Showing 60001 words to 63000 words out of 84568 words
Chapter 21 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt
na gilma mata, ƙirjinta ta dafe da wani baƙin ciki ya tokare.
Tana cikin da hawaye ta ji shigowar sa, ƙara rintse idonta ta yi "Yau nan za mu kwana kenan Madam? Ta ji muryarsa sai kuma ta ji ya fita.
Ba a daɗe ba ya dawo gadon ya hau ya kwanta a bayanta ya rungume ta,jin ta ƙanƙame jikinta ya ƙyale ta ya shiga barci.
Da gaske dai Abdurrashid aure zai yi kuma kanuri zai auro mata da take ji ake cewa sun iya riƙe miji, gaskiya ne ko da wannan fitinannen ƙamshin sa janye namiji, ita kam tana sayen turaren feshi da Air freshener amma su humra turaren wuta ba su gabanta, ta ina za ta soma ne? Ta tambayi kanta.
Da ƙyar ta samu barci ya ɗauke ta.
Da gari ya waye da wuri ta tashi ta fara ayyukanta, sai zuci-zuci take Abdurrashid ya fita gidan.
Bai fita ba sai ƙarfe uku ta ce ita ma za ta je ma wata course mate ɗinta barka ta haihu. Ya ce ta zo su fita tare ya sauke ta ta ce A'a ya je kawai ita sai ta yi La'asar.
Yana fita dama a shirye take jakarta da ta sanya Atm ɗinta da wayarta ta rataya sai matafinta,da kanta ta ja motar ta bar gidan.
Wani Mall da suke zuwa ta yi wa tsinke, wani shago na saida turaruka da ke kusa da wanda take zuwa a saman shi an rubuta *HAJJA YANAH KANURI* ta shiga, a saman bene yake hawa na biyu.
Masu aikin wurin sun tare ta da maraba ,mai wurin da ke zaune a wuri na musamman hango shigowar Hamida da ganin ta a jiƙe take jagab cikin Naira ya sa ta ce wa ɗaya cikin masu aikin ta ta kawo mata ita.
Ta isa Hajiyar ta yi mata maraba aka ba ta wurin zama har da lemo aka kawo mata ta ce "Me kike so ƙanwata?
Sai da Hamida ta ja wata gwauruwar ajiyar zuciya ta ce "Ina son humra masu kyau da turarukan ɗaki."
Ta ce "Da waɗanne iri kike amfani?
Ta girgiza kai "Ban amfani da su yanzu dai zan fara." Cikin mamaki ta buɗe baki kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa ta miƙe, Hamida sai kallon ta take yadda har ƙafafuwanta ke iya ɗaukar gangar jikinta saboda tsananin ƙibarta.
Kala-kala ta zaɓo ta dawo ta ajiye su gaban Hamida "Waɗannan suna matuƙar kyau,sai dai suna da tsada."
Hamida ta ɗauka tana shinshinawa tana lumshe ido ƙamshin su ya gamsar da ita.
Ta kuma tashi ta ɗebo humrori "Waɗannan ma na musamman ne,su ɗin ma duk sun yi ma Hamida, a jikin kowanne akwai kuɗinsa, Atm ta miƙa masu su cire kuɗaɗensu Hajiyar ta ce "Daga kin ce ba ki amfani da su ƙanwata, ga abin da za ki dinga turara suturunki, ga kuma su bunner ya kamata ki s gaaya."
Ba musu Hamida ta saisaya.
Har ta miƙe ai yafuto ta Hamida ta dawo sai da ta rage murya ta ce "Ba za ki sayi na gyaran aure ba? Muna kuma yin gyaran jiki."
Hamida ta ce "Ina so."
Wani itatuwan turare ta ɗauko ta ce "Kin ga wannan sai mace ta isa, kina tsuguno da su mijinki zai ji ki daban,ba zan iya tsayawa yi miki bayani ba sai kin gwada,kar ma ki biya sai kin gwada."
Hamida ta saki ajiyar zuciya "Na gode, ina so,ina ake gyaran jikin?
Ta ce "Ciki ne,yarana ke yi, amma zan miki da kaina."
Suka shiga inda ake yi, kamar yadda ta cen da kanta ta yi mata.
Awanni suka ɗauka wanda ya ja lokaci.
Yamma sosai aka kammala ta ce "Kyan ki sati guda za ki samu kina zuwa ƙanwata, zan gyara ki sosai."
Hamida ta yi murmushi "Na gode sosai in sha Allah zan zo."
Suka yi musayar lambar waya, ta sa yaranta suka ɗaukar wa Hamida amma ban da wanda ta ce na tsuguno ne ta ce Hamida ta sanya a jakarta ta kula da shi kamar yadda za ta adana da kudadenta.
Sun yi sallama ta yi mata godiya sai da ta shiga mota fargaba ta rufe ta yamma ta yi sosai kar Abdurrashid ya riga ta dawowa,sai addu'a take har ta isa, ilai kuwa motar da ya fita da ita ga ta nan a ajiye, ta ɗauki kayanta ta nufi ciki yana zaune falo idonsa na kan TV motsin buɗe ƙofar da ƙarar takalmanta bai sa ya ɗago ba, ta isa inda yake jin bai amsa sallamarta ba ta ce "Sannu da hutawa."
Ko motsi bai yi ba gabanta ya ƙara faɗuwa ta wuce ciki alwala ta yi jin an soma kiran sallah.
Tana idar da sallah ta ciro kayanta bunner ta kunna ta ciro kayan da za ta sanya ta turara, sannan ta fita falo shi ma ta sa turaren sai ta wuce bed room ɗinsa don bunner uku ta sawo shi ma ta sanya mishi ta ƙara gyara shimfiɗar sai ta fito.
Knocking ta ji ana yi ta isa ta buɗe mai aikin Aunty Karima ce ta kawo abinci don har yanzu daga can ake kawo mata,ta kan faɗi abin da take so in kuma za ta shiga kitchen da kanta sai ta shaida musu.
Sai da ta shirya tebur ta wuce ɗaki, bayan ta gamsu da daddaɗan ƙamshin da ko'ina ya ɗauka wanka ta shiga bayan ta haɗa wani ruwan turaren da ta sawo wanda Haj Yanah ta ce kar ta yi wasa da shi matuƙar namiji ya shaƙa sai ya biyo, ta gama ta fito ta yi kwalliyarta ta shafa humrorinta kayan da ta turara ta ɗauko ta sanya riga ne da skirt na material da suka yi mata dam! Ko'ina ya fito ta ɗaura ɗankwalin, ta tsaya shawarar ta yi turaren tsugunon ko ta bari sai anjima ƙarshe dai ta yanke ta yi yanzu, key ta danna ma ɗakin duk da sanin Abdurrashid na fushi da ita ba zai zo ba sai da ta gama ta fito ta samu Abdurrashid zaune ya fara cin abinci ta ƙarasa ta zauna "Sannu da zuwa." Wani kallo ya ɗago ya yi mata sai ya ci gaba da cin abincinsa,
ta zuba ta fara ci "Ina kika tsaya har magrib? Ta tsinkayi muryarsa ba zato cikin kanta. "Shopping Mall na biya na sawo turare."
Ta faɗi da sanyin murya "Amma kin san ban son ki fita ki kai magrib ko? Ta ce "Ka yi haƙuri don Allah." Bai ƙara magana ba har ya kammala sai ya koma kan kujerun falon ya zauna, ta tattara kayan abincin ta kai kitchen sai ita ma ta zauna, miƙewa ta ga ya yi ya nufi ɗakinsa ta bi bayansa da kallo a ranta tana faɗin "Fushin bai ƙare ba kenan ko da na bayar da haƙuri?
Tun tana jiran zai fito sai ta ji shiru don suna daɗewa suna hira kafin su kwanta.
Ranta ya ɓaci tana ta masifa a ranta ba don Aljanna da kake nema ba aljanna kuma ba ta samuwa ta sauƙi, yaushe za ka zauna a yi ta maka wannan latsin?
Ta miƙe ta fara kashe kayan kallon da nufin ta wuce ɗakinta ta kwanta ta ji wayarta ta soma ƙara, hannu ta kai ta ɗauko ta sai ta ga shi ne tana picking ya kashe ta san kiran ta yake.
Ta kama hanyar ɗakin nasa, tura ƙofar hango shi ta yi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa daga shi sai guntun wando ƙirjinasa ta kalla sai ta ji wani shauƙi ya kamata hannayensa ya miƙo mata ba ta yi saurin zuwa ba ta ce "Zan je in canza kaya."
Ƙara miƙo mata hannun ya yi ta ƙarasa ya janyo ta ya sa ta cikin jikinsa,wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji ya fidda wanda ta san sai ya daɗe rabon shi da ita yake yin hakan.
A wannan daren Hamida ta ga tarairaya da soyayya na musamman har safiya ji yake da ita.
Sun gama break past ta yi wanka nan ma bin gaɓoɓinta ta yi da humrorin,ta turara kayan da za ta sanya doguwar riga ce, ta shiga ɗakin ogan don gyarawa sai ga shi ya shigo "Ki fito ku gaisa da Usman." Nan da nan ta sha mur ya gyara tsayuwa "Wai meye haka da na ce Usman sai ki ɓata rai?
Shiru ta yi ba ta tanka ba "Ki fito ku gaisa." Ya faɗi sai ya juya ta raka shi da ido.
Sai da ta kammala gyaran ta fito ta same su falon ta zauna ta soma gaishe shi yana amsawa cikin fara'a, knocking ɗin da ake ya sa Abdurrashid miƙewa ya nufi ƙofar ganin mai gadi ne sai ya fita suna magana.
Usman na ganin ya fita ya juyo gabaɗaya wurin Hamida "Madam kenan sai ƙara kyau kike abokina na hutawa,dubi safiyar nan amma ko'ina ƙamshi yake mai kwantar da hankali, ke kanki ƙamshi kike mai tayar da sha'awa."
Zumbur ta miƙe "A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim, ina neman tsarin Allah daga shaiɗancinka Allah ya.. Jin ƙarar buɗe ƙofa ya sa ta yin shiru sai ta dafe kanta, Abdurrashid ya shigo ganin ta dafe da kai ya sa ya ce "Lafiya? Ta ce "Kaina ke ciwo." Ya ƙaraso inda take "Shiga ciki ki sha magani." Sai kawai ta ɗora kanta jikinsa ya fara tafiya zuwa ɗakinsa, suna shiga ta mamutse shi zuwa gado ganin abin da take yi duk da hankalinsa ya fara tashi ya ce "Me kike yi haka? Ga Usman can na bari a falo."
Hannunta ta cusa cikin jikinsa wata irin shafa take yi masa wadda ta sanya shi manta komai, sai ita kaɗai yake so.
Ta gamsar da shi matuƙa da gaske sai da ya dawo daga duniyar da ta kai shi ya ce "Kash yanzu me zan ce wa Usman?
A ranta ta ce "Ɗan iska ba? Ya gaji ya kama gabansa.
Jallabiya ya sa ya fita ta gyara kwanciya ta shiga barci don ba ta san yadda suka ƙare ba. Ta farka ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta sai ta fito ta mayar da kayanta a falo ba ta ga Abdurrashid ba sai ta zauna tana taɓa wayarta. Cikin masu aikin Mami ta yi knocking sai ta buɗe goro da sweet da cingam take ɗauke da su niƙi-niƙi "Wai in ji Mami na sa ranar Anisa." Cikin ɗaure fuska tana hararar ta Hamida ta ce "Na sa ranar ta da wa? Sunkuyar da kanta ta yi cikin daka tsawa ta maimaita na ce "Sa ranar ta da wa? Jikin yarinyar ya ɗauki ɓari cikin rawar baki ta ce "Da yallaɓai."
Juyawa kawai Hamida ta yi ta rufe ƙofarta yayin da ta bar yarinya da tararrabi, don ta san ba ta isa ta koma ma Mami da waɗannan kaya ba, ga wadda aka kawo ma wa ba ta karɓa ba,duƙawa ta yi ta ajiye su a ƙofar ta koma inda ta fito cikin sanyin jiki.
Abdurrashid ya dawo daga fitar da suka yi da Usman yana buɗe ƙofa goro da sweet suka yi mishi maraba. Da mamaki ya wuce ya buɗe ƙofa ya shiga yana ƙwala kiran sunan Hamida,jin shiru ya sa ya nufi ɗakinta. Rub da ciki ya same ta tana zuba kuka, daga inda yake ya soma tambayar ta abin da ya same ta ba ta yi magana ba har sai da ya ce bari ya kira Aunty Karima ko ta san abin da ke faruwa.
Saurin tashi zaune ta yi "Don za ka yi aure Abdurrashid, wani duba ya yi mata jin ta ambaci sunan sa da ko da wasa bai taɓa ji ta faɗi ba,sai dai ta kira shi Hamma kamar yadda ƙannensa ke kiransa.
"Sai a riƙa ci min fuska,a aiko min kayan sa ranar ka."
Ido ya zuba mata kafin ya ce "To ki yi haƙuri." Maganganu ta ci-gaba da saki da suke nuna tsantsan kishin da take ciki yana sauraren ta.
Kiran wayarsa da daddynsa ya yi ya sa ya juya ya bar ɗakin, ita kuma ta yi amfani da hakan ta ja mayafinta ta fito ta bar gidan
[2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH....RAYUWA*
NO.28
Tana tafe tana share hawaye har ta isa gidan Gwoggonta.
Ita kaɗai ta samu tana kallo, ta zauna sai ta rushe da kuka. Gwoggon da ke duban ta tun shigowar ta hankalinta ya yi matuƙar tashi ta fara tambayar ta abin da ya faru, cikin kuka ta zayyana mata
auren da za a yi wa Abdurrashid don ba ta haihu ba, har rana an sa.
Hankalin Gwoggo ya ƙara ɗagawa sai haƙuri take ba Hamida ta ce "Na soma amso miki taimako na haihuwa sai ki kama min dariya ki ce ke ƙalau kike."
Haka Abdurrashid ya shigo ya same su haƙuri ya yi ta bayarwa ƙarshe ya nemi Hamida ta tashi su tafi fafur ta ƙi Gwoggo kuma ba ta matsa mata ba don yadda ranta ya yi mummunan ɓaci, itam ma kamar za ta fashe da kuka.
Da ya gaji ya ce ma Gwoggo ta ƙara ba ta haƙuri zai tafi zuwa dare zai zo su tafi, da safe zai koma Abuja tare da Hamida don ya gaji da waɗannan fitintinun.
Gwoggon ta ce "Idan ka tafi da ita karatun da na ji tana faɗin za ta cigaba fa?
Ya ce "Sai ta cigaba a can." Ya tashi ya tafi.
Bayan tafiyarsa Gwoggon ta rarrashe ta ta yi shiru har abinci ta matsa mata ta ci.
Yamma liƙis sai ga kiran Hajja Yanah,suna gama gaisawa ta ce "Sai na ji shiru ban gan ki ba ƙanwata.
Ta ce "Wallahi kuwa da ma zan kira ki ban samu fitowa ba, mijina kuma ya zo daga Abuja ya ce gobe zai koma tare da ni can,ni fargaba ta idan na tafi can ya zan yi in samu kayayyakinki? Ga dilka da aka fara min."
Ta yi murmushi mai sauti da har Hamida ta ji "Kar ki damu ƙanwata a Abuja ma muna da branch,zan turo miki address na wurin, kina shiga Abuja ki nemi wurin za ki samu komai har ma da waɗanda suka fi waɗanda na ba ki.
Daɗi ya kama Hamida ta ce "Na gode Aunty." Ta ce "Ba komai ƙanwata ni ma na gode." Suka ajiye waya ta tura wa Hamida lambar da ta ce.
Har takwas Abdurrashid bai dawo ba. Hamida ta shiga ɗakinsu suna yammata har yau komai na nan, kullum kuma sai Gwoggo ta gyara shi tana sauke baƙi idan ta yi.
Ta haye katifar bayan Sheltos ɗin da ta fesa ya baje, barci ya fara ɗaukar ta sama-sama ta jiyo muryar Gwoggo tana kiranta,ta buɗe ido Gwoggon na tsaye "Ki tashi mijinki ya zo ku koma gida.
Ba tare da ta tashi ba ta ce "Don Allah Gwoggo ki ƙyale ni in kwana anan ba na son gidan can."
Gwoggon ta yi shiru cikin tausayin ta sai ta juya falo inda Abdurrashid ke zaune "Ta roƙe ni in bar ta kar ta koma gidan yau, ko za ka yi haƙuri da safe sai in rako ta ta ɗauki kayan da za ta tafi da su ?
Ya yi shiru cikin tunani kafin ya ɗago "Ki yi min izni in shiga in fito da ita Gwoggo."
Hanya ta ba shi ya tashi ya shige gefen katifar ya zauna yana jan ƙafarta, tunanin ta Gwoggo ce ta dawo cikin marairaicewa ta furta "Don Allah Gwoggo ki tausaya min ki bar ni ko na koma can ba zan iya barci ba." Sai kuma ta ji ƙamshin turaren Abdurrashid ɓigit ta buɗe ido amma ba ta juyo ba "Ki yi haƙuri ki zo mu koma, ki yi sallama da Daddy da su Aunty Karima, don sammako za mu yi ki kuma yi parking ɗin kayanki."
Ko motsi ba ta yi ba ya matso kusa da ita sai ta ji ya kwanta bayanta "Mu kwana nan kenan?
Gabanta ta ji ya buga meye haka Abdurrashid zai yi ? Ko da ta san ba ya jin nauyin Gwoggo ba ta zaci zai iya shige ta ya shigo ciki ba.
Ba ta karaya ba ƙin ko motsi ta yi don ta ga idan ya ji ta ƙi tashi zai tashi ya tafi sai dai har suka kai minti ya yi ashirin ba shi da niyyar tashin sai ma wasannin da ya fara yi da ita "Tashi to mu je." Ta furta a hankali, zaune ya tashi bai yi magana ba,sai da ta ɗauki mayafinta ta bar dakin ya miƙe ya bi bayanta shi ya yi wa gwoggo sai da safe ita wucewa kawai ta yi.
Suna zuwa gidan sun shiga sun yi wa Daddy da Aunty Karima sallama ba ta tsaya shiga part ɗin Mami ba tana ganin ya karkata zai shiga can ta wuce ta yi tafiyarta,ɗakinta ta shige ta datse shi ma da ya zo ya taɓa ƙofar ya ji ta datse sanin ko ya yi faman bugu ba za ta buɗe ba na shi wurin ya koma ya kwanta.
Ita sai da ta gama shirya kayanta sannan ta kwanta.
Kamar yadda ya ce da sassafe suka bar garin don haka sha biyu na rana sun shiga Abuja.
Sai kallon barrack ɗin Hamida ke yi tana auna banbancin su da waccan ta Kano.
Wasu rukunin gidaje masu kyau ya tsaya kafin tsayawar tasu sai da ya nuna mata wani gidan ya ce shi ne na Usman,kauda kai ta yi ba ta yi magana ba.
Ta yaba da kyan gidan na su an kuma ƙayata shi da komai na more rayuwa.
Kan Sopa ta miƙe tana jin wata gajiya na ƙara bin gaɓoɓinta,sai jin daɗi take sanin Aunty Ainarta anan barrack ɗin take,duk da ba wata jituwa a tsakanin su ta roƙe shi a washegarin zuwan su ya bar ta zuwa gidan Aunty Aina, a murtuke ya ce "Ba yau ba." Ya dai yi mata bayanin mai mishi kula da gida Namiji ne, amma ya sallame shi saboda zuwan ta. Sai dai zai nemi a samo musu mace ko dan makaranta da za ta koma.
Ya fita sai ga Jamilar Usman ta zo mata wuni tana ta murna da dawowar Hamida, yamma sosai ya zo suka tafi.Da daddare Abdurrashid ya ce ta shirya gobe zai turo akai ta gidan Momi,idan ya tashi aiki sai ya je su dawo. Tana gidan Momin ta samu wayar Aina ta ce ta zo ba ta nan, kunya ta kama Hamida ta ce "Ki yi haƙuri Aunty Aina,jiya na tambayi zuwa gidanki ya ce sai weekend. Ta ce "Allah ya kaimu."
Kafin wucewar ta sun