Showing 75001 words to 78000 words out of 131263 words

Chapter 26 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4629

tsananin gaske wanda iya shi kadai ya isa hana mata nutsuwarta. Kafin suyi Kwana uku a garin ta rame tayi fari, tayi xuruxuru se idanuwa a warwaje. Abinda ya daga mata hankali Tunda Yaya Suhaila ta tambayeta Abinda Ke damunta Tace babu basu Kara komawa ta kanta ba, suka cigaba da sha'anin gabansu. Hakan yasa ta kulle kanta a daki ranar ta dinga kuka saboda ta riga ta gano kuskurenta, tasan da Junaid ne bazai taba barinta a Wannan halin ba amma gashi yan uwanta da suke bata da kamarsu sun manta da rayuwar ta, basu damu da ita ba a cewarsu ta dagawa kanta hankali saboda namiji kilan yana can ya manta da ita gaba daya gwara ta saki jikinta kawai.


Duk ganin hakan da take Kara daga mata hankali yake yasa tayi wanka a daddafe ta shirya cikin abaya baka tayi rolling ta fito inda ta tarar Suhaila na waya da Fannah, Tana fitowa taji Suhaila tace


Ga Mimin nan ma.


Mika mata wayar tayi, Subay'a ta karba suka gaisa da Fannah tana ta bata Sautin abubuwan da take so, Subay'a ta mata alkawari sannan ta kashe wayar tace da Suhaila.


Zanje gurin Sulma.


Me yake damunki ne, kinga yadda kika rame kuwa?


Salima wadda fitowar ta kenan daga daki ta iskesu tsaye. Baki Samiha ta tabe tace


Tace Sulma zata fadawa damuwarta, Kinsan ita kadai ce me hankali cikin mu.


Salima ta ja hannunta suka koma kujera tace


Fada min Menene.


Hawaye a hankali ya fara gangaro mata Daga idanu, se kuka me Cikeda nadama me tsanani, me yasa tabi son zuciyarta ta taho gashi ta kasa samun farin ciki Koda na awanni ne. Sosae ta dinga kuka hakan yasa Suhaila jikinta yayi sanyi ta dawo ta zauna Itama suna lallashinta. Amma ta kasa daina kuka ana haka sukaji sallamar Sulma hannunta na rikeda na Amna yar Kimanin shekara da wani abun.


Tunda suka amsa tasan babu lapiya, hakan yasa ta shigo da sauri sede ganin 'yar uwar da tafi soyuwa cikin zuciyar ta na kuka yasa Gaba daya taji hankalinta ya tashi, gefenta ta zauna ta kasa furta komai se patting bayanta da take a haka har tayi shiru, Salima tace


Kuje daki ta fada miki abinda yake faruwa.


Tare suka shiga daki su kuma suka koma dakunansu zuciyoyinsu babu dadi, haushin kansu sosae sukeji na barinta da sukai cikin damuwa for almost 3 days kenan, Anya su din sisters dinne kamar yadda take daukarsu. A daki Subay'a ta gyara zama ta kwashe duk yadda sukai da Junaid ta fadawa Sulma tana kuka Marar dadin saurare, gaba daya wuta ta daukewa Sulma don Bata taba tunanin wautar Subay'a ta Kai wannan extent din ba, Amma yanzun ba lokacin putting blames bane mafita shi ne Abinda zasu nema. Cikin nitsuwa Sulma tace


Sister bakya neman shawara, Tunda yace ki hakura me yasa zaki taho? Kinsan fushin Allah kuwa akan kin bin miji, he said all this to you and you left without his consent? Ya salam!


Sosae Subay'a ke kuka tace


Na gane kuskure na sister, Nayi dana sanin abinda nayi don haka Nigeria zan......


Bata karasa ba saboda wani sharp pain da ya turnuke mata mara, hakan yasa ta rike cikin tana fitarda wata Irin Kara da ta jawo hankalin su Salima dake dakunansu, a guje har suna Karo da juna suka nufi dakin Subay'a wadda Ke durkushe jini yace a bashi guri ya nuna nashi basirar, suna bude kofar sukai karo da Sulma wadda Ke kokarin fita kiran su, ba wanda yayi magana saboda firgici, Sulma ta Fara kiran Daddyn Amna, Salima ta kira ambulance, Suhaila kuwa tana kokarin hada kaya. Kuka Sulma take sosae saboda yadda Subay'a ke axabtuwa. Within wani Lokaci Daddyn Amna ya iso kusan tareda ambulance din akai Asibiti da ita. Anfi two hours kafin aka basu izinin shiga gurinta, Tana kwance idanunta na digar da hawaye, jini da aka karbo daga Lab Yana jikinta haka suka sameta suna mata sannu don nurse din ta tabbatar musu idanunta biyu.


Fita Daddyn Amna da Sulma sukai Don zuwa enquiring akan maganar subay'a. Seda suka zauna doctor yayi musu bayanin ciki ne da ita na wata daya da kwanaki ya samu zubewa, sunyi mata wankin ciki sannan yayi directing dinsu inda zasu biya bill din.


Suna fitowa Sulma ta sauke ajiyar zuciya saboda dadin da taji cikin ya fita kada yazo ya shiga gararin rayuwa kamar yadda uwarshi zata jefa shi a ciki, itama uwar batasan halin da take ciki ba Balle dan da bai zo duniya ba ma.


Honey ka kira Yaya Junaid ka fada mishi halinda ake ciki.


Wayarshi ya fito da ita ya fara neman layin Junaid lokacin yana zaune a office yana magana da Ridwan akan case din auren dan duk yadda Junaid yake tsamannin maganar ta wuce haka, Duk yadda yaso Mami ta fahimci inda ya dosa Amma taki hakan yasa duk hankalinsa baya jikinsa, ya rasa abinda Ke mishi dadi, the only moment dayake samun nutsuwa shi ne idan yana tare da Sulaim din to yakan manta da cewar rabasu ake son Yi, kullum tamkar son ta ake Kara mishi cikin zuciyarshi, abubuwan da a da suka fi karfin shi yanzun a saukake yake samun shi, hakan yasa sonta ya mishi mugun kamu, in har ya dawo gida to damuwa ya gama samunta Sede idan kebewa yayi a daki Amma Sulaim da gaske take ta kwace shi, Ta shiga rayuwar shi ta bashi yadda yake so, Mami ce kawai matsalar a Wannan lokacin itama ya rasa ta inda zai shawo kanta kuma baisan saka wani cikin maganar yafi son sui ita dashi. Jabir ne ma ya shiga amma ta ce ya fita ba huruminshi bane hakan yasa ya hakura.


Seda Daddyn Amna ya kira sau biyu sannan Junaid yayi picking, jin muryarshi yasa ya saki jikinshi sukai magana anan yake sanar dashi halinda Subay'a take ciki,


Yanzun ya zaayi kenan?


Ya tambaya bai masan abinda yake ji akan abinda yaji ba


Tana kwance amma jikin da sauki yanzun.


Kanshi ya gyada yace


Ka Turomin account details dinka, zan tura maka bill din asibitin se sako da zaka bata.


Inshaaa Allah zan turo maka. Bari akai mata wayar.


Bai amsa shi ba ya kashe wayar, me zaice mata ko ita me zatace mata. Bai tashi a gurin ba seda ya tura komai, Tunda ciyarwar ta akanshi take dole ko ina taje Tunda da aurenta akanshi dole ya bata abinci.


Kwanaki uku tayi a Asibiti sukai discharging dinta ta warke garau se tarin damuwar da take ciki don ta samu sakon Junaid a hannun Daddyn Amna, Tana dawowa Tace da Sulma Nigeria zata koma amma hajiya tace Allah ya bata saa, daga Wannan kuwa se ta hakura abinta ta dangana ta Fara fafutukar kiran Junaid amma Tunda yayi picking sau daya yaji muryarta, yayi blocking contact dinta don har yanzun fushi yakeyi da ita kuma bai zo gabar yanke mata hukunci ba.




Sorry for d little page.... We meet later Inshaaa Allah!


Shatuuu ♥️


*MACE A YAU*
35


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Gabaki daya yau dinnan jinta take tamkar tafi kowacce mace sa'a a Wannan ranar, jinta take tamkar something great awaits her, hakan yasa ta Mike ta daura towel don yin wanka ta Ajiye wayar ta, ta nufi bayi. Ta jima tana wanka tayi sitbath don yau dinnan jinta take samasama gwara ta kalkale ko ina.


Tana fitowa ta Fara gyara jinkinta da sababbin mayukan da ta Fara amfani dasu, tayi kyau se sheki take tana daukar ido, ta daina bleaching ta zama babbar yarinya wadda zamani ke yayi, Dama tana bleaching saboda rashin kudi yanzun kam kudi Sede ka kalla amman ba dai ta kalla naka ba haka abin yake.


Saffa saffa tayi kwalliyar tata saboda yanzun ta Fara blending da 'yan gayu ta yarda da abinda Aimana tace mata yan gayu basu kwaliyya ta hauka ta gani duk lokacin da zasu fita se on special occasions. Trolley ta bude ta Nemo wani dandatsatsen lace na idon duniya dinkin fitted gown me kyau, ta saka a jikinta. takalmi da jaka ta saka bayan ta kalli katon mirror data kafe a dakin. Tana fitowa call din Haris ya shigo, wani abokin Ashir ne wanda ta biya shi Yana fada mata move din Ashir don kome zatayi tafi son tayi Abinda yafi nashi, tafi son taji wanne step yake takawa hakan yasa ta bashi wannan aikin


Haris ya ake ciki?


Ta tambaya kanta tsaye Bayan tayi picking, Seda ya gama mata kirarin da ya saba sannan yace mata


Wani satin zai wuce Texas, wani abokin babanshi yayi sponsoring dinsa yaje yayi Chemical Engineering.


Idanu ta bude tace


How genuine labarin nan yake?


Murmushi yayi yace


100%.


Kanta ta gyada zuciyarta Cikeda hassada tace


Karka damu, nagode.


Daga haka bata jira cewar shi ba tayi cutting layin, tareda kaiwa iska naushi cikin takaici don Abinda take tsananin son gani shi ne Ashir ya kaskanta ita kuma tayi gaba amma babu komai jikinta na Bata akwai babban abu dake jiranta. Hakan yasa ta daidaita kanta ta fito Zuwa tsakar gida, Mama na Zaune tana yiwa Amira tsifa, Aisha na girki se Amir dake gefe yana duba books dinshi dake ya fara zuwa school shima. Kuma Tunda abin ya faru Baba Ke iya bakin kokari wajen ganin ya kawo abinda zasu saka cikin bakinsu, yasan barin Khulthum da yayi tana ciyar dasu shi ne Abinda ya kashe shi, ya zubar mishi da kima da darajar shi, ya Jawa yaron kunne akan ko me zata kawo Kada wani ya ci, su barta da tsiyar ta akwai ranar nadama. Sede akwai abu daya dake hunting dinsa yana ganin ko yaya ne akwai gazawar shi wajen lalacewar rayuwar Khulthum Tunda shi yayi alkawarin kula da ita Tunda ita din marainiya ce amma here she's ya tabbatar abinda yake zargi akan yarinyar kusan gaske ne amma ya kasa samunta da maganar.


A pounded yam joint dake lodge road anan ne inda Khulthum ta hada AP dinta da Salim don tuntuni tafi karfin kwanyar Huzaifa ta wuce class din Yusuf wanda Zamu iya cewar shi ne ya fara bude mata idanu to such life amman yanzun Khulthum tafi karfinshi, ta girmi tunaninshi ta Riga ta zama abinda bai taba tunani ba.


Juice kawai tayi order saboda tana jiran Salim yazo se suyi lunch tare, a hankali take sipping cikin yanga da class na mussaman da take Kara, wayarta take daddanawa tana duba latest fashion trends saboda tana son tana tafiya daidai da zamani. Tun tana enjoying abin har ta Fara gajiya da zaman baki daya ta Fara neman layin Salim Amma network ya hana communication din haka tana gani ta hakura ta cigaba da surfing cikin wayarta.


Kamar daga sama ta Fara jiyo kamshi me sanyi me kuma sanyaya zuciya Yana shiga kofofin hancinta, karku manta Khulthum din da data yanxun akwai banbancin, dukda urge da take ji na sanin me turaren haka ta danne ta cigaba da Abinda take har Seda sukai wajen Mintina goma kafin Kabir yayi clearing throat dinsa yace


Kinada class!


A hankali ta dago fararen idanunta wanda suke rikita Maza ta aje Kan fuskar Kabir wanda ya bude hanci, baki, kunne yana kallonta ya shagala sosae.


Mutane da yawa sun fadi hakan.


Ta fada Tana maida kanta Kan wayarta, cikin Mintina uku Kabir ya gama assessing dinta, balle da ta kalli idanunshi ya gama hango tsantsar zulama a ciki. Murmushi ya saki yace


Bari Naje Naga kamar I'm not welcomed here kamar Kina jiran wani ne.


Kanta ta dago tareda kallon shi tace


Ina jiran wani amma ya gaza cika alkawari bai zo ba, Kaga kenan I'm waiting for no one.


A hankali yaji Tana dada fitting gurin da yake son sakata hakan yasa yace


Then, ni kike jira dama, bari muyi order ko.


Murmushi tayi tace


Hakan ma yayi.


Cikin nitsuwa suka ci abinci suka gama babu Wanda ke magana dukkansu har suka kammalla, kafin ya dubeta yace


Muje ko?


Kanta ta gyada tareda mikewa tabi bayanshi yayi settling musu bill sannan suka nufi wata golden Benz dake Parke a gefe, seda ta shiga kafin ya bude shima ya shigo ya fara driving Yana ta harhada kalaman da zai fada mata, Amma se yaga tamkar abin yayi wuri ya kamata ya fara tuntubar me gayya me aiki kafin.


Seda ya rakata har gida, Tun daga unguwar, layin har Zuwa gidansu ya tabbatar khulthum ce kadai zata iya wannan aikin ita kadai tayi soothing abinsu, Tana da kyau na shiga taro, zamansu ya fahimci akwai turanci a bakinta, kuma babu damuwa ta waye dukda ya Lura ba wayayyiya bace tayi forcing kanta tayi blending da rayuwar da take ciki!


Bayan sun rabu yayi mata alkawarin kiranta yayi mata bayanin dalilinshi, da haka suka rabu tana ta anticipation na Abinda zai kasance kuma. Yana barin gurin Khulthum ya wuce gaida don secretary Musbahu ya tabbatar mishi Musbahu na gida. Haka akai mishi iso ya shiga suka gaisa da Musbahu dake zaune yayi zurfi akan aikin shi, Seda ya kammalla kafin ya dawo kujerar dake facing Kabir yace


Akwai wani move ne?


Dauke da murmushi Kabir yace


Babba ma kuwa, yau ka gama damuwar gwoggo sede wani abin.


Wa ka samu? A ina?


Cikin nitsuwa ya fayyace mishi komai ya kara da fadin


Idanunta na fada maka cewar kwadayyayi ce, kuma she's no one don ta Fara Law an anguwarsu ance ta bari ta fada tarkon shedan , kaga tayi daidai da taste dinmu.


Murmushi me kyau Musbahu yayi yace


Abokina.......


Se kuma yayi shiru hakan ya tabbatar mawa Kabir ya rasa wanne word zai mishi godiya. Sun tsara duk steps din da zasu dauka akan maganar sannan suka rabu.




Ranar ta kasance Monday, karfe shida na safe Junaid, Sulaim, Ahmad da Muhammad suka dauki hanyar Kaduna, ko Sulaim Bata fada ba murna farin ciki ne fal cikin zuciyata har ta gaza boyeahi ya fito karara kowa na gani. Junaid farin cikin da ya gani yasa shima yaji duk duniya kuncinshi ya yaye, farin cikin rayuwarshi, sanyin idaniyarshi na farin ciki shi waye da zai yi bakin ciki amma dukda haka deep down inside him Yana jin tsoron approaching Mami, yana jin yau yakai karshe in har Bata amince ba to tabbas komai zai iya faruwa. Sunyi nisa sosae motar shiru babu me magana yaran duk sunyi bacci, Sulaim tayi breaking silence din da fadin


Yaya


Juyowa yayi ya dubeta sannan ya kara dafe steering tare dage girarshi daya yace


Yaya..... Yaya.. Yaya! Shi ne kadai abinda bakinki ya iya fada, come on nothing sweet ko?


Dan murmushi tayi Cikeda kunya ta rasa abinda zata ce mishi, shi kuma dariya yake kasa kasa don yasan ya kashe mata baki ba zata kara magana ba. Daga nan yace


Dove.


Har cikin zuciyar ta taji Wannan sunan, she loves the name without even knowing me yake nufi, tasan whatever ya fito Daga bakin Junaid daban yake kuma me ma'ana ne, a kalla tayi soyayya da mutane kusan uku amma akwai unique abubuwa a tare dashi, abubuwa da ko bai nanata son da yake mata ba tasan a yanxun Itace a birnin zuciyarshi kuma ita take Jan ragamar shi Sede bawai ta manta Subay'a bane a'a tana nan daram cikin ranta, musamman in yayi kwance kwance ya kasheta da daddan kalamai se taji kada fa Subay'a ta dawo abu ya canxa, Tana kishin Subay'a sosae me zafi ma kuwa.


Kina ganin soyayyar Dana nuna miki ta sati biyu is sufficient for you ki zauna Dani?


Kallonshi tayi yana driving cikin kwarewa, ta yaya zatace son da yake gwada mata bai isheta ba, ko kuma yace Bata yadda Yana sonta ba, kanta ta girgixa Tana ganin lokaci yayi da zata bude mishi zuciyarta amma tana ganin kamar Lokaci baiyi ba amma abinda take kallo kadai cikin idanunshi sonta ne me tsananin gasken gaske aciki, ga kuma tsoro wanda duk yadda taso fahimtar tsoron menene ta kasa hakan yasa ta zame mishi shoulders da zai kwanta akai lokacin bukata.


*If you in d rain I'll cover u, lost I'll found u my love don't lie, E no dey lie, don't worry I'll be here and I'll catch you if u fall, I no lie, I no dey lie, give me ur hands and I'll show u which way to go, lemme be ur guide, hold on don't be afraid trust me and have some faith u be alright u be fine*




Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
36


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Lokacinda suka isa gidan, shiru tamkar masu gidan basu tashi ba, se ma'aikata dake ta aikin gyara gidan. Yana gama parking ya juyo ya dubi Sulaim da take kokarin tashin Ahmad yace


Ku shiga ciki, zan wuce wajen seminar din. A gaida su Mami.


Murmushi tayi ta gyada Kai tareda fadin


Mami zataji, take care please.


I'll definitely do that Dove.


Murmushinta me kyau tayi daga nan ta tashi su Ahmad suka shiga ciki shi kuma ya wuce. Da murna dukkansu suka shigo gidan, sojojin dake bakin gate suka kawo musu kayansu ciki. Tun a tsakiyar parlour Ahmad yake kwalla kiran Mami wadda ke kitchen tana kokarin hadawa Baba breakfast Don batayi tunanin zasu zo da sassafe haka ba. Fitowa tayi ta tsaya bakin kitchen tana binsu da kallo fuskarta Cikeda murmushi da murnar ganinsu.


Mami!


Sulaim ta fada lokacin da ta isa inda take tsaye.


Ummu_Sulaim sannunku da zuwa marhaba..


Murmushi tayi tace


Mami kun tashi lapiya?


Lapiya lau Sulaimi, Me ya samu Muhammad yake cin kunu. Kai fita a gidannan dan kaniya kawai!


Turo Baki yayi ya nufi Sulaim wadda Ke ta dariya, rungumeta yayi Mami ta kame hannun Ahmad dake sunfi shiri saboda copy din Baba ne, Muhammad kuma gidansu Subay'a yayo.


Yi hakuri rabu da Mami ko?


Kanshi ya gyada, Mami ta girgixa kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login