Showing 81001 words to 84000 words out of 84568 words

Chapter 28 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

Aunty Karima ta zauna ta gaishe da Engineer sannan Aunty Karimar fuskarta na ƙasa.
Engineer ya ce "Ya aka yi ɗiyata, Mijinki ya ce kin ce ba ki bin shi Abuja? Shiru ta yi don ba za ta iya magana gaban shi ba "Ki yi haƙuri ɗiyata, ki shirya ki bi mijinki kamar yadda yake so ba ma daɗewa zai yi ba ai Abujar bai fi saura wata biyu ba ya dawo nan ɗin."
Ita dai ko motsi ba ta yi ba har ya ƙare maganganun lallashin ta ya sallame ta.
Ta ce musu sai da safe ta tafi ba ta tsaya ko'ina ba sai ɗakinta, hijab ɗin jikinta kawai ta yaye ta haye tsakiyar gadonta ta fara kuka a haka ya shigo ya same ta tsaye ya yi yana kallon ta kafin ya ce "Duk maganar da aka yi miki ba ki haƙura ba kenan? Ba laifi."
Ya sa kai ya fita ta share hawayenta ta tashi ta soma haɗa kayan da za ta tafi da su, ba ta kwanta da wuri ba sai sha biyu, hakan ya ja mata makara don ba ta tashi buɗe idonta ba sai da haske ya fara shigowa ta window ta ta tashi da sauri tana salati sai ta dubi agogo, bakwai tuni ta wuce cikin matuƙar baƙin cikin rasa sallar asuba da ta yi ta shiga bathroom, ta fito ta kabbara sallah tana idarwa ko azkar da karatun Alƙur'ani da ta saba yi ba ta tsaya yi ba ta tuɓe hijab ɗin ta nufi wurin Abdurrashid tsaye ta same shi cikin shiri ya waiwayo ya amsa sallamarta a hankali ta ce mishi "Ina kwana? Tana kaiwa zaune bakin gado amsawa ɗaya ya yi ta ce "Na makara, shi ne ba ka tashe ni ba? Ya noƙe kafaɗu "Na san don in yi fushi in tafi in bar ki ne kika ƙi tashi, kuma kin samu nasarar yin hakan zan tafi in bar kin sai dai ki sani ba ƙaramin cutar da ni hakan zai yi ba, tsawon watanni biyu muka ɗauka ba kya tare da ni yanzu daga dawowar ki ki guje min, sai dai kar ki ga laifina idan ban zo ba don sai kin neme ni."
Hawaye Hamida ta ji suna zubo mata na baƙin cikin juya maganar da ya yi ta sauko gadon ta durƙusa ƙasa ta shiga kuka sosai.
Ya dubi inda take sai ya ajiye jakarsa da ya ɗauka ya tako zuwa inda take tsugune ya kamo ta ta ƙwace ta ci-gaba da kukan ƙarfi ya sa mata ya ɗago ta sai ya haɗe ta da jikinsa tana sane ta shiga goga fuskarta a jikin fara ƙal ɗin shirt ɗinsa, duk ta goge masa hawayen da ya damalmale fuskarta.
Zuwa bakin gado ya ja ta ya zauna tare da ita tana cikin jikinsa da dukkan hannayensa ya rungume ta "Me ya sa kike so ki yi ta ɓata ranki alhali kin san ba ke kaɗai ba ce? Ya shafa cikin "Me kike ma kuka? Ta ƙi magana ya kuma maimaitawa nan ma ba ta ce uffan ba.
"To ki yi haƙuri daga ba ki son zuwa zan ƙyale ki." Da sauri ta ce "Daddy zai ga na raina maganarsa."
Ya zare hular kanta ya soma shafa calabar kanta "Ba zai ce ba zan mishi bayani." Ganin ya zare rigar barcin jikinta ya soma tube tashi ta san abin da kenan, zagewa ta yi ta faranta mishi tana mishi kukan shagwaɓar ɓata mishi rai da ta yi daren jiya ya yafe mata.
Bai raba jikinsu ba bayan kammala komai barci ya ɗauke ta shiru ya yi yana duban fuskarta, a hankali ya zare jikinsa sai ya miƙe zuwa bathroom wani wankan ya sake ya fito ya sake shiri cikin wasu ƙananan kayan sai ya ɗauki jakarsa ya dubi inda Hamida ke barci sai ya dubi agogonsa lokaci ya fara tafiya, ya fita ya ja ƙofar.




Sai da ya zauna a motar ya zaro wayarsa ya tura ma Hamida saƙo, ya tayar da motar mai gadi ya wangale gate yana wa mai gidan nasa fatan sauka lafiya.




Wayar Hamida da ke kan gadon ta tayar da ita da rurin da ta ɗauka, ta buɗe idonta tana duban ɗakin da yadda suka yamutsa shimfiɗar gadon sai dai ba Abdurrashid, tunanin ko ya tafi ya bar ta ne ya sa hankalinta tashi ta gaza ɗaukar wayar har ta tsinke.
Ta rafsa tagumi tana duban agogon bango sha ɗaya saura, wayar ta kuma ɗaukar ƙara a karo na biyu cikin sanyin jiki ta miƙa hannu ta ɗauko ta, Ahmad ne mijin Aunty Laila, cikin mamakin kiran ta yi picking sai ta soma gaishe shi cikin girmamawa kamar yana ganin ta, ta tambaye shi su Aunty Laila da yaran ya ce duk suna lafiya.
Ya ƙara da tambayarta "Oga ya wuce ne? Ta amsa da "E." Ya ce "Da ma wata magana nake so mu yi da ke saboda yaba hankalinki da nake yi da ɗabi'unki."
Ya ɗan tsahirta ko za ta ce wani abu, jin ta yi shiru ya cigaba "Game da zamantakewa ta da Laila ne tun kina ƙarama na san kin san komai ina zaune da Laila ne don ina son ta, shi ya sa nake haƙuri da ɗabiunta, amma yanzu an kai lokacin da dole ina buƙatar sama ma kaina mafita shi ya sa na nemi ƙarin aure, Laila ta dira ta yi tsalle ba za ta yarda ba.
Me Laila ta riƙe wanda zai hana a yi mata kishiya?
A ran Hamida ta ce "An zo wajen." Ta daɗe tana ma yar'uwar ta ta fargabar ranar da za a zo haka. Ta ja ajiyar zuciya ta ci gaba da sauraren shi.
"Komai da ake wa miji ban san shi ba daga Laila ba abin da ta sani sai ta ci ta kwanta ta ɗauki wayarta, yarana su za su yi ma kan su komai har ni ma su yi min, wanka da kwalliya su kaɗai nake samu daga Laila su ma ɗin ta watsar ta rungumi waya. Ni dutse ne da ba zan buƙaci inda zan samu kula ba? Don haka na kawo koke na gare ki, kina da hankali da sanin ya kamata ki yi mata nasiha ta nutsu ta gyara aurenta."
Jin ya yi shiru ta ce "Ka yi haƙuri Baban Amir."
Ya ce "To na gode."
Suka yi sallama ta ajiye wayar ta zauna shiru cikin tunani ita ya ma za a yi ta fuskanci Aunty Laila da zancen za ta yi mata nasiha duk girmanta? Amma tsakani da Allah ta san Laila tana da buƙatar a zauna a yi mata nasiha ta gyara yadda take tafiyar da rayuwar gidanta, in kuwa ba ta gyara ba aka auro mata wadda ta san kanta Aunty Laila ta kaɗe har ɗan ganyenta.
Ta daɗe cikin tunanin ƙarshe ta miƙe zuwa ɗakinta, wanka ta yi ta gyara jikinta sai ta gyara ɗakin.
Ta fita zuwa dakin Abdurrashid ta gyara nan ma sai ta fito don barin gidan suka yi kaciɓis da mai yi mata aiki sai da suka gaisa ta ce ta ce ta zo ta yi ta knocking ba a buɗe ba. Ta ce barci take.
Tare suka tafi wurin Aunty Karima can Hamida ta wuni har girki ta yi mata ta ci kuma ya tsaya mata ba ta yi amai ba.
Yamma sosai ta koma gida.




Washegari ta nemi iznin Abdurrashid ta je gidan Laila, zagewa ta yi ta yi mata gyaran gida amma ta kasa ce mata komai domin dai Laila ba sa'ar ta ba ce ko da wasa. Sai da La'asar ta yi mata sallama ta koma gida.




Har Abdurrashid ya yi sati biyu bai zo ba, tuni zaman ita kaɗai ya gundure ta.
Suka sha bikin Ahmad mijin Laila yan Daura sun zo sosai cikin su har da Innarta wadda ta ji daɗin ganin ta sosai.




Ranar wata Laraba da hantsi ta shiga wurin Aunty Karima Auntyn ke faɗa mata Mami ba lafiya kan dole ta tashi ta tafi gaishe ta ba dan ta so ba.


Su uku ta samu falon Mamin, Mamin sai Haj yar Yaya sai wata mata da ba ta san ta ba. Su biyun suka yi mata caa! Da ido, don duk da ƙaton hijabin da ta sanya cikin ya turo ya fito.
Wuri ta samu ta zauna tana gaishe su da tambayar Mami jiki Haj yar Yaya ta taɓe baki "Bikin Anisa kafin ta haihu za a yi shi." Mami ta ce "Da an bari in ta haihu sai a haɗa da suna."
Suka cigaba da zancen auren Anisa da Abdurrashid kamar ba ita ce a gaban su ba. Ta miƙe ta yi musu sallama sai ta bar sashen zuciyarta na mata zafi jin waɗannan mutanen ba su haƙura ba da ƙarin auren Abdurrashid.


A falonta rasa inda za ta zauna ta yi tana cikin haka kiran Abdurrashid ya shigo wayarta, ta ɗaga sai ta kama mishi kuka hankalinsa ya tashi don tunanin ko wani abu ya faru, ya shiga tambayar ta ta ce ita dai yaushe zai dawo? Ya ce ba yanzu ba ta ci-gaba da kukanta tare da magiyar ya zo ya ce to zai dawo da ƙyar suka rabu.
So take ya dawo don idan yana can gani take za su yi ta soyayya da Anisa hankali kwance ita tana nan.
Tashi ta yi ta rufe ƙofar falon ta dawo ta baje a falon cikin damuwa a taƙaice kasa shiga ɗakin ta yi a falon ta ƙaraci damuwar ta barci ya yi awon gaba da ita.
Cikin barcin ta ji ana shafa ta ta tashi a razane sai ya riƙe ta "Ke ni ne."
Ta buɗe idonta da ta rufe don tsoron da ya rufe ta ta gan shi tsugune gaban ta, tare da ita ya miƙe hannunsa na kan cikinta suka nufi ɗakinsa.
Sai da ta wartsake ta tambaye shi hanya har yake gaya mata ko lokacin da suka yi waya ya shigo garin yana barrack ɗin da ya bari, ta nemi ta yi masa girki mai sauƙi ya ce a'a dare ya yi bai tare da yunwa.
Ba su jima ba suka kwanta don dare ya fara nisa.


Kwana biyu kawai ya yi mata ya koma.


Rayuwa tana ta tafiya cikin Hamida yana ta girma da na Aunty Karima.
Nata ya kai watanni takwas na Aunty Karima shida Abdurrashid ya dawo Kano da aiki, wai sai ga Anisa ta dawo gidan tunda Hamida ta gan ta hankalinta ya tashi don ba ta san da zuwan ta ba sai wani dare suna zaune a falo ita da Abdurrashid ita tana zaune kan Sopa ta bubbuɗe ƙafafu shi kuma yana zaune a ƙasan carpet kusa da ƙafafun nata yana cin apple ta yi knocking shi ya amsa yana duban agogo cike da mamakin waye me zuwa musu yanzu, Anisa ta shigo cikin karairaya.


SHIRIN ALLAH... RAYUWA






END






MARYAM LITEE






Ta zauna tana pasing ɗinsu, ba ta damu da kallon da suke mata ba ba wanda ya yi mata magana sai ita ta gaida Abdurrashid.
"Ba ka shigo ba." Ta ce da ta ƙare gaisuwar, ƙara ɗaure fuska ya yi bayan shakkar Haj yar Yaya da yake da tuni ya kore ta ya yi mata fata-fata.
"E ban shigo ba. Ya amsa mata a taƙaice."
Ta ci-gaba da zama tana jan shi da magana, Hamida ta ƙi magana don tana son ta ga ƙarshen rashin kunyarta, idan ma ta yi magana tana ganin ta mayar da kanta baya. Ta gama firiritarta ta tashi za ta tafi ganin Abdurrashid ya yi banza da ita daga inda yake ko motsi bai yi ba ta fice. Hamida ma ta cicciɓa ta miƙe tsaye ta fara takawa ya kira sunanta ba tare da ta waiwayo ba ta amsa "To zo mana." Ya ce mata
Nan ma ba ta tsaya ba ya miƙe taku ɗaya ana biyu ya cim mata,hannu ya riƙe mata sai ya janyo ta suka koma kan kujera "To fushin na mene ne? Uhm na ce na mene ne? Ta turo baki "Wallahi wannan ne na ƙarshe da za ta shigo min wuri wai ta zo wurin ka."
"Ina ce yanzu ba za ta dame ki ba? Ya g
faɗi yana shafa cikin ta.
Hamida dai ba ta samu sukuni ba sai da Haj yar Yaya ta zo kan batun auren Abdurrashid da Anisa ya basu tabbacin ba zai auri Anisa ba don dama an ce don ya samu haihuwa to shi yanzu ba shi da wannan matsalar.
Da Mami da Haj yar Yaya ba a san wanda ya fi shiga tashin hankali ba da wannan hukunci da Abdurrashid ya yanke.






Hamida ta ziyarci Asibiti a hanyarta ta dawowa ta yi karo da baban Amir mijin Laila ya ce ta ƙi zuwa ta ga amarya ta ce za ta zo. Don haka da ta tashi zuwa gidan Gwoggonta sai ta fara biyawa ta can part ɗin yar'uwarta ta fara shiga ba ta nan sai yaran, da yake Weekend ne.
An gyara wurin don ta yi sabuwar mai aiki, yaran suka kewaye ta ta raba musu Chocolate ɗin da ta ruƙo musu har da abin wasa ta sawo ma ƙananan su biyu, ta kama hannun ƙaramar daya ta bi ta a baya zuwa part ɗin amarya.


Da ta yi knocking aka amsa shiru ba a zo an buɗe ba sai da ta ƙara yaran ma suka ƙara ta ce su bari sai ga wata mata ta buɗe cikin matuƙar kwalliya take tana ganin yaran ta ɗauki ƙaramar ta kama hannun ɗayar ta yi ma Hamida maraba da tayin shigowa ta bi bayan ta ta zauna kan ɗayan daga cikin kujerun falon da ya sha gyara yana fitar da ni'imtaccen ƙamshi.
Baban Amir da ke zaune kan dinning ya ce "A'a ƙanwata ke ce a gidan? Barka da zuwa." Ta ce "E tana gaishe shi matar ba ta zauna ba sai da ta kawo ma Hamida abinci ta zubo ma yaran ta sanya ƙaramar a cinya tana ba su tana gaishe
da Hamida.
Kaɗan kaɗan Hamida ke amsa hirar da baban Amir ke mata, da yaran suka ƙoshi ta shiga ciki ta kwaso musu kayan wasa ta basu tana taya su wasan Hamida tana karantar su, awa biyu ta yi ta miƙe ta ce "Na ga amarya baban Amir, Allah ya sanya alheri."
Ta yi ma amaryar sallama wadda ta ce ta bar mata yaran.
Ta fita ya raka ta har waje ta tafi.




A gidan Gwoggo ta samu Laila tana ta razgar kuka wai yanzu baban Amir bai son ta amaryarsa mai shegen sanabe nema take ta karɓe shi ita kaɗai.
Duk da nauyin ta da Hamida take ji zama ta yi ta faɗi mata gaskiya yadda za ta yi mu'amalarta da mijinta,tun kafin a karɓe mata shi gabaɗaya.
Ta yi mata alƙawarin turarukan ɗaki da Lailan ta ce tana so ina Hamidar ke saye.
Sai La'asar Abdurrashid ya zo suka koma gida.






Washegari tana zaune a falonta ta ji ana knocking daga inda take zaune ta bayar da izinin a shigo, aka buɗe aka shigo.
Ƙura wa wadda ta shigo ido ta yi don son tuna inda ta san ta. Ta tako cikin falon sai ta zauna a ƙasa "Barka da hutawa Haj."
Ta furta cikin sunkuyar da kai "Rabi! Hamida ta ambaci sunan cikin wani irin mamaki da ya rufe ta "Na'am Haj Hamida."
Hamida ta yi murmushi "Da ma Rabi kina duniyar nan?
"Ina nan Haj Hamida, bayan tafiyar da aka yi da ni aka yi min aure, auren ne ba daɗi shekara guda kenan da mutuwar shi, zaman ƙauye sai a hankali shi ne na yanke dawowa wurin Haj (Gwoggo Indo) sai kuma na iske ta bar sana'ar, da na tambaye ki sai ta bani labarin kina nan shi ne na taho ki taimaka min ki bani aiki a wurin ki kowane iri ne."
Hamida da ke ta kallon Rabi cike da tausayawa don ganin yadda ta koma gabaɗaya ta rafke ta yamutse saboda wahala.
Ta ce "Ina da mai aiki Rabi, sai dai hakan ba zai hana in ɗauke ki ba."
Ta cicciɓa ta miƙe Rabin na mata sannu ta isa kitchen abinci ta zubo mata ta fito ta kawo mata ta amsa tana godiya tana ci suna ɗan taɓa Hamida ta tambaye ta ba ta da yara ne ta ce haihuwa shida ta yi ukun da ta haife su suke mutuwa saura uku yanzu suna gidan uban su.
Sai da ta ƙare cin abincin Hamida ta shiga ciki yan suturu daga cikin nata ta zaɓo mata don ganin tana buƙatar su, da sabulai da man shafawa har da kuɗi dubu uku ta zo ta ba ta ta ce ta koma gidan Gwoggo za ta sanar da mai gidan idan ya dawo. Ta yi ta godiya ta tashi ta tafi.
Da Abdurrashid ya dawo ta faɗi mishi bai ƙi ba don haka ba ɓata lokaci Rabin ta tare a gidan ɗaki ta ware mata can ta baya tana taimakon ta ƙwarai musamman da cikinta ya tsufa sosai, zuwa yanzu duk sun gama sayayyar kayan haihuwa sai jiran haihuwar kawai inda Hamida ta dage da roƙon Allah ya sauke ta lafiya.
Innawuro ta zo daga Daura Daada ma ta zo daga Yola.


Ana gobe babbar Sallah kowa ya ɗauki azumin arfa Hamida ma duk da faɗan da Abdurrashid ya yi kan ta bar azumin hakuri kawai ta ba shi ta ci-gaba da azuminta.
Bayan Rabi wadda ke mata aiki kafin zuwan Rabin ta shigo suka haɗu suka yi mata aikin sallah zuwa yamma sun kammala komai.
Ta yi wanka ta ɗauki kunun ayan da ta yi da cincin ɗin da suka yi su take so ta fara buɗa baki da su idan an kira Sallah,ɗakin su Daada ta nufa ta zauna kan carpet ta buɗe ƙafafuwanta suna mata sannu, ba ta fi minti biyar da shigowa ba aka fara kiran sallah ta d
ɗaga kofin kunun tana ta addu'a ma fi yawan addu'ar ita ce Allah ya raba ta da cikin nan lafiya, sai ta kafa kofin ai kam tana shanyewa mararta ta amsa da ciwo ta miƙe ta kabbara sallah a ɗakin, har ta idar marar tana ɗan taɓa ciwon tana bari sai dai duk yadda ta so ta yi buɗa baki kasawa ta yi har suna haɗa baki wurin tambayar ta lafiya dai ta ce lafiya lau, Abdurrashid ya yi sallama daga bakin ƙofa saboda Innawuro ya ƙi shigowa ya gaishe su da yi musu barka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login