Showing 111001 words to 114000 words out of 131263 words
Chapter 38 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
ta zageshi, Bana son ki daga hankalinki akan hakan ina fada miki don kisan matsayinki, zaman mijinki kike not for any other person. Ki kwantar da hankalinki sanann ban yadda ko kallon banza Ya hadaki da Subay'a ba, ku gaisa that's all nothing more kinji? "
Kanta ta sake gydawa tana jin damuwar da take ciki ta Fara yayewa, Mami uwa ce ta gari cikin hikima ta dinga koyarda Sulaim yadda zata kwaci kanta, bata barta tayi bacci ba Seda ta cire mata inferiority complex dinnan ta gina mata jin ta isa, Junaid ba mijin Subay'a bane ita daya aa mijin sune dukkansu me kyan hali ita ce tauraruwa a zuciyar shi.
Washegari tun safe suke aiki da Mami da Sulaim don Imratu cikin jikinta me saka morning sickness ne hakan yasa ko fitowa Batayi ba. Gaba daya Sulaim zuciyarta da gangar jikinta kewar Junaid suke Don rabonta dashi tun jiya, ko sallama bai zo yayi musu ba da zai kwanta. Sun kusa kammalla aikin kamshin turaren shi ya iso cikin kitchen din wanda yasa Sulaim saurin lumshe idonta saboda nutsuwa da ta mata dirar mikiya, shigowa yayi ciki tareda tsugunnawa ya gaida Mamin wadda ta amsa kamar ko Yaushe, fita tayi don basu guri tareda fadin
"Auta ki karasa"
Tana bada baya ya matso ya rungume ta tareda sakar mata wasu trails na kisses a wayanta, Kara ta dan saki tareda janye jikinta tana murmushi ta riko hannunshi tareda fadin
"Good morning "
Harar ta yayi yace
"Ba wannna maganar, jiya kika sha bacci ko missing dina Bakiyi ba, ni kuma ina can Inata missing dinki"
Kashe gas din tayi sannan ta juyo Tana facing dinshi tayi dage kasancewar ya kereta a tsayi, a hankali ta hade bakinsu guri guda tana mishi wani seductive and sensual kiss, seda ta gama sannan ta rungumeshi tare da fadin
"Ka yadda I missed you? "
Da sauri ya gyada kanshi don ya yadda kam. Baki daya suka hadu don cin abinci amma babu Subay'a, Imratu dake ta shan kunun gyada ta dubi Mami tace
"Tace na fada miki ta tafi kano"
Babu Wanda ya kuma maida maganar suka ci sannan Mami ta hada Junaid, Jabir , Imratu da Sulaim ta Kara musu nasiha. Wajen laasar Mami ta rako Sulaim da yaran zasu tafi Kano.
Maimakon gidan da suka saba zama se sukai parking kofar wani flat duplex akan BUK road, kallonshi tayi kamar yadda take kallonta, kunnenta ya matso dashi yace
"Wancan gidan aro ne, wannan namu ne ni dake and our babies to come"
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
52
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Of course, you know that this page is yours the people of Maman mama novels, ina godiya sosae da goyon bayanku.....*
A'ISHA ASHIR
Bari mu leka muji yadda rayuwar Wannan bayun Allah ta kasance bayan Auren Khulthum.
Rayuwa ta mika musu, abubuwa sun sauya ciki Harda Fara makarantar Aisha wadda ta samu gurbin karatu cikin North west University wadda iyayen Ashir suka dauki nauyin karatun. Amir shima yayi nisa cikin karatun da yake ga kuma budi da Allah yayi mishi gurin kasuwancin da Khulthum ta dade tana mishi dariya, wato saida gwanjo. Sede gashi Allah ya albarkaci abin har ya fara gyara musu dan gidan da suke ciki, wannan abin ba karamin faranta ran Malam Suleiman yayi ba domin yasan tabbas Allah ya amshi adduar da ya dade yana Yi.
Ranar wadda ta kasance asabar tun sassafe A'isha ta tashi kamar yadda ta Saba, babu Wanda ta tada haka ta fito daga daki ta Debi ruwa tayi wanka sannan ta dawo daki ta gyara kanta ta shirya cikin doguwar rigar farin material me fatsi fatsin Baki. Dukda ba mai tsada bane amma yayi mata kyau, fitowa tayi ta hura wuta sannan ta Fara Sharar tsakar gida, ta hada wanke wanke tayi a lokacin Amira ta fito Tana ta murtsuka idanu, kallon A'isha tayi tace
"Kai Yaya A'isha duk ke daya kika yi wannan aikin?"
Harara A'isha ta makawa Amira tare da cigaba da aikinta sannan tace
"Waye zai biyewa lalacin ki, kamar ba mace ba ace se yanzun kike tashi a bacci"
Baki Amira ta turo tace
"Rayuwarki tayi tsauri Yaya A'isha, amma ina yiwa Yaya Ashir samun ki"
Sunan kawai da Amira ta ambata Seda wani sihirtaccen murmushi me kayatarwa ya kubce daga kyakyawar fuskar A'isha, Dama ita din ma'abociyar murmushi ce amma na Ashir na daban ne. Ita kanta ko cikin mafarki ko burika Irin nata bata taba tunanin zatayi soyayya da Ashir ba, Ashir daban yake wanda samun mutum kamarshi se an sha wuya, kullum rana se A'isha ta kara godewa Khulthum akan bar mata Ashir da tayi. Halayenshi kadai sun isa ya sace zuciyar mutum dashi. Mutum ne me takatsantsan akan dokokin Allah, hardly Kaga ya ketare abinda Allah da manzonshi sukai Hani akan, mutum ne that's very caring dukda ya kasance baya kasar amma bai taba jera hour biyar ba tareda ya ji muryar A'isha din ba, hakan yasa suka mugun sabo da kuma shakuwa da junansu.
Da farko kasa sakin jikinta tayi saboda tana ganin kamar ana amfani da ita ne wajen huce haushi Amma a hankali yadda yake tsumata da Wannan zumar tashi yasa ta bada Kai bori ya hau. Cikin nitsuwa suka dinga shimfida soyayya me Cikeda amana, karko da kuma fahimtar halayen juna, cikin kankanin lokaci sukai clearing differences dinsu hakan yasa basu sha wahala ba.
Amira dake gefe tana kallon Yayar tata da tayi zurfi cikin tunanin Ashir wanda ko bata fada ba hakance don wani Irin soyayya me rikitarwa ce tsakaninsu. Daki ta koma jiyo ringing din wayar A'ishan, murmushi tayi ganin Ashir dinne hakan yasa tayi saurin kai wa A'ishan wayar tareda fadin
"Gashi nan dan halak ya huttar dake"
Maficin dake hannunta ta wullawa Amirar wanda ta zulle Zuwa daki Tana dariyar kunyar A'isha. Se kira na biyu ta samu ta dauki wayar dan tuni wancan call din ya katse
"Yau Queen da rowar murya kika tashi? "
Dan murmushi tayi tace
"Ni na isa, tana daki wayar"
Kanshi ya jinjina tareda fadin
"Dan Allah Queen ki dinga hutawa da Wannan ayyukan da kike, ace kullum mutum tamkar inji yayi ta aiki babu Hutu Haba mana! Shiyasa dole a matso da date din aurenmu!"
Dariya ta saki a hankali wadda take nuna Irin nishadin da take ciki, shima lumshe idonsa yayi yace
"You will not answer me right? Anyways Dama zan miki zancen next week zan dawo"
Da sauri ta Mike wani Irin farin ciki Marar misaltuwa ya mamaye mata jikinta da zuciyarta tace
"I'm so happy blood, Awnnnn!"
Haka suka Bata Lokaci me tsayi suna waya har ta kammalla ayyukanta, lokacin sukai sallama shima don ganin mutanen gidan sun Fara fitowa ne. Tunda Mama ta fito take shiwa Aisha albarka, har zuciyarta take jin dadin wannan halin na A'isha ko ta so ko taki A'isha tafi Khulthum sau dubu kuma Tun ranar da Khulthum ta bar gidan taji wata nutsuwa ta saukar mata, taji tamkar an sauke mata wani babban nauyi ne daga kanta, haka bata ji wani kewar ta ba, to ta yaya zataji Bayan nemar mata magana kawai take yi, yanzun hankalin kowa ya kwanta tunda bata nan.
Bayan sun kammalla cin abincin Baba ya dubi A'isha yace
"Ya kamata kuje ku ga dakin 'Yar uwarku, ko mai ya faru ina son ku manta da hakan, Ummu_Khulthum yar uwarku ce"
Kai A'isha ta gyada tana jin komai ya wuce dama ita bata rike Khulthum ba don kuwa tasan ba'a canjawa tuwo suna Yana nan a tuwonshi! Tare suka shirya Mama kamar ta Goya su da taji inda suke haramar Zuwa, dukda Tunda Khulthum ta saka kafarta ta bar gidan babu Wanda ta taba Kira da sunan gaisuwa, se Mama dince kan kirata time to time.
Tunda aka sauke su A'isha kofar gidan Baki daya suka saki Baki da hanci suna kallon wannan tafkeken gidan, mamaki cike a zuciyar kowannensu saboda babu Wanda yazo ganin daki don ba'ayi rabuwar arziki ba Balle har su raka ta in fact lokacin bikinta ma gaba suke me tsanani. Seda A'isha ta kira Mama ta tabbatar mata gidan ne sannan suka kwankwasawa, kasancewa securities din sun saba da kawayen Khulthum masu didif didif a gidan suka Barsu suka shiga tareda nuna musu part din Khulthum din. Daidai zasu shiga Musbahu na fitowa daga part din Sanye da jallabiya brown, Fuskarshi babu digon annuri an dinke tamkar anyi masa sakon mutuwa, a tare suka gaishe shi kawai se ya samu kanshi da amsawa saboda kana kallon Amira Kaga Khulthum saboda yadda suke kama da junansu sosae,
"Ku shiga ciki mana tana nan "
Ya fada Yana basu guri tareda Kare musu kallo, kana kallonsu kasan talauci yana damunsu Amma a idanunsu zaka fahimci they're contented. Gaba daya bin parlon sukai da kallo saboda tunda suke a rayuwarsu basu taba gani Balle har su shiga makamancin gurin. Zama sukai kan kujera shi kuma ya nufi dakin don kiranta, tana kwance inda ya barta ko hannu ta Kasa dagawa, kamshin turaren shi da taji yasa ta mugun firgita don babu Abinda take tsoro yanzun a rayuwarta shi ne Musbahu, azabar da yake mata Allah kadai yasan hakan amma tasan kaddarar ta ce hakan!
"Kinyi baki"
Bai jira amsarta ba ya fito Bayan yasa a kawo musu abinci, baki daya A'isha tsoron karbar da Khulthum zatayi musiu take, da Khulthum bata da komai take rashin mutunci Balle gata da kyakyawan miji na nunawa duniya, ga kudi da katon gida. Ai se abinda yayi gaba, suna nan Zaune zaman kurame Don babu me magana cikinsu se gata ta fito, ta kintsa kanta cikin voile Red dinkin skirt da Riga, tayi kyau amma tayi Baki, idanunta sunyi ja tareda fadawa ciki, fuskarta kadai zaka kalla ka gano tsantsar damuwa da tashin hankalin da take ciki, tana ganinsu A'isha ta nufe su da sauri tareda rungume su dukkansu, sunyi mamaki canzawar ta da kuma Wannan ramar da tayi.
Tsakiyar su ta shiga tana jin kamar an jefata a Aljannah, dadi kamar me daga baya ta kwashesu Zuwa dakinta tana ta musu hira har suka saki jikinsu suka ci abinci. A'isha karshen gado ta koma ta kwanta tare da amsa kiran wayar Ashir, tunda ta Fara wayar hankalinta Baki daya ya bar dakin da mutanen dakin, Khulthum na ankare da ita Tana ta son jin da wanda A'isha ke waya hakan yasa ta tambayi Amira wadda ta bata amsa da
"Yaya Ashir ne"
It takes a huge of sacrifice typing this peace..... Dan Allah kui manage dashi.
Shatuuu ♥️
[9/6, 6:55 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
53
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Thank you for patiently waiting, thank you for the prayers! Amarya na dakinta*
Amira bata jira gama ganin reaction din Khulthum ba ta cigaba da fadin
"AI an saka ranar biki, wata uku ya rage yana zuwa Hutu xa'ayi bikin su tafi tare. Wanda ya dauki nauyin karatun nashi ya hada da nata"
Wani yake Khulthum tayi tace
"Ikon Allah, to Allah ya kaimu "
Tana fadar haka ta mike ta fita daga dakin, Rana ta farko a cikin rayuwarta da ta Fara jin tayi kuskure, Rana ta farko da ta Fara jin wani abu yana bin zuciyarta na Anya ta yiwa rayuwarta daidai? Taji anya akan turba me kyau take? Jingina tayi da kofar dakin dake gefe idanunta na cikowa da wata zazzafar kwalla, a hankali wasu abubuwan na rayuwarta suka Fara bayyana a idonta, tamkar wani flashback a film haka suka dinga bayyana mata, tabbas kwadayi mabudin wahala ne, tabbas wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a Tashar wulakanci, gashi nan bataje ko ina ba ta fara gani, kwatakwata Watannin ta biyu kawai cikin gidan amma gashi Anyi mata mummunan tabo cikin zuciyarta da rayuwarta baki daya. A halin yanxu babu Abinda take matsanancin tsoron ji Irin muryar Musbahu Balle ta ganshi, idan kuwa hakan ta kasance ba karamar gigicewa take ba saboda irin axabtuwa da take, ta yi kukan tayi Allah ya isa wa Maimuna ta Kuma tsine mata yafi cikin carbi Don Tana ganin ita ta Fara kaita ta baro ta, Sede Khulthum ita ta Fara cutar kanta, ita ta Fara kashe kanta da hannuwanta kamar yadda tayi destroying kanta ba tareda taimakon kowa ba.
Kuka sosae Khulthum ta tsaya a gurin Tana yin, kuka Marar sauti Marar dadi dake fitowa Tun Daga karkashin zuciyarta, kuka ne takeyi na rashin makama, na bakin cikin halin da ta jefa kanta ciki, kuka take sosae tamkar ana cire mata wani sassa Daga jikinta. Ta dabbaka a kukan da take taji hannu an dafa kafadarta ko bata juyo ba tasan waye Musbahu ne, take jikinta ya dauki rawa da kyarma tamkar kura ta hadu da zaki, kukan da take dif ya dauke se hawaye dake sakko mata a fuska, juyo da ita yayi tana fuskantar shi Sede maimakon ganin Fuskarshi a murtuke kamar kullum se taga sassauci a Fuskar tamkar "pity" a kwance wanda suna hada ido yayi saurin tamke fuskar tashi a ranshi Yana kokarin yakice tausayinta da ya Fara rinjayar shi daga zuciyarshi,
"Bakin sun tafi ne? "
Da sauri ta girgiza kanta batareda ta iya furta kalma ko daya ba saboda yadda ta kidime, Fuskarshi ya kara daurewa yace
"Ku shirya muje gaba daya"
Yana fadar haka ya fice, wani farin ciki taji ya sauka a ranta at least zata fita daga gidan. Dakin dayake kusa da ita ta fada ta wanko fuskarta amma dukda haka alamun kuka na nan hakan yasa ta dauki kwalli ta zizara akan idanunta tareda shafa powder sannan ta dauki ciro lace me kyau da akai dinkin gown me tsari, Seda ta shirya ta karewa kanta kallo jikin mirror, tasan in har mace ake nema to tabbas ta kai mace, babu inda zaka kushe ta wala halitta ko kyaun fuska amma tayi fatali da wannan baiwar ta Allah da ya bata kawai ta dorawa kanta matsanancin kwadayi da yayi clouding mata vision dinta har ta kasa ganin wutar data tunkaro ta, Lokaci daya ta tuno ranar da ta iske Musbahu a office farkon haduwarsu abinda ya fada mata wanda kusan gugar zana ce amma dayake burinta a rayuwa kudi ne kawai yasa bata fahimta ba, here she's today ko hakkin Ashir tasan bazai barta ba, mutumin da ya so ta yayi hakuri da halayenta amma tayi fatali da hakan ta ki aurenshi.
A hankali ta tura kofar dakin dasu A'isha suke ciki, dukkansu sun shirya tamkar Dama jiranta suke Tana shigowa suka Mike, kallonsu tayi tace
"A'a ku tsaya tare zamu fita"
Kai A'isha ta gyada tana mamakin yadda bakin Khulthum Ya mutu, ga wata rama Marar tsari da Khulthum din tayi, gaba daya ta koma wata iri kamar ba ita ba, matching veil ta dakko ta yafa sannan ta dakko wata Leda ta shiga zuba kayan kwaliyya da atamfofi tana gamawa akai knocking softly jikin kofar, wata Irin muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta har Seda ledar hannun nata ta kubce daga hannun nata wanda yasa Aisha kallonta Cikeda mamakin Abinda ya sata rikicewa har haka. Duk yadda Khulthum taso regaining nutsuwarta amma Shigowarshi da kuma kama hannunta da yayi cikin tattausan hannunshi yasa ta kuma rikicewa haka dai suka nufi mota babu me magana yayi driving dinsu Zuwa gida, yana parking Bata jira komai ba ta bude ta shige gidan kusan a guje, wani Irin missing din gidan taji, ji tayi tamkar an cire ta daga wuta haka taji, ga wata nutsuwa da ta kwarara mata. Da Baba suka Fara cin Karo wanda yayi Alwala don yin sallar isha'i, kallonta yayi itama ta tsaya abin mamaki ta tsugunna har kasa ta gaisheshi daidai lokacin su A'isha suka shigo, suma mamaki kamar ya kashe su, amsawa Baba yayi ya fice da hanzari Don A'isha tace tare suke da Musbahun Yana waje. Ciki suka shiga inda ta tarar Mama ta Idar da sallah Tana zaune Tana cin tuwo, da gudu ta isa gareta ta rungume ta tana sakin wani matsanacin kuka Wanda takiyi ranar da zaa kaita tana ganin dan me zatayi kuka tunda ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda sede what she thought is not what she met, it was two different things that are parallel to each other.
Gaba daya Mama hankalinta ya tashi har suma su A'isha wadda suka tabbatar Khulthum ta fada mugun hannu daga yadda take abubuwa, tambayar duniya Mama tayi mata amma shiru a haka Musbahu, Baba da Amir suka shigo inda Aisha ta shimfida mishi tabarma ta kawo mishi tuwo, babu musu ya saka hannunshi Yana ci kuma abincin yayi mishi dadi sede gabanshi faduwa yake ganin yadda Khulthum ke kuka, hakan yasa yayi saurin gamawa yace
"Zamu tafi, bata da lapiya ne"
Nan Baba ya sata gaba da nasiha ita kuwa kuka kadai take a haka babu yadda zatayi ta biyo bayanshi Mama na kwantar mata da hankali, suna shiga mota ya kalleta ya maida kanshi kan tukin da yake har Seda suka kusa gidan Gwoggon kafin yace
"Nan ma idan Kinje Kiyi kukan"
Wani dummm taji a kirjinta haka ta biyo bayanshi Zuwa ciki, Rana ta uku da Taxo gidan gwoggo kenan, Tana zaune kan kujerar ta ta kullum da kullum. Wannan Karon papers ne hannunta tana dubawa idanunta Sanye da medical glasses wanda ya Kara boye tsufan da tayi. Zama sukayi kan carpet suna gaisheta, baki daya ta maida hankalinta Kan Khulthum wadda ta lura kamar kuka take, ko gaisuwar Bata amsa ba ta dubi Musbahu dake gurfane gabanta tace
"Me ka yiwa Ummu_Khulthum dinne?