Showing 102001 words to 105000 words out of 131263 words

Chapter 35 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4631

color, Abayar tayi mata kyau sosae abinka da farar mace, kanta na cikin wani milk scarf wanda ya zauna daidai da tsarin jikinta. Flat milk vine ta zura ta fito bayan ta feshe jikinta da sassanyan Arabian turaren ta. Tana fitowa Linda na kokarin setting table, kallonta tayi tace


"Ina ne part din Musbahu? "


"Ma'am ta gefen naki yake"


Kanta ta gyada ta nufi kofa zuwa nashi haka kurum gabanta ya dinga faduwa, amma ta cigaba da nufar part din, babu kowa a parlorn se sanyi da kamshi dake tashi, parlon ya hadu ba iyaka don haduwar shi will put her own into shame! Rarraba idanu ta tsaya yi se taji bude kofar bedroom din dake fuskantar ta, hankalinta ta mayar kofar take wani charming guy wanda shekarunsa bazasu dara 23 ba ya fito bayansa Musbahu ne Fuskarshi a wani yalwataccen murmushi ne wanda ake gani kamar sau daya a shekara!... Lol.... Ko kallon inda take baiyi ba sema guy dinne ya gaisheta ta amsa Tana nemarwa kanta masauki cikin daya daga cikin Royal Cushions din dake cikin parlour.


Tafi Mintina talatin zaune kafin Musbahu ya shigo Yana binta da kallo Marar ma'ana, kasa tayi da kanta har ya sami guri ya zauna sannan yace


"Me ya faru? "


Da sauri ta dago idonta tana kallonshi don ba haka ta Zata zaice ba, ta yaya ma zai mata wannan maganar Bayan yasan ba hakan ya kamata yayi ba.


"Naga baka shigo bane, nazo naga lapiya"


Tana rufe bakinta yace


"Lafiyata kalau, bana san sake ganinki a part dina, duk Abinda kike so zaki iya kirana, idan kuma ina bukatar abu zaki ganni. Ina fata zaki kiyaye saboda gudun mummunan gani"


Cikin rashin fahimtar furucinshi na karshe ta dago Amma har ya nufi dakinshi, kanta ta dafe a ranta tana fadin Khulthum me kika siyawa kanki? Tana nan Zaune tana jiran ya fito ta fada mishi batada contact dinsa amma shiru, har ta Mike zata fita Sega wani matashi wanda shekarun shi bazai wuce 19 ba ya shigo kuma straight dakin da Musbahu ya shiga nan shima ya fada ko kallonta baiyi ba.


Kwadayi mabudin..........


Shatuuu ♥️
[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
47


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad




*Where are you my best friend, beloved and my other half, the first person I know _Salma Hassan Kwalam_ take this page please! My everything.... The person that always brags I'm not missing you but keeps on calling asking se Yaushe zaki dawo? That's my sister for me*






_VALLETTA_


Sulaim na tsaye gaban water dispenser hannunta rike da Tea mug, ruwan zafi ta tsiyayo sannan ta dawo cikin parlon dake suite din nasu, tea bag ta jefa ciki tareda cube din sugar. Seda ta juyo kafin na samu damar kare mata kallo, tayi kyau kamar ba gobe dukda babu Abinda ta shafa a fuskar Amma kana kallonta kasan Hutu, Jin dadi da kwanciyar hankali sun samu guri. Ta kara haske fatarta se glowing Take tare da murmurewa. Tana Sanye da mini skirt fari me ditson gold, rigarta wadda ko cibiyarta bata rufe ba gold da fari farin lacy design a jiki, kanta babu dankwali se parking da tayi in a ponytail design. Transparent golden jacket ta daura saman kayan wadda akaiwa ado da gashi me laushi a jiki.


Single bedroom din dake cikin suite din ta nufa, Junaid na tsaye jikinshi Sanye da bathrobe wanda ya tabbatar mata da fitowarshi kenan daga wanka, tea din ta Ajiye Kan dan table din dake gefen gadon wanda Junaid ya maida gurin wajen aikinshi system dinshi a gurin take dindin da papers yana aiki, gurin no go area ne ga Sulaim don ya hana ta saboda yace aikin school yake bai son ta gani Tunda she's still thier student.


Inda yake ta isa fuskarta dauke da madaukakiyar fara'a wanda ya bayyanar da hakoranta, wushiryar ta da kuma dimples dinta da suka lotsa baki daya, shima wani kwantaccen murmushin ya dinga binta dashi wanda yake sa takan manta har kanta, murmushin nan ba karamin kwantar mata da hankali yake ba, tana jin duk duniya in har zata cigaba da ganin Wannan murmushin Fuskarshi to she need nothing again in her life, he's everything he needs, har ta isa inda yake bai daina murmushin ba, zagaye hannunta a jikinshi tayi tareda kwantar da kanta kan kafadarshi ta na mishi kallo cikin idanu. Hannunsa yasa ya shafa kanta yace


Kinyi kyau Dove.


Thank you....


Se tayi shiru bata karasa ba saboda yadda ya tsareta da idanunshi Yana jiran tace Yaya, sakinshi tayi ta isa kan gadon ta zauna tareda fadin


Hearthrob!


Gurarshi guda ya daga tareda karasowa inda take ya zauna Yana rike hannunta tareda fadin


I'm I as sweet as that?


Dariya ta saki tana rufe fuskarta, janye hannunta yayi tareda matso da ita jikinshi yace


Comeon Dove tell me mana!


Ya fada kamar yaro a shagwabe, turo bakinta tayi tace


Kafi haka ma.


He was stunned saboda yadda tayi maganar Daga karkashin zuciyarta yake, wani farin ciki Marar misaltuwa ya kara mamaye ilahirin jikinshi, tashi yayi Daga gefenta bata tsammata ba ya daga ta sama yana rocking dinta tamkar baby, se dariya takeyi tana jin kamar duk duniyar nan su biyu kadai suka rage kuma babu Wanda ya kaisu farin ciki


"Hearthrob Kaga I'm feeling dizzy"


Jin hakan yasa ya sauketa tareda danneta suna maida numfashi kafin kuma Sulaim ta Fara ihu


"Ka daga ni "


Kafada ya maqe alamun No, hannunta tasa ta Fara tutture shi har ta samu ya zame zuwa gefenta ya kwanta Yana sakin ajiyar zuciya, wannan shi ne babbar dacewa auren abinda kake so yake sonka don shi yasan yasha Kwana!


Tare suka shirya Don yace mata zasuje restaurant din dake cikin hotel din suyi breakfast, jeans ta saka wanda ta cikashi tayi dam revealing dukkan wasu curves dake jikinta, Top ta zura wadda ta sha rubutu masu yawan gaske with different colors, wata lallausan kimono baka ta daura tareda rolling karamin veil daya sakko ya rufe mata kirjinta, tare suka nufi kofa se Lokacin ta tuna da ashe tea zata sha, dariya tayi Wanda yasa shi dubanta amma baiyi magana ba, haka abin yake lokuta da dama takan manta abubuwa da yawa, Junaid ya zama babban jigo cikin rayuwarta.


Simple abinci na breakfast aka musu serving, Cikeda nutsuwa suka ci sannan suka fita don yin walk, garin badai dadi ba ga weather dinsu itama is favourable, a yanzun Satinsu biyu kenan da isowa kasar, Seda sukai kwanaki hudu ko kofar suite dinsu basu leka ba suna ciki suna honeymoon dinsu me kyau, hakan yasa suka shaku sosae har Sulaim ta zama 'yar gari a fannin, wannan zaman ta kara fahimtar abubuwan da Junaid yake so da wanda baya so, shima kuma da Wannan damar ya daura mata mugun sabo dashi wanda an inch suka kasance basu kusa se jikinsu ya fada musu, haka Kuma yayi nasarar kawar da 60% na kunyarshi a kanta. A Kwana na biyar suka samu cab ta dinga kaisu gurare cikin Valletta basu suka dawo suite dinsu ba se yamma likis Wanda gajiya take neman ruguza su. Kwana biu suka huta sannan suka dora da gurare cikin kasar ta Malta.


Daf da Za'a Fara shiga sallar Azahar ta zauna kan wani bench dake gefen titi shi kuma ya shiga massallaci don yin sallah, wayarta ta dakko ta Fara chatting nan taga message din Jabir da na Anty Imratu, cikin hanzari ta bude na Imratun it says


"Matar Yaya, Nanda eight months kui expecting baby from me Inshaaa Allah"


Gaba daya se taji tamkar wani awaited burunta ne aka cika mata shi, Anty Imratu nada ciki, dukda ta kasance a yanayin rashin sallah hakan bai hanata yin sujudus shukr ba don nuna godiyar ta ga Allah. Tana dagowa ta Fara kiran Jabir Allah ya taimaka wayar ta shiga aikuwa yana dauka ta Fara fadin


"Alhamdulillah Yaya! I'm so happy for you guys "


Ko ba'a fada ba tasan yana cikin farin ciki Marar iyaka


"Nagode sosae mutanen Valletta, Ina Yaya "


"Yana sallah"


Ta bashi amsa, kanshi ya gyada yana Kara mata godiya bai jira sunyi sallama ba ya kashe saboda wani call dake shigowa, Jin dadi sosae yasa bakinta kamar zai yage ta Kira Mami da Imratu Amma amsa daya ce wayarsu is not reachable at the moment. Haka ta hakura badan taso ba, wani Irin dauki take ji take kamar ta shiga massalacin ta fada mishi sakon Amma babu Hali, haka Tanan Zaune se murmushi take tana jin tamkar tayi tsuntsuwa Zuwa Nigeria don taya su Yaya Jabir murna, dama rayuwar hakuri ce kawai gashi su At longest last gashi sun haihu, Dama haka abin.......


Bata karasa tunanin ba taji tattausan hannaye sun rufe mata idanu, ko baa fada ba tasan Junaid ne don kuwa turarenshi ya tona asirin shi, dariya ta saki tareda fadin


Heartthrob!


Sakar mata ido yayi, tare da jiyowa ya tsaya a kanta yasa hannunshi ya rankwashi kanta, kanta ta yi saurin mikewa tare da Dora hannunta daidai inda ya rankwashe tan, ta zumburo bakinta idanunta sun cika taf da hawaye don taji zafin rankwashin ba karya! Wuceshi tayi har lokancin Bata daena sosa kan ba, ganin haka yasa yayi saurin bin bayanta tareda shan gabanta Yana mata Abinda yasan shi ne weakness dinta wato wannan kayataccen murmushin, Hararshi tayi tana bawa hawayen damar zuba kan kuncinta, da sauri ya zaunar da ita don rabon da yaga hawaye a fuskarta tun ranar da zasu zo Malta, yasan wancan ma shagwaba ce amma wannan fa? He's the cause Bayan alkawarin da Yayi mata da kanshi akan he'll do whatever it takes to see batai kuka ba. Poor him gashi baaje ko ina ba ya sata kuka.


Itama ganin yadda Fuskarshi Lokaci daya yasa ta share siraran hawayen zafin rankwashin tace


I'm OK, kawai heartthrob mugunta kamin"


Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumota jikinshi ya rada mata abu a kunne, dariya sosae ta dinga yi hakan ya mantar da ita rankwashin da yayi mata. Seda suka koma suit dinsu ta Fara fada mishi cikin Imratu, sosae yayi murna sannan ya kira Jabir sun jima suna magana har bacci ya fara fizgarta akan carpet din kafin taji ya matso da ita jikinshi Yana fadin


"Raguwa kawai, 3 months har yanzun kin kasa conceiving se bar mana babies kike suna ficewa"


Ya fada Yana murmushi, hannunta tasa ta toshe kunnenta tana jijjiga Kai irin bata ji ba, dariya yayi yace


"Take your time dear"


A hankali yayi slipping bakinshi cikin nashi, itama cikin bukata ta bashi hanya suka Fara kissing junansu.........




🎤Zuciya ta da taka abokan juna, da basu rabuwa ko a gun Kwana! Ina a farke ko a cikin barci na kai nake tunani cikin kwakwalwa ta....
🎶






The page is very small I know.... Just manage OK..... I love you guys! Irin one love dinnan!


Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
48


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Ranar ta kasance Lahadi wanda yayi marking Kwanaki ashirin da uku da Subay'a ta baro garin na Cyprus ta dawo gida zaman jiran gawon shanu, zaman da bata san Meye makomar ta ba, zaman da wanda take dominshi bai san tanayi ba. Gabaki daya tayi rama ta kare tamkar kudin guzuri, Duk wannan abubuwan da ta dauka ta aza a kanta sun sauka da kansu ba ita ta sauke su ba. Hajiya kam bata wani koma ta kanta ba don itama tata ce ta same ta, kwata kwata ta rasa direction din Alhaji ya saka gaba, ta kasa fahimtar ina ya nufa, ita karan kanta Tana iya Kwana biu bata saka shi idanunta ba, da sassafe yake fita as early as six am sanann bazai shigo gida ba se ta twelve am, hakan seda ya tayarwa da Hajiya hawan jininta wanda ta dade da mantawa cewar Tana dashi saboda yadda take bin doka tareda kaffa kaffa.


Hankalinta a tashe ta nufi dakinshi bayan taci kwalliya kai kace sabuwar Amarya ce amma har dare ya raba gida biu babu alamar Alhaji, Karo na farko da Hajiya ta samu kanta da zubar da hawaye don tasan komai ya lalace kenan! Ita babu Abinda bata yadda ta aikata ba Irin neman taimako hannun wanin Allah, a ganinta Allah kamar yadda yayi alkawari bazai yafe shirka ba, Tasan bin malaman tsibbu manyan shirka ne hakan yasa as much as she can take kokarin ganin ta kaucewa hakan. Amma haduwa da hatsabiban Kawaye seda suka gama mata dukkan hudubiobin tsiya suka jefata hanyar malamai hakan yasa ta dage a tsaye wajen ganin 'ya'yanta imanunsu ya tsaru kuma tayi wannan nasarar don kuwa kowanne abu ya lalace ita kanje gurin malaminta ya gyara abubuwan Sede bai taba nasara akan Junaid ba hasalima baya kwatanta aiki akanshi don se ya rushe saboda tsananin adduar da rike Allah da yayi.


Wayarta ta janyo a hankali tana jin Lokaci yayi da zata bi Abinda zuciyarta Ke raya mata, ya kamata ta Fara gyara mistakes din da tayi kusan shekaru bakwai tana yi. Lokacinda Subay'a ta Fara dialing number Mami gabaki daya wata iriyar kunya ta mamaye ta hade da tsoro me firgitarwa saboda bata san wanne irin karba Mami zatayi mata, zuciyarta taji tana bugawa da karfi saboda jin call din ya fara ringing, ga mamakinta se jin muryar Mami tayi tana fadin


Subay'a!


Baki daya se ta duburburce ta Fara kame kame words din bakinta dukka suka dauke har Mamin ta Kara fadin


Subay'a Kina jina?


Ma...Ma.... Mi ina yini iiii


Ta fada Tana stammering, murmushi Mami tayi tace


Lapiya lau Subay'a kin dawo lapiya? Yasu Hajiya


Se kawai hawaye ya Balle mata, dama haka rayuwar take kayiwa mutum sharri ya saka maka da alkhairi, gashi ta gani taga wanda suka gaji arziki suke Daga gidan girma Wanda jira kawai suke mutum yayi nadama sui embracing dinshi.


Three weeks kenan Mami.


Bude Baki tayi Cikeda Al'ajabi tace


Amma babu labari, kina ina yanzun?


Ina gidanmu


Shiru Mami tayi don ta rasa me zatace, what if idan Subay'a bata san yayi aure ba taji a bakinta? Hakan babu dadi amma se tace


Ai Junaid din yayi tafiya zuwa Malta amma cikin week dinnan muke expecting dinshi, yaran kuma suna Delta wajen Imratu.


Wata ajiyar zuciya ta sauke jin inda yaranta suke in a safe hand, tasan wacece Imratu bazata cutar da yaran ba amma ita abu daya kawai take jira Mami tayi testifying auren Sulaim da Junaid don gani take karya ne Duk dare gani take kamar idan ta tashi zata ganta gefen mijinta amma ina ta riga tayi sake da damarta, Dama Anty Takori tace A BARI YA HUCE shi ke kawo rabon wani....


Mami ce ta katse mata tunaninta da fadin


Ki gaishe min da Hajiyar da 'yan uwanki.


Kanta ta gyada tace


Inshaaa Allah Mami nagode!


Daga haka sukai sallama ta kwanta tare da sakin kuka don tayi hakan saboda Mami ta shiga lamarin amma poor her Mami bata bata Koda number Junaid din ba.


Ta dade a kwance se ta jiyo muryar da ta Sata saurin mikewa don if she's not mistaken Suhaila Tajiyo, da sauri ta fito Zuwa parlourn amma mamakinta ya girmama saiamakon ganin sauran yan uwanta su bakwai gata ta takwas, kowaccensu ka kalla jikinta babu wani kwari haka suka samu guri cikin kujerun suka zauna, itama gefen sister ta zauna Tana fadin


Meye haka kamar wanda akai mutuwa zakuzo dukkanku jiki a sanyaye.


Babu Wanda ya bata amsa don babu me bakin amsar, hakan ya kara daga mata hankali se ta Mike Tsam ta nufi bedroom din Hajiya ta sameta hankalinta a matukar tashe tana amsa waya, gefe ta zauna Tana jiran hajiyar ta kammalla wayar wadda ta fahimci da Anty Kubra take wayar hakan ya kara bata mata ranta don ta tsani Anty Kubrar saboda ta hannun daman Hajiya ce, babbar aminiyarta ce wadda dukkan wani abun hajiya babu Wanda bata sani ba akan hajiyar dasu su Subay'a duk Abinda Hajiya keyi wannan matar ke daura ta akan hanya, hakan yasa Subay'a ta tsane ta itama Matar ta sani Shiyasa basa shiri kuma Subay'a ta zama koma baya a tallafin da Anty Kubra ke kawowa sauran.


Ya akai Subay'a?


Hajiya ta tambayeta bayan ta aje wayar don hankalinta yadan dawo jikinta saboda Antyn tayi mata alkawarin yau dinnan Za'a sabunta aiki, Nawa Alhajin yake da har zai zauna Yana daga mata hankali ita kuma ta wani tsaya har kwanakin nan tana kunsar bakin cikinshi.


Hajiya bazaki rabu da Anty Kubra ba? Hajiya kina kallon Abinda ya fara kunnowa cikin rayuwar mu, Duk yadda kike tsaye kanmu amma haka Junaid yayi aurenshi! Inace hakan ya zame mana izina gaba daya......


Da sauri Hajiya ta katse ta da fadin


Ke gidan ubanwa kika ji Junaid yayi aure? Waye ya fada miki?


Itafa Hajiya bata san dalilin dawowar Subay'a ba don Bata bi ta kanta ba kasancewar itama tana cikin matsalar Ashe....


Ba wanda ya fada min Hajiya, a social media na gani Shiyasa na dawo na daidaita rayuwar aurena kafin wankin hula ya kaini dare.


Hajiya ta bude Baki ta bata amsa Subay'a ta tari numfashinta da fadin.


Kizo parlour Kinyi baki!


Tana fadar haka ta fito jikinta a matukar sanyaye, tabbas basui Saar uwa ba don kaso mafi girma ita ce ta watsa musu rayuwar gidan mazajensu, ita ta dora musu halin cewar mace ita ce shugaba gidan aure ba miji ba hakanan ta sakasu suka dinga zuba iskancin su wanda duk a cikinsu Sulma ce kadai ta fita zakka.


Tana isa parlon ta koma inda ta tashi babu Abinda ya canza, gurin is so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login