaid sonta yake!


So!? Haba dai Sister wanne irin so kuma?


Wallahi ba wasa nake miki ba, walahil azim sonta yake.


A'a dai Sister sede idan baki lura ba ta yaya Papa zaiso wannan yarinyar? Kede kawai insecurities ke damunki amma da Papa zaiyi aure ai da tuni yayi, Dan Allah ki fitar da hakan daga zuciyarki babu wani abu. Amma ke how sure are you?


Hawayenta ta goge tana jin haka ne kuma tabbas insecurities Ke damunta Tunda tasan Junaid ba tsoronta yake ba idan har yana son yarinyar da da ta tambayeshi se ya fada mata koda zatai Meye ne.


Yana bata kulawa wadda ta wuce gaban misali


Shikenan? Karki manta yarinyar marainiya ce kuma batada kowa se su idan basu kula da ita ba yakike so suyi. Kiyi hakuri sister ki kwantar da hankalinki Zamuyi magana da safe Abban Amna Yana jirana.


Babu yadda Subay'a zatai haka sukai sallama ta koma ta kwanta zuciyarta kamar zata fito ga wani kululun abu da ya tokare mata makoshi amma ta kasa Miqewa ta sameshi.


Yana zama ta Mike Don komawa daki Amma cikin gaggawa yace


Koma ki zauna


Babu yadda zatayi haka ta zauna Tana jujjuya fork din data dauka, bai kara ce mata komai ba ya dauki tea ya kai bakinshi Yana Sha yana dubanta se lokacin ya fahimci kuka take. Tsaki yayi Wanda yasa ta dago idonta tana kallonshi tareda fadin


Yaya kayi hakuri


Shuru yayi ya aje mug din hannunshi tareda runtse idonshi, Sulaim is not helping matters kara tabarbara komai take idan ba haka inhar tasan yadda kukanta yake dukanshi baya tunanin zata yi Koda fushi balle takai ga yin kuka.


Is ok, tashi kije ki kwanta.


Kanta ta girgixa Tana share hawayenta Tace


Kuma fushi kakeyi fa, ni bansan Meye nayi maka ba


Kinsan bana son musu ki tafi daki.


Haka ta Mike ina mamakin kukan me takeyi, seda ta shiga daki kafin ya dafe kanshi, inhar ya cigaba da haka tabbas zuciyarshi ta gaji da boyewa, he's tired ya kamata yayi uncaging zuciyarshi ya sanar mata amma yana ganin kamar Lokaci baiyi ba, Yana ganin is too early hakan ya kasance.


Washegari karfe bakwai Sulaim ta fito da books dinta tayi bak yard din gidan inda nan ne window din Junaid yake ta zauna kan kujera dake aje a gurin ta Fara karatu Tunda jiya Bata samu tayi ba batasan se su Khulthum sunzo ana karatu tayi kirikiri. Tayi zurfi sosae cikin karatun taji muryar Junaid Daga dakinshi Yana fadin


Ya zanyi Ridwan na rasa tattaro karfina Naje, ina ganin kamar Lokaci baiyi ba.


Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take, se can wayarta ta Fara ringing tana dagowa taga Junaid dinne, Seda gabanta ya fadi kafin ta tattara courage din ta dauka kafin ta gaisheshi yace


Ina kika je


Kallon gurin tayi tace


Ina backyard karatu nake


A hankali ya sauke ajiyar zuciya yace


Ki dawo ciki.


Bai jira amsarta ba ya kashe wayar sannan ta tattare books dinta ta nufi cikin gidan, suna zaune a parlour suna kallo, ta zauna a gefe tace


Yaya ina Kwana, Anty an tashi lapiya?


Lokaci daya suka amsa mata, Subay'a Tana ta binta da ido tamkar tana son gano wani abu a tattare da ita, haka ta wuce daki tayi wanka ta shirya cikin gown ta material sannan ta zauna gefen gado ta dauki wani picture dake jikin wani kyakyawan frame ta kalla tana shafawa idanunta sun cicciko da kwalla, hoton Daddy da mummy ne suna murmushi sosae, da na kalli hoton tabbas Junaid da Baban Sukam yake kama tamkar yayi kaki haka suke. A hankali ta furta


Allah ya jikanku ya rahmushe ku.


Kafin ta aje ta dauki wayarta ta turawa su Khulthum address din. Tana nan Zaune ta dauki wayarta ta kunna data ta shiga Wattpad don debewa kanta kewa, dake bata iya karatun Hausa ba yasa yawancin novels din library dinta are English. Wani a ciki ta Fara karantawa kafin wani Lokacin har hankalinta ya kau Daga tunane tunanen da take. Atika ce tayi sallama ta shigo tace


Anty Sulaim Kinyi baki a parlour.


Da sauri Sulaim ta Mike ta fito fuskarta kamar gonar auduga Don murna she can't believe cewar su Khulthum ne, ai kuwa su dinne suna Zazzaune Khulthum tana ta kalle kalle, kujera ta samu ta xauna Tana fadin


Sannunku da zuwa har nayi fushi.


Khairi ta maka mata harara tace


Ke kika sani dai


Dariya sukai sannan suka gaisa tace


Muje ku gaisa da Anty Subay'a.


Tashi sukai suka bi bayanta har parlon Subay'a Tana zaune itada su Ahmad tana koya mishi two letter words, dago idonta tayi tana kallonsu fuskarta kamar kullum har suka zauna suka gaisheta ta amsa musu sannan suka Mike suka koma dakin Sulaim inda Atika ta cika musu gaba da abinci da drinks seda suka ci suka sha ana hira sannan suka Fara karatu. Se Azahar sukai sallah sannan Khulthum ta bude Jakarta ta ciro hadadden lallai da cone na kunshi tace kowa ya zauna ta mishi kunshi, gaba daya suka tsaya kallanta Irin kada kiyi mana jagwalgwalo fa, dariya sosae Khulthum tayi for the first time ever ta Fara basu labarinta tanayi tana musu kunshin da suke gani a Temple of Hennah. A karshe tace


Don haka gaba daya rayuwata na tsara ta a Auren me kudi don yadda na tashi a talauci bazan dawwama a talauci ba.


Khairi for the first time ta fadi abin hankali tace


Bake zakiyi deciding haka ba Allah shi zai tsara miki yadda zakiyi, kuma akwai masu kudin da kwatakwata hankalinsu ba a kwance yake ba.


Sulaim tace


Hakane Wallahi, Kede Kiyi addu'a kuma kinga Ashir dinnan Allah ki daina wulakanta shi.


Dariya Khulthum tayi tace


Ku bazaku gane ba, ki kalla dakin da kike ciki fa Bana aurenki ba na gidanku, kingani da banbanci sosae.


Kai Sulaim ta girgixa tace


Ke kuwa ki godewa Allah wasu basu da gida gaba daya fa, kuma kina zancen me kudi kince Marar aure, to at that tender age ina kike tunanin zai samu kudin da kike mafarkin Kiyi?


Akwai su Bakiga Huzaifa ba, ba kiga Yusuf ba?


Se lokacin Aimana tayi magana tace


Ki daina wannan zancen Huzaifa ba kudinshi bane na iyayenshi ne kuma ko yau suka fadi suka mutu dole a raba gado, yusuf is too young ace yanada kudin da yake dashi Kinsan sana'ar da yake? Kimsamshi waye? Baki sani ba kun hadu a titi kawai ya gaya miki kin zauna akai, Bari in fada miki bawai zagi ne ba amma yanzu rayuwar da ake Bani gishiri na baka Manda, Dan wane se dan wancan kin taba jin dan Dangote ya auri yar Malam Ayubah? Baki taba ba Sede dan Mangal da dan Ndimi, dangote da 'yar yaradua! Ina ma zaki gansu ke balle suce sun kyasa is better ki zauna daidai inda Allah ya ajeki ina ganin burin ki zaifi saurin cika amma idan kika matsa zakiyi da na sani nan gaba.


Tabbas abinda Aimana ta fada is in place, daidai ne daidai kudinka iya shagalinka ki tsaya inda kike kada rudin social media ya fitsare miki kanki, *MACE A YAU* ta dauki buri ta daurawa kanta se tayi abinda waccen tayi is not right ki zauna inda kike rabon kwado baya Hawa sama ko yaje se ya sakko haka bahaushe yace kuma haka yake. Most charming guys masu kudi at a young age are arm robbers, thieves, gays ko wani abun ina ganin guntun gatarinka yafi sari ka bani. Is high time we change that fact na cewar mijin da zan aura se ready made not sugar daddy, single ta yiwu babanki at that age baya da komai to meyasa zakice se Kinyi, *KALUBALEN MU* wannan Itace *RAYUWARMU A YAU* sannan komai *MUQQADARI NE* daga Allah shi zai tsara maka komai Amma rashin yadda da hakan yana daya daga cikin *MATSALARMU A YAU* kuma ita mace Allura ce cikin ruwa *ME RABO KA DAUKA* Shiyasa *GIDAJENMU* bazasu taba rabo da matsala ba saboda hakan ya kamata mu gyara rayuwarmu.


Shatuuu ♥️


[7/15, 10:32 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*


19




✍️Shatuuu♥️




🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION




#⃣shatuuu095@wattpad






Duk wanda aka yiwa maganar da Aimana ta fadawa Khulthum idan har zai dauka yaci ace ko da na wannan lokacin ne ya dauka amma khulthum gani take to idan ta tsaya a wannan gurin me ta samu? Wacce ribar zatace ta samu? Babu! Tunda har yanzu cikin samarinta babu Irin Wanda idan ta tsaya sukai hoto dashi tayi posting zataji ana comments da irin "oh Allah ina kika hadu dashi? Awwnnn Dama kinsanshi ne? I'm envying you? Wannan crush dina ne" words of such haka take so to wanne ne a ciki? babu shi. Tana gama yiwa Khairi ta aje cone din tayi mika sannnan ta koma gefen gado ta zauna Tana ta kallonsu kamar yadda suma suke kallonta, se tayi murmushi tace


Dangin babana basu nema na, sun Kori Mamata da ni basu kuma nemeni ba, so inason na auri me kudi wanda aurena se ya girgixa ilahirin Nigeria, se sunyi Dana sanin abinda sukai.


Tana yin shiru Khairi da Aimana suka kwashe da dariya, Harda rike ciki saboda maganarta ta basu dariya, a yanxun ka kyautata rayuwarka ma kaga ba daidai ba Balle ka rike wani shirme, yadda sukeyi babu kakautawa itakam Sulaim tambayar kanta take shi aure ba bautar ubangiji bane ko kuma shi source din yanke talauci ne?


Kinsan ni ban taba mafarkin auren me kudi ba, ni akaran kaina nake son Nayi kudin. I want to be my own boss naci gashin kaina ba under umbrella wani ba.


Khairi ta bata amsa Bayan ta gama dariyar.


Kinga wannan ra'ayinki ne, so nima hakane ra'ayina Duk inda me kudi yake ko saurayin waye inhar yayi min I'll definitely make him mine.


Baki bude Sulaim tace


Muyi kaffa kaffa kenan.?


Gaskiya kam yadda nake ji da baby tsaf zan miki duka akanshi


Khairi ta fada suna kara kwashewa da dariya Don su duk tunaninsu wasa take, abinka da wayayyu take aka bar maganar aka cigaba da zancen wani Korean movie da Sulaim ta samo musu lokacinda taje kaduna daga gurin Jawad Kings woman. Sunata hira Aimana tace


Nifa babu jaki a film dinnan irin Min Feng yana sonta amma shi dole gadinta yake a karshe ya tashi a tutar babu se Kisa da akai mishi


Dariya Sulaim tayi tace


The useless brat ba kuma bata taba recognizing halin da yake ciki ba.


Khairi tace


Hakane fa, gwara mashi fa yana ganinta amma kinga Jin Ke dinnan Allah kadai yasan yadda na tsaneshi naji dadin kasheshi da akai Wallahi.


Khulthum tace


Ni kuma baki daya Yin Zheng din na tsana


Ido a waje Khairi tace


King baki daya? Gaskiya kin zake.


Kafin a Bata amsa sukaji ana kwankwasa kofa, Khulthum ce ta Mike ta nufi kofar ta bude gaban Sulaim ya dinga faduwa tamkar wadda Abu ya biyo ta, a ranta addu'a take ubangiji yasa ba Junaid bane Don maganar Khulthum ta tsaya mata a rai so se taji batason su hadu. Fortunately sega Atika ta shigo hannunta rike da fararen envelope guda uku, Tana shigowa ta Kara gaishe dasu Aimana kafin ta mikawa Sulaim tace


Alhaji yace a Baki, wai ina Wayarki?


Se lokacin ta tuna wayar ma baki daya a silent take hakan yasa tace


Oh tana silent, ya fita ne?


Eh


Ta bata amsa sannan ta fice, Khulthum da babu kunshi jikinta yasa ta miko mata wayar Sega missed call na Yaya, ya Ja'afar, Salim da wata unknown number. Ita basuyi waya da Salim din ba jiya ya Kira tayi bacci gashi yanzun ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login