Showing 9001 words to 12000 words out of 84568 words

Chapter 4 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

ta shiga zubawa aka murɗa ƙofar sai a ka shigo "Likita bokan turai ba dai ba ka je Office ba? Ahmad ya fadi yana mikewa tsaye "Haba dai ko kuma na dawo ba? Wanda ya shigo ya bada amsa Hamida ta baro inda take don ta gama zubawa idan su ya shiga na juna da wanda ya shigo sai ta ji wani iri don wanda ya cece ta ne daga hannun Alh Danlami yau ma Allah ya kuma haɗa su, shi kuma a ransa cewa ya yi "Ita din ce dai kenan? yau ma na kuma ganinta a Office din wani, wai ina iyayenta suke take famar gantali a ma'aikatan nan? Don ya taho ya ga wata kamar ita sai ya biyo bayanta a hankali har ya ga ta shiga Office din.
"Na tafi Baban Amir." ta faɗi a hankali tana barin Office din kamar ana tunkuɗa ta.
Zauna mana." Ahmad ya ce yana nuna masa wurin zama ba sai na zauna ba a kan hanya nake. Ya mika masa hannu suka yi musabaha ya juya Ahmad ya bi bayansa don yi mishi rakiya. Sai da suka isa inda ya adana motarsa ya shiga ya bar wurin yana tafe kansa na chargy me ya sa duk san da zai ga yarinyar nan sai tare da namiji? Wadanne irin iyaye gare ta da basu gudun ta lalace? Ya daki sitiyari! Mahaukacin horn din da yake dannawa ya sa masu kula da gate din ɗebowa a guje suka wangale gate din, a wuce a guje abin da ya basu mamaki suka bi motar da kallo, fitowa ya yi bai ko rufe motar da kyau ba ya yi ciki.




Wani ƙasaitaccen falo ya fada ba kowa ciki ya fada kan sopa ya dafe kansa yarinyar kawai ke masa yawo a ido. A ranar farko da ya soma ganinta ya gan ta ne a Office ana ƙokarin keta mutuncinta. Rana ta biyu ya ga ta bi bayan wani matashi, rana ta uku yau kenan ya gan ta Office din Ahmad da alama kuma ta saba da shi.
Hannu ya sa ya daki kujerar da yake tuna yadda yarinyar ta hana mishi sakat yarinya ƙarama da iyayenta suka sake ta cikin company nan da sunan talla, alhali cike take da bunsurai maza da ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da ƙarfin aljihu sun ɓata ta.
Idan ya zo nan a tunanin sai ya ce to meye nawa a ciki? Meye haɗina da ita? Tunda ya gan ta a Restaurant yake zagaya wurin ko zai ƙara ganin ta, to ko mai kama da ita bai sake gani ba, tuna ko tafiya ta yi ya sa ya daina ganin ta ya sa ya mike zumbur! Ya suri key dinsa bari ya koma Restaurant din ko zai gan ta. Sai idonsa ya shiga cikin na Auntynsa tana tsaye ta rungume hannuwa "Kansa ya shafa "Aunty. Duk da bai fi shekaru biyu ta ba shi ba yana girmamata yana mata kallon uwar da ba shi da kamarta tunda ya mallaki hankalinsa. "Tunanin me kake? Ta jeho mishi tambaya Ba komai Aunty." "To ina kuma za ka? Ko abinci ba ka ci ba? "Mantuwa na yi yanzu zan dawo." Ta bi shi da kallo har ya fice.


Da shiga motarsa Restaurant din ya nufa, har masu saida abincin suka tashi ba ta ba labarinta. To ko tambayar su zai yi? Idan kuma ya tambaya ya ce me ye sunanta? Cikin wani zafi da yake ji a ransa ya ja motar ya koma gida.








Ahmad bai shigo gidan ba sai Yamma lis. Tana gama abincin ta shirya musu kamar yadda ta saba sai ta koma daki.
Sai dai bayan Isha'i har ta kwanta ta fara lumshe ido Laila ta shigo ta ce Baban Amir ya ce ta fito. Ta fitan sai da ta kuma gaishe shi yana cewa "Ke ba ki gajiya da zaman daki ne? Zauna a yi hira da ke." ta zauna a ɗarare, Amir ya yi barci ballantana ta samu abokin hira, tana zaune tana wasa da yan yatsunta ya ce me ya sa take zaune kawai ba ta karatu? An sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ta ce "Gwoggo ta ce in saurare ta, za ta sanya ni." ya ce "Shekarunki nawa? Ta ce "Sha hudu ya kaɗa kai "Me zai hana ki yi zamanki nan in sanya ki boko da Islamiya? Ta dan narke fuska duk da ta gaji da zaman gidan shiru ta ce "Ka tambayi Gwoggo." "Zan tambaye ta, amma gobe zan kai ki Islamiya ta cikin Estate din nan, zuwa Monday sai in kai ki boko." Hamida ta ce "Na gode." Laila da ke sauraren su ko tari ba ta yi ba.


Kamar yadda ya ce washegarin ya kai ta ya yi mata Register suka ba shi unifoam da littattafai, suka dawo gida Hamida na ta murna. Da safe kafin ya fita ya ce mata yana fita zai bayar a sawo mata jaka da za ta rika sanya littattafan makarantar. Ta ce ta gode.




Sai ƙarfe uku aka kawo mata jakar tana yin sallar La'asar ta sanya unifoam sun ɗan yi mata yawa amma da yake hijab din wadatacce ne tana sanya shi shi kenan, ta yi wa Laila sallama ta fita gidan Amir na kuka sai ya bi ta.
Aji hudu suka sanya ta a bisa gwajin da suka yi mata, amma yan ajin sun kusa shiga aji biyar.
Ana tashi sauri ta yi ta koma gida saboda girki sai dai tana tura ƙofar falon Gwoggo ta gani zaune, jin suna gaisawa da Laila ta gane zuwanta kenan. Ta kalli Hamida baki buɗe "Ashe har makaranta suka sanya ki? Ba ku da niyyar bani ɗiyata ko Laila, to yau ƙafata ƙafarta za mu koma gida." Laila ta ba ta hakuri ta ce ta bar mata Hamida cikin satin nan za a kawo mata mai aiki.
Ta ce sam ki yi aikin gidanki, zuwa sati daya dai ba mutuwa za ki yi ba.
Laila ta ce "Baban Amir ba ya nan Gwoggo, idan ya dawo ba zai ji dadi ba ya samu ta tafi ba sanin sa.
Ta buntsura baki "Sai fa ki yi Laila ta karuwa da ta ji mai wa'azi, ta ce ka yi kanka a ke ji, ni sinima za ni."
Maza Hamida shiga ki tattaro abin da kika san naki ne ki zo mu je gida."
Hamidar ta mike ta shiga ta hado ya na ta ya na ta ta fito. Gwoggo Indo ta gyara zaman mayafinta "Mu je, ke kuma Laila abin da kuka yi niyyar ba ta idan mijinki ya dawo ku kawo mata."
Da haka suka bar gidan Hamida na rike da kayanta.




Suna isa da Aina suka fara karo da ke tsaye da wani tana zance.
Ta baro shi ta zo ta rungume Hamida suka shiga ciki, Hamida ta ce "Ko ki zo ki duba ni Aunty Aina." ta ce "Yi hakuri yar ƙanwata, zuwan ne dai ban yi ba amma kina raina kamar kudin haya."
Suka yi dariya "Kin yi kumatu kin ƙara haske gidan Laila da daɗi kenan? Wata dariyar suka ƙara.






Washegari ta kama Alhamis da safe bayan sun gama ayyukan da za su yi har an wuce da abincin, sai suka yi wanka jallabiya ta sa mai yankakken hannu, ta yi rolling da gyalen rigar kamar yadda Aina ta koyar da ita. Takalmi flat ta sanya. Su ukun suka tafi kamar yadda suka saba, ƙawarta Rabi an mayar da ita garin su.


Karfe daya da rabi lokacin wurin cin abincin ya ɗinke da jama'a, ana ta sallamar su wani matashi ya shigo, kallo daya Hamida ta yi masa ta kawar da kanta wanda ya cece ta ne, sai ta ga ilahirin mutanen wurin suna kawo masa gaisuwa, daidai da teburin da ya nufa don ya zauna wanda ke zaune wurin tashi ya yi da sauri yana kakkaɓe masa wurin.
Ta juya kawai don ci gaba da aikinta, wadda ke ba mutanen kusa da shi abinci ta matso "Yallabai me za a kawo? "Kira min waccan yarinyar." ya fadi yana nuna mata Hamida, ta je ta isar da sakon.
Ko da Hamida ta zo nesa kadan da shi ta tsaya, duk da daɗin da ya ji na sake ganinta, gefe guda yana jin wani irin ba dadi da ya gan ta tana sayar da abinci, yarinya kamar wannan da ya kamata yanzu a ce tana makaranta. "Me za a kawo maka? Ta tambaye shi ganin ya bar ta tsaye bai amsa ba don wani sabon tunani da ya shige shi game da ita. Tsayuwa ta cigaba da yi har dai ta gane wannan mutumin ba shi da niyyar kula ta, ga jama'a na jira sai ta juya ta yi tafiyarta.


Ya dawo daga duniyar da ya lula ya ɗago iso sai ya ga wayam waige waige ya shiga yi sai dai har ya gaji da ware ido ba ta ba alamarta, tashi ya yi ya bar wurin cikin tunani.



Ranar Asabar babu aiki don haka ba sa yin abinci sai ga baƙuncin Alh Mustafa sun samu ya zo wurin Hamida. Fada Gwoggo Indo ta yi ta surfawa me Hamida za ta ci da wannan mutumin? Ban da kuma Malam da ya yi mata waya ya sanar mata zai zo ba, da ko ganin Hamida ba ta bari ya yi ba, kora shi za ta yi. Ba ta ko ce ya shigo ciki ba albarkacin tafiyar nesan da ya shawo ta ce Hamida ta fita ta same shi bayan an shanya shi na kusan awa daya.
Ta sanya hijab ta fita tana tura baki, shi kuma fara'a ya ɓalle da ita yana ganin Hamida wadda bai iya hana kansa yin ta matukar zai dora idonsa kan yarinyar.
A darare ta gaishe shi yana ta jan ta da labari.


Abdurrashid wanda ya fito daga gidansu zai fice daga Estate din, idonsa ya gano masa Hamida yarinyar da ya tambayi daya daga cikin masu sayar da abincin ta ce mishi sunanta Hamida, wani mamaki ya kama shi ganin ta tare da wani Wai su waye iyayen yarinyar nan? Ya ƙara tambayar kansa a karo na barkatai.
Ajiyar zuciya ya fidda ya tsaida motar ya jinginajikinsa a bayan kujerar yana cigaba da kallonsu, ransa na daɗa ɓaci.
Mintuna sun yi arba'in suka dauka mutumin ya shiga motarsa ita kuma ta shiga gida. Wani lokacin ya dauka yana shawarar ya yi tafiyarsa ko ma mai zai faru da rayuwarta ba matsalarsa ba ce, ko kuma mai cewa ya yi sallama yau dai ya ga su waye iyayenta? Jikinsa a mace ya yi wa motar key ya karasa kofar gidan Gwoggo indo sai da ya gyara parking sai ya fito






















Maryam litee
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH..... RAYUWA






No.4




DAGA




MARUBUCIYAR


*CANJIN BA ZATA*
*WA GARI YA WAYA*
*RANAR NAKA*
*HATTARA*


And now


SHIRIN ALLAH... Rayuwa






MARYAM IBRAHIM LITEE










Jin ya sake ta yasa ta bude ido tana kallon kofar. Wani matashin saurayi ne tsaye ya harɗe hannayensa yana duban su waige -wangen inda za ta ga gyalenta ta kama yi takalmanta ta fara gani ta wawuro su kafin ta ga gyalen ta hada da shi ta nufo kofa matashin ya ba ta hanya duk abin nan kuma kuka take tana fita ya mara mata baya yana duban yadda take tafiya tana kuka sai da ta yi nisa ta tsaya ta sanya takalmi da gyalen tsirarun ma'aikatan da ke bin ta da kallo ba ta ko san suna yi ba.
Maimakon shago gida ta wuce ƙwanƙwasa get din ta yi ta yi duk da ba ta da yaƙinin akwai mutum, sai kuma ta ji takun tafiya an zo an buɗe , Malam Buhari ne wanda shigowar sa kenan daga wurin aiki, ganin ta a birkice yasa ya tambaye ta abin da ya same ta ta ce ba komai, ciki ta wuce ta haye saman katifarsu tana kuka tana kullawa da kwancewa yadda za ta koma Daura.
Muryar Gwoggo Indo da ta ji ba ta sanya ta ɗaga kai ba har ta dafa kafaɗarta "Me zai sanya ki yi mini haka Hamida? Me ya faru kika taho ban sani ba? Shiru ba ta ba da amsa ba tsawa ta kwatsa mata "Tashi zaune mu yi magana! Ba shiri ta tashi don ko banza ba ta taɓa yi mata tsawar ba "Na ce "Me ya same ki? Ta fada cikin zare ido cikin inda inda ta bata labarin sama sama. Wayarta da ke hannunta ta shiga latsawa "Sannu tsohon banza mai kokarin ɓata ƴaƴan jama'a." abin da ta fara cewa kenan tana huci, da alama shi ma tsiyar ya tarbe ta da ita. "E ko da nake kwaɗayayya ban zama fasiƙa ba, ka gode wa Allah da ya ce ce ka ba ka ɓata mini yarinya ba, da Kano sai ta yi maka kaɗan."
A takaice dai tsiya suka kwasa ta sauke wayar tana ci gaba da masifa, bala'inta ya shigo da Malam Buhari yana tambayar abin da ya faru ba ta saurara ba da ƙyar ya lallashe ta suka bar falon.





Tun daga ranar Hamida ba ta kuma yarda ta je kai abinci kowanne Office ba.
Kuma ta rage walwala, abin da ya damu Gwoggo Indo kenan ta shiga tambayar ta abin da yake damun ta ta ce ba komai. Ranar da ta rutsa ta sai ta faɗi mata damuwar ta sai ta samu kanta da cewa ita makaranta take so a sanya ta. Lallaɓa ta ta yi ta ce akwai shirin da take yi, lokaci na yi za ta kaita makaranta, makarantar ma ba ta kowa da kowa ba ta yayan masu fada aji za ta kaita tana sane ba mantawa ta yi ba.
Dadi ya kama Hamida hakan ya sa ta maido da walwalarta ko don ta faranta ran Gwoggonta ta da kullun take tattalin farin cikin su ita da Aina, duk da kasancewarta mace me zafi su kam ba ta yi musu.






Sati uku da afkuwar abun Hamida na zaune a shagon su na provision wani matashi ya shigo ya ce ta ba shi tissue gudar dubu daya ya miko mata ta ba shi ta juya dauko masa canji, juyowarta ya fice, bin bayansa ta yi da canjin cikin sauri ta hango shi yana tafiya kamar zai kifa ita ma ta daga kafa ta bi bayansa da kyar ta kamo shi sai da ya shiga wata kwana ta ba shi sai ta juyo daidai wata mota da ta wuce a yayin tafiyarta ta gan shi tsaye gabanta ya buga tuna a inda ya fara ganin ta da abin da ya faru a ranar.
Ya za a yi ta manta da mutumin da ya tseratar da ita daga shaiɗani Alh Ɗanlami? Wani irin kallo yake jefa mata da ya sanya ƴan hanjin cikinta hautsinawa, don yadda ya yi mugun ɗaure fuska da sauri ta wuce shi kamar ana hankaɗata ta shige shago.


A ranar kuma da daddare sai ga Laila da mijinta wai sun zo roƙon Gwoggo ta basu Hamida mai aikinta ta koma garinsu kafin ta samu wata.
Da ƙyar Gwoggo Indo ta yarda shi ma saboda tana jin nauyin mijin Lailan don yana matukar yi mata alheri.


Sun taho bisa hanya yana ta nuna mamakinsa kan Hamida, wai shi bai taɓa sani tana nan ba don bai ma san ta ba.


Da suka isa Laila ta nuna ma Hamida dakin da za ta zauna sama sama ta gyara dakin ta kwanta.
Da asuba har ta gama abin da take ta fito ba ta ji motsin kowa ba.
Sai karfe goma LailDuk a fito, Hamida ta gaishe ta sai ta tambaye ta ta karya? duk da Hamida take karamar yarinya sai da ta ji mamakin tambayar ita bakuwa ita ake tambaya ta karya.
Ta dai ce a'a kitchen ta wuce ta ce Hamida ta zo ta mike ta bi bayanta, tea ta haɗa sai ta dubi Hamida "Ki duba akwai komai ki dafa abin da kike so, daga yau ma kar ki kara jirana ki shigo ki nemi abin da za ki ci in kin tashi. Hamida ta ce to ta dauki tea dinta ta fice. Ita ma tea din ta haɗa sai ta fito ta sha. Ba ta zauna ba aikin tsaftace wuri ta kama da ta gama ta riƙa jiyo kukan yaron Laila kamar ta share sai ta kasa, ta isa har bedroom dinta, ta shiga da sallama kwance take kan gado riƙe da wayarta yaron na gefenta yana kuka. Daukar shi ta yi tana tambayar me ya same shi? Ta ce "Rigima ce kawai yake ji." Hamida ta juya dauke da shi, ta kai ƙofa ta ji muryarta "Ki shiga kitchen ki duba abinci me sauki ki ba shi." Da "To. Ta amsa.
Indomie ta dafa mishi ya ci sosai daga nan ya kama wasan sa. Ganin ba alamar matar gidan za ta fito don ɗora girkin rana sai ta bi ta dakin ta tambaye ta ce mata ta yi ta je ta dora da ta kara tambayar me za ta dafa ta ce komai ya yi mata ta dafa, ta fito cike da mamaki, ganin akwai komai yasa ta yi niyyar yin fride rise wanda ta koya wurin Aina da take yawan yi musu. Ta yi ta gama ta shirya musu nasu a dinning, duk kuma abin nan Amir yana tare da ita sai da ta ba shi abinci ta ga yana lumshe ido sai ta kwantar da shi. Shigowar maigidan yasa ta tattara ta koma daki.


Sai La'asar ta fito ta tambaye ta abin da, za ta dafa a matsayin abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login