Showing 57001 words to 60000 words out of 131263 words

Chapter 20 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4613

Junaid dake zaune kan carpet ya kura mata idanu, itama kallonshi take hawaye wani na bin wani dukkan jikinta na rawa wanda hakan ya tabbatar masa mummunan mafarki tayi! Hannunshi ya mika mata babu musu ta zura nata tareda sakkowa ta lafe jikinshi kukanta na Kara karuwa jinta jikinshi, Baki daya tashin hankali da tsoro suka addabe ta, Tana son tambayarshi ko Abinda ya fada mata cikin mafarki gaske ne sede tana gujewa kunnenta mugun ji.


Cikin sassanyar murya yace Yana shafa gashinta wanda ya bayyana sakamaakon hular da tayi nata gurin har Zuwa bayanta


You had a nightmare?


Kanta ta gyada tana sake bawa hawayen idanunta damar zuba freely. Gogesu yayi da tafukan hannayenshi yace


Ya isa haka, Bakiji you're safe ba kina arms dina just pray ko zaki fadamin?


Da sauri ta girgixa mishi kanta hakan yasa ya rabu da ita, daga karshe da kukan ya lafa ya jata suka koma gado batareda ya karasa tsayuwarshi ba. Da kyar bacci ya dauki Subay'a saboda ta kasa manta mafarkin.




Washegari Tunda suka tashi ta Fara bashi wata care wadda ko lokacin farkon aurenshi ban tunanin an bashi, haka shima saboda Kwana tayi da zazzabi Shiyasa tausayinta kawai yakeji. Tare sukai wanka ta shirya shi sannan ta shirya kanta kafin ta fito don ganin yaranta. Tana fitowa sukai kicibis da Sulaim wadda take kokarin komawa dakinta. Kallo ta bita dashi gabanta na faduwa kamar zai balla kirjinta Don fargaba, tsana Sulaim ta mata dirar mikiya Sede ita Sulaim din bata ma lura da halinda Subay'a ke ciki ba hasalima tana gaisheta ta wuce dakinta zuciyarta a cunkushe tana ganin kamar ita din tsaiko ce tsakaninta da Junaid din.


Tare sukai breakfast gaba dayansu, kasancewar Junaid na ganin har lokancin Subay'a bata ware daga firgicin mafarkin jiya ba yasa yake nan nan da ita, motsi tayi kwakwara zaice


Are you OK Dear?


Hohohoho? Hakan da yayi ba karamin Sosa ran Sulaim yayi ba, itakuma Subay'a kamar ta zuba ruwa kasa Tasha. Can ana tsaka da cin abinci mistakenly Subay'a ta kware cikin hanzarta Junaid ya balle murfin bottle water dake gefenshi Don ka'idar shi ce shan ruwa after breakfast, da kanshi ya kafa mata a baki Wanda idanun Sulaim sukai kir Akansu, zuciyarta ta buga da sauri kuma ta janye idanunta tareda daukar spoon sede tana dibar abincin hannunta ya kifar dashi saboda rawar da yake, Jabir ne ya gyara murya yace


Sulaim are you OK?


Se lokacin Junaid ya dubeta idanunta sun cika taf da hawaye kadan suke jira sui splitting mata a fuska.


Meye ke damunki?


Junaid shima ya tambaya amma se ta dauke kanta daga kallonshi Tace da Jabir


Na koshi.


Then jeki karasa shiri muna gamawa zamu wuce.


Da sauri ta Mike har tana tuntube ta nufi dakinta, baki daya suka bita da ido Subay'a na mata rakiya da harara, she hate the girl that is just the fact!


Tara na safe suka fito baki dayansu a gefen mota, ita Subay'a tuntuni ta fice itama yaran dake Muhammad ma an kaishi kingdergaten, Tunda ta fito ya lura fushi take wanda ya rasa dalilin da yasa Sulaim Keda saurin fushi haka to shi bai masan ko me akai mata ba amma dukda haka kallonta yayi tana kokarin bude bayan motar yace


Sulaim.


Ko tana so ko bata so dole ne ta juya Don kuwa zuciyar ta bazata yafe mata ba matsawar taki yin hakan. Cikin ido suke kallon juna kowa nutsuwarsa na dawo mishi, tayi saurin dauke kanta ta sunkuyar tana mitar abinda yasa take kallonshi, envelope ya mika mata yace


Se Saturday.


Amsa tayi ta mishi godiya sannan ta shiga ciki Jabir Yana kallonsu yana murmushi sannan sukai sallama sannan suka dau hanyar.


Awanni biyu cif ya kaisu gurin Birnin kudu, gaba daya Sulaim a gajiye take sosae kamar dukanta akaI sauki daya ta sha bacci wanda da wannan damar Imratu ta samu itada Jabir ya tsegunta mata abinda Ke faruwa. Itama farin ciki sosae tayi amma tana ganin yadda zaayi da Subay'a.


Kwananta uku a Birnin kudu Mami, Baba, Jawad da oga Ja'afar suka iso, wannan kwanaki uku babu Daren da Batayi kuka ba saboda yadda zuciyarta Ke axabtuwa da rashin Junaid a Rayuwarta, baki daya tayi mamaki yadda Lokaci daya soyayyar Junaid take neman farautar farin cikin ta. Duk yadda take cikin dangi anata shirin biki Amma ita abin baya burgeta ko daya hasalima kullum tana dakin Neneh kamar yadda ake kiran kakarsu, Mama Sauda da kullum Se taxo gidan tayi fadan har ta gaji, Sulaim ce kadai tasan Abinda Ke damunta ita kadai tasan kuncin da zuciyar ta ke ciki. Ranar Sulaim murna gata ga Mami duk inda Mami zataje Sulaim Tana bayanta Mama Sauda ta dinga mata tsiya wai makon uwa ne da ita itakam sede dariya.


Da daddare babu kowa parlor kowa na dakinshi Sulaim ta fito da gifts din, wayarta a kunnenta tana kiranshi Ja'afar don ya karba,


Luff ina parlon kasa kazo.


On my way Sweetm.


Baifi 5 minutes ba ya fito cikin 3 quarter jeans da top armless, Baki daya ta bayyanar da damtsen shi dake a murde saboda gyming. Zama tayi akan carpet shima ya zauna gefen ta Yana kallonta yace


What do we have.


Me zance tsautsayi? Ko kuma karar Kwana? Sulaim Bata bashi amsa ba ta farke wrapping sheet din tace


Yaya Hanan tace na kawo maka.


Cikin sauri ya kai hannunshi don kwatar komai Amma it was late don ta riga tayi tozali da rose flowers biyu, turare amma Abinda yafi daukar hankalinta shi ne wani kyakyawan frame me rubutu kamar haka


_When you are in love, the heart works faster than the brain, without the brain the body survives but when the heart fails the body dies! You're my heart and I love you!-


Dago idonta tayi tana kallonshi kamar yadda shima kallonta yake ba tareda yasan abin yi ba.........




Shatuuu ♥️*MACE A YAU*
26


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣shatuuu095@wattpad




Halo people of *SHATUUU's KINGDOM and MAMAN MAMA NOVELS* Double hey! Triple godiya for the love and everything I'm very happy having u guys as my Buddies 😘




*A broken heart can be pieced back together, it might be a heart again but it's still a BROKEN HEART*




Shima cikin idanu yake kallonta kamar yadda take kallonshi mamaki karara saman fuskarta.


Sulaim lemme explain.


Wani kallo ta watsa mishi wanda a take yasa shi rufe bakinshi Wanda DA ya bude da niyyar sake wani protest din amma kallon da tayi mishi yasa ya hadiye maganar tashi, mikewa tayi daga zaunen da take har lokacin hannunta na rike da frame din, kallonshi kawai take da idanunta da suke cike taf da hawaye Wanda by mistake tayi magana to tabbas zasu zubo, wata Irin bugawa zuciyarta take, wani Irin ciwo take ji kirjinta nayi mata, frame din ta doka da kasa akan tanganyar tiles babu jira glass din gaban ya tawarwatse, perf din ta dauka shima ta buga da bangon parlon sannan ta toshe bakinta da hannunta dan kuka ne ya taho mata tun karfi, then komai ya kare kenan her only hope ja'afar bai daina kule kule ba bayan ample of chances da ta bashi, zuciyata data mika mashi that's the pay back daya bata. Ga zuciyarta mayaudariya, macucia, azzaluma data zalunce ta take son Junaid wanda baisan abinda take ciki ba, take hawaye ya balle mata babu waiwaye ta nufi staircase a million don tana bukatar break, me tayi haka da tayi deserving such treatment? Me tayi.


_Call the man who deals in love beyond repair, he can heal the world of heart in need of care... Shine the light ahead when the next step is unclear....._




Jaafar na tsaye tamkar an dasa shi akan kafafuwanshi haka ya tsaya yana kallonta, ya kasa furta komai na kare kai saboda yadda idanun sulaim suke ko shi waye bazata saurareahi ba, to shima bashida abin fada sede idan karyar da ya saba zai mata. Jagwab ya zauna kan kujera tareda buga tagumi ya rasa abinda yake ji Yafi Mintina goma kafin Zuciyarshi tace mata nawa ke binka kana dodging? Mata nawa kuke soyayya dasu?don kwaya daya tace batayi shi ne abin damuwa? Abin daga hankali?kanshi ya girgiza ya mike yana daga kafadarshi irin ko a kwalar rigarshi but deep down him yasan he missed an angel Don ko ya yarda ko yayi denying Sulaim is still Sulaim. Sede yana ganin tayi kadan ta juya shi kuma yasan son da take mishi ba zata jure been away from him! Se muce tunanin Ja'afar kenan ba namu ba! Ko ba haka ba Shatuuu's kingdom and Maman mama people?




Mami Zaune Kan kujera a parlonta se Jabir da Imratu dake gefe, Jawad na kan carpet yana cin abinci Se Subay'a da Junaid wanda zuwansu kenan kasancewar very late ya tashi a office Shiyasa basu zo da wuri ba kuma Mami tace lallai ya bar Duk Abinda suke shi har da Subay'a din su taho, yaran babu yadda Junaid bai yi ba akan su taho tare se cewa tayi wai sauro jigawa yaran bazasu iya coping ba zata kaisu gurin Sulma. Maganar ta bugeshi saboda yana tsananin son jigawa, Yana son mahaifarshi bai son wani ya karce su amma baya son magana hakan yasa baice da ita komai ba ita kuma gani take tamkar she won the medal and lottery!


Mami ta dubi Mama Saude dake gefenta tace


Nikam Maman Nusaiba ya akai har Sulaim tayi kwanaki hudu amma bataje gidan Engineer da Zunnuraini ba. Dazu wajen daurn aure sukewa general complain.


Tabe Baki tayi tace


Tunda Taxo se jiya Naga ta ware, bansan abinda yake damunta ba amma akwai damuwa a tattare da ita hakan yasa na kyalle ta.


Kai Mami ta dafe don ta lura da hakan kuma ko yau da safe Seda ta tambayeta da ta sameta tana kuka a daki Amma se tace babu komai dama tana jiran Junaid yazo ne taji abinda Ke samun 'yar gidan nashi. Kallonshi tayi tace


Junaid kaji da kunnenka ni na rasa yadda zan bulo mata bansan me take so ba.


Subay'a ta tsirawa Mami idanu don yadda ta ji zancen Mamin banbarakwai, ita bazata lallaahe ta ba se mijinta? Lallai wannan rainin hankali ne ma. Junaid ya dago idanunshi ya rasa me zaice shima yana bukatar kulawar sede Lokaci daya hankalinshi ya koma kan Sulaim din so yake Yaji damuwarta.


Imratu kira min Sulaim.


Tohm Mami


Ta fada Tana mikewa yayinda suka cigaba da tattaunawa Sede baki daya hankalin Junaid din ya koma kan Sulaim, me ke damunta? Meye matsalar ta? Bakinta kadai amsar take hakan yasa hankalinshi rabuwa kashi kashi gashi Imratun is staying longer than expected kusan Mintina goma sun wuce Bata dawo ba.


Mami kizo


Yaji muryar Imratun ta katse mishi tunanin da yake, ya manta Subay'a na gurin ma yace


Me ya faru?


Mami mikewa tayi tabi Bayan Imratun, Junaid da Mama da Jabir Harda Jawad suka bi bayansu ya rage Subay'a kawai wadda ta kasa digesting abinda kwakwalwar kanta ke karanta mata.


Tana kwance tayi rub da ciki, ta nutsa kanta cikin pillow tana ta kuka bawai Marar sauti ba ba kuma me kara Ba amma kana shigowa xakaji sheahekar shi, Mami ce ta Fara isa gefenta ta dago ta tareda fadin


Sulaim Menene?


Me zatace mata for all this while your son who happens to be a monster ya yaudareni ko kuma ina cikin muguwar azababben son babban danki..... Kai life is unfair a ganinta, Wanda kake so baisan Kanayi ba, Wanda Kake da hope akanshi ya debo kasa ya bula maka cikin ido, to ya zatayi? Babu wani dalili da zaisa taji rayuwar ta da dadi .....that's emphatic NO!


Kankame Mami tayi ta Kara sakin kuka Wanda fitarshi ba sauki bane se radadi da takeji cikin zuciyar ta, inama inama ana cire so a yar tabbas da tuni ta cire na Junaid ta yar dashi Amma hakan is impossible.


Washegari an gama biki baki daya ita Sulaim da Ciwon Kai ta tashi wanda da kyar take iya budesu saboda yadda suka kumbura suka mata nauyi na gaske... Wa yace mata kuka karamin Abu ne. Tana kwance kan gado tayi shiru idanunta a runtse kamar me bacci Sede kallo daya ya isheka amsar she's awake. Mami da ta shigo ta karaso jiki a matukar sanyaye ta zauna gefenta, gaba daya guilty tension ke damunta tana jin tamkar bata rike marainiyar da kyau ba, jiya haka ta kwana da tunanin Sulaim a ranta to ya zatayi bata san Meye matsalar ta ba.


Sulaim idanunki biyu tashi ki zauna.


Babu musu a hankali ta tashi ta xauna idanunta ta bude a hankali kafin tayi saurin rufesu saboda yadda rana da tayi haske take barazanar kashe mata su. A hankali ta kuma budewa wannan karan da dan sauki kafin kuma a hankali tayi balancing da rays din.


Mami ina Kwana


Ta fada da dusashiyar muryarta


Lapiya lau, ina jinki fadamin me ya saki kuka jiya?


Dagowa tayi ta kalli Mamin tana tunanin abinda zatace wanda zaisa Mamin ta yarda da ita don kuwa tana ganin last thing da zai taba faruwa da ita shi ne tona asirin zuciyarta she can't ko Khulthum bazata iya fadawa ba Balle mahaifiyar gwarzonta Junaid!


Mummy da Daddy na tuna


Ta fada lokaci daya tareda kankame Mamin ta Kara sakin wani sabon kukan, I missed you more than words can say, I missed you ta fada karkashin numfashinta. Tuni Mami ta Fara lallashi har ta samu sulaim tayi shiru tayi wanka sukai breakfast tare kafin ta Sata tayi bacci. Dama anci bashi tana kwanciya ya dauketa. Mami haka ta zauna zuciyarta fal tausauyin sulaim.


Turo kofar dakin Junaid yayi muryarshi dauke da sallama, Yana Sanye cikin Kaftan coffee wanda sukai mishi kyau suka kawata shi rare shiga kenan don yawancin shigarshi ba manyan kaya bane amma yau se girmanshi, kwarjini da cikar haiba ta fito sosae, yayi kyau babu macen da zata kalleshi bata Kara kalla ba amma banda ni Woooooo... Lol... Fuskarshi tayi fayau idanunshi sunyi sunken ciki saboda rashin bacci, tarin gajiya, soyayya da uwa uba rigimar Subay'a don jiya Allah ne yasa bai bude zuciyarshi ba saboda ta kaishi bango tana tuhumar shi akan nuna kulawa ga Sulaim wadda ita kadai ya kamata ta samu hakan. Tun yana shiru har ya biyeta ganin ta fishi danyen Kai yasa ya juya mata baya tayi ta gama ta kwanta, a lokacin hankalinshi ya nutsu ya fara tunanin Meye ke damun Sulaim har ya sata take Irin wannan kukan haka.


Mami barka da safiya


Barka dae, ya Subay'a take


Kanshi ya shafa don yasan Bata shigo gaida Mamin ba don a bargo ya barota.


Lapiya lau zazzabi take yi ne Shiyasa, ya Sulaim din ta fada miki wani abu?


Kai ta gyada ta shafo Fuskar Sulaim din tace


She's missing her parent.


Tausayinta sosae ya kara kamashi, rashin iyaye babu dadi bai san zafin ba amma zai iya fada.


Ya kamata , Allah ya jikansu.


Amin, Allah ya bawa Subay'a lapiya ko zakuje Asibiti?


Kanshi ya girgixa yace


No Tasha magani, Anjima zamu wuce jibi ne tafiyar Estonia.


Murmushi tayi tace


Yayi kyau Allah ya kaiku lapiya amma kana ganin Sulaim zata iya zama dasu Ahmad.


Kanshi ya gyada yace


Banida haufi kanta, idan ba ita ba duk kano bazan barsu hannun kowa ba Sede su dawo kaduna.


A haka suka gama hirar Bayan La'asar su Sulaim se Kano, Tun a motar batace komai ba Tunda Subay'a na nan gashi kanta har lokancin ciwo yake mata. A haka suka isa gida inda komai yake daidai a muhallinsa. Da daddare ya fadawa Sulaim tafiyarshi tare da sabon responsibility da ya hau kanta. Ko kadan bata damu ba tana ganin Nisan zuciyoyinsu zaisa sonshi ya yaye Daga zuciyarta.


Ranar Sunday karfe hudu na yamma Sulaim, Ahmad da Muhammad suka raka Junaid da Subay'a airport Bayan komai da yasan zaa bukata a tafiyar ya bar mata, ita kuma da farko tace yaran gidan hajiya zata kaisu Amma Junaid yace karta fasa haka ta hakura ta fito musu da komai da tasan zasu bukata tare da cewa Sulaim


Idan kika zaluncesu Allah bazai barki ba.


Ko ta kanta Sulaim Bata bi ba don da tasan yadda takeji da Bata Fara fada mata zancen banza ba. Akan idanunsu jirgin ya fara tafiya kan runway kafin ya cilla sama, idanu Junaid ya runtse wani sabon abu yana piercing zuciyarshi kamar kullum son Sulaim daban yake da na kowa incomparable!!!




*Have you ever been hurt? The place tries to heal a bit and you just peel the scar off hurting yourself over and over?*






Shatuuu ♥️[7/27, 5:21 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
27


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






Sati daya kenan da tafiyar su Subay'a komai na gidan a hannun Sulaim yake wani sabon responsibility ya hau kanta tamkar Marar gidan haka take ji. Alarm din dake gefen bedside drawer ne ya fara ringing alamar lokacinda akai setting dinshi yayi. A hankali ta bude idonta Wanda yake Cikeda bacci tasa hannu ta kashe tareda gyara kwanciyarta don baccin bai isheta ba, sede ta kasa komawa saboda yadda ake ta kiraye kirayen sallar subhi, haka ta mike Tana mutsitsika idanta tayi zauna bayan tayi addu'a ta shiga toilet, wanka ta Fara yi sannan ta daura Alwala ta fito. Bayan ta Idar da sallah ta wuce kitchen inda ta tarar har su Atika sun Fara aiki, gaiswaw sukai sannan ta dubi Atika tace


Atika jeki ki tashe su kiyi musu wanka Bari na karasa girkin.


Tohm


Ta amsa mata sannan ta wanke hannunta ta fice don aiwatar da umarnin Sulaim, kallon kayan da Atika ta fito dasu tayi, wasu ta mayar ta dakko wasu kayan ta Fara aiki, tanayi tana Azkhar baki daya zuciyarta na rage damuwar da take jibge a ciki.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login