Showing 42001 words to 45000 words out of 46920 words
Chapter 15 - NI DA KE COMPLETE Document from Feedy Abdallah.txt
mum tayi tana girgixa mishi kai ta dauki lokaci kafin tace
"Khalil karka manta fa Yar uwarka ce???"
"mum I known amma wannan hadin da kuke kokarin koma hadawa baxeyu ba kawai ayiwa baba me gadi magana idan ta haihu a daura musu aure idan xe iya sai yabar aikin gadin ni xan bashi abun yi don in ba haka ba baxata auru ba kwata_kwata don wannan mummunan tabo da aka makala mata"
yafada yana sauke ajiyar xuciya
"koh ma waye ne ai asirin shi xe tonu cuz haihuwa kawai muke jiran tayi sai mu fara bincike"
wani irin kadawa yaji kayan cikin shi yayi Yar baraxanar murmushi yayi a xuciyar shi kuwa yake cewa dole ne insan yanda xanyi in barar da cikin nan kafin asiri na ya tonu d'an washe baki yayi yana cewa
"hakan ma yayi"
"Kaje dad dinka nason magana dakai"
tafada tana tashi nan tabar part d'in tana fita ya hade hannu yana kaiwa bangon dakin naushi tsabar haushi da sauri ya dauko phone d'in shi ya kira saif
"saif Ku dakatar da aikin nan"
yana fadar hakan ya datse wayar fita yayi ya nufi main part d'in gidan a xaune ya tarda iyayen shi koh wanne ka kalle fuskar shi kasan cike yake da bacin rai xama yayi a kasa ya sunne kanshi kasa kafin dad yayi magana ya fara cewa
"Dad don Allah kuyi hakuri gameda abunda ya faru daxun ba hali na bane kuma ba tarbiyar da kuka bani bane raina ne yayi matukar bacewa please Ku yafe mun...."
sanyayyar iska dad ya furxarda ya hade hannayen shi a kirjin shi
"Idan rai ya baci sai hankali ya gushe...???"
cewar dad yana kallon khal
girgixa kai yayi yana dafa kafar mahaifin shi tareda cewa
"please dad ka yafe mun"
cikin muryar tausayi yayi maganar hannu dad d'inshi daura a kanshi yana cewa "na yafe maka Allah yayi maka albarka"
"Ameen"
yace yana tashi nan yabar gidan gaba daya direct asibitin wani friend d'inshi ya nufa Wanda sukayi karatu tare.
Bangaren Firdausi kuwa duk ta kasa sukuni amai kawai take xabgawa ga abun kasala da take ji kuka take me tsuma rai hakan ta tashi jiki ba kwari ta nufi part d'in dad sallama tayi ta fada parlourn
A jikin mum ta xube tana kuka
"mum don Allah Ku cire mun cikin nan mutuwa xanyi.....cikin matsanacin kuka tayi maganar ajiyar xuciya mum ta sauke tana kara rumgume Firdausi a jikinta tace
" mamana kiyi hakuri Allah yayi miki maganin wannan abun"
"Allah mum baxan iya ba ji nake kamar baxan kara kwana a duniya ba
Saurin toshe bakinta dad yayi yana sharar xaxxafan kwallah dake anbaliya a fuskar shi cikin tattausan murya me cikeda tausayi yace
"mama kiyi hakuri har Allah ya sauke ki lafiya"
cikin kuka tace
"Dad wallahi bana son cikin nan please ka fitar mun dashi"
mum ce ta gyara ta tana kallon wuyanta ta daura da cewa
"Waya rik'e miki wuya haka....??"
xaxxaro ido tashiga yi tana tunanin abunda xata ce don batason tace khal ne wani sabon kuka ta fara nan taji amai na shirin xuwa ba shiri ta tashi da gudu tafara kwarara amai bin bayanta sukayi bayan ta gama suka fito tare kwantarda ita sukayi nan tayita sauke ajiyar xuciya har bacci yayi awon gaba da ita around 3:30pm ta tashi Barin dakin tayi ta nufi Nata wanka tayi ta dauro alwala ta gabatarda sallah nan ta kishingide tana jan tasbi
Gabbbbbb taji an bugi kofar dakinta da sauri ta waigo tana kallon me shiga dakin tsaye ta Ganshi ya hade hannu a kirji face d'inshi a murtuke kamar Wanda be taba dariya ba kallo daya xaka mata kasan cike take da tsoro cikin takun shi na kasaita ya iso gabanta ya durkushe yana mata kallon tsantsar tsana
Wani kololo me dacin ta hadiye tana jin xuciyarta yanda yake bugawa da Sauri ta toshe bakinta sanadiyar amai dake son kufce mata da sauri ta yunkura ta tashi ya riko hannunta da karfi fara yunkurin aman tayi ba shiri ta sakar mishi shi a rigar sa ganin ta bata mishi Riga yasa ya sake hannunta tana ganin ya sake hannunta tayi toilet da gudu ta rufe kofar bala'in haushi ne ya cika shi ya dade wajen
Sai huci yake kamar wanda xe hade xuciya haka ya juya yabar dakin cenxa kaya yayi wanka nan ya dawo dakin nata a kwance ya sameta tana ganin shi ta tashi tana rabon ido kama hannunta yayi
muryanta na cracking tace "don Allah ka fita wallahi banason kamshin turarenka pls"
kamar xatayi kuka tayi maganar cikin muryan rashin tausayi yace
"Ki mutu mana shashashar banxa kawai ki tsaye allura xan miki kuma kuka kuskura kuka yards aka komai had a auren nan. Saina hallaka ki Ni DA KE baxamu taba yin rayuwa ba"
share hawaye dake rolling a beauty face d'in ta tayi tana cewa
"allurar me....???"
"ta ubaki ce"
cikin xafin rai ya fadi haka marairaice fuska tayi ta hade hannu Biyu waje daya alamar roko tace
"don girman Allah yaya Khalil ka taimake ni ka rabani da cikin nan wallahi mutuwa xanyi inhar nacigaba da rainon wannan cikin bakin ciki xe kashe ni kuma su dad sunce idan na haihu xasuyi bincike gameda dan kuma ni banason asirin ka ya tonu"
cikin matsanacin kuka tayi maganar
Xama yayi ya dafe kanshi yana jin kalaman ta na mishi yawo akai murmushin mugunta yayi yace
"Ki tashi inyi miki wannan allurar shi xe xubda cikin yanxun nan"
da sauri ta mike tsaye duk da tana tsoron allura sosai hakan ta hakura ta tsaya yayi mata yana mata ta kwanta don jiri da takeji komawa part d'inshi yayi ya xauna yana
Tunani kala kala agogo dake daure a hannunshi ya duba da sauri ya tashi ya nufi dakin nata a kwance yasameta tana bacci xama yayi yana facing dinta lokaci daya yaji tausayinta ya saukar mishi a xuciya dafe kanshi yayi yana furxarda xaxxafan iska daga bakin shi a hankali ta bud'e sexy eyes dinta ta sauke su a kanshi ta sauri ta tashi ta nufi toilet ta shiga kwarara amai kamar xata amaye kayan cikinta xaune yake nan yana jin wani irin tausayinta bayan ta dawo ne ya kalleta yana cewa
"bakiga alamar komai ba...??"
ataikace yayi mata tambayar gyada kai tayi alamar eh ajiyar xuciya ya sauke ya dauko wayar ya kira wani number ringing daya akayi picking
"Doctor bafa alamar komai har yanxu almost 1 hour kenan"
"Khalil inafa ganin wannan yarinyar jininta nada matukar karfi don ba abunda yakai wannan allurar karfi wajen xubarda ciki ina ganin kawai ka kawo ta asibiti sai ayi mata abortion yafi.."
"alright insha Allah xan kawota gobe"
yafada yana kashe wayar daga nan ya tashi yabar dakin.
Da safe around 7:30pm ya shirya tsapppp cikin suit brown color wanda yayi matukar yi mishi kyau sai kamshin turare yake dakinta ya nufa a hankali ya murda handle din kofar dakin yaji a rufe take knocking yayi cikin bacci taji ana knocking d'in kofar jiki ta kwari ta tashi taxo ta bud'e door d'in "ki shirya yanxun nan.."
yafada yana barin wajen cikin kankanin lokaci ta shirya tsabb tasa dogon hijab a parking space tasame shi nuni ya mata data shiga motar
Basu dauki lokaci ba suka isa wani asibitin direct office din doctor ya nufa hannu yabashi suka gaisa nan ya nuna mishi Firdausi nan ya fita nuni doctor ya mata da kujerar dake gabanshi alamun ta xauna xama tayi tareda sunne kanta kasa waya ya dauka ya kira wata nurse taxo cikeda da girmama ta gaida me gidan nata tana jiran umurnin da xe bata nuna mata Firdausi yayi yana cewa
"ki kaita ki cire cikin"
"ok sir
Tace tana cewa Firdausi tashi muje, wani daki suka shiga xama Firdausi yayi itama nurse d'in taja kujera ta xauna cikeda kulawa take kallon Firdausi tace
"baiwar Allah meyasa kikeson cire cikin nan meyasa kikeson aikata abunda yake haram....???"
shiru tayi tana share hawaye masu xafi da suka fara sauka daga idonta tace
"don cikin bata ta hanyar haram aka same shi..."
jim nurse d'in tayi tana cewa
"Shine kuma kikeson aikata wani haram din ga xunubin xina gana xubda cikin da xakiyi da wanne xakiji...???"
shiru Firdausi tayi ta kasa motsi maganganun nurse d'in ne kawai ke yawo a kanta "kin cenxa shawara ne koh kuwa kina akan bakar ki....??"
Taji nurse d'in tafada
"a cire kawai...."
[6/17, 11:11 PM] Feeby: ♣️♥️♣️
*_NI DA KE...!!!_*
♣️♥️♣️
```♥️Dole muyi rayuwa........♥️```
_😘😘By fêêbyrh😘✍️_
*Alhamdulillah am back Ina godiya matuka da irin kaunar da kuka nuna mun Allah yasaka da mafificin alkhairi😘*
page 3️⃣2️⃣
"A cire shi kawai"
tayi maganar ba alamun tausayi a fuskarta don xuciyarta ya rigada ya gama bushewa
Xaxxafan iska nurse d'in ta furxarda daga bakinta tana kallon Firdausi dakyau kafin ta Dora da cewa "ai dama ku Yan matan bariki karuwai wa'inna suka gama bada mutuncin su a titi ba tsoron Allah kuke ba"
tayi maganar batareda ta juya ta kalleta ba sosai maganan ya batawa Firdausi rai amma hakan ta cije ta sunne kanta kasa tana wasa da faratan hannunta masu kyau da daukar hankali wani irin kuka mexafin gaske ke kokarin kufce Mata da sauri ta runtse bold sexy eyes d'in ta
Ba abunda ke mata yawo a kai sai maganganun nurse d'in wa'inda suka matukar bata mata rai
"gyara allura xan miki kiyi hakuri fa naga ranki ya bace...."
shiru Firdausi tayi tana goge xaxxafan hawaye dake rolling a beauty face dinta ajiyar xuciya ta sauke tana tashi tsaye nan nurse d'in ta matso dafffff da ita ta mata allurar "ki cire kayanda ke jikin ki ga wannan ki saka"
tafada tana mik'a mata wani riga Wanda ake sakawa idan xa'ayi operation saka rigar tayi ta nufi gadon da nurse ta nuna mata alamun ta kwanta kwanciya kayi gabanta sai bugawa yake kamar xe fasa kirjinta ya fito ware kafafunta nurse d'in tayi tana dauko wani karfe wanda ta saka agiyan shi a socket ta kunna tana kokarin sakawa Firdausi shi ihu tasaki tana tashi da sauri "na fasa wallahi.."
tayi maganar jikinta na mugun rawa cikeda mamaki nurse d'in ke kallonta tana mamakin yanda akayi ta cenxa ra'ayinta nan take duk da ta nace akan a xubda cikin da sauri taja kayanta ta shiga inda ta cenxa kayan da farko nan ta saka kayanta da ta cire jikinta na rawa ta iske nurse d'in tana kuka tace "don Allah ki taimaka mun ki gayawa musu cewar kin xubda cikin please"
dan murmushi tayi tana dafa shoulder d'inta tace "insha Allah xanyi miki yanda kika ce Allah ya rabaki lafiya"
"Ameen"
Tace tana share hawaye dake rolling a beauty face d'in ta nan suka fita nurse d'in ta sanarda doctor d'in cewar an cire cikin kudi masu matukar yawa khal yabawa doctor d'in harda nurse nan suka bar asibityn suka nufi gida a hanyar su na komawa gida ya tsaya bakin wani shago ya siyo Mata pad basu sauki lokaci ba suka isa gidan cikin tsanda ta isa dakinta cenxa kayan jikinta tayi saboda xafi takeji toilet ta nufa tayi wanka ta fito kwanciya tayi ba'a dauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.
Kwanaki sunja inda khal kusan watan shi biyar a Oman cikin Firdausi kuwa ya tsofa sosai hakan su mom ke Kula da ita sosai ba abunda sukeso ya taba ta balle cikin da take dauke dashi.
b'angaren khal kuwa rayuwar yake cikin jin dadi duk mugayen halayen shi ba Wanda ya Bari sai abunda ya karu don nan ne yake samun Yan matan larabawa yana morewar shi shaye shaye kuwa sai abunda ya karu yama manta da wata Firdausi balle ya tuna cewar cikin shi na'a jikinta.
B'angaren momyn Firdausi kuwa tuni sukayi aure da malam inda dadyn khal yabashi manyan kwangiloli yana yi yaxama babban mutum duk yanda yaso abashi Firdausi firrrrrrr dad yayi ya hana shi hakan suka cigaba da rayuwar su.
Safiyar ranar lahadi matsanacin ciwon Mara da baya ne ya tayar da Firdausi ba abunda take sai kuka a hankali ta tashi tana jan kafa harta fito dakin dakyar ta sauko down stairs nan ta fadi tana juyi su mom dake xaune suna breakfast ne sukayi kanta da gudu ba'a dauki lokaci ba ta haihu ta haifo da namiji nan da nan suka shiryata daman sun saye komai na haihuwar har kayan jarirai ba abunda suka Bari duk wannan abun da ake mom jin take kamar xuciyarta xe fasa kirjinta ya fito sanadiyar mummunan abunda ta gani sakkk yaron da Firdausi ta Haifa kamannun shi daya da khal hoton khal da yana karami ta dauko tareda baby d'in ta kaiwa dad xama tayi ta hade hannu tayi tagumi hawaye masu xafin gaske ke fita daga idonta tsananin bacin rai da take ciki jinjirin ya kalle batareda ya kalli hoton data kawo masa ba
"Ai wannan Khalil ne...."
yafada voice d'in shi na rawa, cikin muryan kuka ta soma magana
"yanxu abunda yaron nan ya mana yayi daidai....?"
tafada kuka na k'ara kufce mata mom d'in Firdausi ce ta shigo dakin don tun lokacin da take labour aka Kira ta ganin fuskar yaron ne yasata yin suman tsaye saurin dafe xuciyarta tayi don bugawarda take xama tayi tana karban yaron , nan da nan dad yasa aka Kira mishi Firdausi mom ce ta Kirata sun dauki lokaci a dakin ba Wanda yace komai dad ne ya dauko wayar shi ya Kira khal yayi mishi kusan 19 missed call amma be daga ba nan ya tura mishi text message cewar yana son ganin shi yau d'in nan daga nan ya juyo yana facing d'in Firdausi wacce ta sunne kanta kasa hawaye na wanke mata fuska
"Mamana yanxu kin kyauta boye mana gaskiyar da kikayi..?"
Da sauri ta dago da kanta tana kallonshi matsanacin kuka ne ya kufce mata dasauri ta tashi tabar parlourn direct dakinta ta nufa rufe kofar tayi da key ta fada kan tafkeken bed d'inta tana kuka me tsuma xuciya yinin ranar haka ta wuni.
Su dad kuwa wa'inda ke xaune kamar masu amsar gaisuwa sallama akayi gaba daya suka juya ganin me sallamar mamaki ne bayyane k'arara a fuskarsu ganin abokin khal Wanda tun suna yara suke abota yanxu wata shida kenan kullum sai yaxo Neman khal idan kuma aka tambayeshi lafiya yake Neman shi sai yace eh xama yayi gabansu yana hawaye
"Lafiya ...?
Suka tambayeshi baki dayansu.
😘😘FÊÊBYRH😘
[6/17, 11:12 PM] Feeby: ♣️♥️♣️
*_NI DA KE...!!!_*
♣️♥️♣️
♥️```Dole muyi rayuwa.........```♥️
_By 😘😘fêêbyrh😘✍️_
Page 3️⃣3️⃣
"Lafiya....?
suka tambaye shi baki dayan su, dogon nunfashi yaja ya sauke tarefa furxarda xaxxafan iska daga bakin shi
"Dan Allah dad kuce Khalil ya yafe mun har kuma ku yafe mun dan Allah...."
yayi maganar matsanacin kuka na kufce mishi baki suka Saki gaba dayan su suna mamakin irin wannan al'amarin Anya kuwa yana cikin hanyacin shi? haka suketa maganganu a xukatan su
"kwantar da hankalin ka Lamir kayi mana bayani dallah dallah yanda xamu fahimta...."
dad ya fad'a yana gyara kwanciyar jinjirin dake hannun shi
"Dad na xalunci Khalil na cuce shi na bata mishi rayuwa"
yayi maganar yana kuka sosai rik'e baki mom tayi tana Kara mamakin maganar shi
"Dan Allah ku yafe mun wallahi duniya ta juya mun baya na cuce shi....be gama magana ba dad ya katse shi da cewa
" wanne cuta ne ka mishi dahar duniya xata juya maka baya kashe shi kayi ne...?
Ajiyar xuciya ya sauke tareda shak'o nunfashi me xafi yace
"A'a amma na tabbata idan ya mutu a cikin wannan mummunan halin nasan ba shakkah wuta yayi sai dai shi Allah ba axxalun wani bane..."
"hakane..."
cewar momyn Firdausi.
"A lokacin da muke karatu khalil ba ruwan shi da duk shashancin da muke da abunda ya dame shi da sha'anin wani ba ruwan shi da Yan mata balle shaye shaye da muke shi karatun shi kawai ya saka a gaba duk yanda xanyi in bata masa rayuwa nayi amma banci sa'a ba na bashi mugayen shawara amma koh sau daya be dauka ba naso in yaudare shi in mallaki duk dukiyar da ya mallaka amma hakan yaci tura hakan yasa na yanke shawarar Neman boka Wanda xe tarwatsa masa rayuwa, naje wajen bokaye sama da goma amma duk abu daya ake fada cewar baxa'a samu nasara ba saboda riko da addinin da yayi hakan na hakura da karshe na samu wani bokan nan ne nayi arxiki aka samu akayi masa aikin nan ya fara banxar rayuwa irin wacce nake bukatar yayi nan muka cigaba da hole rayuwar mu ganin Khalil ya fini kwamkwajewa wajen harkar shiyasa na fita sha'anin sa har xuwa lokacin da xamu gama karatu bayan rabuwar mu nayita aika mishi mutane wa'inda xasu mayarda shi baya su kwashe duk dukiyar