Showing 36001 words to 39000 words out of 46920 words

Chapter 13 - NI DA KE COMPLETE Document from Feedy Abdallah.txt

20 Dec 2024

3944

Hankalin kowa ya tashi musamman da mutane suka fara hallara ana shirye-shiryen d'aurin aure, ango ya sha kwalliya cikin shadda gizna sai bada kamshi yake yi inda har dad d'inshi da sauran Yan uwa da abokan arxiki sun hallara a wajen kowa cike yake da fara'a musamman ango faruq
Alhaji Muhammad sai sassarfa yake yi ya kasa xaune ya kasa tsaye.........dungule hannun shi yayi cikin takaici ya kaima iska duka yana wuci.........., Me yasa Firdausi take nema ta basu kunya? Da wani ido zasu kalla mutane suce amarya ta b'ata? wani B'angaren xuciyarshi kuwa yana xargin khal gameda bacewarta Cikeda takaici ya dubi khal ya dauki lokaci yana mishi kallon rashin yarda "Khalil kaje ka dauko yarinyar nan inda ka ajiyeta......!!!!" kamar daga sama khal ya tsinci wannan maganar wani irin mummunar fadiwar gaba yaji karfin halin saita kanshi yayi tareda marairaice handsome face d'inshi lumshe sexy bold eyes d'inshi yayi ya bud'e a hankali yana cewa "subhanallah dad bana tunanin xa'ayi xargeni a wannan lamarin mexe sa in dauke kanwata and dad duk abunda kuke ganin inayi nasan halin faruq ne ciki da waje shiyasa kaji ina magana akai kuma tunda kayi mun magana ban koma saka bakina a lamarin ba ai farin cikina nane inga mun aurar da ita lafiya...."
Ajiyar xuciya dad ya sauke ya rasa inda xe saka kanshi.






Waliyin ango ne ya shigo yake shaida musu cewa su fito a fara d'aurin aure mutane sun fara gajiya dan jira Alhaji Muhammad ya ja shi gefe shi baban Faruq ya hau kora mishi baya ni.
Ran Baban faruq ya baci sosai ya hau masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba ya za'a yi sai bayan an gama shirya komai suce amarya ta gudu? wannan ai zancen banza ne. Dama can y'ar su karuwa ce Allah ya taimaka ma da basu lik'a ma d'an shi ita ba.
Mahaifin khal dai shiru yari yayin da katutun bakin ciki ya tok'are mishi zuciya......,
Alhaji Muhammad ne yayi gyaran murya ya daura hannun shi a kafadar lukma wato baban faruq cikin tattausan lafaxi ya soma magana
"Haba lukman kayi hakuri wannan ba magana bace sarai kasan wannan yarinyar baxata bata ba tareda wani kwakwaran dalili ba don Allah ka fahimceni....."
"kaga Alhaji Muhammad ba'a shaidar yaro tun dama faruq ya sanarda ni cewar Khalil baya son wannan auren kuma meyasa tun farko Baku sanarda mu batan ta ba sai yanxu xaku gaya mana maganar banxa.....???"
dafe kai dad yayi yana jin yanda kanshi ke sarawa kamar xe bar kanshi Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yaketa furtawa a hankali
Alhaji lukman ne ya kira danshi faruq yaxo ya zauna a kasa, idan nine na haifeka ina son ka fasa auren nan domin baza ka aure ballagaza yar iska ba......da sauri ya d'ago yana kallon mahaifin shi lokaci guda zufa ya fara k'aryo mishi.
"Dad me yasa ka kira Firdausi da sunan karuwa? Ka tab'a jin labarin cewa ta aikata zina ne?
Banji ba amma abakin iyayen ta naji labarin cewa ta gudu, babbu mace mai kamala da zata gudu daga gidan iyayen sai dai idan dama can yar dandi ce"
















B'angaren lukii da Salma kuwa bayan ya fitarda ita gidan satin ta biyu a hannunshi baci ba sha haka tayita rayuwa cikin kunci da masifa wahala kuwa ba irin wanda be nuna mata ba daga karshe kuma ya dauki kaddara suka cigaba da xamanda suke na alfasha amma bame dadi ba kamar na da mahaifiyarta ladi tayi bakin cikin wannan lamarin kamar ba gobe amma hakan ta hakura...








Sumayya kuwa da john har an samu ciki bayan sun dawo daga garin su john nan taje ta nunawa iyayenta shi sunyi matukar bakin ciki ganin ta nace sai shi yasa suka hakura sukayi magana dashi ya amince xe musulunta yanxu haihuwa kawai ake jiran tayi a daura musu aure.
















Ba kad'an faruk ya raxana ba dajin kalaman dad d'in nashi ba tsamm ya tuna da kalaman khal xaxxafan iska ya furxarda daga bakinshi
"dad baka taba Neman abu a waje na ka rasa ba amma ina neman alfarma a wajen ka don Allah ka tausayawa rayuwata wallahi Ina matukar kaunarta baxan iya rayuwar ba ita ba............
yafada voice d'inshi na cracking
"faruq idan har ni na haifeka baxan yarda ka aure wannan karuwar ba wacce batada tarbiya wacce batasan darajar aure ba ai mun gode Allah da tun yanxu ta nuna mana halinta ba bayan auren naku ba........,
"Dad wllh wannan ba halinta bane..."
"Faruq idan ka yarda ni na haifeka ka janje wannan maganar inba haka ba bani ba kai.....!!!!"
da sauri ya dago kanshi yana kallon mahaifin nashi abunda kunnensu ya ji musu ne yasa shi kara raxana na an daura auren
*Firdausi Yusuf da Khalil Muhammad*
wani irin jiri faruq yaji yana Neman dauke shi Alhaji lukman ne yayi dariyar takaici yana cewa
"Ai gara a daura auren dashi don mukam baxa'a hada muda bun kunya ba....."
nan ya tasa kan yaran shi suka bar gidan
Bayan Yan daurin auren sun watse dadyn khal ya koma dakinshi kwanciya yayi yana jin kamar nunfashin shi xe dauke gupppppp yaji an bugi dakin shi a raxane ya dago khal ya gani yana huci kamar wani xaki sai nunfashi yake fitarwa da gaggautawa
dad wallahi baxan iya rayuwa da itaa ba type d'ina bace ba xan iya rayuwar da ita ba wallahi bana kaunarta na tsaneta , ya fad'a da wani irin murya har ranshi yake jin ba zai yarda da wacce ya riga da ya latsa xumar ta ba.
Ran sh ya matukar baci sosai a kufule yace" ba shawara nake baka ba umurni ne kuma dole ka bi muddin kana son zaman lafiya.
"Idan ina numfashi a doron kasa baka da wata macen da zakayi xama aure idan ba Firdausi ba ita ce zabina".
Sosai hantar cikin shi ya kad'a zuciyar shi na mishi turiri" dad ba zai fahimci halin da yake ciki ba.....ta yaya yake tunanin xai aure yarinyar da ya ci ta kuma ya rigada ya gama da tarihin ta a jerin matan da yake sha'awa..........ajiyar xuciya ya sauke yana kokarin fita dakin ya tsaya cakkkk
"basai na wahalarda kaina ba sakinta kawai xanyi..."
"Khalil ka barni da bakin cikin da ke Neman dauke rayuwata idan ka kuskura wallahi bani ba kai har abada.........










*🤔🤔🤔tirkashi to ya wannan abun xe kasance*






Please Kuyi mun share
[6/17, 11:07 PM] Feeby: ♣️♥️♣️
*_NI DA KE...!!!_*
♣️♥️♣️




```♥️Dole muyi rayuwa........♥️```








_*Wattpad@feebyrh*_












*Wannan page din sadaukarwa ne ga yan kungiyar mu SHINNING STAR'S WRITER'S ASSOCIATION*














page 2️⃣6️⃣
"Khalil ka barni da bakin cikin da ke neman dauke rayuwata idan ka kuskura ka sake yarinyar nan wallahi bani bakai har abada......
Har cikin kanshi yaji wannan kalaman dad ajiyar xuciya ya sauke yace
"dad bafa wannan auren...."
Da sauri dad ya dago da kanshi yana kallon khal cikeda bacin rai
"Me kake nufi a daura aure yanxu kuma kace ba auren...!!???"
Ba tareda ya tsaya bawa dad amsa ba yabar dakin direct parking space ya nufa inda ma'aikatan gidan da baki take taya shi murna wani bala'in haushi yakeji hakan ya shiga mota yabar gidan direct guest house d'inshi ya nufa yana shiga gidan yayi parking d'in motar bud'e murfin motar yayi ba tareda ya tsaya rufewa ba ya kutsa kanshi cikin gidan kai tsaye dakin da take ya nufa har yanxu tana bacci kujerar dake facing d'inta ya xauna akai cikeda fusata da tsanananin bacin rai xama yayi tareda crossing kafar shi daya kan daya yana furxarda xaxxafan iska daga bakin shi ganin batada niyar tashi yasa, ya tashi ya nufi fridge bottle water ya dauko me mugun sanyi wanda ya fara kankara da sauri ya dawo dakin tun daga kanta ya fara xuba mata ruwan har xuwa tafin kafarta a firgice ta mike a kanshi ta sauke dara daran sexy eyes d'inta mugun xafinda taji a kasanta ne yasata komawa gefe ta hade jikinta tana xan blanket ta rufe jikinta hada kai da gwiwa tayi tanata shashsheka gabanta kuwa sai faman bugawa yake dappppp da ita yaxo ya kama kunnenta da karfi a hankali ta dago da kanta tana kallonshi cikeda tsantsansar tsana da karfi ya aika mata mari wanda yasata ganin stars yace
"xaman me kike mun a gida abunda nake nema nasamu sai ki tashi kije gidan ubanki kuma karki kuskura ki koma gidan ubana......."
yayi maganar yana huci kamar wani xaki
wani kololon bakin ciki ta hadiye idonta sai hawaye me xafi yake fitarda....me wannan macucin mutum ke nufi ne yaxata da rayuwarta.....???
"karki kuskura in koma hada ido dake....bana kaunar koma ganin me irin wannan mummunar fuska naki....."
yafada yana janta da karfi saida ya kawota bakin kofar parlourn kafin ya tsaya kallonta yayi up and down yace "ki fitar mun daga gida tunda bana ubanki bane....."
Durkushe kasa tayi tana rushewa da matsanacin kuka me tsuma rai sake kallon kanta tayi a xindir take ba komai a jikinta kuma a hakan yake nufin ta fita tabar mishi gida voice d'inta na cracking tace "ka tai....maka...mun in dauki kayana.....nima....bana fatan....in koma....kara numfashi a doron....duniyar nan....balle a gidan ka....."
ba tareda ya tsaya jin maganarta ba ya fice daga wajen a fuskarta ya cilla mata kayanta yana cewa
"Minti biyu na baki kibar gidan nan...."
Jikinta na rawa ta saka Yan kayan baccinta tabar gidan ta dauki lokaci tana tafiya duk inda tabi sai an bita da ido hakan yasa ta saida me Napep ta gaya mishi gidan da xe kaita dappp da gate din yayi parking ganin an dauki lokaci bata sauka ba yasa ya juya summamiya ya ganta cikin tashin hankali ya soma kiran mutane
Nan akayi kanta direct asibity aka wuce da ita....






B'angaren khal kuwa cikeda tashin hankali ya yini ranar tsoron shi daya karta sanarda su dad abunda ya faru yayi nisa cikin tunani yaji wayarshi na ringing saida akayi wajen 5 missed call kafin ya dauko wayar xe kira saiga kiran yashiga Watan daddan murya yaji tana gaida shi cikin sanyayyar murya ya amsa B'angaren ta kuwa murmushin mugunta tayi tana cewa
"nasan Baka gane me magana bako....??"
Jim yayi kafin yace
"eh wacece...??"
dan murmushi tayi tana cewa
"Khalil da wuri haka koh toh leenah ce kawar Salma..."
Xumut ya tashi da kwancenda yake coz yana son yaji labarin Salma daga bakinta don yaje gidansu ance ba'a San inda take ba da sauri yace
"Ina Salma..."
"kwantarda hankalin ka Salma na nan...."
"a ina take..."
Ya tambayata da sauri
"inason in ganka ne muyi magana xan gaya maka komai....mu hadu emerald suit anjima karfe uku....."
"alright....."
nan ta kashe wayar tana sakin shu'umin murmushi Tun 1:00pm ya shirya yaje cen a garden ya xauna yana xaman jiranta




B'angaren Firdausi kuwa an samu ta farfado har an sallame su sun bar asibityn bayan duk mutanen da sukaxo bikin sun watse nan suka tasata a gaba suna tambayarta yanda akayi abun ya faru Jim tayi tana naxarin abunda xata sanarda su a hankali ta bud'e bakinta tace
"da dare ina xaune a bedroom dina ina shirin yin bacci sai naji knocking ina bud'e kofar ban koma sanin inda nake ba sai gani na nayi a asibity tareda Ku......"
Jikinta na rawa tayi maganar ajiyar xuciya suka sauke koh wanne da irin tunanin da yake
Khalil kuwa sun hadu da leenah nan ta shaida mishi komai har kashe khairat da Salma tayi nan suka dukuma nemanta don ba wanda yasan duniyarda take kusan kullum kuwa sai sun hadu da leenah har sun fara shakuwa....








Bayan wata daya
Firdausi ce durkushe a gaban iyayen nasu sai kuka take faman yi
"Kiyi magana kinyi shiru kin maida mutane sakarkaru waya miki ciki.....????"
mamanta tayi mata wannan tambayar cikeda fada da tsananin bacin rai
nan ma shiru tayi bata Basu amsa ba lafiyayyen mari mamanta ta aika mata wanda yasa ta rikice tana koma tambayarta voice d'inta na mugun cracking tace
"Khalil....ne"
wani irin mugun damka mamanta takai mata ta rike wuyanta da kyau tana cewa
"karya kike yanxu ki rasa wanda xakiyiwa karya sai khalil ki rasa wanda xaki cuta sai shi....??"
dad ne yayi sauri riketa yana cewa
"kiyi a hankali mana ai ba'a shaidar yaro...."




















*gaskiya kun bar sharhi da dogon comment shiyasa nabar typing*[6/17, 11:07 PM] Feeby: ♣️♥️♣️
*_NI DA KE...!!!_*
♣️♥️♣️




```♥️Dole muyi rayuwa........♥️```








_*Wattpad@feebyrh*_








page2️⃣7️⃣
"Kiyi a hankali mana ai ba'a shaidar yaro...."
cikin xafin rai ta koma riko wuyanta tana neman kashe ta,da sauri momyn khal ta amsheta daga hannunta tana cewa "kinada hankali kuwa koh kin manta anyi mata fyade ne shiru kawai nayi ina kallon ki don ina tunani baki manta da kaddaran daya risketa ba.....??" cikin fada tayi maganar tana shigarta Firdausi jikinta wacce keta faman kuka kamar ranta xe fita ,nauyayyen ajiyar xuciya ta sauke ta dawo kan tafkeken kujera dake parlourn ta xauna tana mayarda numfashi tagumi tayi tareda share xaxxafan hawaye daya fara sauka daga idonta tace
"Aunty na manta wallahi"
Cikin kuka tayi maganar tana koma share hawayen dake ambaliya a fuskarta gyaran murya dad yayi yana cewa
"akwai alamar tambaya a wannan lamarin ina tunanin Khalil ne ya aikata mata wannan mummunar lamari....katse shi Maman Firdausi tayi tana cewa
" a'a yayah yaxa'ayi ace Khalil ne ya aikata mata wannan mugun ta'asar ita da ma tunda aka dauketa bata San inda kanta yake ba har xuwa mayarda ita da sukayi....kuma Khalil baxe taba aikata irin wannan mugun lamarin ba...."
numfashi momyn khal ta sauke tana gogewa Firdausi hawaye dake kwaranya a idonta tace
"Ku kwantarda hankalin Ku mu kara tambayarta..."
dago da beauty face d'in Firdausi tayi tana cewa
"mamana Khalil ne ya aikata miki wannan ta'asar.....?"
shiru tayi tana binsu da ido wanda yayi masifar yin ja tsabar kukan da taci
"Shine koh....???"
dad yace yana karasowa inda take
Dakyar ta iya bud'e bakinta voice d'inta na cracking tace
"Kuyi hakuri da abunda xan gaya muku bansan wanda yayi mun wannan abun ba sunan yaya Khalil dana kira rud'ewa ce tasa na kira sunan shi don Allah Ku yafe mun wallahi na kwammace in mutu da irin wannan bala'in dake addabar rayuwata...." tayi maganar cikin kuka sosai rumgumeta momyn khal tayi tana rarrashinta nan bacci me nauyi ya dauketa koh wannen su cikeda bakin ciki yake khal ne yayi sallama ya fada parlourn sanye yake cikin gixnah brown colour sai kamshi yake xubawa gaida iyayen nashi yayi yasamu waje ya xauna yana aikawa Firdausi wacce ke kwance sai sharar baccin wahala take harara Jim dakin ya dauki shiru ba me magana kohwa da abunda yake tsak'awa a ranshi
"Dad lafiya dai duk na ganku haka.....???"
shiru dad yayi maman Firdausi ce tayi kokarin bud'e baki tace mishi
"ciki ne da kanwar ka......"
raxana yayi ya xaro ido yana cewa
"ciki fa...?? garin yaya gaskiya ban yarda ba yaxa'ayi ta samu ciki lokaci daya.....??"
takarda ta dauko ta nuna mishi karba yayi ya karanta tsaki yaja tareda cewa
"wallahi koh waye ne karya yake xa'ayi ace cikine da ita infact a ina xataga namiji balle ayi mata ciki..."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login