Showing 24001 words to 27000 words out of 47716 words
Chapter 9 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
da ita, “dari biyar kawai kike bukata”?, tace “eh”, sai ya ce “ba damuwa, kibari gobe sai in baki”, “ki gayamin inda zamu hadu”, sai ta ce da shi “kawai ka zo makarantarmu dai dai sabon titi da akeyi na makarantar horar da sojoji, da zarar an tadamu tara sai mu fita”, “okay ba damuwa” kawai ya fada. Tareda girgiza kansa.
Da suka karaso daf da unguwarsu inda zai ajiye ta, sai ta ce da shi, “ko zaka iya zowa unguwarmu da daren yau ka ga idan da dama sai mu fita?”, sai ya ce “ba damuwa zanzo idan aka kammala sallar isha, mu hadu dai dai inda na ganki a kofar gidansu SAKEENA”.
Nan ya buga mota ya fice.
Ba tareda ya koyi sallar isha baya zo inda sukayi alkawari ya fake, tun bayan magariba yayiwa abokinsa ali magan kan cewa zai zo da budurwarsa saboda haka ya ajiye masa makullin dakinsa inda idan ya zo zai ganshi, sai faman latsal wayarsa yakeyi bugun Samsung note 5, a kusa da shi sai ya ji motsi, dagowa da zaiyi sai yaga nusaiba ce, duhu ya jima da sauka shiyasa ya kasa gano fuskar karamar kanwarta da ke tareda ita wacce iyakanta shekaru takwas zuwa tara, a hannunta bokiti ne kamar da alama ruwa zasu tafi diba. Murmushi kawai ya sakanmata, sai yace wannan fa, kanwata ce ta fada, tareda yi masa dariya a dai dai lokacin kuma take wasa da bokitin hannunta, wallahi anhanani fita ne, shi yasa na dauko bokiti nace ruwa zan debo domin inzo in shaida maka, gudun in barka tsaye kayit jiran tsammani, bayan ya saka murmushi sai ya ce ba komai, si kanwarta tace da shi, yaya ka bani dari biyu ina so in kashe a school gobe. Kash ya fada sai ya fidda yar dubu daya ya ce da ita kin gani wannan ce kadai nakeda banida canji, idan na baki ita kuma gida zaki ci duka, ki bari gobe zan ba nusaiba ta kawo maki, cikin nuna aalamar jin dadi ta ce ba damuwa. Sai ya juya ya wuce, bayan ta kara jaddada masa zancen da sukayi na haduwa a safiyar gobe.
‘yan kudin da ke hannunsa duka suka kare a dare, kasancewar mutum ne mai masifar kyauta ga kokarin saka kati a waya,, sai ya kasance a aljihunsa ko aho bai kwanta da shi ba.
Kashe gari da ya laluba yaji ba ko sisi a jikinsa, sai ya sake komawa barci kashi na biyu, kasancewar baya so ya hadu da nusaiba ba tareda ya cika mata alkawarinta ba.
Da misalin goma da mintutuka na safe sai ga kiran abokinsa rayyanu a waya, ya shaida masa gashi kan junction na tashar kola yazo ya karbi jersey da zasuyi wasa da ita gobe da maraice, kasancewar yafi kowa saurin fita fili sai ya zo da su, cikin sauri ya taso daga shi sai t shirt sai wando na sport wanda da kadan ya wuce guiwarsa, sai sauri yakeyi, duk da sauti ke tashi a kunnuwansa na wakar ZAINUDDEEN ZAIN mai taken juyin rayuwa dai dai verse three inda yake cewa
“ RAYUWA GUDA CE DAN UWA IDAN KA GANE
MAMA TA FADA A FARKO SAI YANZU NA GANE
IDAN KANADA SHI KAINE ABOKI NA KOWA
IDAN KA RASA A MAKA KALLO NA WAWA
NAI NADAMAR ABUNDA NA AIKATA CEN A FARKO
SHEGIYA RAYUWA TA KASA TAIMANI KARKO
UBANGIJI KAMIN AFUWA KAMUN LAMUNI
ZUNUBAN DA NA AIKATA YA ALLAH GAFARCE NI
MALAM KOMAI KAKE GANI FA DA LOKACINSA
KOMAI SHAKIYANCIN MUTUM AI DA MAGANINSA
NI DALIBI NE NA RAYUWA NA WA’AZTU
GASHI DUK NA KAKKABE NADAWO GIDAN RUBUTU
‘YANUWA MU DAUKI DARASI A RAYUWATA
KOMAI KYALEKYALI NA DUNIYA FA ZAMU BAR TA
KUNCE BANA IYA HAUSA HIP HOP WANNAN ME NENE
GASHI NAYI DALLA DALLA KOWA MA YA GANE”
Yana tafiya yana yin wakar gashi ya iya sosai kamar shi yayi ta.
Kanar a mafarki sai ya hango tafiyar NUSAIBA daga nesa tana kokarin nufato hanyar da yake kokarin ficewa daga, tun kafin ta karaso kusa da shi ya tabbatar ita ce, har yau din cikin duda take
“Ina zaki je ya fada?” cike da daukin son jin me zata bayar a matsayin amsa
Cen sai aka kira su, dalili da ya katse wannan labari ke nan da yake ba su
DR. ZAIN
[2/3, 4:59 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣1⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Do not think about the past_
_Accept the Present._
Think for the Future, and _face tomorrow with a sweet and beautiful smile._
*Shafin Masoya*
*YAKI DA RASHIN GASKIYA WHATSAPP GROPU*
***CI GABA***
*Cigaban labarin ‘yan gudun hijira*
Shiru har zuwa maraice, har dare ya soma ba labarin kira daga shugaba, dlili da ya sa suka tafi sabgoginsu kenan, shi ya baiwa Sajida damar zagayawa sosai a sansanin domin shaidawa idanuwanta halayya da yanayi da mazauna wurin suke. Ba shakka taga abubuwa da dama wadanda suka sanya imaninta ya karo, tausayinta ya karu, haka tsammaninta da kuma jajircewarta da idanuwaanta suka kara budewa. Yanayi da ta ga wasu mata musamman hankalinta ya tashi, yadda gaba daya an kawo su an jibge, akwai abinci sosai, har asibiti akwai cikin wannan sansanin, amma rayuwarka ba za ta tafi yadda kake so ba, shuwagabannin sun fake da musulunci suna zaluntar mazauna wurin, idan ka motsa a kafurta ka, a kasheka kai tsaye, idan ma me ka yi, sai a ce shari’ah ko haddi za a tsayar a kanka. Kuma abin haushi da yawa daga cikin wadannan mabiya boko haram din ba musulmai ba ne, ta fahimci haka, lura da da yawa daga cikinsu ba sa sallah, wasu kai tsaye zaka ga cross a wuyansu. Wannan lamarin ya bata mamaki matuka.
Cen bayan isha sai ga dan aiken shugaba, cewar yana neman su Sajida, da yake su kadai aka kawo a ranar.
Suka gabata a gabansa, kamar dalibai sun zo diban karatu a gaban malami. Ya fara musu jawabi irin nasa: “nan da kuka zo, kun fito ne daga biladi kufrin ya zuwa biladi Islam, inda za a baku kulawa karkashin kaantarwar addinin musulunci wanda shi kadai ne mafita gareku. Cen inda kuke, yahudawa sun cakuda kafircinsu da al’adunku kun zama ‘yan bidi’ah kuma mushrikai fasikai, nan zamu musuluntar da ku, mu shayar da ku romon musulunci zalla domin gobe kiyama ku samu rabo……..”
Bayan ya kammala jawabinsa, sai ya ce “idan da mai tambaya zai iya yii ko guntun jawabi”
Dama tun fara zancensa, bakinta yake rawa tanaso ta furta zance. Sai ta mikar da hannunta, alama tanaso tayi magana. Aka bata dama, sai ta mike.
“kace zaku bamu kulawa karkashin karantarwar musulunci, naga mu duka ba wacce take muharrama a gareku, me yasa kuka killace mu, ko shima wata karanatrwa ce ta musulunci da bamusan da ita ba? Iya namu karatu, kisa kaba’ira ce da ubangiji ma ba ya yafe maka gaba daya idan ba kaffara ka yi ba ko masu hakki suka yafe, ku naga kun mayar da kisa kamar numfashi, ko kunyi shi ba kwa damuwa, me hakan yake nufi? Dazu da nake zagaywa, naga mayakanku da dama cikin tantuna tareda mata da aka kamo wasu wurare da alama zamntakewa suke kamar ma’aurata, wannan kuma musulunci ne? abubuwa da dama misali wayar salula kalar tufafi kai har kalar abinci da kuke ci, duka na yaudawa ne da kuka ce karatun da suka zo da shi haramun ne, shi haramun din ba ya aiki ne a kanku? Wadnda wannan hare-hare naku ke shafa, galibi mata ne da yara kanani sai kuma wasu da gaba daya a rayuwarsu ba sa boko, su mnayan masu bokon sunada tsaro wasunsu ma kamar tare kuke da su, idan da gaske boko kuke yaka, me yasa hakan ke faruwa/ dama shi jihadi akan yi shi ne ta hanyar kama yara da mata azo a buya tsakiyar jeji……..”
Kafin ta karasa wani ya shareta da mari, har sai da yatsunsa suka kwanta a kumatunta, nan Bilkisu ta fashe da kuka. Wanda suke tareda shi tuni ya sha jinin jikinsa, ya fara bari, domin ya fara shinshino mutuwa kusa.
Ya sake sa kafa ya shureta, ta fadi a gigice, ganin haka, sai shugabansu ya tada hannu alamar ya dakata. Ita kuwa ba ta damu ba ta waigo ta kalle shi, ta ce. “ni fa ba daren da jemage bai gani ba, idan aka cire daren mutuwarsa, kuma aka yi sa’a ko yanzu kasuwa ta waste dan koli ya dade da cin hajarsa, ba dukana ya dace kayi ba, zai fi kyau idan ka bani hujjoji ta hanyar amsa tambayoyina, domin hakan da ka yi, ya nuna bakada amsa ga tambaya ko daya daga cikin tambayoyi da na yi maku”
Shugaban sai ya karbe zancen, “tun farko mun sanar da ku mu zamu kula da ku karkashin karantarwar addini. Da kike zancen jihadi, ai yaki dan zamba ne, dole sai ka hada da dabaru idan kanaso ka cinma burinka, haka lokaci na zuwa da zamu fito gaba da gaba da ‘yan bokon. Kan mata kuwa, ai ba lalata muke yi da su ba, aurensu muke yi, dama mata biyu nake da, yau dinnan za aurar min da ke na cika ta uku”
Ya yi alama da hannunsa cewa akira jama’a domin su shaida auren. Cikin mintuna kadan aka tara jama’a.
Tayi murmushi, dalili da yasa shugaban nasu ya tabayeta kenan, “ko kinada abin fada”
Ta ce “sosai kuwa ni keda abin fada”
“ki gaggauta kinga jama’a sun taru”
“a karatu da mukayi a Qurani, idan mace mijinta ya rasu za ta yi idda ne na tsawon wata hudu da kwana goma (Bakara aya ta 234) da cewar _kuma wadanda suke mutuwa daga gare ku suna barin matan aure (ma’ana wadda mijinta ya mutu ya barta) matan suna jinkiri da kansu wata hudu da kwana goma……._
Haka ya zo a Bukhari hadisi mai lamba 1280 da mai lamba 1281 da kuma lamba 5334 ya zo a Muslim 59/1486 ya zo a Abu Dawuda 2299 a Tirmizhi 1195 a Nasa’I 3533 cewa iddar mace tsawon wata hudu ne da kwana goma idan mijinta mutuwa ya yi yaa barta.
Haka akwai wannan zancen har wayau a Bukhari 313 da kuma 5341-5343 a Muslim 66/938 Abu Dawuda 2302 da 2303 Nasa’I 3536 ibn Majah 2087.
Ba nan kadai ba ka duba Bukhari 5336 da 5338 Muslim 1488 da 1489 Abu Dawuda 2299 Tirmizhi 1197 Nsa’I 3540-3543.
Da yake ku malami ne, bana bukatar na sanar da ku cewa haramun ne aure a kan idda.
Ya kwashe da wata dariyar keta, sai ya ce “ ai ba kan idda zamu aureki ba, wa ya gayamaki akwai idda a kanki, kar ki manta fa, ke ganimar yaki ce a wurinmu”
“ganima kuma?”
Ta fada cike da mamaki.
“haba malam, jiya ne fa cikin dare yaranka suka kamo mu, a lokacin da muke kokarin ganin munsami malaba, ba wanda ya gwabza yaki da mu, bare mu zama ganimar yaki, ku daina yin ta’awili kan zantukan ubangiji da ma’aikinsa, kawai domin ku biya bukatunku. Muna ciki gida aka zo aka kashe mijina gaban idanuwana”
“tau kingani, ki ganimarmu ce, kika gudu, ga shi kin dawo hannunmu”, ya fada yana kallon taron jaama’a da suka zo shaidar wannan mugun aure.
Nan ya wakilta wani ya zama waliyyi gareta, aka yi nema aka bayar, aka yanka sadaki dubu, dari, ya biya nan take, aka yi khduba aka daura aure. Duk a gaban jama’a, ita dai Sajida gaskiya ta yi mata yawa, ta kasa furta ko oho. A ranta tana mai cewa, “wallahi da na bari ya yi lalata da ni gara naa rasa rayuwata, wannan ai gara yahudanci da kasan fyade ne za a maka, da wannan zina da sunan daurin aure”
Mutane suka watse, wasu mata suka ja amarya har tantin da ango yake zama, Bilkisu sai kallon mahaifiyarta take, inda Amisha ita ma kllon take baa tareda ta fahimci me ke faruwa ba.
Shigowarsa dakin ta sa matan gaba daya suka tashi suka fita, aka bar bilkisu sai Amisha, ya ce “tau sai ki salami yaran naki ko”
Ta ce. “yaraa ba inda za su je, me kake nufi ne, wannan ba fa aure ba ne, hanya ce ta zina, ina ka taba ganin an yi aure haka? Sai kace auren Aladu?”
Ya harzuka, amma sai ya hadiye abinda ke ransa, ganin haka sai Bilkisu ta fita waje, amma sai ta tsaya kusa da tantin tana sharar kuka. Amisha kuwa sai taa kara matsewa a jikin mahaifiyarta ganin yadda mahaifiyar ta fara daukan zafi, ta fahimci cutar da ita ake so ayi.
Gaanin haka ya zaburo, ya rarumi Amisha daga jikinta, da kyar ya kwace ta ya wurgar da ita, har sai da sautin buguwa da kanta ya yi a kasa ya girgiza mahaifiyarta, inda ta doshi wurin da take a guje cikin matsanancin tashin hankali.
09039951083
DR. ZAIN
[2/3, 4:59 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣2⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_We waste time looking for the perfect lover, instead of creating the perfect love._
*Shafin Masoya*
*AMEESHA*
*HALIMA MUHAMMAD*
***CI GABA***
Tana zubar hawaye ta rungumota da zinmar ta rarrasheta, amma sai ba ta ji ta koksa ba, ko motsi batayi ba, sai jini da ya bata mata jiki wanda ke fita daga inda kanta ya yi mummunar fashewa. Ganin haka hankalinta ya kara tashi. Ta sake fashewa da wani sabon kuka, wanda ya sa gaba daya ta ji kamar ba a jikinta take ba, idanuwanta suka rufe, zuciyarta ta fara zafi. Shi kuwa gogannaka, sai cewa yake, “ki ajiyeta kizo, kinsan hadisi yana fadar duk mace da mijinta ya kirata ta ki ta zo, ya kwana yana fushi da ita, mala’iku zasu kwana suna tsinemata” gaba daya jin surutunsa take kamar ana kara rura wutar da ke tafasa a zuciyarta. Ta juwo da karfi ta yi kukan kura tayo cikinsa, ta kama wuyansa. Ya tunkudeta ta fadi yana fadar “kinada hankali kuwa?” Ta sake mayar da kallonta inda Amisha ke kwance a mace,zuciyarta ta sake rufewa, ta sake kawo masa wawa, ya zame ya kaimata naushi a baya, ta fadi, ta sake tasowa tayo cikinsa, ya sake kai mata naushi a fuska, har ya fasa mata baki, amma ko a jikinta, miki da tunanin rasa yarta ya makautar da ita. Sai yowa take yi cikinsa, shikuwa yana kaimata duka, a duk lokacin da ya daketa, ai ta fadi gaba daya fuskarta ta kumbura tana fitar da jini, amma ko kadan jikinta bai mutu ba, har sai da ya gaji da kansa, da ta kam shi, a wuya sai shure-shure yake yana neman mafita, amma ina ba zai iya kwatar kansa ba hannun Sajida saboda haka kirarta take kamar basamudiya ga tsayi ga kaurin jiki. Ta shake shi har sai da ya mutu, ta wurgar da gawarsa cen gefe. Ta yo gefen ‘yarta ta cigaba da kuka na wani lokaci mai tsawo.
Cen tana kuka ta tuna, matsawar safiya ta waye aka tarar da danyen aikin da ta aikata, tabbas ita da ‘yarta sai dai buzunsu, domin kuwa kashe su za ayi, sai ta leko kofar tantin, ta yi sa’a kuwa Bilkisu na zaune kusa tana faman zabga kuka, ta soke kanta a tsakanin kafafuwanta. Ganin haka sai mahaifiyarta ta je kusa da ita ta dafa ta, cikin firgita ta waigo. Ganin mahaifiyarta ce, sai ta rungumeta cikin sabon kuka.
Ta ce da ita; “ajiye kukan, abinda ke gabanmu yanzu shi ne, muyi kokari mu nemi ta inda zamu fita daga wannan wurin, domin na kashe shugabansu” cike da tsoro ta kalli mahaifiyarta da ke magana jikinta na rawa. “ina Amisha” zancen da ya fara fitowa daga bakinta kenan. Bataan lokacin da ta sake fashewa da wani sabon kuka ba, tana so ta gayamata me ya faru da kanwarta amma kuka ya hana, ganin haka, Bilkiu ta mike zunbur ta shiga tantin, ai ko sai ta fadi kasancewar ta kasa rike kafafuwanta, nan ta fara kuka tamkar an baiwa yaro alawa an kwace, har da ajiyar zuciya. Saai jijjigata take, a tunaninta zata farka, amma ina.
Cen Sajida ta shigo cikin tantin ta fara rarrasarta tana fadar “ki taso mu tafi kafin azzalumannnan su Ankara da ta’asar da nayi, kar gudunmu da kwnakin da mukayi muna shan wuya a jeji su tashi a banza, kinsan matsawar wadannan mutanen suka fahimci me ya faru, sai dai gawarmu”
Budar bakinta, ta ce, “gaskiya umma bazan iya barin gawar Amisha a nan ba”
“ka jimin karanbanin banza, kinaso ki gayami cewa kin fi ni son ta ne? akwai abubuwa da ke faruwa wadanda mutum ba yadda ya iya dole ya rungume su yadda suka zo, wannan kaddara ce ba mu muka tsara ko muka zabi rayuwarmu ta zo a haka ba, tsarin ubangiji ne kuma shi ya fi mu sanin dalili da ya sa ya aikata hakan akanmu, inada tabbaci ubangiji ya mana tanadi da zamu yi farin ciki da shi. Ki zo mu tafi, karshen rayuwarta kenan, babu wani