Showing 48001 words to 51000 words out of 84568 words

Chapter 17 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

ba ma za ta iya, sai dai yanzu tana buƙatar a bar ta ta ɗan huta don da alamu ta ji jiki, na so duba ta sosai amma kin ga ta ƙi idan ya zo zai kula da kayansa.
Aunty Zainab ta yi mata godiya likitar ta faɗa motarta ita kuma ta juya zuwa part din Aunty Karima labarta ma yan'uwanta yadda suka yi da Dr ta yi kowacce ta ce da ma ta zargi haka "Momi Binta ta ce "Ɗan rainin wayo to da yana a'a kar akai ta."
Sauran suka fashe da dariya ita ba ta yi dariyar ba sai ƙarawa ta yi da cewa "Ni da ma ban so aka kai masa yarinyar nan ba ya je ya kashe musu 'ya, to Daada ta ce sai dai a yi haka, don haka Karima ki je ki dauko yarinyar nan ki kawo ta wurin ki maza ba haƙuri ne da su ba dubi yadda ta koma yau kawai ba kuma ɗaga mata ƙafa zai yi ba.
Aunty Zainab ta ce Dr ta ce ba wata matsala na farko ne kawai, da an bar masa matarsa ga shi tafiya zai yi."
Hannu ta ɗaga mata "Ban yarda ba, ki ɗauko ta Karima ki faɗa mishi in ji ni.
Yanzu ki je ki ba ta abinci ki tabbatar ta ci kafin ya dawo ya duba ta."
Aunty Karima ta ɗaga kai sai ta miƙe "Bari in duba sun kammala girkin in kai mata kuma ku ci kafin ku wuce.
Ta wuce kitchen din ta ɗauki wasu yan mintoci ta fito mai aikinta na biye da ita da tray ba ta samu kowa ba cikin yan'uwan nata a inda ta bar su sai suka shige part ɗin Abdurrashid ita da ke gaba ta yi knocking Hamida ta buɗe tana faɗin "Sannu Aunty."
Za ta karɓi tray a hannun mai aikin Aunty Karima ta hana ita ta karɓa, shigar ta ganin Abdurrashid wanda ba su san sadda ya shigo gidan ba yana gyara gado ya sa ta ji kamar ta koma sai dai ya riga ya gan ta, ta wuce ta ajiye musu tray ya gaishe ta yana ba ta labarin kiran da ya samu na gaugawa wanda shi ya hana shi shigowa, amma yanzu zai shigo ya yi sallama da su Momi ta ce "To amma don Allah ka tsaya sai ta ci abinci na zo dama in tsaya ta ci a gabana na ga kuma ka dawo."
Ya ce "Za ta ci Aunty na gode." Ta juya ta fita.
Sai da ya gama gyara shimfiɗar ya wuce bathroom zanen gadon da ta ɓata ya wanke sai ya fito tana ta satar kallonsa daga inda ta idar da sallah "Taso to." Ya ce yana nufar wurin cin abincin, wanda ya zuba mata ya kuma matsa mata sai da ta kusa cinye shi ya ƙyale ta da ƙyar don cewar da take ta ƙoshi.
Hannunta ya kama zuwa bakin gado maimakon ya bar ta ta zauna kan cinyarsa ya ɗora ta wasa ya riƙa yi da ita yana hura mata iska a kunne wanda duk ya ta da mata tsigar jiki.
Ba ta ankara ba sai dai ta ji ya soka mata allura yau ma ba ta ji zafi ba sai da ya gama liliya mata ya ja ta suka kwanta, ba ta ɗau wani lokaci ba ta yi barci ya zare jikinsa ya rufe mata rabin jikinta sai ya bar ɗakin.


Ya samu suna ta shiri. Shi da Aunty Karima suka yi musu rakiya Air port.
Momi kuma da kanta ta faɗa masa Hamida ta dawo part ɗin Aunty Karima.
Shiru ya yi cikin tunani don ba halin tambaya sai dai ya zargi sun gane abin da ya faru da Hamida a yau.
Sai da suka ga tashin su suka juyo Aunty Karima kaɗai ta koma gida shi komawa ya yi wurin patients ɗinsa.
Tana ajiye mayafinta wurin Hamida ta tafi ta samu ta tashi har ta yi sallar La'asar ta tambaye ta jiki ta ce ta ji sauƙi ta shaida mata za ta koma part ɗinta don haka ta ɗauki kayan amfanin ta.
Akwati guda ta cika Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ɗauka wani ɗaki da ke jikin wanda su Hanan suka sauka Aunty Karima ta kai ta aka sanya mata akwatin a wardrobe sai ta kwanta kan lafiyayyen gadon.
Auntyn ta ce "Ko za ki zo mu je falo ki ɗan huta da zaman ɗakin? Kai ta girgiza "Zan kwanta Aunty."
Ok kawai ta ce ta fita sai ta ja mata ƙofa.




Abdurrashid sai da aka yi sallah ya dawo, saboda aikin da ya tare shi amma duk abin da yake Hamida na maƙale a ransa ya ƙosa ya dawo don ya ga halin da take ciki.
Da ya shiga ɗakin bai gan ta ba sai ya nufi part ɗin Aunty Karima ita ya tambaya inda Hamidar take ta nuna masa hanyar ɗakin da hannunta.
Ya shiga da maƙallaliyar sallama ta ɗago daga kwancen da take tana amsawa zama ya yi bakin gadon yana jin sannu da zuwan da take masa kanta ya ruƙo ya ɗora saman cinyarsa yana shafa calabar da ke kanta, "Ya kike jin jikin yanzu? Ta ce "Na ji sauƙi."
"Kin ci abinci? Ta ɗaga masa kai "Me ya sa ba za ki fita wurin Aunty ba kin kwanta nan ke kaɗai?
Ta ce "Na fi son in kwanta." Wayarsa ya ciro ya kira Aunty Karima ya ce ta sanya a kawo masa abincinsa nan. Anan ɗin ya ci har ya sa Hamida ta ƙara, sai goma ya tafi da ya ga Hamida ta soma barci.




Ya gama duk shirin kwanciya amma ya gaza barcin kewar Hamida yake ji yana jin tsaurin hukuncin Momi Binta da ta raba shi da matarsa a daidai da ya san muhimmancinta. Sumarsa ya shafa yana mai lumshe idonsa tunanin cikin nishaɗin da ya kasance a daren jiya yana gilma mishi, hannu ya sa ya shafo inda ta fi kwanciya ɗankwalinta da ke wurin ya ɗauko ya kai fuskarsa ƙamshin da take yi da ke fita cikin ɗankwalin ya natsar da shi har ya shiga barci cikin kwanciyar hankali.




Da asuba yana dawowa sallar asuba ta ƙofar da ke sa da mutum da part ɗin Aunty Karima ya bi ya isa ɗakin Hamida ya samu ta idar da sallar Asuba ya ja ta zuwa gado suka kwanta, tambayar yadda ta kwana da jiki yake yi, ta ce ta samu sauƙi.
Ya ce ta huta yau ba sai ta je Sch ba zai faɗa musu ba ta da lafiya. Ta ce za ta iya zuwa, ya ce a'a ta dai kwanta.
Sai da gari ya yi haske ya zare ta cikin jikinsa ya fita.
Ko da ya shirya bai dawo ta nan ba sanin Aunty Karima a daidai wannan lokacin barci take.






Barci sosai Hamida ta yi bayan tafiyar Abdurrashid. Da ta tashi sai ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar materiyal ta fita tana ƙamshi mai sanyi.
Kan ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna TV ta zura wa ido har ta ji shigowar Aunty Karima ƙara shiga nutsuwarta ta yi kafin ta soma gaishe ta, ta amsa cikin fara'a ta gayyace ta zuwa wurin cin abinci tare suka karya sai suka dawo falon suka zauna suna kallo.
Kiran Gwoggo Indo da ya shigo wayar Hamida ya sa ta miƙewa ta koma ɗaki ko da suka ƙare wayar yan Daura ta kira daga nan ba ta koma falon ba a ɗakin ta zauna ta ɗauko littattafanta na makaranta tana dubawa da ta yi sallar Azahar samun kanta ta yi da son yin kwalliya don ta burge Abdurrashid ganin duk sa'adda ta yi kwalliya yadda yake yawan kallonta wanka ta sake ta yi kwalliya sosai don zama da Aina ta ƙware a naƙaltar yadda ake yin ta.
Yau har da su jambaki ta gyara girarta ta feffesa turaruka less ta sanya ɗinkin riga da skirt da suka yi cif a jikinta ta yi kyau ba kaɗan ba, sai ta samu kanta da kasa fita wurin Auntyn don tana jin kunyar Auntyn ta ga ta sake kwalliya ta gane don Abdurrashid ta yi.
Gado ta koma suna chart da Hanan ƙarar buɗe ƙofar ya sa ta ɗago ido ganin shi ne ta ji mamakin hakan ta duba agogo sai lokacin biyu ta yi.
Sannu da zuwa ta yi masa ya miƙo hannu sai ya kamo ta ya sanya ta a jikinsa sun daɗe a hakan kafin ya ce mu je falo ki ci abinci in ji Aunty. Ta kaɗa kai ya sake ta sai suka fito falon tare da Auntyn suka ci abincin shi yana gamawa ya ce zai je ya yi barci bai fito ba sai La'asar gidan ya bari sai dare ya dawo shi da abokinsa Usman.
[6/30, 10:12 PM] Maryam Ibrahim Litee: SHIRIN ALLAH... RAYUWA




N0.21








Ana gobe tafiyar Abdurrashid da daddare ya kwanta amma sam ya gaza barci.
Wayarsa ya jawo ya kira layin Hamida wadda ke zaune tana karatun makaranta, ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama "Ki zo yanzu ki same ni." Ya faɗi cikin dakewa ga mamakinsa ji ya yi kamar za ta fashe da kuka ta ce "Kar Aunty ta gane Hamma."
"Sai me don ta gane? Ina jiran ki." Ƙit ya katse kiran tagumi ta rafka da hannu biyu ta shiga tunani.
Ta jima a haka kafin aka turo ƙofar ɗakin saurin kai dubanta ta yi Abdurrashid ne, ji ta yi gabanta ya soma bugawa da sauri "Tashi mu tafi." Ya faɗi ba alamar wasa a fuskarsa ta miƙe ba ta ɗau komai ba har wayarta daga ita sai wata yar yala-yalan rigar barci mai guntun hannu tsawon ta iya gwiwa sai wata yar mitsitsiyar hula a kanta.
Gaba ya sanya ta yana biye da ita, ta ƙofar da za ta sada ka da kitchen ɗinsu suka bi, suna shiga bathroom ta faɗa kafin ta fito ta hau gado, shi zama ya yi riƙe da laptop dinsa har ta soma barci ta ji an rungume ta abin da yake mata ya sa dole ta wartsake.
Daren dai bai bar su sun samu isasshen barci ba ta yi koke kokenta har ta gaji ta yi shiru da ƙyar ta tashi sallar Asuba da ya tashe ta, tana idarwa gadon ta koma duk da barcin da ke idonta ƙin yi ta yi tana jiran ya shigo ta shaida mishi za ta tafi.
Da ya shigo ta faɗi mishi shiru ya yi sai da ya hau gadon ya janyo ta jikinsa bayani ya yi mata za a riƙa sanya mata rabin albashinsa duk wata ta riƙa yin duk buƙatunta, sai gargaɗin kar ta kula ƙawayen banza ta kuma dage da mayar da hankali a karatunta.
Da ya gama gaya mata barcinsa ya shiga yi yayin da ita zullumi ya hana ta yi har dai ba ta san sa'adda ya yi awon gaba da ita ba.
Zare jikinsa da ya yi cikin na ta ya sa ta buɗe ido Meye tuna abin da kenan ya sa ta fara zare ido tana ganin ya shiga bathroom ta miƙe da sauri har tana tintiɓe ta fice shigar ta ƙofar da ta haɗa sasan Aunty Karima da na shi sauri ta ƙara ta samu ta shige ɗaki sai dai haɗa idon da suka yi da Auntyn wadda ke zaune bisa dinning tana break past ya sa ta tsayawa cak cikin wata irin kunya da nauyi da ta ji sun lulluɓe ta "Ki zo ki karya."
Ta ji muryar Auntyn cikin kunnanta "Zan yi wanka tukun Aunty."
Ta faɗi cikin dauriya sai ta cigaba da tafiya.
Wanka ta fara ta
[6/30, 10:12 PM] Maryam Ibrahim Litee: SHIRIN ALLAH... RAYUWA






No.20






Washegari da safe ko da ta yi sallah shirin makaranta ta soma. Wadda Aunty Karima ta ɗora wa alhakin gama abin karin Hamida kafin fitar ta Sch ta zo ta gaya mata ta kammala.
Ta fita zuwa dinning ɗin ta haɗa tea ta zuba agada da ƙwai a flate sai ta koma ɗakin, akan mirror ta ajiye flate ta tsaya tana karyawa tana duban agogo don lokacin tafiyar su ya yi ko me ya hana Abdurrashid fitowa? Turo ƙofar da aka yi da shigowa gabaɗaya ya sa ta kai idonta wurin, a shirye yake ya yi kyau kamar kullum sauke idonta ta yi ƙasa ta yi sai ta soma gaishe shi, ya tako inda take kasa cigaba ta yi da karin sai ta juya bakin gado inda ta ajiye hijab ɗinta da Sch bag ɗinta sai ta dawo ta ɗauki kayan karin nata ya gane nufin ta ta kammala sai ya fice ta bi shi a baya.
A kitchen ta ajiye sai ta bar sallahun idan Auntyn ta fito a ce mata ta wuce.




Yau a makaranta Walida ba ta zo ba Hamida ta rasa yadda za ta yi ta san ko lafiya har sai da aka tashi Abdurrashid ya ɗauke ta ya hau titi ta ce "Yau ƙawata ba ta zo ba."
Ta gefen ido ya dube ta kamar ba zai yi magana ba har sai da ta fitar da ran zai ce wani abu kafin ya ce "Me ya hana ta zuwa? Cikin damuwa a fuskarta ta ce "Ban sani ba, ko za ka kai ni gidan su in gano? Shiru ya yi bai amsa ba har ya sa cikinta ɗurar ruwa, don sai take ganin ta ɓata mishi ne.
Sun zauna shiru har suka isa barraks ɗinsu.
Suka fito ganin Sojoji ko ta ina ya kayar da gaban Hamida sai dai ganin Abdurrashid tare da ita ya ɗan kwantar da hankalinta, suka wuce Sojoji na ƙasa da shi na sara mishi.
Wani kyakykyawan Office suka shiga wuri ya nuna mata ta zauna shi kuma ya hau kujerarsa Computer yake taɓawa tsawon lokaci kamar ma ya manta tana wurin har zaman ya soma gundurarta.
Knocking aka yi kafin ya bada umarnin shigowa wani soja ne ya shigo sai da ya sara mishi kafin ya ajiye wata jaka da ya ɗauko me ɗauke da kayan abinci.
Sai da ya juya Abdurrashid ya miƙe wurin da ya ajiye ya nufa ya zuba abincin da ke ta turiri, da hannu ya kira ta ta taso kujera ya ja mata ta zauna, shi yana tsaye "Ki ci abincin sosai ina zuwa zan duba wani patient ɗi na."
Ya faɗi yana tsiyaya mata drinks sai da ya fita ya ja ƙofar ta fidda ajiyar zuciya, cokalin ta kama ta shiga cin abincin a hankali, ta ci ya yi rabin wanda ya zuba mata sai ta sha drinks ɗin ta rufe komai, nan ta cigaba da zama tana kallon TV da ke aiki a Office ɗin.
Ya dawo wata ƙofa da ke a cikin Office ɗin ya buɗe sai ya shiga ya kira sunanta, a hankali ta taka ta same shi gado ne ƙwaya ɗaya rak a ɗakin yana kwance a kai, ganin ya tuɓe kayan jikinsa ya sa ta sunkuyar da kai hannuwansa ya buɗe "Zo nan."
Ta ji muryarsa kan nata na sunkuye ta ƙarasa gaban gadon "Ki zo nan." Ta ji ya kuma maimaitawa ta tayar da kai ta dube shi sai ta ga inda yake nuna mata ta zo ɗin ƙirjinsa yake nunawa da hannu ba ta da zaɓi dole ta taka ta kwanta kan ƙirjinsa ya kai hannu ya cire hijab ɗin jikinta da ƙyar ya samu ya cire rigar don yadda ta kamata ta ƙanƙame jikinta a jikinsa kasantuwar ba komai jikinta sai rigar, ya shiga sha'aninsa ya yi nisa komai ya kwance masa wayarsa ta shiga kukan neman agaji bai kula ta ba har sai ta katse ta kuma ɗaukar kuka a kasalance ya kai hannu don kashe ta gabaɗaya, idonsa ya yi arba da sunan Aunty gyaran murya ya yi don saita kansa ya ɗaga wayar "Lafiya Abdurrashid har yanzu ba ku dawo ba? Ya jiyo muryarta cikin damuwa. "Lafiya lau Aunty na biya barrak ne, muna nan dawowa."
Kamar za ta ƙara magana sai kuma ta yi shiru "Sai mun dawo Aunty."
Ya ce cikin muryarsa da ba ta gama dawowa daidai ba yana shafa sumar Hamida da ke hawaye don azabar da take ji wadda ta kasa banbance ta da ta ranar farko.
Aunty ta yi zaune saƙare da waya a hannu cikin tunani kiran Aunty Zainab ya shigo wayar ta ɗaga suna gaisawa da tambayar lafiyar iyali Aunty Karima ta kada baki "Ita Momi me cewa a ɗauko matar Abdurrashid kar ya kashe musu 'ya, to kiran da ki kai min zaune nake ina jimami, tun safe da ya fita da yarinyar nan zuwa makaranta har yanzu bai dawo da ita ba."
Dariya Aunty Zainab ta yi "Kin ji ki za ki damu kanki da gangan, kina biyewa Momi sai ma ya biyo ta har ɗakinki idan ba ki mayar masa da mata ba za ki gane Allah da girma yake."
Dariya suka yi Aunty Karima ta ce "Ni dai umarnin Momi nake bi." Ta ce "Ai sai ki yi ta bi ki takurawa ɗa na, bawan Allah ya kusa tafiya ku bar shi da matarsa sai ku wani ɗauke masa ita. "
Aunty Karima ta yi dariya tana jinjina kai. Suka canza hirar zuwa ta wajen birhtday ɗin da yarinyar Aunty Safiya za ta yi wani satin.




Bayan dogon lokaci Abdurrashid ya sarara wa Hamida bathroom ya shige yayin da ita kuma ta dunƙule wuri ɗaya wani barci na fizgarta.
Ya fito yana goge kansa da tawul bai tashe ta ba, kintsa kansa ya yi sai ya fice.
Ta ɗan jima kwance kafin ta yi ƙarfin halin tashi zaune sai ta miƙe a hankali ta shiga bathroom ɗin, wankan tsarki ta yi sai ta kuma yin wanka ta fito unifoam ɗinta ta mayar kasa fita Office ɗin nasa ta yi ta zauna bakin gadon don kunyar abin da ya faru tsakanin su.
Ta daɗe zaune sai ga shi ya shigo "Zo mu tafi." Abin da ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login