Showing 48001 words to 51000 words out of 131263 words

Chapter 17 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Shatuu   

20 Dec 2024

4601

ta kasance Tate dashi an Raya Daren, sayayyarta da ta kwanta ta dan kankaro wani potion daga ciki, Tana bacci ya Mike yayo Alwala ya fara kai kukanshi ga Rabbul Izzati! Baice Allah bani Sulaim ba a'a yayi addu'ar Allah ya bashi alkhairi idan ita ce, idan kuma babu alkhairi Allah yasa zuciyarshi ta dangana!


Washegari karfe bakwai Ja'afar ya iso, Junaid ya takura masa seda sukai breakfast tare, Karo na farko cikin mutunci suka gaisa shi da Subay'a daga nan Sulaim ta fito sede jikinta dukka yayi sanyi se satar kallon Uban Ahmad take, shima hankalinshi na kanta Yana kallon duk Abinda take amma bai nuna ba. Takwas daidai suka rakosu har bakin mota an zuba kaya da komai, Junaid ya miko mata envelope wadda bandir din sababbin 200 naira notes ne sannan yace


Wannan naki ne, ki Turon account details dinki zan turo miki kudin da zaki bawa mutane, Kai kuma


Ya juya kan Ja'afar


Be careful as you drive, Bana son Wannan gudun please.


Murmushi Ja'afar yayi yace


An gama babban yaya.


Itakam zuciyarta kunci take so take ko digon hawaye ya zuba mata taji sauki dukda ta rasa me yasa take jin hakan, Ahmad da Muhammad suka zo sallama aikuwa Ahmad se kuka zai bita, dama kukan take nema se kuwa ta Fara, Ja'afar yayi tsaki yace


Kin fiye shirme meye abin kukan.


Shikam Junaid kanshi ya girgixa mata yace


Ya isa haka Allah ya tsare .


Bata amsa ba amma tana ta kokarin shanye kukan a haka tana gani ta tafi ta bar Junaid kewarshi ta mamaye ta har ta kasa sakin jiki sui hira sosae itada Ja'afar seda Junaid yayi mata text din


_Those tears mean alot, is not every time ya kamata suna zuba. Allah ya kiyaye hanya_


Wata Irin ajiyar zuciya ta sauke tanajin sabon abu Wanda bata san Meye ba Yana huda mata jiki yana shiga zuciyarta, Lokaci daya kasala ta mata rubdugu Daga wannan se bacci me Cikeda farin ciki!




Gbam! Gbam!! Gbam!!! Muuna kallon kowa a 3D screen.... Ehen rate this page on a scale of 10.....


Shatuuu ♥️[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
21


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Seda suka zo Funtua kafin Sulaim ta farka Daga baccin da take shima sanyin AC Ke damunta dukda akwai hijab a jikinta amma bai hana taji sanyin na ratsa ta ba, daidaita zamanta tayi ta dubi inda Ja'afar yake tirelessly driving, a kirjinshi yaji ta farka hakan yasa ya dubeta yace


Sweetm kin tashi?


Kanta ta gyada tareda janyo bottle water dake gefenta ta Fara sha, seda Tasha Rabi kafin tace


Munzo Gusau?


Kanshi ya girgixa yace


Yarinya wasa farin girki muna Funtua.


Bakinta ta turo ta janyo wayarta ta Fara danne danne, ita kanta bawai tasan me takeyi bane,


Sweetm se Yaushe zanyi making move ne, ya kamata by now ace kowa yasan halinda muke ciki?


Da sauri ta dago kanta ta dubeshi se murmushi yake, kanta ta girgixa tace


Kai a'a gaskiya!


Kallonta yayi yace


A'a me? Sulaim bafa aure nace muyi ba at least mu sanar dasu Mami yadda Lokaci nayi dama ansan da maganar.


Kanta ta girgixa tace


Nidai a'a gaskiya


To saboda me?


Yaya yace Se naje level 3 kafin nan


Idanunshi a waje yace


Kice babanki bai amince ba, shikenan yadda kike so haka xa'ayi.


Cikeda jin dadi ta sauke nannauyan ajiyar zuciya har Seda Ja'afar ya dubeta sede ya cigaba da tukinshi, itama ganin ya bar Wannan zancen yasa ta ware suka Fara hira dukda karfin hirar shi ne, hira me dadi me tsayawa a rai.


Lokacinda suka isa garin jega sun gaji likis, nanne garinsu Mami asalin mahaifarsu itada Mummyn Sulaim anan family house dinsu yake cikin Shiyyar Ni'ima, katon gida ne ginin zamani me part biyar a cikin compound din, Tunda aka bude musu gate din wani Irin yanayi ya lullube Sulaim ta tuno lokutan da suke zuwa tareda Mummyn ta, Allah sarki mummy Allah dai ya kara haskaka kabarinsu ,bazata taba daina kewar su ba, komai zata samu bazata taba daina cewar ina ma Daddy da mummy suna raye.


Cikin parlour kayattace wanda idan ka shiga zakayi tunanin gidan wata Amarya ce amma ko daya mahaifiyar Mami ce a gurin Hajiya Juwairiyya itada megidanta Alhaji Alkasim se jikokinsu guda uku da suke Zaune dasu, Hanan yarinyar Kawu Ali wanda ke bin Mami iyayenta suna birnin kebbi, Amaturrahman diyar Kawu Mamman shi kuma Mummyn Sulaim ke binshi sa'ar Sulaim dince yan watanni ne tsakaninsu, se Najib shi kuma Yayan Hanan ne. Sauran part din gidan na sauran yaransu ne su Mami idan sunxo se su bude su Zauna.


Tunda tayi sallama Yaya Hanan dake zaune ita daya cikin parlour ta taso ta rungume Sulaim tana fadin


Oyoyo Autar Mami.


Oyoyo Yaya Hanan


Ihunsu ya janyo hankulan mutanen gidan, Amaturrahman ce ta Fara fitowa itama tana buga nata ihun kafin Hajiya ta fito Cikeda farin ciki. Cikin parlour suka zauna anata gaishe gaishe kafin Hajiya tace


Ummu tashi kuje ki dan watsa ruwa kar maghariba tayi, Jafaru kaima wuce dakin Najib ka watsa ruwa.


Duka suka Mike Don Dama abinda suke jira kenan, Amatu ce ta kaita dakin hajiya don sun San indai tazo nan take sauka, wanka ta Fara yi Allah ya taimaka tana period hakan yasa bata dauki bashin sallah ba. Gefen kujera ta zauna ta janyo wayarta, missed calls kalakala haka ta tarar, a hankali ta Fara da Baba ta sanar mishi sunje lapiya sannan ta kira Mami kafin daga karshe ta kira Junaid.


Yaya ina yini?


Lapiya lau Auta kunje lapiya?


Lapiya lau kowa Yana tambayarku.


Kanshi ya gyada yace


To ayi Hutu lapiya, Duk inda ya kamata ki tabbatar Kinje.


Kanta ta gyada kafin sukai sallama ta Mike Don ficewa se kiran Salim ya dakatar da ita


Haba princess Kinsan yadda kike wahalar da zuciyar Salim kuwa.


Dan murmushi tayi tace


Ni din?


Ke mana inda Kinsan yadda kika hana Salim sakat I don't think zaki cigaba da gasa ni fa.


Dariya tayi daidai shigowar Yaya Hanan, ta bita da kallo sannan ta shige ciki, itama sulaim din se tace


Kaga a gajiye nake ka Bari mayi magana anjima


Ina kika je?


Ya tambaya


Naje jega ne


Dama ke yar jega ce ?


Kasan jegan ne?


Farin sani kuwa amma Kada ki damu ki huta zan baki mamaki.


Kashe wayarta tayi a ranta bata ji komai game dashi ba, ita haka kurum ma take jin Bata wani aminta dashi ba. A parlor kowa na zaune har Alhaji Kasim Baffa shida Yaya Najib da Yaya Ja'afar suna zaune se zuba hira ake, gefen Baffa taje ta tsugunna ta gaishe dashi, Cikeda farin ciki ya amsa Yana saka mata albarka tareda yiwa Anty Zahra addu'a wanda hakan yaso bata atmosphere gurin.


Tana gama musu kunshin ta mike tsaye Tana buga Hamma tareda kashe torch din wayarta, seda tayi mika kafin ta shiga daki Don shirin wanka, tana shiga ta Fara daukar wayarta tayi dialing number Sulaim, bugu daya ta dauka


Hajiyan Kebbi kunje lapiya?


Khulthum ta tambaya Cikeda kulawa, itama sulaim Daga dayan barin tace


Bakiga text dina bane? Ina isowa na miki.


Kanta ta girgixa tamkar tana gaban Sulaim din tace


Ban gani ba Wallahi, kunshi nake yiwa wata Amarya.


Cikeda jin dadi Sulaim tace


Ranki ya dade, kina wuta fa


Dariya Khulthum tayi tace


Kinganni shiryawa zanyi Yusuf zan raka dinner abokinshi.


Dinner Kuma? Ke Khulthum


Rabu dani naje naga gari Kede ki zauna kiyi ta ninkaya a son Yaya!


Tsaki Sulaim tayi tace


Your skull is thick Wallahi, se anjima.


Dariya Khulthum tayi ta kashe wayar ranta fal ko ba komai yau zataje gurin da bata taba Zuwa ba. Fitowa tayi daure da towel taje ta sheka wanka kafin ta dawo daki tayi shafe shafenta kafin wani Lokaci ta fito tayi dau kamar a saceta, fuskarnan dolled up. Kunsan fa Sulaim kyakyawa ce babu karya, fatarta tana da haske amma bawai can ba, zama a iya saka ta layin matsakaita, asalin skin color dinta me kyau ne Amma saboda yadda take bleaching skin din yasa tayi haske kamar rana. Fuskarta round face ce me manyan idanu hancinta Yana da tsayi, bakinta matsaikaici ne sede batada cikar gashin gira hakanan eyelashes dinta ba can dogaye bane Amma bazaka saka Khulthum a matsayin marar kyau ba, kallo daya kayi mata se ka Kara Balle uwa uba jikinta, shape dinta me kyau bata cikin gajeru haka bata cikin masu tsayi average height gareta. Tanada hips wanda ya kawata ta yake saka ta jin ita din tayi Saar halitta, tana ji dashi tamkar kwai.


Wani cord net peach dinkin fitted gown ta saka wadda ta kamata sosae daga kasa ta bude, high heel ta dakko Baki ta saka, haka dankunnenta bakake sannan ta daura wani bakin scarf yayi kyau, ya amshe ta haka ta fito Tana fitarda fitinannen kamshin da sai wanda ya kai zuciya nesa ne zai iya jurewa.


Tana fitowa sukai kicibis da Mama wadda dawowarta kenan daga suna itada A'isha, matar badai yawo ba. Kallonta tayi tace


Khulthum ina zaki da daddare haka.


Agogon dake manne a hannunta ta kala takwas da rabi sannan ta dubi wanda tayiwa kunshin tace


Zan fita ku bawa Amira kudin ta aje min


Ta fada Tana nuna Amira don duk gidan sunfi shiri da Amira hakanan tafi yadda da ita, se kuma ta dubi Mama wadda tayi jagalo tana kallon Khulthum din tace


Dinner zanje, anjima zan dawo?


Ta fada Tana juyawa Don ficewa, Mama ta dubeta tace


To yanzun saboda Allah wani Irin biki ne se dare, kalleki ko lullubi babu, a haka zaki fita?


Kafarta ta buga tace


A haka ake zuwa, kuma ba dadewa zanyi ba fa.


Badon Mama taso ba tace


Allah ya kiyaye ki kula da kanki.


Bata jira cewar su ba ta fice, nan A'isha ta zauna dabas tana mamakin Khulthum Yaushe idanunta suka bude har haka, to idan an Fara biki 8pm Yaushe zaa saka ran tashi kenan?


Yar president tana wuta fa! Kalla batafi two hours ba yadda tayi dolling fuskarta.


Daya daga cikin yan kunshin ta fada, amaryar ta girgixa Kai tace


Ni kuma na raina mata Wallahi yadda ake zuzuta ta banyi tunanin nan ne gidansu ba.


Mhmmm ga shegen girman kai!


Ke ni abinda yake dauren Kai yadda bata girmama iyayenta, Zuwa na kusan biyar kenan amma Karki so kiga disrespect.


Fitowar A'isha ya saka sukai tsit. Ita kuwa Khulthum tana fita sukai karo da natacce kamar yadda ta rasa mishi yanzun wato Ashir, dauke kanta tayi tamkar bata san Allah ya halicce kamar shi ba, shima se ya bita da kallo tamkar idanunshi zasu fado kasa har ta bude motar Yusuf tayi wa kanta masauki. Haka yana nan Zaune Yusuf yayi reverse ya fice abinshi. Ashir ya runtse idonshi tareda kaiwa iska naushi, Allah kadai ne bai saka zuciyar Ashir fashewa ba, shi kanshi baisan lokacin da ya dauka yana zaune kan Lifan dinshi ba. Yanzun ya daina mamakin Khulthum abu daya ya yanke gobe zai sameta ayi Wacce xa'ayi don ya gaji, yanzun ya fahimci kwatakwata Khulthum ba shi ne a gabanta ba, ya tuna wata magana da ta taba fada mishi cewar matsawar ta samu me kudi to zata iya barinshi tayi aure me kudi, don haka better yayi kudi. Dukkan tunaninshi ya tafi a wasa take amma yanzun ya tabbatar da gaske take.


A FABS event center dake Magajin Rumfa nan ake kayataccen bikin, Tunda suka shigo taji ta kaskanta, taga mata iri iri Maza daban daban Kala Kala. Sede babu halin jamming dasu don Yusuf ya kafa ya tsare, basufi 20 minutes ba yace mata ta tashi zata rakashi wani guri, kamar kada ta tafi haka taji don Bata gama feeding idanunta ba. A cikin harabar Royal Tropicana Hotel yayi parking lokacin agogo ya buga Tara daidai. Kallonshi tayi yayinda yake kakkashe sauran abin motar yace bai ko kalleta ba


Muje ko?


Ina ne nan?


Ta tambaya gabanta na faduwa


Bakiga Hotel aka rubuta ba ko bakya ganewa ne?


Wani mugun yawu ta hadiya tace


Kaje ni zan jiraka daga nan!


Kallonta yayi yace


Me yasa kike abu kamar baki waye ba? Muje Karkiyi dare


Tsoro sosae cikin idanunta tace............






Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
22


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






I'm so sorry people of shatuuu kingdom.... Labarin haka ya tafi dole haka zaayi. Nasan Kuna son Khulthum amma kui hakuri don't throw me out of the kingdom pleaseeeeeeeeeeeeeee


Idanunta a runtse amma ba bacci take ba Sede hawaye da suke zuba daga idanunta, me take ji yau nadama ce? Wadda batada amfani ko kuwa? Mikewa tayi ta dubi wayarta dake gefen pillow dinta, unlocking tayi don duba karfe nawa, it's 1am na dare amma idanunta babu alamar akwai wani abu waishi bacci, yau tana tunanin ta karyata maganar da bahaushe yace Bacci barawo ne! Yau duk satar shi bai isa satarshi ba, baccin ma dama ce kuma samun guri ne amma yau tasan babu Wannan damar babu Wannan gurin. Mikewa tayi ta dubi Amira da A'isha dake bacci sadidan amma ita ya kauracewa idanunta. Gefe daya ta koma ta hada kanta da gwiwarta ta saki kuka a hankali me cin rai amma kasancewar dukka bacci suke me nauyi yasa babu Wanda ya farka.


*Some hours ago*


Idanunta Cikeda tsoro tace


Bangane Abinda kake nufi ba Yusuf, Dan.....


Bai bata damar karasa maganar ba ya samu damar hade bakinsu guri guda, cikin nitsuwa yake Bata sensual kiss me tafiyar da hankali da kuma sanya nutsuwa ga wanda ake yiwa. Sede komai is based on nutsuwa da kwanciyar hankali, Khulthum ta rasa duka kokarinta kawai ta kwace kanta sede waye yace mata shi Yusuf din rukon wasa yayi mata. Kuka sosae take tasa hannayenta Baki daya tana dukanshi amma ko gezau baiyi ba, Seda ya nutsu kafin ya sake ta, Yana mata wani Irin duba irin na goggagun yan duniya wanda suka kware a bariki, se lokacin ta lura Baki daya he's not that gentle yusuf she knew wannan Ya koma mata wani iri Wanda batasan ta yadda ma zata muku describing dinshi ba.


Meye kike kuka? Is just a kiss


Hannushi dake saman kafadarta ta doke, cikin idanu take kallonshi hawaye na bin kuncinta tace


Dama ba so na kake ba? Dama yaudara ta kazo yi, jikina kake so?


Kallonta yayi ya langwabar da Kai kalar tausayi yace


Come-on Baby, zuciyarki da jikinki duk mallakin Khulthum ne kinga don naso abu daya daga cikin ai ke naso. Ki share hawayenki I didn't mean to kinji, mistake ne Babe. Muje na kaiki gida.


Rufe fuskarta tayi da palms dinta ta shiga kuka Tana tayi amma Marar sauti, bata san ya takeji a zuciyarta ba amma kunci ne fal a ciki tana ganin tamkar rayuwarta ta tarwatse kenan. Shikam Yusuf pretending kawai yake amma haushinta yakeji fal zuciyarsa, Tana tunanin taci banza ne, karya take ai bani gishiri in baka Manda dan haka definitely se yayi Abinda yayi niyya. Shi da take tambayarshi Dama Baya sonta ne mamaki ta bashi, Bayan bai taba ganin kwayar so cikin idanunta ba se zallar zalama da son abin duniya, Tunda ita son abin duniya take to tabbas zai bi hakan ya karbi abinda yake so.


Har kofar gida ya rako ta lokacin goma saura, Seda ya saka ta gyara fuskarta don kar a fahimci wani abu sannan ya kara assuring dinta shi he never mean any harm, kawai sonta ne yake saka yake jin wani mugun feelings akanta wanda tasan idan da so definitely akwai Sha'awa.


*Present*


Asabar fari tayi sallah sannan ta samu bacci ya dauketa, kasancewar babu inda zataje yasa se karfe goma na safe ta tashi lokacin Mama ce kawai a gidan. Da shirin wanka ta fito ta fara lekawa dakin Mama tace


Ina Kwana Mama.


Lapiya lau Khulthum, me ya samu idanunki suka kumbura.


Kanta tayi saurin juyar wa tana ganin kamar Maman tasan Abinda yayi transpiring tsakaninta da Yusuf.


Mmm.... Kin.... Ga... Bacci ne


Kanta ta gyada kafin ta bar gurin da hanzari to avoid further questions. Seda ta shirya kafin ta dauki wayarta tana ganin ya kamata ta fadawa Sulaim abinda ya faru, ko ta bata shawara. Sede tana Fara ringing tayi saurin katse kiran saboda tana tunanin me zata fada mata, Bayan sau nawa tana mata fada akan kule kule yanzun ai dariya zatayi mata batasan wannan ba Sulaim bace, ba kowacce kawa ce Sulaim ba she's one among millions, kuma ba zata taba barinta cikin wannan halin ba...... Tunaninta ya katse lokacinda Sulaim tayi returning call din, babu yadda zatayi haka tayi picking Din sede kafin ta kai ga fadin Abu Sulaim din tace


Kin kyauta Khulthum ko dan birthday wishes dinnan babu kowa yayi min banda ke.


Kai Khulthum ta girgixa Wayyo bestie's birthday ta manta amma taji rashin dadi, cikin lallabawa tace


Ayya! I'm sorry Wallahi kaina ke ciwo yanzun tashi na kenan.


Ayya Allah ya baki lapiya.


Amin..... Happiest birthday dear


Murmushi Sulaim tayi tace


Thank you.... Kinsan wannan Salim da na baki labarinshi?


Kanta ta gyada tace


That Arab?


Yawwa Kinsan Mamanshi ce Egyptian, babanshi kuma full blood shuwa ne. Shekaranjiya that's ranar da naje Jega yake cemin yasan jega he'll surprise me, dazu wajen 8 na safe naga blinking din location dina kamar ana tracking dina......


Me ya faru?


Khulthum ta katse ta idanunta a warwaje, Sulaim ta buga tsaki tace


Labari fa nake Baki Kiyi shiru, se nayi saurin kashewa Kinsan ko Mintina ashirin ba'ayi ba Yaya Najib yazo yace nazo nayi bako, I was like waye? Tunda banda AP da kowa kinga jiya birnin kebbi muka wuni, Amma Hajiya tace na wuce Kada na wulakanta mutum. Unbelievable

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login