Showing 30001 words to 33000 words out of 84568 words

Chapter 11 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

sha mamakin sasan su Laila, an buge ginin ƙasa an mayar da shi bulo da bulo, ta samu Amir ya tashi bacci, Laila ta miƙo mata shi anan sasan ta samu ruwan zafi ta yi masa wanka, sai da ta gama shirya shi ta tafi da shi sasan su, ba ta yi mamakin daga wayewar gari har Innarta ta gyara wurin kamar ba mai yara ba.
Ta tambayi ƙannenta ta ce sun wuce Islamiya, Babanta yana zaune yana shan koko da ƙosai, kwanon ya turo mata bayan ta gaishe shi "Maza ki sha." Shan ta yi tana ba Amir suna hirar su, har sai da babanta ya fita kasuwa sai ta bar sashen.
Wanka ta koma wurin Innawuro ta yi ta so zuwa inda su Amina ke zaman sitting daga ita ce kusan sa'ar ta, to amma saboda Walida dole ta nufi inda su Aina suke.
Daga can suka wuce wurin su Amina, a can suka wuni.




An fara shagalin biki sosai ana gobe durin aure da safe misalin ƙarfe goma Hamida ta shiga wurin Aliyu don tun ran da ta zo ba ta ƙara shiga ba suna tare da Walida da ta saba da kowa ana ta hidima da ita.
Sun shiga zai fita ya ce "To mu je." ya wuce suka bi shi a baya har waje inda Walida ke raɗa mata "Wannan hand some din fa waye? Murmushi ta yi tana duban sa tuna uban kishin Asabe a kansa, amma ba ta ga laifinta ba don ya Aliyun ne ya haɗe kyakkyawan bafulatani ne ga jiki ya ajiye na shaidar hutu da yake ciki.
Za ta yi magana ya juyo sai ta yi shiru, sun isa inda ya ajiye motarsa bai shiga ba jingina ya yi jikinta yana tambayar Hamida har da ita za a Abujar? Ta ce "Ka ji ya Aliyu, in ban je gidan Aunty Aina ba wa zai je? Ya ce "Haka ne."
"Aunty Asabe fa za ta? Ya girgiza kai "Ba inda za ta." Wata haɗaɗɗiyar mota da ta tsaya Hamida da Walida suka bi da kallo, ta daɗe tsaye ba wanda ya fito har suka cigaba da hirar su, Hamida ta shagala tana dariya har gyalenta da ta rufe kanta saboda ba ta sa dankwali ba yana zamewa ta kamo shi sai ta ga an buɗe motar, ganin wanda ya fito ya sa ta gintse dariyarta. Cikin mamaki suka dubi juna ita da Walida Abdurrashid ne, tana jin kunyar Aliyu ba za ta iya ce mishi wurin ta Abdurrashid ya zo ba, sai Walida da da ma ke neman shiga wurin Aliyu ta ce "Ya Aliyu ga fa saurayin Hamida ya zo." Ɗan murmushi ya yi "Kauce Hamida." ta matsa daga jikin kofar1)j motar ya bude ya faɗa ciki yana faɗin "Ki gaida surukin nawa."
Hannun juna suka kama zuwa inda Abdurrashid yake da sallama suka karasa gabansa bai amsa ba illa saman lebensa da yake cijewa. Suka haɗa baki wurin gaishe shi Hamida ta ce "Ka zo mu shiga ciki." Ya girgiza kai "Waye wanda kuke tare? "Yayana ne." "Yayanki? Ya tambaya cikin ɗaure fuska "Yaya Aliyu ne, Baban shi Yayan babana ne, maman shi kuma ƙanwar kakata ce." Hamida ta yi mishi wannan bayanin don kare kanta daga fushin da ta ga Abdurrashid ya shiga.
Ba ta san ambaton sunan Aliyu ƙara tunzura shi ya yi ba don ba zai manta wanda ta ambata a wayar da ta yi ba tana farin ciki, yau kuma ya gan su tare "Ok yi min iso wurin Malam." Ta juya Walida ta bi bgidan a ta ssmu Malam din na haramar fita, Innawuro ta gaya mawa ita kuma ta gaya wa Malam ɗin ya ce Walida ta koma ta yo mishi jagora.
Walidar ta juya cikin mugun saƙe saƙe tunda ta zo ta ga gidan su Hamida ta ji ta ƙara raina masu kuma ɗan Shehu Bello ne ke son yar cikin gidan, wani ƙyashi ta ji tana wa Hamida tare da addu'ar watsewar abin.
Ta samu Abdurrashid ta faɗa mishi saƙon ya bi ta a baya suka shiga gidan
har ɗakin Malam.
Sosai Malam ya yi masa kwarjini don cikar kamalar da yake da ita ya gaida Malam cikin girmamawa da nuna surukuta ya kuma gabatar da kanshi a mai son Hamida.
Malam ya ji dadi sosai, ya ce Idan Allah ya kaimu gobe mahaifinsa zai zo nema masa auren ta. Sun daɗe suna hira a cikin hirar Malam yake ba shi labarin mahaifin Hamida ƙane ne a wurinsa, mahaifiyarta kuma mahaifiyarta yaya ce wurin mai ɗakinsa mai ɗakinsa ta dauko mahaifiyar Hamida tun tana ƙarama ta riƙe ta, da ta girma suka aurar da ita ga ƙanensa suka haifi Hamida da ƙannenta.
Natsuwar da Abdurrashid ya samu da Malam ya sa shi ma ya ba shi labarin Course din da zai tafi, da kuma rashin son da yake ya bar Hamida a Kano, ya roƙi Malam da ya dawo da Hamida gida sai a nema mata wata makarantar anan, kafin ya dawo."
Malam dai jinjinawa ya yi ya ce shekaru huɗu nan gaba Hamida ta ƙara su ba a kauda ita ba? Ya ce shi dai a taimaka mishi duk da hankalin shi ba kwance yake ba da barin ta a Daura idan ya tuna zai bar Hamida da dan'uwan nan nata.
Malam saboda yadda ya ji yaron ya kwanta mishi ya ce zai duba. Abdurrashid ya yi ta godiya. Innawuro ta shigo suka gaisa, ta ajiye mishi fura da ta dama mishi, bayan ta fita kuma ta sa aka kira mata Asabe ta ce ta yi abinci mai kyau suna da baƙo sai dai zuwa sha biyu ya yi musu sallama bayan Gwoggo Indo da ta ji labarin zuwan shi wurin Walida ta zo sun gaisa, sai dai bai yarda ya tafi ba ya ce a kai shi ya gaishe da mahaifiyar Hamida, Walida Innawuro ta aika ta gaya mata mai son Hamida zai shigo ya gaishe ta.
Walidar ta raka shi ya dubi sasan nasu na ƙasa ne da aka kewaye da kwano, ƙasan wurin a share yake tas, sai gefe guda randunan ruwa, da sallama suka shiga dakin kujera ƙwaya ɗaya ce rak sai tabarma da aka shimfida ɗakin sai ƙamshin turaren tsinke da aka kunna, akan tabarmar ya zauna daga uwar ɗakanta ta ɗan leƙo ta sha lulluɓi ban da aiken daga Innawuro yake da ba abin da zai sa ta yarda a turo mata mai son Hamida ya gaishe ta ta amsa ya ajiye kuɗi masu kauri a saman tabarmar suka fito haka Malam da Innawuro ma ajiye musu, a mazan gidan Baban Laila ne kadai bai fita ba, don akwai aikin da ba a ƙarasa ba a sashin nasu wanda Laila ce ta sa a ka gyara part din iyayen nata.
Ya gaishe shi shi ma ya yi mishi alheri.




*Book one na Shirin Allah free ne za a biya book 2 500 book one zai ƙare iya page 18 ne*


*A sanya kuɗin karatu a 3195398684 Maryam nasir first bank*
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH...




Daga


Marubuciyar


WA GARI YA WAYA


CANJIN BA ZATA


RANAR NAKA


HATTARA


MARYAM LITEE




No.14






Ƙarfe sha ɗaya na safe aka wuce da Aina zuwa gidan mijinta da ke Abuja.
Bayan wucewar su kuma su Malam suka zauna shawara kan yadda za a yi da Hamida, Gwoggo Indo ta ce a ba ta ita na sati biyu ta tafi da ita Kano ta gyara ta, sai ta dawo da ita Daura inda yan'uwan Abdurrashid za su zo bikon ta.
Malam ya ce sati biyu ya yi yawa, kwata kwata saura wata guda tafiyar mijinta.
Ta ce to kwana goma
ya ce ba laifi. Don haka ana tashi taron Gwoggo ta soma harhaɗa nasu ya nasu zuwa Azahar suka bar garin don shatar mota ta dauka.


Suna isa ko gama hutawa ba su yi ba Gwoggo Indo ta fara haɗa abubuwan da Hamida ta ga tana ba Aina kuma ta san tana sai da su "Ai yanzu dole in miki shirin da duk san da ya san ki zai kiyaye, daga nan mu za mu fara juya shi, wannan biyayyar da kika ga ina mishi shi zai dawo yana min.
Kunya ce ta lulluɓe Hamida jin zancen ta ko da take da shekaru sha biyar sarai ta fahimci inda zancen Gwoggo ya dosa don ba abin da ba ta sani ba a karance karancen da take ko da ta miƙo mata cup ƙin karba ta yi sai da Gwoggon ta yi da gaske ta sha kaɗan dole aka sa a fridge sai fada Gwoggo take ta ce ke da alama wannan shegen rashin son maganin naki ba za a yi abin arziƙi da ke ba. Tana cikin faɗan Nurse Saratu ta shigo ta tambayi abin da ya faru Gwoggo ta gaya mata abin da Hamida take na ƙin shan maganin gyara, ta ce sam ba ta kyauta ba ta dubi Hamida "Tashi mu je gidana ni in ba ki, Haj Indo ɗauko maganin." Gwoggo ta ɗauko ta ba ta Hamida har da ƙwalla.
Kafin zuwan Hamida ba wata hulɗa tsakanin Gwoggo da Nurse Saratu illa ta idan an haɗu a yi ina kwana ina gajiya, amma tun zuwan Hamida take son ta bunu-bunu ta sayi abu ta aiko ta ce a ba Hamida hakan ya janyo shiri sosai tsakanin ta da Gwoggon.
Tana gaba Hamida na bayanta har suka shiga gidan, an yi sa'a yaranta ba su nan suna gidan kakannin su tun sallah sai hutu ya ƙare za su dawo.
Ajiye cup din ta yi ta shiga kitchen ɗinta sai ga ta ɗauke da wani cup din ta miƙa wa Hamida "Sha wannan." Hamida ta mika hannu ta karɓa don girman matar da take gani ta kai bakinta, nan da nan ta shanye saboda maganin ba ɗaci ba komai sai lemon tsami da aka saka wanda ta ji ya yi mata daɗi.
"Maganin sanyi ne Hamida." Ta faɗi tana ƙoƙarin zama "Shi ya kamata mu maida hankalin ba yaranmu ya yin da muka zo aurar da su. Ba mu yi ta ɗura musu magungunan ƙara ni'ima ba, ba yanzu suke da buƙatar maganin ƙara ni'ima ba sai sun haihu tukuna, idan za mu aurar da ƴaƴanmu ba mu bar su sun je ma mazajen su da ainahin ni'imar da Allah ya yi musu ba mun ƙara musu da wani daɗi na musamman wanda idan ya sake su zai yi wahala su gamsar da mazajen su da ainahin ni'imar su.
Ki yi ta zuwa Hamida ina ba ki magungunan sanyi kin ji? Hamida ta ɗaga mata kai.
Tashi ta yi ta koma kitchen din ta fito da wani haɗin maganin ta ba hamida shi kam babu daɗi amma da yake ta iya dabara da madara ta haɗa tana sha ta ba ta madara ta ce sai kuma gobe. Da haka Hamida ta tashi ta tafi gida, Gwoggo ta yi ma Saratu waya ta ce ta sha ta ce tas ma kuwa, ta ce to ita za ta dinga aiko mawa tana ba ta.


Ranar da suka yi kwana biyu da dawowa hankalin Gwoggo ya soma tashi tana ta magana Abdurrashid ba kira ba zuwa tunda aka ɗaura aure, wane irin abu ne haka? Hamida dai da ta fito wanka tana kwalliya tana jin ta ƙaramar riga ta sanya don uban zafin da ake zambaɗawa baƙa da dogon skirt komai ba ta sanya a kanta ba ta fito falo ta kwanta bisa dogon cushion da wani littafi da ta samo a gidan Saratu mai suna RANAR NAKA na marubuciya Maryam Ibrahim litee hakika ya yi mata daɗi.


A daidai wannan lokaci da Gwoggo ke sababinta Abdurrashid bai daɗe da isowa daga birnin Ikko ba ya samu ƙannen mahaifiyarsa su uku sun iso kowacce daga inda take aure bisa jagorancin mahaifiyarsu Daada don taran ɗan nasu su yi masa murnar aure.
Haj Binta da suke kira Momi Binta ita ke bi wa mahaifiyarsa a Abuja take aure wani ƙusan gwamnati take aure ita ma kuma babba ce a Jami'ar Abuja da ke gwagwalada, yaranta hudu duka mata.
Sai mai bi mata Aunty Safiya ita kuma sarkin Katsina na lokacin take aure yaranta biyar mata uku maza biyu.
Sai Aunty Zainab a Yola take kusa da mahaifiyarsu ita ma dai mijinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne yaranta uku biyu mata sune manya sai karamin namiji.
Aunty Karima ce autar su da Allah bai ba haihuwa ba.
Wanka kawai ya yi ya fito wurin su yana ƙoƙarin gaishe su Daada ta ce "Ya na ga kana wani ɗaure ɗaure miskili ka fi mahaukaci ban haushi. Har ranar auren naka ma ba za ka yi fara'a ba? Ƙara shan mur ya yi ya zauna yana gaida iyayen nasa Daada ta ce "Ka ji yadda mahaifin naka ya yanke ko? Za a kawo maka amaryar taka bayan sati biyu da ɗaura aure, za a ajiye ta a sasanka ya ce yanzu zai fara maka ginin gidanka wannan filin na jikin gidan nan. Jin ya ƙi magana har ta yi shiru sai ta ce "Wai meye damuwar ne? Kai fa ka kawo yarinyar nan, an kuma ɗaura maka aure da ita ka kasa farin ciki." ya ce "Ko da na kawo ta ni na ce a ɗaura min aure yanzu? Just 15 years ne fa da yarinyar Aunty." Ya ƙare maganar yana duban Aunty Safiya wadda duk a cikin su ta fi tsananin kamanni da mahaifiyarsa don haka sai ya yi ta ganin ta kamar mahaifiyar tasa, ko gidajen su kafin ya je na kowa ya je na ta.
"Haƙuri za ka yi ɗa na daga ka ga yadda abin ya zo." Ta ce mishi cikin sigar rarrashi .
Amma Daada ɗaga kai ta yi "To sai me, ko shekarunta sha biyu ba ta isa aure ba? "To idan kun ɗauko ta ku kawo ta part ɗin Aunty Karima." ya ce ma Daada
"Nakan dai za mu kawo ta sai in ga tsiya." Miƙewa ya yi ya ce musu zai je ya dawo, Momi Binta da ta kafe shi da ido cikin medicated glass dinta, ta dubi Aunty Zainab "Part din nasa za mu kai ta Zainab mu ga idan zai koro ta."
Dariya sauran suka yi "Daada ta ce "Za ta yi maganinsa ne, ba dai mace take ba yake raina ta?




Fitar Abdurrashid gidan Gwoggo Indo ya nufa, yau bai tsaya kiran waya ba kai tsaye ya shiga gidan da sallama.
Gwoggon ce ta amsa sallamar don daga ita sai Hamida ne a gidan suna zaune a falo Hamida na kwance tana karatunta, Gwoggo na gyara ƙumbarta.
Gwoggo ta yi mishi iznin shigowa ya shiga Hamida dai ko motsi ba ta yi ba har ya zauna ya gaida Gwoggo, sannan ta ce "Ina wuni? Ya share ta kamar bai ji ba, Gwoggo ta miƙe ta yi waje Hamida ta tashi, zaune amma ta gaza ɗaga idonta don kunyar shi da take ji wai
shi ɗin yanzu mijinta ne.
A hankali ta miƙe zuwa kitchen ta ɗauko ruwa ya bi ta da kallo wai wannan yar yarinyar ce matarsa, ta kawo ruwan ta koma ta zauna ya shiga tambayar ta game da karatunta za a koma meye da meye take buƙata? Ta faɗa mishi, kiran da Gwoggo ta ƙwala mata ya sa ta ficewa daga falon ta isa tana fadin "Ga ni Gwogg."
"Ki yi mishi maganar kuɗaɗen gyaran amarya da na ƙawaye, kina dai ganin kudin da a ka ba Aina.
Ta ɗaga mata kai ta ce shi kenan ta je Hamida ta koma jiki a mace sai dai ba ta san wane baki za ta buɗe ta yi masa maganar kuɗi ba.
Ganin ya share ta sharewar ma har ta fi ta kullum ya sa ta janyo littafinta ta ci gaba da karatu. Jin motsin keys ɗinsa ya sa ta ɗaga kai sai ta ga ya miƙe ya fara tafiya ita ma ta miƙe ta bi bayansa har inda ya saba ajiye mota buɗewa ya yi ya ɗauko wani kwali sai ya miƙa mata ta amsa da godiya sai ta koma ciki jikin Gwoggo har rawa yake wurin karɓar kwalin ta buɗe, waya ce dalleliya samfurin Samsung. Gwoggo ta ce "Ita kenan ya ba ki ina kuɗin? Ta girgiza kai "Bai bani ba." Sababi sosai Gwoggo ta hau yi har Allah ya gajishe ta ta yi shiru.




Abdurrashid zaune falon wani abokinsa ko ma a ce amininsa mai suna Usman a washegarin ranar da ya dawo Lagos fita za su yi amma Usman ɗin ya ishe shi da mitar tun aurensa wata uku kenan Abdurrashid bai zo ya ga amaryarsa ba.
Shi ne yau ya zo wayarsa yake taɓawa amma yana hankalce da sakarcin da amaryar ta Usman ke ta zubawa angon nata, shi kuma yana aikin tarairayarta.
Abin ya ishi Abdurrashid ya dubi agogonsa sai ya miƙe tsaye "Haba Malam ka zo mu tafi."
Usman ɗin ya miƙe amaryar ta sha gabansa wai ba zai fita ya bar ta ba. Ya riƙe ta a jikinsa yana faman rarrashi Abdurrashid dai ficewa ya yi ya rabu da shi ya dan jima a motar sai horn yake danna masa ya fito ya same shi yana shiga motar Abdurrashid ya tashe ta, sai da suka yi nisa ya dube shi ta wutsiyar ido "Mace ta yi ta maka sangarta kana faman biye mata." Cikakken murmushi ya yi "To ai shi ne son." Abdurrashid ya jinjina kai "Sai ku yi ta fama ai." Usman zai yi magana ya ga Abdurrashid ya tsaida motar ya ciro wayarsa Gwoggo Indo ya kira ya ce ta turo mishi Hamida ƙofar gida. Sai duban ƙofar gidan Usman din ke yi har Hamida ta fito Material ne jikinta ɗinkin doguwar riga sai ɗan gyale da ta yane kanta.
Abdurrashid bai buɗe mota ba ta tsaya saitin inda yake ta gaishe shi kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login