Showing 75001 words to 78000 words out of 84568 words

Chapter 26 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

Faɗa ta yi mishi kan tafiyar dare ta ce maza ya iso Katsina, gobe da safe sai su wuce. Inda Hamida ke zaune ya duba sai ya ajiye wayar a gefensa, ita da ba ta san me aka ce mishi ba har ya canza hanya ba ta ce komai ba.
Ganin sun shiga birnin Katsina ya sa ta mamaki a ranta ta ce da ma Katsina zai tsaya?
Ya shiga masarautar Katsina aka kuma kiran wayarsa, har kuma ya yi parking bai gama wayar ba ya fito cikin motar ya jingina jikinta ya ci-gaba da wayarsa.
Hamida ta fita ta kama ɓangaren Aunty Safiya, tana ta shan gaisuwa daga barorin gidan aka yi mata iso kafin aka zo aka yi mata jagora zuwa wani shiryayyen falo da take hutawa, daga inda take kishingiɗe kan kilishi take ma Hamida murmushi da barka da zuwa,ta zauna gefen ta tana miƙa gaisuwa, aka shiga hidimar kawo mata abin tarar baƙi, Abdurrashid ya shigo apple ɗin da ke gaban Auntyn ya ɗauka sai ya zauna daf da ita sai sannan ta tashi zaune gaisawa suka yi cike da bayyana so da ƙaunar da ke tsakanin su.
Suna nan zaune har aka kira sallar magrib, Aunty suka tashi ita da Hamida maimakon inda take saukar baƙinta bedroom ɗinta ta kai Hamida ta yi sallah, ƙaramar yarinyarta ta shigo ta ce mommynta ta ce ta fito su ci abinci, ta ɗaga mata kai sai ta miƙe da hijab ɗin ta fito wani wuri na musamman da aka shirya don cin abinci ta gano su zaune Aunty Safiya da Abdurrashid, ta isa ta zauna kan tattausar shimfiɗar sai ta ƙara gaida Aunty Safiya.
Kowannen su ya zuba abin da yake so amma Hamida ƙamshin da suke fitarwa ma tayar mata da hankali yake saboda Aunty Safiya ta zauna suka zuba har sun fara ci Abdurrashid dai ganin idon Auntyn ya hana shi mata magana sai Aunty Safiyan ce ta ce "Yaya dai Hamida ki zuba mana."
Ta ce "To." Ta zuba kaɗan sai dai cin ya gagara ta ce "Ko akwai abin da kike so a yi miki?
Da sauri ta ɗaga kai "Idan akwai tuwo ina so Aunty, na dawa ko na Semo."
Take Auntyn ta zargi wani abu wanda take fatar ya tabbata.
Kira ta yi ta sa a tuƙa ma Hamida tuwon Semo, suna kuma gama cin nasu abincin ana kawo tuwon su Auntyn suka koma falo ita kuma ta zauna ta ci tuwonta wanda ta ji daɗin shi, da ta gama ba ta zauna inda Abdurrashid da Auntyn ke hira ba wuce su ta yi ta je ta hau gado ta yi kwanciyar ta ba ɓata lokaci kuma barci ya yi awon gaba da ita.
Sama sama ta ji muryar Auntyn tana cewa "Anya Hamida kwanciya da wannan dogon hijabi."
Ba ta yi magana ba ta gyara kwanciya, kukan wayarta ya tashe ta ta ɗauka ta kai kunne Abdurrashid ne ke faɗa mata ta zo ta same shi cikin muryar barci ta ce ba ta san inda yake ba. Ya ce ta fito za ta gan shi. Ta ce "Haba ga Aunty ya za a yi in fito?
Ya ce "Ba Aunty daga ta bar miki ɗakin, da asuba sai ki dawo." Ta ce ita dai ya yi haƙuri tana jin kunyar Aunty ta gane ta kashe wayar ya sake kira bai shawo kanta ba ƙarshe ya turo mata text ƙyale shi ta yi ta sanya wayar a silent ta tura ta ƙarƙashin pillow ta shiga barcinta.


Da asuba ko da ta farka sallah ta yi karatun Alqur'ani don akwai complete Quran a wayarta, da azkar da yanzu ya fara zame mata jiki. Sai ta koma saman gado ta koma barcinta.


Ƙarfe takwas ta shiga bathroom ta yi wanka ta yi kwalliya wata doguwar riga ta sanya ɗinkinta mai girma ne don haka ya ɓoye cikin da ba ta so a gani, tana fesa turare Aunty Safiya ta shigo ta ɗan ranƙwafar da kai ta soma gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce ta zo su je ta gaida mai martaba, suna dawowa suka samu Abdurrashid ya shigo cikin shiri yake Aunty Safiya ta ce "Duk saurin ka dai ka tsaya ku yi break past."
Kamar jiya ma tare suka yi zaman karyawar cikin ya sa Hamida ba ta iya shan madara sai Lipton ta sha ta ci wani Farfesun kaza.
Suna gamawa Abdurrashid ya ce za su wuce kyautar wasu turaruka Aunty Safiya ta yi wa Hamida.


Sun ɗauki hanya babu mai magana duk da mamakin canjin da ya gani tattare da Hamida na mu'amala da dogon hijab da Safa bai mata magana ba.



Ƙarfe Sha biyu suka shiga Kano. Suna shiga Estate ɗin ta kira Gwoggo Indo ta waya ta ce ta dawo, yana sauraren ta har ta ƙare wayar sai ta dube shi "Ka fara sauke ni wurin Aunty Karima." Jin bai tanka ba ta ce "Don Allah."
Can ɗin ya yi horn aka wangale gate ya cusa hancin motar.
Masu aiki na ta mata barka da zuwa ta isa falon Aunty Karima Abdurrashid masallaci ya wuce ta tambayi Aunty Karima suka ce tana bedroom ɗinta.
Can ɗin ta isa ta yi knocking ta ji muryarta ta ce a shigo ta shiga da sallama kwance ta samu auntyn ta tashi zaune da ƙyar, cikin mamaki Hamida ta ce "Ba ki da lafiya ne Aunty?
Ta janyo tissue ta zubar da yawu sai ta yi murmushi "Ai na kwana biyu."
Hamida ta nuna damuwarta ta yi mata fatan samun sauƙi.
Anan ta yi sallah suka fito falo ana kawo abinci Hamida na buɗewa Aunty Karima ta tashi da sauri tana toshe hanci ta ɗan jima ta dawo Hamida ta yi mata sannu sai ga Abdurrashid ya gaishe da Aunty Karima ya ce Hamida ta zo su tafi, ta miƙe ta yi wa Auntyn sallama da addu'ar samun sauƙi sai ta bi shi a baya, part ɗin Mami da ta ga ya nufa ya sa gabanta bugawa tunawa da Anisa.
Fara'a sosai Mamin ke yi da suka shiga, da suka gaishe ta ba su jima ba ya miƙe sai suka bar part ɗin.


Ba ta yi mamakin ganin falonta fes ba don ta san Abdurrashid na zuwa, a hand bag ɗinta ta ciro keyn ɗakinta sai ta nufi can ya yi ƙura sosai ta fara gyarawa Abdurrashid ya shigo "Ki bari a kira masu aikin Aunty mana su gyara "Ta ce "Zan iya." Ya ce "To zo mana."
Ya juya ta ɗan bi bayansa da kallo sai ta taka ta rufe ƙofar bunner ɗinta ta jona sai ta ɗauko turare ta ɗan turara gabanta, ta shafa wata humrarta sai ta fito.


Tana tura ƙofarsa ta hango shi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa, a bakin gadon ta zauna sai hannunsa ta ji ya janyo ta, yana samun nasarar kai ta gado sai ya ɗora mata nauyinsa "Wayyo numfashina." Hamida ta ce cikin haki, jin nunfashin da take ya sassauta dannetan da ya yi sai ya fara ƙoƙarin raba ta da rigarta, bai sha wahala ba ya cire ta sai bin ta yake da kallo ganin ainahin canjin da jikinta ya samu ba kamar tana da kaya ba, yana zuwa cikinta wani abu ya ji ya buga a ƙirjinsa, hannayensa duka ya sanya kan cikin "Faɗi min da bakinki Hamida, alherin da na daɗe ina roƙon Allah ya ba ni shi na samu kika ɓoye min.
Sai ya sake ta ya sauka gadon ya yi sujjada, ya daɗe kafin ya ɗago ya dawo gadon ya rungume ta tsantsan har sai da ta ƙara cewa numfashina sai ya sassauta mata "Gaya min Hamida tun yaushe ne,wata nawa kenan? Da hannunta ta nuna mishi ya shiga wata na biyar mamaki ya kashe shi yadda aka yi ya kasa ganewa tun tana Abuja. "Me ya sa ba ki kira ni kin faɗa min ba? Ya ce yana kafe ta da ido ta ɓata fuska "Ka kore ni sai in kira ka? Yar dariya ya yi wadda bai faye yin ta ba sai ta ƙure "Korar ki ma na yi? Kunnenki na ja." Ya faɗi yana jan hancinta.
Tambayoyi ya ci-gaba da yi mata kan cikin tana ba shi amsa abin da ya shagaltar da shi bai samu yin abin da yake ta kwaɗayi ya samu su keɓe da matar ta sa ba, sai kiran sallar la'akari suka ji, tilas ya janye ta daga jikinsa ya shiga bathroom ɗauro alwala.
Ita ma ta tashi ta yi ta ta sallar.


Yana fitowa sallah yan'uwan mahaifiyarsa suka soma kiran sa suna tambayar ya Hamida ba wata dai matsala kansa ya ɗaure bai samu amsa ba sai da Daada ta kira shi hamdala take ta yi da Allah ya sa tun tana raye za ta ga wannan rana Karima da matarsa na da juna biyu tana ta addu'ar Allah ya sauke su lafiya.
Abdurrashid da ya yi shiru yana sauraren ta ya ce "Wai Daada wa ya gaya miki Daada? Ta ce "Karima ta kira ni ta ce yanzu mahaifinka ya kira ta ya ce shi ma yanzu ya samu labari a Daura, Karima kuma jiya ta faɗa mata na ta, yana shiga falo Hamida ma wayar take da su mimi suna murna don gabaɗaya labarin cikin ya karaɗe family ɗin su har sai da Abdurrashid ya gaji ya ce "Wayar ta isa ina jiranki." Ya faɗi yana wucewa "Mijina na kira na sai anjima. Ta ce wa hanan da suke waya a lokacin ba ta saurari sharrin da take mata ba ta bi bayansa.
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH...RAYUWA




NO.33




MARYAM LITEE






Da zuwan su ta sallami me nafef ɗin, a hankali ta shiga asibitin sai da ta karɓi babban katin ta samu wuri ta zauna inda sauran mutane ke zaune suna ganin likita.


Abdurrashid ya ɗan jima bai fito cikin motar ba yana duban gidan, ya dai gyara farking sai ya fito kai tsaye ya shiga gidan wanda yanzu kowa ya ja doguwar katanga ba wanda zai san ka shigo sai wanda ka shiga wurin sa.
Sasan Innawuro ya shiga da sallama wadda ke taya me aikinta girkin tarar tsohon mijinta, ta amsa tana fitowa daga kitchen mamaki ne ya rufe ta ganin me sunan mijinta, duk da daman kullum addu'ar ta kenan Allah ya kawo mijin jikarta ta ta koma ɗakin ta.
Ta faɗaɗa fara'arta tana mishi sannu da zuwa ya zauna yana gaishe ta cikin girmamawa sun ɗan yi shiru ya ce Malam yau za su sauka Kano."
Ta ce "Ma sha Allah, Allah ya kawo mana su lafiya."
Ya ce "Amin zan je in gaishe da mutanen gidan." Ta ce "Ai kam mazan duk sun fita." Ya ce bari ya gaido Mama. Ta san maman Hamida yake nufi ta ce "To."
Ko da ya je ya gaishe ta ya dawo suka ci gaba da zama ya ji Innawuro bata da niyyar kira masa Hamida sai ya tambaye ta ta ce "Da ciwon kai ta kwana, ta je Asibiti." Da damuwa a fuskarsa ya ce "Ina ne asibitin? Ta ce "Bari dai in sa a raka ka." Ta fita ta samo yaro ya miƙe suka fi ce.


Asibitin babu nisa da gidan, yana yin farking ya sallami yaran ya shiga ciki.
Wani mai saida kati ya tambaya ko ya ciro katin wata Hamida Ibrahim a yau? Ya ce "Bai ciro ba." Ganin Abdurrashid babban mutum ne ya sa ya ce bari ya tambaya mishi, fita ya yi yana tambaya wata Nurse ya samu ta ce ya tambaya wurin masu ciki, ilai kuwa yana zuwa aka ce ta zo, ya duba ta wurin ganin likita, sai ya koma ya faɗa wa Abdurrashid hannu ya sa aljihu ya yi masa kyautar girma, ya shiga godiya ya bi Abdurrashid ɗin shi ya tambayi Hamida Ibrahim wasu mata biyu suka faɗi yanzu ta shiga wurin likita. Abdurrashid ya nemi ya nuna masa Office ɗin likitan, ya nuna mishi knocking ya yi daga ciki likitan ya amsa ya murɗa handle ɗin ya shiga, sun kalli juna da likitan ya ƙarasa ya bashi hannu suka yi musabaha Hamida wadda zaman ta kenan cikin dogon hijab ɗinta da safa jin ƙamshin turaren Abdurrashid ga kuma ƙarin mamakinta kamar muryarsa, ID Card ɗinsa Abdurrashid ya nuna masa wanda yasa likita ya ƙara shiga nutsuwarsa ya ce "Me ke damun Madam ɗi na? Likitan ya ce
"Ciwon kai ne ranka ya daɗe ka san mata masu irin lalurarsu, can na ciwo nan na ciwo." Kan Abdurrashid ya ɗaure wace irin lalura ce da matata?"Kafin likita ya bada amsa ya kai wurin Hamida hannayenta ya lalubo cikin hijab ɗin ya ɗan rankwafo har suna jin nunfashin juna "Wa ce lalura ce da ke Hamida?" Ba ta yi magana ba hasali ma ko motsi ba ta yi ba "Wata biyu bana nan, ban san me yake faruwa da ita ba." Abdurrashid ya fuskanci likita ba tare da ya ɗago ba likitan ganin kamar Abdurrashid ya manta yana wurin ya miƙe "Yallaɓai bari na dan tsahirta muku ina ganin tunda ka iso za kayi maganin ciwon kan.". Da haka ya bar kujerarsa ya fita ya ja musu ƙofa.
Ajiyar zuciya Abdurrashid ya fidda gabaɗaya ya cafko ta ya miƙar tsaye ya sa ta jikinsa sai ya ji cikinta da ya yi tauri ya cire hannun ya kama hannunta suka fito Office ɗin, sai da suka kai inda ya adana motarsa ya buɗe ya cusa ta ciki sai ya shiga glass ɗin tintek ne hakan ya ba shi damar ƙoƙarin cire mata hijab, duk da riƙewar da ta yi sai da ya yaye shi cikinta yake lalube taurin da ya kuma ji ya ce "Me ya same ki a ciki? Jikinsa har rawa yake don son jin amsar da za ta ba shi amma ta ƙi magana "To koma gaba mu tafi." Nan ma banza ta mishi ya gaji ya koma gaban ya ja motar.
Ganin ya nufi GRA gidan Daddynsa inda yake sauka idan zai kwana garin ya sa ta ce "Ina za ka kai ni? Ya ce "GRA za mu in yi rarashin a can." Ta ce "Wallahi ka kai ni gida ba zan je ba." Ganin ba shi da niyyar canza hanya ya sa ta ce "Ko ka tsaya ko in buɗe ƙofa in fita, wallahi ba zan je ba." Wawan burki ya ja ya mayar da motar gefen hanya "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe." Ya faɗi sai ya tashi motar zuwa gidan su Hamida yana tsaida motar ta riga shi fita ta shige ciki ba ta ga Innawuro ba ta shige ɗakinta kan kujerar mudubi ta zauna kawai ta rasa wane ma tunani za ta yi?
Ta samu ya yi minti talatin a zaune Innawuro ta turo ƙofa sai da ta tambaye kan wanda har ta manta da ciwon ta ce mata ana kiran ta a falo. Da ma ko hijab ɗin ba ta tuɓe ba ta miƙe cikin sanyin jiki sai ta isa falon bayan kujera ta ɗan raɓe ganin duk babanninta na wurin.
Sai da aka buɗe taro da addu'a sannan Baban Laila ya nemi Abdurrashid ya bayyana matsalar da ta haɗa shi da matarsa har ya turo ta gida ta zauna tsawon watanni biyu."
Tiryan tiryan ya faɗi abin da ya sani da sakon da aka turo mishi da wanda Hamida ta ba shi labari."
Baban Amina da duk cikin su shi ne mai zafi ya ce "To ka amince da abin da aka turo makan shi ya sa ka turo mana ita gida wata biyu?
Abdurrashid ya yi ɗan jugum kunya da nauyi suka kama shi ya yi ƙarfin halin amsawa da cewa "Ban turo Hamida gida don ina zargin ta ko na yarda da abin da aka turo min, na turo ta ne don in ja kunnenta na ji zafin abin da ta yi min ƙwarai na ɓoye min abin da yake faruwa, abokina Usman wanda yake aminina na tunkare shi a ranar da Hamida ta tafi ya kasa fuskanta ta ƙarshe sai gudawa ya yi yanzu haka iyalansa da iyayensa ba su san inda yake ba. Ya turo min text yana neman gafara ta tare da bayyana min komai, ya kuma ƙara wanke Hamida kan mace ce ta ƙwarai kuma Allah ya kare ta kan mummunan ƙudirunsu akan ta. Falon suka ɗauka da faɗin Alhamdulillahi. Sai da suka tsahirta ya ce yana roƙon a ba shi Hamida su wuce yau.
Baban Amina ya ce Hamida za ta koma amma ba yau ba sai Malam ya dawo.
Dafe kai kawai Abdurrashid ya yi ya rasa yadda zai roƙe su su yi haƙuri su ba shi matarsa ita ya hukunta amma ya fita shiga damuwa na rashin ta kusa da shi bai ankara ba sai dai ya ji suna yi mishi sallama kowa ya fice Hamida ma da ke raɓe ta miƙe ta shige ciki Abdurrashid ya bi ta da kallo.


Sau biyu Hamida tana leƙowa sai ta gan shi zaune,kuma hakika yunwa take ji, ana ukun ne ta ga ya fita ta fito ba ta ga Innawuro ba a falon ta wuce kitchen ɗanwake take sha'awa da miya tana da garin ɗanwaken da Innawuro ta sa aka yi mata rogo ne da dawa da alkama da wake da gujjiya har kuka an sanya wurin niƙan. Akwai jiƙaƙƙen ruwan kanwa sai ta kwaɓa ta ajiye wuri ɗaya sai ta soma haɗa muryar akwai tantaƙwashi da ganyaye a fridge ta haɗa lafiyayyar miyar gyaɗa, sai da ta gama haɗin ta kunna ɗaya kan gas ɗin ta sanya ruwan ɗanwake da ta riga ta tafasa ruwan a kettle nan da nan ta fara saki tana gamawa ta koma kan miyarta tana cikin juyawa ta ji muryar Abdurrashid yana kiran sunan ta, ƙofar ta harara ta ci-gaba da abin da take.
An ɗan jima yana kiran ta kafin ta ji shigowar sa kitchen ɗin gyalen abayar jikinta ta yi saurin warwarewa ta rufe kanta zuwa kafaɗa sai kallon ta yake daga sama har ƙasa duk da ta ba shi baya "Hamida." Ta kuma ji ya kira sunan ta, ko motsi ba ta yi ba har ya iso inda take sai ta ji ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login