Showing 69001 words to 72000 words out of 84568 words
Chapter 24 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt
zam ririta ni da yake da abubuwan buƙata da yake mana ni da yayana ya rage hakanan dai nake zaune duk wani farin ciki na shi ya mayar da shi wurin amarya, na tashi haiƙan ina amfani da magungunan nan ashe kuma sanyi ya yi min mugun kamu hakan ya hana ni gane amfanin abin da nake shan, na gaji na watsar na ci-gaba da zaman haƙuri.
Ana nan sai Allah ya haɗa ni da wata mai sayar da magungunan mata da ƙyar ta sani na ɗauki wani ta ce in gwada, na dai karɓa na biya ta na zo na ajiye ya yi wata uku da safe ban koma ta kanshi ba sai watarana na ɗauko shi na yi amfani da shi a ranar na ga abin mamaki don gabaɗaya susucewa ya yi, in taƙaice miki magani ya yi daga nan bunu-bunu mutum na manne da ni, abubuwan cikin gida da duk ya maƙale hannunsa duk ya saki ya dawo yana mini hira da da ta soma gagara tsakanin mu.
Zai yi ma yarana hidimar duk da ta kama, tun daga nan na kama matar nan na riƙe da ta samu masu kyau za ta kawo min. Amir (Yaronta na farko) da ya ga matar ta shigo sai ya yi ta jin haushi wai in ta kwashe kuɗina ina ba ta, a raina sai in ce yaro har kai wannan matar tana ma amfani.
Wato ni Hamida abin da na fahimta game da waɗannan magungunan, ba wai za ka mallaki namiji ba ne ko ya yi ta kwasar abin duniya yana ba ka, a'a za ka tsira dai da ƙimarka, Hamida ta gyaɗa kai "Na gamsu da bayanan ki, ni ma ban da ban iya sha da na saya."
Ta ce "Ai akwai masu daɗi irin su zuma da gumba, za ki iya ci."
Ta ce "Sai na tashi amfani da su zan sa ki saya min, ke ma zan ba ki nawa da nake amfani da su."
Wayar Hamida da aka shiga kira ta katse su Hamida ta ɗaga kiran tana murmushi ganin sunan ya Aliyu ne kan screen ɗin ta ce "Ya Aliyu, yayana ni kaɗai."
Murmushi ya yi mai sauti har ta ji "Yanzu dai kina ina? Innawuro ta kira ni hankali tashe wai har yanzu ba ki dawo ba."
Murmushi ta yi "Ita Innawuron? Sai dai in ta soma ruɗewa amma na gaya mata zan shiga gidan Amina, in gaishe ta ta samu miscarrige ka sani."
Kai ya gyaɗa kamar tana kallon sa "Zan zo in kai ki gida."
Ta ce "To ya Aliyu."
Ta ajiye wayar suka ci gaba da hirar su har ya kira ta ya shaida mata isowar sa, hijab ɗinta ta janyo dogo har ƙasa ta sanya Safa sai ta miƙe Amina ta biyo ta don mata rakiya sai da suka zo zaure Hamida ta tsaya ta buɗe jakarta kuɗi ta ciro masu kauri ta kama hannun Amina ta damƙa mata Aminar tana meye haka ta ce "A sayi kayan gyara a ƙara gyarawa Baban su Amir."
Suka yi dariya ta ce "Ya za a yi in amshi kuɗinki ke da kike zaune? Murmushi ta yi don ta san ba ta da matsalar kuɗi duk wata sai Abdurrashid ya turo mata kuɗaɗen da ya saba ba ta.
Ta ce "Kar ki damu ina da kuɗi." Ta kaɗa kai "To na gode sosai."
Suka isa inda ya ajiye motar Amina ta gaishe shi sai suka wuce.
Yammacin wata Laraba ta fito wanka ko da zaman ta gaban mirror sai ta samu kanta da son yin kwalliya wacce tun da ta zo ba ta yin ta, ta murza hoda ta gyara girarta ta goga wet lips sai ta sanya turare.
Jin ƙamshin ya tuna mata da rayuwarta da Abdurrashid hannayenta ta haɗe ta shiga tumani, ta jima kafin ta miƙe ta nemi kayan da za ta sanya cikin ya fara fitowa duk da ya sa ta yi ƙiba jikinta ya kuma yin lukwi-lukwi ta dai yi kyau irin na mata masu ciki.
Wata doguwar riga ta zura ta wani yadi mai taushi, sai ta sanya hijab takalmi flat da jakarsa.
Ta fito Inna Innawuro na zaune a falo tana kallon shirin Kwana casain da ake gabatarwa ganin ta da hijab ya sa ta ce "Ina kuma za ki? Ta ɗan zauna hannun kujera "Ka ji Innawuro sai ka ce wadda ke fita kullum, ya Aliyu zan dubo."
Baki ta riƙe "Yau kaɗai da bai shigo ba za ki duba shi son yawo dai."
Ta langaɓe kai "Kai Innawuro ina nake zuwa? Ya Aliyu fa ya ce yau ko fita bai ba ciwon kai ya matsa mishi."
Tausayi ta ji ta ba ta ta ce "Shi kenan, ke da wa za ki? Ta ce "Keke napep yara za su samo min.".
Ta fita falon Innawuro ta bi ta da kallo.
Sasan su Aina ta fara shiga ta yi wa matar Baban Aina barka don Ainar ta haihu ta samu ya mace, da ta fito na su Laila ta shiga akwai yaron da ke kwance yana fama da gaida, nasu sasan ta shiga ƙarshe ta samu Innarta na girkin abincin dare, nan ta zauna suna hira har aka aka samo mata mai napep ta fita suka tafi.
***********
A falo ta samu Aliyun yana zaune ta zauna tana duban shi yana mata murmushi "Sannu ya Aliyu."
Ta faɗi tana langaɓe kai, Asabe da ke kallon su tana goge goge daga nesa takaici ya rufe ta.
Hamida ta zame hijab ɗin jikinta don wani zafi da take ji "Asabe ba ki ga zuwan Hamida ba? Aliyu da ya san da wanzuwar ta a wurin ya faɗi
"Ki ba ta ruwa." Ya kuma faɗi yana waiwayawa inda take ta tako zuwa tsakiyar falon ko da Hamida take da aure sai ta yi ta ganin za ta iya zama kishiyarta, yanzu zaman da suka yi wuri ɗaya wata dacewa take ganin sun yi, da ƙyar ta iya cewa Hamida Sannu da zuwa. Ita kam ta gaishe ta cikin fara'a da tambayar ta yara ta ce suna Islamiyya.
Sun ci gaba da hirar su har aka kusa kiran magrib ta ce za ta koma gida, ya ce a'a ta bari ya yi sallah sai su tafi tare.
Ko da Hamida ta yi alwala ba ta ga fuskar shigar ma Asabe ɗaki ba, sai ta yi sallar a falo nan saman carpet tare da yarinyar Aliyun mai sunan Innawuro, wadda take goyo kuma sunan Hamida ya sanya mata, tana idarwa Asabe ta zo kusa da ita "Ba wai mutum ya baro ɗakinsa ba yana bin gidajen mazan mutane."
Da mamaki Hamida ta ɗago "Aunty Asabe ban gane me kike cewa ba? Gabaɗaya ta taso "Ina nufin mutum ya fita hanyar mijina."
Ta buɗe baki za ta yi magana Aliyu ya shigo ganin Asabe tsaye kan Hamida ya ce "Lafiya."
Asabe ba ta tanka ba sai wata cika take Hamida ta ƙirƙiri murmushi "Ba komai ya Aliyu."
Ta miƙe, ya ce "Mu je ko."
Yarinyar ta ce "Zan bi ki gidan Innawuro Aunty Hamida." Ta ce "Gobe akwai Sch maama." Ta ciro kuɗi "Ku yi break ke da su Baffa, gobe a Sch."
Ta bi bayan Aliyu.
Sun bar gidan har ya hau titi yake ce mata "Aure zan ƙara Hamida." Gabanta ta ji ya faɗi don tuna fargabar da ke cikin cewa za a wa mutum kishiya "Kai Ya Aliyu me Aunty Asabe ta yi za a yi mata kishiya? Ta gefen ido ya yi mata wani irin kallo "Sai ta yi wani abu zan ƙara aure? Ina da buƙatar hakan ne, a cikin garin Katsina yarinyar take.
Ina so a yi da zarar ta ƙare karatu."
Hamida ta jinjina kai "Karatu take kenan? Ya ce "Ƙwarai ɗaliba a jami'ar Umaru Yar'adua University karatun digiri take tana shekarar ƙarshe.
Ajiyar zuciya Hamida ta fidda tuna Anisa da zaman da take da ba ta san makomarta ba. Ta ce "Allah ya tabbatar da alheri." Murmushin da ba koyaushe yake yi ba ya yi ya ce "Amin."
Suna isa ɗaki ta shige ta bar su suna maganar dawowar su Malam gobe, duk kuma yadda Innawuro ta so ta ci abinci ƙin ci ta yi sai hura ta sha ta kwanta.
Ta daɗe tana zubar da hawaye, abin har ya kai a fara tozarta ta? Sai da ta ji kanta ya fara ciwo ta ba kanta baki ta yi barci.
Da safe da ciwon kan ta tashi ta ce ma Innawuro za ta asibiti don ba ranar awonta ba ce. Sai da ta karya ta shirya ta tafi, napep ta hau tana kuma wucewa motar Abdurrashid na tsayawa ƙofar gidan.
[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH....RAYUWA
NO.30
MARYAM LITEE
Walida ta duba da ta ga ta ƙura mata ido sai ta ga Walidar ta taso ta kamata bayan ta rataya jakar Hamidar da ake ajiye.
Da taimakon ta suke takawa zuwa cikin Hotel ɗin, dan Hamida daf take da ficewa hayyacinta.
Wani ɗakin Hotel ɗin ta kai ta ta dire ta bisa gado bishi-bishi Hamida ke kallon ɗakin idonta na lumlumshewa, Walida ta kece da dariya "Sorry ƙawata, tun farkon fara ƙawancen mu nake fama da takaicin a komai kin fi ni, don haka da aka nemi in kawo ki za a ba ni maƙudan kuɗaɗen da ban taɓa mafarkin riƙewa ba sai ban yi wasa da damar ba."
Usman Hamida ta ga ya shigo ɗakin yana wa Walida tafi"Kin yi namijin ƙoƙari." Ya faɗi yana duban ta, murmushi ta yi masa ta miƙa mishi hannunta "A ba ni balance ɗi na." Ya ciro wayarsa "Zan miki transfer yanzu."
Ya matso kusa da Hamida ya kama hannunta sai ya sake shi hannun ya tafi yaraf, dariya ya kece da ita sai ya ɗauke ta hoto.
Shigowar Brigadier ya ɗauke ji da ganin Hamida. Sara mishi Usman ya yi suka juya shi da Walida don barin ɗakin, Brigadier ya bi bayan su ya murza wa ƙofar key, ya dawo yana murza hannuwa yana ƙare wa Hamida kallo.
Ya zauna gefen gadon so yake ya cire komai na jikinta kafin ya gabatar da ƙudirinsa, amma matsuwar da ya yi ya ji shi cikin jikinta ya sa ya fara kwance zanenta, ya zare skirt ɗin da ke ciki kyawawan cinyoyinta suka ƙara ɗimauta shi ya ja fant ɗinta pad ɗin da ya gani ya sa shi janye hannunsa da sauri, sai ya dafe kai komai ya tsaya mishi, ɓacin rai ya maye gurbin farin cikin da yake ciki, tsaye ya miƙe sai ya zura kayansa da ya tuɓe ya bar ɗakin.
Ganin motar Usman a harabar Hotel ɗin ya ba shi mamaki ya isa ya ƙwankwasa glass ɗin, Usman ya fito yana sara mishi "Ya ba ka wuce ba? Ya tambayi Usman kame-kame ya hau yi don saƙe-saƙe yake yadda zai samu damar ɗaukar hoton Hamida yayin da brigadier ke kwance da ita da vedio yake so ya yi mata barazana ta ba shi kanta, don shi ba zai amfani da ita tana wata duniya ba ya fi so ta faranta mishi da kanta hakan zai sa ya samu gamsuwar da kullum yake mafarkin samu.
"Yallaɓai ka fito kuma? Usman ya tambaya yana wani sunkuyar da kai "Mance kawai, abin su na mata take zan jira har ta tashi, idan ta wuce sai in tafi." "Ok Sir" Usman ya faɗi ya faɗa motarsa ya ja ya bar wurin jin Brigadier ba tafiya zai yi ba, don da ya san zai fito yanzu da ɓoyewa zai yi har sai ya wuce ya shiga ya rage zafi.
Awa uku Hamida ta ɗauka tana barci sai ta farka zaune ta tashi ta dafe kanta da ke saDra mata. Ta ɗan jima a haka kafin abin da ya faru ya fara dawo mata zumbur! Ta miƙe tsaye salati take tana ƙarawa ganin zanenta da skirt a yashe tunanin sun keta mata mutunci ya sa ta fashe da kuka, sai dai tuna halin da take ciki na al'ada ya sa ta shafa wurin, fant ɗinta na nan haka pad ɗin, sai ta yi wa Allah godiya da ya kare ta.
Usman, Brigadier, Walida. Ta riƙa kallon hotunan su a cikin ɗakin da Walida za a haɗa baki a tarwatsa rayuwarta? Komai na ta ta ɗauka sai takalmanta ne ba ta gani ba, ba ta damu da tsayawa neman su ba ta fita dakin, sai da ta je gaban motarta ta lalubi key a jakarta, yana ciki da wayarta, tana tayar da motar ta fara kuka iya ƙarfinta.
Har ta kusa gida ta tuna da Abdurrashid, agogon motar ta kalla takwas saura na dare gabanta ya yanke ya faɗi me za ta gaya mishi yau? Ba ta son ce mishi komai har sai ta nutsu ta yi tunani, tana ajiye motar kusa da ta shi ji ta yi kamar kar ta fito,don shi ma tana jin tsoron abin da zai ce mata ta dai daure ta fita, a hankali take takawa har ta isa ƙofar falon ta yi sa'a ta ji ta a buɗe sai ta shiga da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta "Ina kika tsaya sai yanzu kike dawowa? Cak ta tsaya jin muryar Abdurrashid cikin kanta wanda sam ba ta lura da shi a cikin falon ba. "Ban san sau nawa zan faɗa miki ba na son ki fita ki kai irin wannan lokacin matuƙar ba tare muka fita ba, amma kin raina ni, zan ɗau ki mataki a kanki."
"Ka yi haƙuri." Ta furta ba tare da ta waiwayo ba "Kar ki damu ki cigaba sai dai kar ki yi kuka da matakin da zan ɗauka kanki."
"Don Allah dai na ce ka yi haƙuri." Ta ƙara bada haƙurin cike da ƙosawa ta samu ta shige ɗakinta jin ya yi shiru ta san ba zai ƙara cewa komai ba sai ta wuce ɗakinta kamar ana tunkuɗa ta.
Gado ta hau ta rufe idonta takaici take ji kamar ta rufe kanta da duka, me ya sa ba ta tona mishi asiri maganganun banzan da ya gaigaya mata da yau ko me Abdurrashid zai yi mata sai ta faɗi abin da suka yi mata a yau shi da Walida, abin da zai taka mata burki Brigadier da ya shigo tsakiyar su, ba za ta so auren yar'uwarta ya mutu ba ɓullar maganar zai iya shafar zumuncin su har a can gida,
don haka ta yanke yin shiru kawai tana kammala karatunta ta bar garin.
Wayarta ta lalubo sai ta gan ta a kashe ta kunna tana neman sunan Walida sai saƙo ya shigo ta tsaya dubawa gargaɗi ake mata kan idan ta tona abin da ya faru a yau kiran sunan wani a cikin su ukun abu biyu zai faru mutuwar auren Aina da tsintar gawar Abdurrashid. Wani busasshen miyau ta haɗiya ta ci-gaba da neman lambar Walida sai dai ba ta shiga, goge ta ta yi gabaɗaya daga wayarta don wani abu da ke tokare ta idan ta ga sunan ta tuna cin amanar da ta yi mata.
Tana nan zaune cikin alhini da baƙin ciki ba ta ankara ba sai ta ga ƙarfe biyu da rabi na dare, ta shi ta yi ta shiga bathroom ta tsaftace jikinta sai ta fito ta tuɓe kayan jikinta ta kashe wutar ɗakin ta kwanta shiru cikin wani sabon tunanin.
Asubar farko barci ya yi awon gaba da ita wanda ya ja mata muguwar makara, sauƙin ta ma da ba sallah za ta yi ba shi ma bugawar da mai mata aiki ke yi ya tayar da ita, don Abdurrashid bai bi ta kanta ba saboda yana fushi da ita ya gama shirin sa ya bar gidan.
Ta buɗe mata suka gaisa sai ta koma ciki ta yi wanka, da fitowar ta wata doguwar riga ta zura ko mai ka sa shafawa ta yi.
Ta fito ta haɗa Tea zalla tana sha bakinta ba daɗi don yadda ranta ke ɓace, gamawar ta ɗaki ta koma tana ci-gaba da tunanin da ya fara addabar ta ta rasa wa za ta kira su raba wannan abu da ya faru da ita ko za ta samu shawara, Hanan da Mimi sune aminan ta amma kuma su ɗin dangin miji ne ita kam tana tsoron dangin miji komai daɗin ka da su.
Tana nan har ta ji dirin motar Abdurrashid ta miƙe ta fita tarar sa jakar da ya shigo da ita ta karɓa tana mishi barka da zuwa ya amsa fuska ba walwala, ko da ya ke fushi da ita yana mamakin abin da ya sa duk ta yamutse bai dai tambaye ta ba ko da suka zauna cin abinci yana kula ba wani na kirki ta ci ba.
Haka suka ɗauki kwanaki uku yana ta tunanin abin da ya same ta, don ya san hakanan yake fushi da ita ba ta bari a kwana za ta yi shigar da za ta ɗau hankalinsa ta sha turarukan da ƙamshin su ke kiɗima shi wanda jikinta ma da gidan sun riga sun riƙe ƙamshin,ta kawo kanta tana kukan kissa tana ba shi haƙuri shi kenan ya wuce.
Ya dawo aiki tana makaranta wanda tun faruwar abin a tsorace take fita sai ta ga kamar za su sace ta su idasa mugun nufin su a kanta, ji take kamar ta haƙura da karatun da aski ya zo mata gaban goshi ta tattara ta koma Kano.
Yana zaune ta dawo ɗakinta ta shige ta fito tana kankare jan ƙunbar da ta sanya a farcenta, kallo ɗaya ya yi mata ya faɗi a ransa ta samu tsarki kenan?
Don haka da daddare tana kwance a ɗakinta ya shigo a wannan daren Allah ya yi ikon sa rabo ya shiga a tsakanin su wanda da wata ya zagayo Hamida ba ta ga al'adarta ba hakan bai wani ɗaga mata hankali ba don ta sha yin haka sai sun gwada su ga ba komai.
Ba abin da ta canza na daga ɗabi'unta ma'ana ba ta wani laulayi kuma Allah ya ɓoye abin sa ko shi likita bokan turan bai gane ba.
A haka ta kammala karatunta ta shiga magiya ga Abdurrashid ya bar ta ta koma Kano shi kuma ya ƙi amince mata.
Wata safiya ta yi waya da mutanen gida mutum na ƙarshe da ta yi wayar da shi shi ne Malam da za su tashi zuwa ƙasar Singapore shi da Engineer, Malam ɗin na fama da ciwon sugar Engineer kuma zai je kan harkokin kasuwancinsa kuma shi ma za a duba shi