Showing 39001 words to 42000 words out of 84568 words
Chapter 14 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt
yi a daren da aka kawo Hamida ɗakinta, manyan mutane ne za su halarta saboda rashin sanar da su ɗaurin aure.
******"*"
Ana gobe za su wuce Daura idan kuma sun je kwana daya za su yi a juyo da ita Kano, Abdurrashid ya iso da yammaci.
Bai shiga ba da wayarsa ya yi amfani ya kira ta.
Ba ta cikin shiri don aiki take taya masu aikin Gwoggo tuni suka koma abincin sayarwar su wanda Gwoggo Indo ta ce ba ta ga dalilin zama har sai Hamida ta tare kafin ta koma sana'arta ba, daga Abdurrashid ba ɓanɓaruwa yake ba.
Cikin sauri Hamida ta shiga ta watsa ruwa wata doguwar riga ta zura ta yane kanta da gyalen rigar sai ta fita, yana cikin mota bai fito ba ta san miskilancin na kai kenan indai ya ƙi fitowa, ta zagaya ta buɗe motar ta shiga ta gaishe shi "Fita za mu yi, zan buɗe miki account saboda tafiyar da zan yi in bar ki zan dinga sanya miki abin da za ki yi amfaninki da shi." Ta ɗaga mishi kai. Daga haka motar ya tada suka bar wurin, har kuma suka isa bankin babu wanda ya yi ko tari a cikin su.
Ba wani ɓata lokaci aka gama komai, muhimmin abin da ya sa ya zo da ita ma ATM da za a yi mata don an riga da an yi mata komai.
Da suka fito ji ta yi kamar ta roƙe shi ya kai ta gidan su Walida duk da sanin da ta yi Walidar na nan tafe da yamma za ta kwana gidansu washegari su wuce Daura.
Sai dai suna rabuwa da Abdurrashid wanda yana sauke ta ya wuce Walidar ta samu zaune ta iso, suka shiga murnar ganin juna Walida ta ce "Ya za a yi da ƙawayena da na gayyata masu son zuwa Daura? Daidai nan Gwoggo ta shigo, ta cafe "Ai ba za ta iya mishi magana ba, shi kuma ba taɓuwa yake ba." Nan Gwoggo ta yi ta surfa uban faɗa kan rashin ba Hamida komai na game da biki da Abdurrashid bai yi ba. Hamida ba ta ji daɗi ba saboda Walida na zaune amma ba yadda ta iya.
********
Abdurrashid shi ya bayar da motar da ta kai su Daura su biyar. Daga Hamida da walida sai Gwoggo da wata aminiyarta sai Laila.
Taran biki suka samu a na yi, yan'uwa duk sun iso dan su iyalan gidan ma kawai Malam, suka ɗauki hanya.
Sun kusa shiga Kano Aunty Zainab wadda ita ta wakilci sauran yan'uwanta zuwa Daura, ta ciro wayarta jin shigowar saƙo *Ka da ku kai yarinyar nan part ɗina, jama'a za su ɓata min wuri Aunty na roƙe ki.*
Saƙon da ta gani kenan daga Abdurrashid ɗan murmushi ta yi "Ja'iri za ka shiga hannu." Ta faɗi a hankali.
****"**
Wani keɓaɓɓen wuri cikin part ɗin Aunty Karima aka sauki amarya da yan'uwanta. Sai da suka ci abinci suka yi sallah a ka zo a ka tafi da Hamida don shirya ta zuwa wurin Dinner.
Yayansu Momi Binta yammata su suka zagaye Hamida da ana yi mata make-up, su kuma suka zame mata ƙawaye a wurin don Abdurrashid ya hana ta faɗi ma kawayenta na makaranta bai so idan ta koma makaranta a gane ita matar aure ce, da ma ita ba faɗi za ta yi ba Walida ce mai giggiwar faɗin.
Duk kuma abin nan da ake Walida na tare da ita Abdurrashid ma ba da son sa ba abokansa masu tarin yawa sun zo bisa jagorancin Usman wanda shi ya gayyace su.
Manya daga ko'ina tun daga Nigeria har ma da wasu ƙasashen sun hallara.
Da aka dawo Dinner ma yaran su Aunty Safiyan ba su bar Hamida ta kwana cikin danginta ba janye ta suka yi duk da su ɗin ba tsararrakinta ba ne, mutum biyu ne suke kai ɗaya.
Washegari aka yi mata buɗar kai irin na su na mutanen Yola yan Daura sun ga ruwan arziƙi wanda aka tura wa Hamida da mahaifiyarta duk da su ma ɗin tushen su yolan ne hausawa suka ce kowa ya bar gida gida ya bar shi. Su yanzu al'adun Katsinawa suke yi.
Idan wannan ta zo ta bayar da nata wannan idan ta fito sai ta bada sama da haka.
Amarya ta yi kyau har ta gaji, ana tashi yan Daura suka wuce gidan Gwoggo Indo bayan sun sha kyaututtuka daga Engineer da kuma atamfofi da aka raba da dardumai ban da ƙananan abubuwa.
Walida ma ana yin sallar magarib ta yi wa Hamida sallama ita kuma ta miƙa mata wasu kuɗi da ta amsa hannun Gwoggo Indo tare da yi mata godiya.
********""
Ta idar da sallar Isha'i a tafkeken dakin da yammatan suke Aunty Karima ta leƙo ta yafuto ta da hannu Mimi ɗiyar Aunty Zainab ta farko da ke kusa da Hamida tana danna wayarta ta ce "Pls Aunty kar ki ɗauke mana ita." Yarinyar Momi Binta ta uku da ma su biyun su ne tsararrakinta mai suna Hanan ta miƙe tana haɗa hannaye "Pls kar ki ɗauke mana ita Aunty." Aunty Karima ta kama baki "Kai ku ji mun yara, dakin mijinta za a kai ta idan kuma a gaya wa Hamman naku kun ce a bar muku ita shi kenan." A tare suka ɗaga hannaye "A'a ba mu ce ba." Dan ba ƙaramin shakkarsa suke ba, ko da ba komai yake musu ba sai dan rashin sakin fuskarsa.
Ta bi bayan Aunty Karima har bedroom din Auntyn, ta wuce bathroom ta haɗa mata ruwan wanka da kanta ta fita ta bar ta wankan ta yi ta fito tana jin daddaɗan ƙamshin da take yi.
Tsaye jikin madubi ta samu Aunty Karimar ta ba ta wuri ta ce ta zauna da taimakon ta ta zuba kwalliya , wasu irin kaya da Hamida ta rasa mene ne ta ba ta ta sanya, doguwar riga ce da lulluɓinta ta kama mata hannu suka bar dakin, don ta rufe har fuskarta, wani falo suka shiga wanda Daada ke zaune da ƴayanta, ta zaunar da ita gaban Daada nasiha sosai Daadar ta yi mata game da zaman aure, maganar mahaifiyar Abdurrashid da ta yi dukkan su sai da suka yi ƙwalla, a ƙarshe ta ce su kai ta wurin mahaifin Abdurrashid da Haj Mariya kafin su miƙa ta ɗakinta, Aunty Karima da Aunty Zainab su manyan suka ce su je su raka ta.
Sam barka da suka fara kai ta sasan maigidan nan suka tarar da Haj Mariya har ma da yayarsa Haj Gambo, bayan ƙare gaisuwa fatan alheri kowannen su ya yi suka kuma ba da kuɗaɗen da ake ba amarya idan an kai ta wurin dangin miji.
Sai suka miƙa ta sasan Abdurrashid ta ƙofar da za ta sa da ka da sasan mahaifin nasa.
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA
No.18
DAGA
MaRuBuCiYaR
WA GARI YA WAYA
CANJIN BA ZATA
RANAR NAKA
HATTARA
MARYAM LITEE
Ranar juma'a da aka tashi makaranta turowa ya yi aka kai ta gida don yana da aiki.
Sai da ta canza kaya ta ci abinci Aunty Karima ta kira ta a waya ta ce ta zo ta yi baƙuwa, ta isa sasan sai Gwoggonta ta gani daɗi ne ya lulluɓe ta ta zauna kusa da ita tana gaishe ta, ita ma cikin farin cikin take amsawa yadda ta ga Hamida.
Hamida ta ce ta zo su je wurinta, falon da ya nuna mata ya ce za ta iya kai baƙinta ta kai ta, ta buɗe fridge ta samu akwai lemo da ruwa ta ɗauko ta ajiye gaban Gwoggon.
Hira suke a hankali Gwoggo tana ba ta labarin jarin ta ya yi ƙasa saboda hidimar bikin nan, hakanan dai take rurrumawa Hamida ta miƙe ta ce tana zuwa ɗakinsu ta koma ta ɗauko hand bag ɗinta ta dawo wurin Gwoggonta.
Ta tura hannunta cikin jakar ta ciro duka kuɗin da ke ciki wanda yake ba ta ba tare da ta ƙirga ba ta miƙa wa Gwoggo su duka.
Sai da ta ƙirga ta ce "Waɗannan fa ba ta ko numfasa ba ta ce "Ba ni yake kullum idan ya sauke ni makaranta."
Gwoggo ta taɓe baki " Mai hali dai bai fasa halinsa, duk wannan uban arziƙin ji abin da aka samu a wurin ki, shi dai na rasa abin da ya sa yake ƙanƙamo.
Hamida dai ba ta ce komai ba duk da ta ji ba daɗi ranta ya sosu da yadda ta aibata shi.
Wata kwalba Gwoggo ta ciro cikin jakarta sauyoyi ne a ciki sai aka zuba ruwan turare "Kin ga wannan Hamida duk dare in za ki kwanta ki ɗan tsiyaya a hannunki ki yi Bismillah ki shafa wa fuskarki, zuwa ƙirjinki har zuwa mararki, namiji duk taurin ransa ya yi amfani da ke sai ya yi ladab, sati mai zuwa zan zo in ƙarɓi kuɗinsa.
Ban da ba ki son na sha an kawo kala daban daban masu kyau kina amfani da su kwana nawa za ki kama shi a hannunki, kina dai ganin yan'uwanki dubi dai Laila yadda Ahmad ya zama kamar bawanta, ba kuma boka ba Malam, kayan nan dai na mata nake kai mata duba ki ga yadda sasan su ya zama daban a gidanmu.
Aina da aka kai jiya jiya da ta ce in turo Acc no dubu dari biyu ta sanyo min, amma ke Hamida duk uban wannan arziki sai tarkacen canjin makaranta.
Ta ciro wani garin magani a farar leda "Ki daure Hamida ki sha wannan da madara yanzu a gabana.
Fuska Hamida ta ɓata tuna maganar Nurse Saratu ta ce "Ba na sallah Gwoggo.
Cikin rashin jin daɗi Gwoggo ta miƙo mata "Ki tabbatar kin sha kina gamawa."
Ta gyaɗa mata kai ta je ta ɓoye ta dawo Gwoggo ta ce za ta tafi suka fito tare tana mata rakiya, hango Mami Haj Mariya tsaye da wata mata ya sa su nufar inda suke, sai da Gwoggo ta gama gaishe su Hamida ma ta bi sahu sai suka wuce har gate ta raka Gwoggon nata ta juyo za ta gifta su Mami ta yafuto ta ta isa ta tsaya "Ba ki taɓa zuwa kin gaishe ni ba, ko da yake wannan miskilin banzan ai ba zai ce ki zo ki gaishe ni ba." Ta taɓe baki Hamida dai ta tsaya shiru sai matar da suke tare ta ce "Tafi yarinya."
Hamida ta juya, Haj Mariya ta kuma taɓe baki "Ai duk shegen jin kansa ya ɗauko inda za a bi da shi." Waccan matar ta ce "Me ya sa kika ce haka? Ta ce "To mariƙiyarta waccan da ta fita ba ƙaramar hatsabibiya ba ce wurin sanin maganin mata masu kyau, duk inda zan zaga in saya sai na dawo wurin ta don nata ne kawai zan yi amfani da shi in rikita Alh, ga shi ta yi kitimirmirar shigo da diyarta gidan nan, dole ina ji ina gani zan haƙura da maganinta."
Waccan ta ce da ba ki yi saurin sarewa ba ki sa a yi miki bincike inda take sarowa ki fantsama can, don yanzu da ma ba za ki haɗa sirri da su ba."
Ta ce "Kin kawo shawara zan gwada yin hakan."
Da Hamida ta koma ɗaki Innawuro ta kira a waya, har Innarta sai da Innawuro ta tilasta ma wa ta karɓi wayar, Hamida ta gaishe ta.
Tana gamawa yau wanka ta yi da wuri ta yi kwalliya da wasu riga da skirt da suka yi matuƙar karɓarta na cikin kayan aurenta, ta sanya wani siririn gyale ta rufe kanta ta zura takalma ta fita da niyyar zuwa part ɗin Aunty Karima.
Fitowarta ta hango Abdurrashid da abokinsa Usman waɗanda suka ba ta baya ta wuce abin ta sai dai tana zama ta dai gaida su Aunty Zainab da ba su daɗe da shigowa gidan ba kiran Abdurrashid ya shigo wayarta tana ɗagawa faɗa ya kama mata wa ya ce ta fita yana kashe wayar ta miƙe tsam Aunty Safiya ta ce "Ina kuma za ki daga shigowa?
Murmushi ta yi Momi Binta ta ce "Yi zaman ki Daugter ga kilishi nan da Zainab ta sanya aka kawo ki ci." Ta sunkuyar da kai "Shi ya ce in dawo." Ƙwafa ta yi tana cije baki "Ban da tafiya zai yi da sai na saɓa wa ja'irin yaron nan, ya bar yarinya ta shiga mutane sai ya ce kullum tana can ɗaka ƙunshe ba sai ya bar ta da Karima ba ta samu abokiyar hira ita ma."
Mai aikin Aunty Karima ta kira ta ce ta ɗebo kilishi ta kawo, da ta dawo aka ba Hamida ta yi godiya ta fita.
Yanzun ma tsayen ta gifta su shi da abokin nasa Usman ya yi dariya "Ka ga abokina ina tausaya ma idan yarinyar nan ta ƙara girma, don ba ƙaramin juya ka za ta yi ba."
Ya harare shi "Sai ka ce wani kai Allah ya kyauta".
Ya ce "Shi kenan ai muna nan, Allah ya nuna mana, bari in barka ka bar yarinya ita kaɗai."
Suka yi musabaha ya faɗa motarsa
Abdurrashid ya shiga ciki zaune ya same ta riƙe da wayarta bai amsa sannu da zuwan da take masa ba illa tambayar ta da ya yi ""Me kike karantawa a waya ne da ba ki gajiya da riƙe ta? Ba ta amsa ba illa ƙara sunkuyar da kai da ta yi
"Ba ni wayar.". Ya ce yana kallon ta, ta tashi a hankali don idonsa da ke kanta sai ta miƙa masa a tsayen yake dubawa ganin novel ne take karantawa ya dago "Me ya sa ba ki dagewa wurin duba takardun ki na Sch sai ki dage kan wannan shiriritar?
Ta ce "Ina dubawa.". Kai ya kaɗa ya wuce ya cire kayansa.
Yau bai yarda sun zauna wuri guda ba don yadda shigar ta ta rikita masa lissafi ya ce su je part ɗin Aunty Karima su yi ma su Aunty Safiya hira.
Suna can har
sai da Aunty Zainab ta ga Hamida ta kwantar da kanta a hannun kujera ta ce "Kai yarinyar nan ta kwanta Abdurrashid."
Da suka kwanta idanuwansa ya rufe da ƙarfi a fatan da yake barci ya ɗauke shi Hamida ce ta tsaya shiga Toilet bayan ta cire kayan jikinta, ta gama abin da za ta yi har za ta fito ƙafarta ta zame ta daki ƙofa sai ta faɗa kan ƙafar wani irin zafi ya ratsa ƙwaƙwalwarta ta fasa kuka lokacin da ta yi ƙoƙarin taka ƙafar ta wuce, sai hawaye wasu na korar wasu.
Abdurrashid da tun fasa kukanta ya buɗe ido ya mike da azama ya yi Toilet ɗin yana turawa ya gan ta inda ta faɗi tana kuka "Me ya same ki?
Ya tambaye ta "Zamewa na yi. Ta ba shi amsa ya miƙo mata hannunsa "Tashi to mu je." "Ba zan iya takawa ba ta faɗi tana cigaba da hawayen hannu ya sa ya sunkuce ta zanen da ta ɗaura ya idasa kwancewa ya faɗi ya bar ta daga ita sai fant da bra haka ya kai ta bisa gado yana soma jan ƙafar ba tare da ya lura da hannayenta da ta sanya gabadaya ta kare ƙirjinta duk da raɗaɗin da ke shigar ta tana hawaye waige waige take inda za ta samu abin da za ta rufe jikinta, sai da ya gama jan ƙafar tana mishi kuka ya shafa mata wani tube mai zafi da ta ji kamar ta saki fitsari.
Ya tashi ya ɗauko mata riga mara nauyi ya ba ta ta sanya ya ba ta magani ta haɗiya sai ta kwanta lamo tana sauraron raɗaɗin da ƙafar ke yi mata gadon ta ga ya hau ya kwanta a bayanta barci ta samu ya ɗauke ta wanda ba ta farka ba sai asuba lokacin har ya fita sallar Asuba, sai dai ta taka ƙafa ta ce ba ta san wannan ba, idon ƙafar ya kumbura suntum, ta sauka ta fara rarrafe sai ga shi ya shigo cak ya ɗaga ta sai Toilet ya ajiye ta ya juya sai ya ja mata ƙofa.
Ta gama abin da za ta yi tana tunanin mafita sai ta ji daga jikin ƙofa yana faɗin "Kin gama? Ta ce "I." Ya shigo ya kuma surar ta sai kan fray mat ya zaunar da ita, a zaunen ta yi sallah tana gama addu'ointa ta cusa kanta cikin gwiwoyinta barci ta ji tana ji nan ma sai ji ta yi an yi sama da ita sai kan gado ya ajiye ta ta gyara ta kwanta ya shafa mata magani sai da ya gama raɗaɗinsa ta shiga barci barci sosai ta yi sai goma ta farka Abdurrashid da ke kwance bayanta bai iya barcin ba, sai juye juye duk da yau ɗin weekend ne a ranakun yake samu ya yi barcin safe tana tashi zaune ya ce "Bari in kai ki ki yi wanka." Ta ɗaga mishi kai sai da ya ajiye ta ya ba ta wuri sai da ta gama wankan ta rasa yadda za ta taka ta ɗauko tawul sai kawai ta yanke ta mayar da rigar da ta cire, ta sanya kenan ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ya ƙara faɗawa wani yanayi, bayan rigar kasantuwar ta ba mai kauri ba lemar jikinta ta sa ta manne mata sai ta fidda komai ya dai fito da ita ya zaunar da ita ta yi kwalliya riga ya ciro mata kalarta blue black an matse ta daga ƙirji sai aka ɗan buɗa ta daga ƙasa tsawonta iya gwiwa miƙe ƙafar ta yi ta kwantar da kanta jikin gadon har nan ya kawo mata abin kari ta karya kiran da aka yi mishi a waya ya sa ta bar kallon TV da take yi ta maida hankalinta kan abin da yake cewa a yadda ta fahimta wata daga cikin Aunty nan sa ce take tambayar abin da ya hana su fitowa har yanzu