Showing 12001 words to 15000 words out of 84568 words

Chapter 5 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

dare kai ta girgiza ta ce ita sau daya take shiga kitchen. Hamida dai ta ce bari ta yi ta fita cike da mamaki idan ta tuna a gidan su na Daura, to ya ma za a yi iyayensu maza su dawo a ce ba a yi girki ba, ita kam bata taɓa gani ba.


Kitchen din ta shiga ta yi tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya wanda ta iya su tun a Daura. Da ta gaya wa Laila tana son kuɓewa ɗanya mai mata wanki ta aika gidan Gwoggo ya karbo tana kammalawa ta shige daki




Da safe ma ita ta fito ta yi musu abin karyawa. Ta koma daki ta ji tana kiranta ta fito, sai da ta gaishe su Laila ta ce ta shiga ta dauko Amir ta yi masa wanka ta ba shi abinci.
Sai da ta yi mishi yadda duk aka ce mata sai ta goya shi ta gyara wa Auntynta ta daki. Ta fito goye da shi ganin babansa wanda ke kokarin fita yasa yaro soma zizzillewa sauke shi ta yi ya isa wurinsa, sai ta wuce daki, sai da ya fita laila ta kira ta ta bata Amir din.










Haka rayuwar Hamida ta ci gaba da gudana a gidan laila, ita ta zama tamkar matar gidan don ita ke gudanar da komai duk da ƙarancin shekarunta.
Laila irin matan nan ne da suke ɗaukar ragamar gidansu su damƙa wa masu aiki, abin da suka sani su mike kawai mai aiki za ta tsaya kan komai. Hamida dai don ta horu da aikin tun tana Daura, sannan zamanta gidan Gwoggo Indo ta kara koyon girke girke na zamani don nan din ma bata zauna ba, hakan ya bata damar iya riƙe gidan Laila wadda kodayaushe za ka samu mike tana charting.




Wata ranar Asabar masu gidan suna zaune a falo, Hamida na ɗaki tare da Amir wanda ya yi matuƙar sabawa da ita. Jan rigarta yake yana faɗin Daddy ta dauke shi don miƙa shi sun zo kofa sai ta ji kamar suna fada. Yadda take jin tashin muryoyinsu sai ta tsaya Laila ta fara ji tana cewa "Ni dai ban ce ka kawo mini kowa ba, abinci ka je Restaurant ku ci." Shi ma ya karɓe da "Nan na yi niyyar kawo su, kuma tilas a girka abincin tarar su, manyan abokaina ne za su taso su ziyarce ni ina da iyalin, sai in kai su Restaurant? Zan fita za a kawo cefane."
Komawa Hamida ta yi ta zauna sai da Amir ya dame ta ta fito, Laila kadai ta samu mike kan sofa tana danna wayarta.
Zama Hamida ta yi tana kallon Tv da ke ta aiki. Wanda aka aiko ya kawo cefane ya yi sallama ya miko, Hamida ta karba ta kai kitchen Laila kuma ta tashi ta yi ɗakinta.
Wurin awa daya da kawo cefanen Hamida ta gane Laila ba za ta yi girkin ba, sai ta tashi ta shiga kitchen iya ƙokarinta da wayonta ta yi kuma cikin ikon Allah ta yi abinci kala biyu masu dadi ta shirya komai kan tebur ta koma daki ta dauki wani littafin hausa da ta samo dakin Laila ta ci gaba da karantawa.


Karfe hudu ta ji hayaniyar bakin da basu wuce su biyu ba.
Yamma likis ta ji shiru alamar sun tafi ta fita ta kwashe komai ta kai kitchen ta wanke.




Sai zuwa dare ta ji an turo kofarta. Kai ta ɗaga sai Ahmad ta gani ta maida kanta kasa ta soma gaishe shi ya amsa da yi mata sannu da aiki, cikin ransa kuma yana mamakin yarinya ƙarama kamar wannan ta iya fitar da shi kunya. Ya ce "Ina ɗan naki? A ɗarare ta ce "Yana wurin Aunty Laila. " ledoji guda biyu da ya shigo da su ya ajiye mata, ba tare da ta ɗago ba ta yi godiya ya juya sai ya bar ɗakin. Ƴan mintoci ta ba shi sai ta dauki ledojin zuwa dakin Laila, tana knocking ta ce ta shigo, zaune take gaban mirror tana ma kanta wankan turare, don ta sha kyau har ta gaji, wata haɗaɗɗiyar rigar barci ce mai kwalliya a kirji ga fuska ta sha make-up. "Ya a ka yi? Ta tambayi Hamida sai da ta ajiye ledojin bakin gado ta ce "Baban Amir ne ya bani." ta ce "Kwashe ki je da su kin gode, ki dauki Amir ya kwana wurin ki." kai ta ɗaga tana kai dubanta inda Amir din ke barci, ta ƙarasa ta dauke shi, sai da ta sanya mishi pamfars sai
koma dauko ledojin babu Laila, ta san ta wuce dakin maigidan, ta koma sai ta koma dakin maigidan.




Washegari da La'asar zafin da ta ji tana ji yasa ta watsa ruwa. Da ta fito kwalliya ta yi cikin riga da zane na atamfa tana fesa turare Laila ta shigo cikin "Ki zo Gwoggo ta zo." Da murnarta ta ajiye kwalbar turaren ta bi bayanta.
Kamar yadda take cike da zumuɗin ganin Gwoggon ita ma Gwoggon haka, kasa ta zube kusa da ƙafafunta, Gwoggo ta shafa sumar kanta "Na yi kewar ki ɗiyata, kuna nan lafiya? "Lafiya lau Gwoggo ina Aunty Aina? Ta ce "Tana gida." Ta dubi Laila "Wai har yau ba ku samu mai aikin ba? Ta ce "Ba a kawo ba Gwoggo, da ma za ki bar mana ita." Saurin girgiza kai da hannu ta yi "Sam! Ku nemo mai maku aiki zan ɗauki ɗiyata, nan da wasu kwanaki ko kun samo ko baku samo ba."
Ta shiga bude ledar gabanta "Yanzu Gwoggo iyakar kudin kenan ba a ragi? Gwoggo Indo ta dube ta da mamaki "Ragi kuma Laila? Wadannan fa ba irin na gama gari ba ne, wannan na manyan mata ne. Daga ke sai Haj Mariya na daukar ma ma, don ke duk tsada na san ba ki ƙyashin saye ki gyara kanki."
Ta jinjina kai "Zan bayar da rabi yanzu, cikon kuma sai nan da kwana biyu."
Gwoggo ta yi fara'a "Yawwa ko ke fa? Allah ya kaimu. Ta maida dubanta ga Hamida "Tashi ki yi mini rakiya mu je mu dawo? Laila ta yi saurin cewa "Ina za ku Gwoggo? "Gidan mai gayya mai aiki, oga kwata kwata." "Waye mai gayya mai aiki Gwoggo? Hamida ta tambaya murmusawa ta yi "Mai wannan Estate din, gidansa za mu maza sanya lullubinki mu je ki kashe kwarkwatar ido." hijab ta sako sai suka bar gidan.
[2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH.....*






*No.6*


DAGA MaRuBuCiYaR


CANJIN BA ZATA
WA GARI YA WAYA
RANAR NAKA
HATTARA*
AND NOW


SHIRIN ALLAH...


MARYAM IBRAHIM LITEE




YA tsaya yana tunanin wanda zai samu ya kira masa ita, wurin shiru yake sai zirga -zirgan ababen hawa jefi-jefi. Bakin Gate din ya zura wa ido ya dauki kimanin minti biyar kafin aka buɗe kofar da ke jikin Gate din Malam Buhari ne ya fito sai ya yi saurin ƙarasa gabansa, gaisuwa ya fara mika wa Malam Buharin amma sai ya sunkuyar da kansa har da yar rusunawa yana gaida Abdurrashid wanda ya yi wa farin sanin ɗan Mai gidan su ne, tare da kakkaɓin abin da ya kawo shi ƙofar gidansa. "Hamida nake nema." Abdurrashid ya ce kamar ya shiga zuciyarsa, ɗan jim ya yi sai ya ce "Ina zuwa, ranka ya daɗe." ya juya zuwa ciki. Gwoggo Indo ya samu tana haɗa miyar taushe, ya dube ta "Zo mana." ta tashi sai ta bi bayansa suna shiga falo ya ce "Wani abin mamaki ya faru yanzu ina fita. " "Uhm me ya faru? Ya ce "Yaron Mai gida na samu a kofar gidan nan ya ce wai yana neman Hamida. Gwoggo ta gwalo ido Hamida ko dai Aina Malam? Ya ce "To ni dai Hamida ya ce mini. Ta tafa hannu cikin matukar murna "Koma Malam ka ce tana zuwa." bata saurari cewar sa ba ta yi dakin su Aina tare ta same su da Hamida, Aina na danna wayarta Hamida na haɗa kayanta za ta wanke "Tashi ki ji Aina, abin alheri ne ya tunkaro mu, ɗan mai Estate din nan ne ya zo har kofar gidan nan neman ki." Zumbur kuwa ta tashi zaune "Ni kuma ya ce Gwoggo anya? Ta ce "Ke dan Allah ba mu da lokaci, irin wadannan ba a ja musu aji, tashi ki gani ko rana aka sanya miki tuni za a warware ta, dan gidan Engineer Shehu Bello ne fa. Aina da tuni ta kai gaban wardrobe ta soga ciro kaya Gwoggo na taya ta har suka kai ga matsaya kan wasu riga da skirt na wani yadi mai taushi tana ma fuskarta kwalliya Gwoggo Indo na mata wankan turare. Hamida da ta gama haɗa kayan wankin ta ɗiba ta yi waje. Sai da suka tabbatar Aina ta yi sannan ta fita Gwoggo na bayanta wadda ke jin kamar su tafi tare gudun kar Aina ta kwafsa musu duk da sanin gogewar Aina me wuya a samu matsala. Dakin masu mata girki ta shige windon dakin su ta waje yake sai dai ba ta hango inda ya tsaya sosai, ta dage sai ɗage take tana miƙa wuya a fatan da take ta hango su da kyau.Aina kuwa tana fita sallama ta yi masa ya dago idanuwansa da ke ƙasa cike da mamaki yake duban cikakkiyar budurwar da ke gabansa ta gaishe shi ya amsa cikin ƙosawa ta ce "Mu shiga daga ciki. Wani sanyi ya ji don zaton ko an turo ta ne ta yi masa jagora ya bi bayanta inda take tafe tana kaɗa jiki don ƙara sace zuciyarsa sun shiga tsakar gidan ba kowa sai Hamida da ke wanki daga ita sai zane da ta yi daurin ƙirji masu girkin suna can karshen gidan suna hira kallo daya ya yi ma Hamida sai ya kauda kai yana jin wani abu na yi masa yawo game da ita, har falon Gwoggo Indo ta zaunar da shi ta wuce ta kawo mishi ruwa, ganin ta koma ta zauna ya sa ya ce "Ina Hamidar ne? Wata faɗuwar gaba ta ji sai kuma ta ji duk ta daburce "E tana nan." ta ba shi amsa "Yi mini magana da ita pls. " ta mike tana jin ƙafarta kamar ba za ta ɗauke ta ba dakin Gwoggo Indo ta faɗa, kaɗan ya rage su gwabza karo don a ƙofar dakin take tana leƙe, hangowar da ta yi sun bar inda suke tsaye tunaninta ya ba ta shigo da shi za ta yi, shi ne ta yi saurin baro dakin masu aikin ta shigo nata. Ya aka yi Aina? Ta fadi tana yarfa hannu "Wai Gwoggo wurin Hamida ya zo." ta fadi cike da sanyin jiki "Hamida kuma? Gwoggo ta yi tambayar mamaki kwance kan fuskarta. "Wallahi ita ya ce." "To ko lafiya? Don ba na ce son ta yake ba, amma dai bari in je in ji." ta fara ƙoƙarin janyo mayafi ta fita ta bar Aina wadda ta fada gadon Gwoggo kwajab kamar tsohuwar jaka rub da ciki ta yi ta rufe idanuwanta. Sallama Gwoggo Indo ta yi masa ya ɗago yana amsawa, tana zama ba ta jira gaisuwarsa ba ita ta soma gaishe shi "An ce kana neman Hamida lafiya? Ya ce "E wurinta na zo? Ta ce "To bari in turo ta. " ta fita ta bar shi cikin wani takaicin da mamaki da sauri ta samu Hamida "Zo diyata." Hamida ta ajiye rigar da take wankewa ta same ta. "Baƙon nan ke yake nema, ki kula da kyau in kin je gaban shi, ɗan me Estate din nan ne." ta ƙwalawa wata yar yarinya diyar daya daga cikin masu mata aiki ta ce ta je cikin kayan Hamida ta samo mata Abaya da gyalenta ta kwatanta mata inda kayan Hamidar suke. Ta amsa ta wuce cikin sauri, dakin masu aikin ta ja Hamida, sai da yaranyar ta kawo ta sanya "To yi maza ki je." Ta ba ta umarni Hamida na fita Gwoggo Indo ta shiga zance Allah ya wadaran rashin sani in na sani ba gyara ta zan yi ba, ko da su Malam suka turo mutumin nan nake cewa auren Hamida ba yanzu ba idan yaron nan ya ce yanzun yake so a aura mishi ita ai da gudu za a yi hakan, ƙanƙanta? Mu da aka yi mana muna da sha biyu me ya same mu? Ji take kamar tana mafarki wai tilon ɗan Shehu Bello ne cikin gidanta ya biyo cikin yayanta, ita kam da wace irin sa'a ta zo duniya? Farin ciki ke ɗawainiya da ita. Hamida dai a sanyaye ta isa falon ta yi sallama a hankali wadda da ƙyar ya jiyo ta kafin ta nemi daya daga cikin kujerun ta zauna. Kanta na kasa ta ce mishi ina wuni. Zaman minti goma suka yi shiru ya mike "Ni zan tafi." ta ce Sai anjima. Ya ce "Ki bani nombarki." kai ta girgiza "Ba ni da waya." "To ki amso mini ta mamanku."Ta miƙe ta je ta samu Gwoggo Indo, jiki na ɓari a ka rubuto ta kai mishi, ya sa kai ya bar falon sai dai kafin ya idasa ficewa ya ji muryar Gwoggo na cewa "Har ka fito? Ya ce "E" ta ce "Sai kja a yi hakuri da ita karamar yarinya ce." ya ce "Ba komai. Ranar Monday daga wurin aiki wurin saida abincin su Hamida ya wuce. Ya kuma samu nasarar keɓewa da ita a cikin motarsa, bai fito ba wayar Gwoggo ya kira ta turo ta. Glass din motar tintek ne don ba ya son jama'a su fahimci shi ne. Tambayar ta ya yi me ya sa ba ta zuwa makaranta? Ta ce Gwoggonta ta ce za ta sanya ta ya ce da ma ba mamanta ba ce? Ta daga mishi kai tare da cewa yayar babanta ce ya ce ina mamanta, ba ta ko numfasa ba ta ce Tana garin su Daura. Ya ja ajiyar zuciya Babanki fa? Ta ce shi ma yana Daura nan Gwoggonta ce ta dauko ta. Ya jinjina kai "Me ya sa ba ki son karatu sai saida abinci? Saurin duban sa ta yi a karo na farko idanuwansu suka shiga na juna, ta janye nata da sauri. "Ina so." "Kina son me? "Ina son karatun." "Yanzu idan na samu Gwoggonki na ce zan sanya ki Makaranta ki bar saida abincin nan za ki yarda? Cikin sauri ta ce "E. "To zan zo gida za mu yi magana da ita." Anan ya ga cikakkar fara'ar Hamida. Ya sallame ta ta fita ya ja motar sai ya bar wurin cikin tunani. A hankali ya ƙarasa a maimakon part dinsa na Auntynsa ya wuce, zaune take ta bi shi da kallo "Yau ma ina ka tsaya? Ta tambaye shi sai da ya zauna kusa da ita ya ce "Na ɗan biya wani wuri ne." ta kada kai ba dan ta gamsu ba. Hira suka shiga yi har aka kawo masa abinci ya ci anan sai ya wuce wurinsa, sai da ya gabatar da duk abin da zai yi kafin ya haye gadonsa don ya yi barci amma tunanin rayuwar Hamida ya hana mishi sakat. Zumbur! Ya mike ya shiga sanya kaya kananan kaya ya sanya da suka yi matukar hawansa, ko da fuskarsa ba walwala bai hana shi yin kyau ba. Ya fito sai da ya biya wurin Aunty Karima kallon mamaki ta yi masa "Sai ina kuma daga shigowa? "Wani abokina zan gani anan gadon ƙaya." ta gyada kai. Ya fice motarsa ya fada ya ja zuwa gidan Gwoggo Indo da wayarsa ya kuma amfani ya shaida mata ya zo. An yi sa'a dawowarsu kenan maimakon ta tura Hamida yarinyar mai girkinta ta aika ta ce ya shigo. Ita kuma ta fada dakin su Aina, dukkan su kwance suke bisa katifa Aina charting take, Hamida na kallon silif tana tunanin Innawuro da iyayenta da kannenta har ma da yan gidan su. "Hamida ga Yallabai nan ya zo." A tare suka ɗago suka dube ta Hamida ta ce "Waye Yallabai? Aina da ta ri ga ta gane inda zancen ya dosa ba ta tsinka ba "Yallabai mana da ya zo wurin ki shekaranjiya. Ganin Hamida ba ta da niyyar tashi ya sa ta zauna bakin katifar ta dora kanta a cinyarta "Na ga kamar ba ki murna da wannan babban kamu da kika yi? Jin Hamidar ba ta tanka ba ta ƙara da cewa "Kin ga duk girman wurin nan na mahaifinsa ne, duk kuma tarin al'ummar da kika gani cikin Estate din nan karkashin mahaifinsa suke, shi din kuma shi ne da daya tilo da mahaifinsa ya haifa. Ina gidan da muka je da ke kina gidan Laila? Hamida ta ce "Na tuna shi." "To shi ne gidan mahaifinsa, ga shi kyakkyawan saurayi ga arziki Hamida, ina gani ban taba rike wadda ta yi sa'a irin wadda kika yi ba." Hamida ta ce "Ya ce zai tambaye ki ya sanya ni makaranta." Gwoggo Indo ta yi cikakkar fara'a Yawwa to kin gani? Maza ki shirya ga Aina nan ta taya ki, ni zan je in tare shi, na sanya yar gidan magajiyata shigo da shi." Ta miƙe sai ta ja musu ƙofar. Ganin Hamida ba ta motsa ba ya sa Aina ta kamo hannunta "Hamida." ta kira sunanta, ɗago fararan idanuwanta ta yi ta dube ta, "Maganganun duk da Gwoggo ta faɗa miki gaskiya ne, kin yi dace da samun miji na nunawa sa'a, kin zo Kano da hannun dama.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login