Showing 18001 words to 21000 words out of 84568 words

Chapter 7 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

Ainar ke miko mata, kudi ne ba ma kuma Naira ba dalar America ce. Ba ta ƙi ba miƙa nata hannun ta yi ta karɓa tana jujjuya su "Duk shi ya ba ki wadannan? Aina ta daga kai "Amma kuma don tsiya ya fito a yi aure sai ya ce ba haka ba? "Wai kuma gobe zai zo in raka shi wani taro, da ni kadai zai iya shiga wurin." Wani tsaki Gwoggo ta ja "Kyale dan iska ya je da matan nasa ba inda za ki. Su kuma wadannan kudi mun yagi rabon mu, ko a waya ya kira ki ki ce idan ba maganar aure zai yi ba ya manta ma ya taɓa sanin ki. Aure nake so ki yi Aina, Daura magana ta fara yawa har yau ba ki yi aure ba, duk yaran gidanmu ba wadda ta taɓa kai kamar shekarunki." daidai nan suka yi ido biyu da Hamida Gwoggo ta riƙe baki "Ba ki kwanta ba Hamida? Ta ɗaga mata kai sai ta mike "Wani film nake kallo Gwoggo ya ma kare yanzu." "To kashe kayan kallon." ta kashe ta wuce ciki ta bar Gwoggo da Aina suna neman mafita, don ita ma Ainar hankalinta ya koma kan ta yi aure har an fara maganar auren ƙannen bayanta, yaran gidansu ba su wuce sha bakwai an kauda su, ko Laila da Gwoggo Indo ta riƙe Sakandire kawai ta ƙare aka yi mata aure ita ce dai da alhazan birni suka yi mata caa! Tun zamowarta budurwa shi kenan ita da Gwoggo sai suka yi fatali da zancen aure, maimakon auren magana ta yi wa Ahmad mijin Laila ya samo wa Aina makaranta. NCE aka samu tun kuma da ta fara karatun idanuwanta suka ƙara budewa, duk kuma da matsin lambar da suke fuskanta daga Malam Aina ta fito da miji, Gwoggo Indo na cewa karatu take don Allah ya yi haƙuri ta ƙarasa daga ta fara. Duk da ba son karatun bokon yake ba ta sani hakanan ya hakura. Maza suna kashe mata kudi suna shan soyayyarsu ta shan minti, Gwoggo na sane amma tsabar son abin duniya ya sa ba ta tsawata mata. Da ta kammala karatun kuma duk wanda ta nemi ya fito ba ya fitowa sun fi son su yi ta soyayyar su a haka, Alh Maaruf shi ya zo da batun aure sai aka yi rashin sa'a mugun shakkar matarsa yake yi shi kuma. Ranar dai haka suka kwana Aina da Gwoggo ba daɗi. Washegari ta kama Alhamis ba Islamiya Aina ta ce wa Hamida da La'asar za su fita a gyara musu kai ta ce "To." Don haka ƙarfe hudu da rabi suka fito cikin shiri Aina riga da skirt ta sanya na Less sun kamata kamar ma da ƙyar take numfashi ta jefa gyalenta a kafaɗa. Hamida ma riga da skirt din ne sun yi cif a jikinta sai bakin gyale da bakin takalmi bayan ta murza farar hoda Aina ta sanya ta ta shafa jambaki ai kuwa ba karamin kyau ta yi ba ta daura mata dankwali tulin gashin ta ma da ya fito ta gefe da gefe bayan ta kama mata shi da ribbom ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba shi maSuka fito suna ƙamshi mai sanyi. Gwoggo Indo ta fita unguwa. Sun yi nisa da tafiya har sun kusa Gate don fita inda za a su samu adaidaita sahu wata mota ta tsaya ba su shaida wanda ke ciki ba har saida suka dubi mazaunin direba Abdurrashid ne baƙar shirt ce jikinsa da ta yi matukar amsarsa "Ina za ku? Ya fadi cikin rashin sakin fuska Aina ta fara gaishe shi sai ta amsa mishi tambayarsa "Za mu je wurin gyaran gashi ne." "Ku shiga mu je ya furta ba tare da ya dube su ba Aina ta bude kofar baya ta shiga Hamida ta mara mata baya sai dai kallon da Ainar ta jefa mata ya katse hanzarinta ya sa ta tsayawa, jin su shiru ya sa shi waiwayowa don ganin halin da suke ciki "Shiga mana." Aina ta ce ma Hamida sai dai ba ta motsa ba ta sake cewa "Me kike yi haka ne Hamida? Ya ce "No bar ta ta zauna nan din." har ajiyar zuciya Hamida ta fidda ta shiga ta zauna gefen Aina. Ya zuge gilasan motar wadanda suke masu duhu ne sai ya tashi motar. Aina na ta jira ya tambaye su inda za su gyaran kan sai ta ji shiru, wani ƙayataccen wuri ya kai su can kusa da Zoo road ya ce su fito. Ya mika wa Hamida Atm ya fada mata pin din ya ce su biya idan an gama masu. Suka shiga ciki ya kwantar da kujerar yana sauraron kiɗan da ya sa a motar. Aina ganin banza ce ta faɗi ya sa ta ce bari su bi ta da yakushi, bayan gyaran gashin ta ce a wanke musu ƙafa, ta kuma jidi maya mayai na kai da na jiki duk a ka cire a kudaden Abdurrashid. An gama musu yamma ta yi sosai Aina ta ce su tafi su samu shatar Adaidaita sahu sai dai suna fitowa suka yi tozali da motar Abdurrashid wurinta suka nufa Aina ta ƙwanƙwasa glass ɗin ya sauke idonsa a kansu bai yi magana ba Aina ta bude suka shiga ya ja, a hanya ya tsaya ya yi sallar magarib don haka duhu ya shigo san da suka shiga gida. Gwoggo Indo sai murna baki ya ƙi rufuwa jin Aina ta ce tare suka fita da Abdurrashid, ita ta bude ledar da Aina ta zubo mayukan tana cewa "Iya wannan ledar kawai ba ta yi kadan ba? Aina ta yi murmushi "Ita din ma ba shi ya bamu ba."Ta kwashe yadda aka yi ta labarta mataTa ɗan yi shiru kafin ta ce "Zuwa yanzu na yi tunanin ya soma jiƙa mu da Naira Aina, amma ko kwabo, gidansu kuma gida ne na kyauta indai ka shiga ba ka fitowa hannu biyu. Aina dai ta dauki ledar ta wuce ciki, da ma Hamida tun shigowar su ba ta zauna ba cikin ta wuce don yin sallar magarib, ta bar Gwoggo Indo da tunanin Allah ya sa Abdurrashid ba hannun jarirai yake da shi ba. Karshe dai ta watsar ta ce koma dai meye gidan arziki ne, kuma abin alfahari ne a ce yarta ta yi aure a gidan. Ranar Monday Abdurrashid ya turo a ka kai Hamida makaranta a ka yi mata komai har unifoam aka ba ta da littattafai. Dan aiken ya shaida wa Gwoggo Indo duk safiya zai riƙa zuwa don kai ta makaranta. Ranar kowa ya ga cikakkar fara'ar Hamida. Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta mai suna *AHLAN Internatonal School* babbar makaranta ce ta yayan masu hannu da shuni da masu riƙe da madafun iko, idan ta dawo ta wuce Islamiya. Abdurrashid ya kan zo daga lokaci zuwa lokaci. Tana matukar ganin girmansa saboda makaranta da ya sanya ta, ba ta damu da mitar da Gwoggo ke faman yi na ba shi da alheri kullum sai dai ya zo ya kakkaɓe rigarsa ya tafi. Tana mayar da hankali sosai musamman da ya zam ba a hausa a makarantar sai dai turanci, ita kuma ba ta iya ba, ranar Alhamis da juma'a tana tsayawa lesson da Abdurrashid ya sanya ake mata har Asabar da lahadi take zuwa tana yi mata da yake tana so ba ta dau lokaci ba ta fara ganewa, ba ta shiga sabgar mutane tana matukar kama kanta duk da su mutanen suna son yin mu'amala da ita, saboda burge mutane da take yi. Yarinya guda ta fi shige mata kuma dole sai da Hamida ta saba da ita duk inda ta sanya kafa nan yarinyar mai suna Walida za ta mayar da ta ta. Walida irin yaran nan ne masu ɗan banzan rawar kai da son a ce su ɗin wasu ne, irin labaran da take ba Hamida na arziƙin iyayenta Hamida jinta kawai take don ita ba ta ga abin da ya dame ta da arzikin su ko rashin sa ba, har sai wata rana da aka kwana biyu ba ta zo ba sai Hamida duk ta ji ba ta ji dadi ba an bayar da sanarwar ba ta da lafiya, lambar wayar Walidar da ta ba Hamida ta ba Malam Adamu direban da ke kai ta makaranta ta ce don Allah za su biya ta gaishe da ƙawarta ba ta da lafiya Mamanta ce ta dauki wayar ita kuma ta yi ta musu kwatance har suka gano gidan, wani tsukakke ne a ɗan dinshe, mai dakuna uku ta gaishe ta sannan suka tafi gida. Bayan ta dawo makaranta ta ce ma Hamida gidan da suka zo gidan kakanninta ne nan kakarta ke ruƙonta wadda Hamida ta gani, ita mamanta na Hotoro, Sai da tafiya ta yi nisa tsakaninsu ta gane nan ɗin dai shi ne gidansu, matar da ta gani ita ce mahaifiyarta, yayarta ce ke aure Hotoro mijin yayar shi ya sanya su makaranta mai tsada ita da kannenta.
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH....




DAGA


MaRuBuCiYaR


WA GARI YA WAYA
CANJIN BA ZATA
RANAR NAKA
HATTARA
SON ZUCIYA
MUTUM DA KADDARARSA




MARYAM IBRAHIM LITEE




No.9




Hamida ta cigaba da karatunta suna tare da Walida wadda yanzu ta zama 'yar gida a gidan Gwoggo Indo. Kafin sati ya ƙare za ta biyo Hamida sau biyu wani satin ma sau uku. Da suka samu hutun second term Gwoggo ta je da ita Daura suka yi kwana biyu suka dawo Aina dai har yanzu tana nan, Alh Ma'aruf ya ɗauke ƙafarsa ba kuma wayarsa in ta kira shi ma ba zai dauka ba, ita da Gwoggo suna cikin tashin hankali. Wani yammaci Hamida ta shigo daga makarantar Islamiya Gwoggo ta samu zaune a falo kusa da ita ta zauna bayan ta amsa sallamarta "Yawwa Gwoggo, an ce a kawo kuɗin sauka dubu 20 sai kaji biyu sai kudin unifoam dubu b... Da sauri Gwoggo ta katse ta "Duk ni kaɗai wannan dogon lissafin? To tun wuri gara ma ki sani wancan mai son naki da ba ya ɓanɓaruwa shi zai yi komai, ki ma gaya masa, in kuma ba haka ba kina kallo yan ajin naku za su yi saukar su bar ki." Kuka Hamida ta sanya, Gwoggo ta ce "Allah na gama magana kowane irin kuka za ki yi." A haka Aina ta shigo ta same su a komai za ka same ta bayan Hamida amma yau ta ce Gwoggo na da gaskiya Hamida ta tambaye shi kawai. Kuka Hamida ta daɗa rushewa da shi. Ranar ko abincin dare ba ta ci ba Aina da ta ga ta ƙi barci sai kuka take ta janyo ta tana rarrashi "Shi ya dace ya yi miki Hamida, Gwoggo gaskiya take fada miki. Gara tun yanzu ya saba da hidimarki ba komai ya rungume hannu, share hawayenki kin ji yar ƙanwata? Ta gyaɗa kai sai ta share hawayen ta ce ta je ta wanko fuskarta sai da ta wanke ta dawo ta kwanta lamo tana tuna tsawon watanni biyu kenan tana fama da karatu don son da take ta yi na ɗaya a jarabawar saukar su. Da safe ba walwala ta tashi, haka ta shirya ta tafi makaranta. Ko a makarantar ma hakanan take sukuku sai tambayarta abin da ya same ta Walida ke yi sai ta ce ba komai. Da suka tashi maimakon Malam Adamu da ya saba zuwa daukar ta yau saɓaninsa Abdurrashid da kansa ta gani tsaye jikin motar ko da ta doshi motar tana takawa a hankali kamar wadda ƙwai ya fashe mawa. Tana isa inda yake ta ce "Ina wuni? Sai ka saurara da kyau za ka ji me ta ce, shi ma ban da ita yake kallo ganin ganin sauyin yanayinta da ba zai gane ta yi magana ba. Ya zagaya ya shiga ita ma ta buɗe ta shiga bai ko dubi inda take ba har sai da suka hau titi. 'Me ya same ki? Ta girgiza kai "Ba komai." "Ba wasa nake miki ba fa." ya faɗi a ɗan hasale. Ta buɗe baki ta yi magana sai kuka kallon ta yake ta yi sai da ya ga ba ta da niyyar shiru ya ce "Ya isa ki yi shiru, an tashi yazan amma gobe zan shigo sch din in ji abin da aka yi miki." da sauri ta ce "Ni ba abin da aka yi mini a makaranta." "To me ya faru? Shirun ta kuma yi tana cigaba da hawaye, ya tsaida motar gefen hanya ya kuma tsare ta sai ta fadi mishi abin da aka yi mata. Kan ba yadda za ta yi ta ta ce mishi sauka za su yi a Islamiya, kuma Gwoggo ta ce ba za ta biya kuɗin ba sun yi yawa. Ya tambaye ta nawa ne kudin ta fada mishi, motar kawai ya tada suka bar wurin bai kuma sake ce mata komai ba har suka isa ya sauke ta. Da yamma lis kuma sai ga shi gidan Gwoggo, ta waya kamar yadda ya saba ya shaida mata isowarsa. Ta ce ya shigo Gwoggon kawai ya samu a falo sai da suka gaisa ta shiga ƙwala kiran sunan Hamida da yake yau ɗin Alhamis ce ba Islamiya kafin fitowar Hamida ta ce "Fushin take har yanzu kenan? Sai ta yi shiru don son jin me Abdurrashid zai ce, jin bai ce komai ba sai ta cigaba "Don na ce ba zan biya kudin sauka ba ta faɗa maka shi ne take fushi."Shi dai ko dagowa bai ba sai wayarsa yake faman dannawa. Hamida ta fito cikin nutsuwa baƙar jallabiya ce jikinta sai hijab ƙarami shi ma baƙi ta zauna Gwoggo ta mike ta bar musu falon, gaishe shi ta yi suka zauna shiru kafin ya mike ya bar gidan. Gwoggo ta dawo falon tana tambayar Hamida ya yi mata zancen kudin saukar? Hamida ta girgiza kai ta zabga ƙwafa "Duk da gaya mishi da na yi da kaina? Nan ta yi ta faɗa har Aina ta dawota ji abin da kenan, hakuri ta yi ta ba Gwoggo . Ranar Asabar da Hamida ta je Islamiya malaminsu mai kula da hidimar sauka ya kira ta ya bata unifoam da sauran abubuwan da aka bai wa masu saukan. Ta koma gida tana ta murna ta gaya wa Gwoggo da Aina baki Gwoggo ta taɓe ta ce hala shi ya biya. Suna ta shirin sauka har lokacin ya gabato Ahmad mijin Laila shi ya kawo abincin da za a ci da abin sha wurin saukar Laila ta yo mata memo mai dauke da kyakkyawan hoton Hamida. Aina ce ta yi mata dinki wanda za ta sanya ranar sauka. Har ana gobe saukar Abdurrashid bai kawo komai ba, Gwoggo ta yi mita har Allah gajiyar da ita. Sai dare Hamida na wanke lallen da aka yi mata ya kira waya yana waje Gwoggo ta buntsura baki. Hamida ta shida nuƙu-nuƙu Aina ta ce jiranki fa ake Hamida. Ta ce "Ban yi wanka ba Aunty Aina Aina." Dan murmushi Ainar ta yi tana duban ta wata yar ƙaramar riga ce jikinta sai bakin dogon wando kanta sabon kitso ne da aka yarfa mata a yammacin yau. "Ai ya san hidima ake, sanya hijab din Islamiyarki daga dogo ne." ta wuce ɗakinsu don ɗauko hijabin Laila da ke zaune wurin ko tari ba ta yi ba, nan za ta kwana saboda bikin saukar. Yan daura mutum uku suka zo da ta shiga saida ta ɗebi abin da aka yi na rabo ta zuba cikin leda sai ta boye a hijab dinta ta fito, jikin mota ta same shi tsaye yana kallon ƙofar gidan har ta iso inda yake yana kallonta ta gaishe shi ya taka zuwa wurin boot ya buɗe ledoji ya yi ta cirowa sai da ya gama ya rufe boot din ya bude kofar baya ya ciro wani kwali "Zo mu gani za ki iya dauka." ta karaso gabansa sai da ta ajiye ledar hannunta sai ta karɓi kwalin "Ki kai ciki sai ki samo mai taya ki ku kwashe waɗannan. Kai ta ɗaga sai ta yi godiya ta juya ciki ta ajiye kwalin ta dawo ta dauki ta ta ledar ta buɗe front seat ta ajiye mishi ya bude ya shiga ta ce mishi sai da safe sai da ya bar wurin ta soma tattara ledojin tana kaiwa ciki. Gwoggo da Aina ke ta buɗewa, shi ma ya yo mata calendar da memo da jaka masu dauke da sunanta sai dai ba hotonta. Sai alƙur'ani hizif bi biyu sune cikin kwali. Sai kaya kala biyar masu matuƙar kyau da tsada. Gwoggo sai aka shiga murna, Hamida dai wucewa ta yi ta juye ruwan wankanta ta yo wankan ta fito ta yi sallah mai kawai ta shafa ta goga Sure sai ta kwanta tana jiyo hirar su Gwoggo har lokacin da yan Daura. Da safe da wuri Hamida ta wuce makaranta. Ita da sauran yan ajin su suna cike da farin ciki a yau, sun sanya kayan sauka an jera su a inda za su zauna, aka soma shirye-shirye. A wurin da manyan baƙi suke zaune ta hango Abdurrashid zaune kallo daya ta yi masa ta kauda idonta, ya yi kyau ƙwarai cikin wani lallausan yadi fari ga hula ya ajiye a sha tara ya yi mata kyau fiye da koyaushe Shi a ka kira ya ba maza shahadarsu, mata kuma wadda ta wakilci matar gwamna ta raba musu. Hamida ba ta samu cikar burinta ba ta yi na daya, ta dai zo ta biyu namiji ne ya yi na daya. Baki har kunne su Gwoggo da aka kira Hamida aka ba ta kyautar wadda ta zo na biyu. Daf da tashi aka shiga rabon abinci da drinks wasu jama'a masu kaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login