Showing 84001 words to 84568 words out of 84568 words

Chapter 29 - SHIRIN ALLAH Complete Book free download by Maryam Ibrahim Litee .txt

shan ruwa sai ya juya ta samu ta miƙe ta bi shi a baya, ba su hawa dinning saboda halin da take ciki ledar cin abincin da aka shimfiɗa suka zauna nan ma kasa cin komai ta yi da ya tambaye ta ta ce ta ci wurin su Daada,yana gamawa aka kira Isha'i har ya fita sallar ya dawo tana nan zaune ya kama ta suka tafi ɗakinsa.
Wasu dogayen riguna ya sawo mata ya ce ta gwada ta gwada ta farko ba ta gama sauka ba ko dan saboda cikin, cikinta ta ji ya yi wata irin murɗawa ta saɓule rigar da sauri sai ta juya ta bar dakin dakinta ta isa ta hau gado tana ta jin ciwon da mararta ke yi, a haka ya shigo ya same ta yanzu kam yana tambayar ta ta ce mararta ke ciwo ya ce ta tashi su je hospital shi ya ɗauki kayan da ta shirya sai da ta zauna a mota ya koma ciki don sanar ma su Innawuro da suka ce ba su ga ta zama ba Asibitin su na sojoji ya nufa da ita cikin sauri suka karɓe ta aka shiga ba ta kulawa Abdurrashid na tare da ita, har sai ƙarfe sha biyu na dare ta haiho santalelen ɗanta mai kama da uban shi sai da aka gyara su aka canza mata ɗaki su Daada sun shigo baki har kunne don Daada ma har da kuka.
Zuwa safiya kowa da ya kamata ya ji ya ji har Engineer da safen ya zo shi da Mami da Aunty Karima wadda ta yi matuƙar nauyi.
Kwana biyu ta yi suka sallame su suka koma gida inda suka shiga karbar jama'a daga ko'ina da ke ta zuwa barka da murna, suna aka yi na ji da gani da ya tara dubban mutane.
Ta samu saƙon Jamilar Usman da ta ce ta kasa zuwa ta yi mata barka amma tana mata fatan alheri.


Ta ci-gaba da kula da ɗanta wanda ya ci sunan Engineer suna kiran shi Affan duk safiya Engineer ke aikowa a zo a ɗaukar mishi shi haka ma idan ya dawo Office, kwanan su arba'in da biyar Aunty Karima ta haihu ta samu budurwa sunan mahaifiyar Abdurrashid aka mayar mata tare suke renon yaran da suka zama kamar yan biyu.


Sai da suka yi watanni biyu ta samu tafiya Daura tare suka tafi da Innawuro a can ta haɗu da Aina wadda kunyar abin da mijinta ya hana ta je wa Hamida sai dai saƙo ta tura mata.
Haƙuri ta yi ta ba Hamida wadda ta ce ba komai Aunty Aina,sai dai ina fatan hakan ba zai raba zumuncina da ke ba.
Tana can ta samu labarin rasuwar Haj yar Yaya dole daga yin sati ta juyo maimakon kwanaki goma da ta samu Abdurrashid ya ba ta da ƙyar.


A gidan mutuwar ta ga su Anisa daga zuwa daya ba ta kuma yarda ta koma ba sai ranar bakwai.


Sannan ta bi gidajen su Momi Binta ta kai musu Affan.
Wata uku da haihuwarta ta shiga Islamiyar da take ta burin shiga ta cikin Estate ɗin.




Rayuwa ta yi wa Hamida daidai don tsakanin ta da Ubangiji sai dai godiya bayan Affan ta kuma haihuwar Abubakar Siddiq sannan ta haifi Fatima sunan mahaifiyar Abdurrashid Aunty Karima dai daga fatimarta ba ta ƙara ba.




Alhamdulillah
Sai Allah ya haɗa mu a book dina na gaba idan mai kowa da komai ya raya mu mai suna Bilkisu mai gadon zinare.
Maryam ɗinku ce.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login