Showing 45001 words to 47716 words out of 47716 words

Chapter 16 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt

shi, ta ce “malam Sani ka ce sunanka ko? Gaskiya ka bani kunya, ai shi taimako idan zaka yi baka tunanin sharrin shi wanda zaka taimaka, annabi cewa fa ya yi, muyi wa muminai zaton alkhairi, ko don tsufan wannan bawan Allah ai zaku taimaka masa, duka saura kwana nawa ya bar muku duniyarku, zancen matanku, wannan ai duk ya isa ya yi jikoki da ku. Ba shakka baka shiga ibtila’I da muka shiga ba, domin da ka shiga kuwa, da da gudu ka amshi wannan aikin ladan. Amma ai gari da yawa maye ba ya cin kansa. Ku zo mu tafi” ta fada dai-dai lokacin da take jan hannun Bilkisu a fussace.






Tsoho na daga bayansu suna tafiya cikin sauri, cen tsohon ya ce “yarnan dakata, kije zuwa in da zaki tafi, ni zan iya kula da kaina, duk abinda ya dace zan aikata ku tafi kawai kada na batamaku tafiya”






Ta kalleshi cikin bacin rai kamar zata shiga jikinsa ta dake shi.






“baba bari na tambaye ka, wa ka sani a garinnan?”




“yata ba wan da na sani”






“shi ne kake so muyi kisan kai ta hanyar barinka kai kadai, ai ko da ba mota ta hadamu ba, kai ka isa ka haife ni sosai, kana ganin ba hakki ne a kaina na taimake ba, annabi ya fada yana daga cikin kyawawa ayuka a girmama mai furfura, gashi baba kanka duka farin gashi ne, idan kuma lada ce baka so mu samu sai ka sanar da mu domin mu tafiya”






“ba haka nake nufi ba yata, kawai dai naga wahala ta maku yawa, kuma naji kina fadar har garin kalgo zaku tafi.”






“kar ka damu baba, mudai gama da matsalarka. Garin kalgo duka minti nawa ne daga nan Birnin Kebbi”






Suka ci gaba da tafiya har suka karaso bakin titi.








Suka tari keke napep suka hau, ta ce ya kai su government house. Ya ajiye su a in da ake parkin motoci ta waje, ta taka ya zuwa gate din gidan, in da ta yi kicibis da masu tsaron kofar, kama da ‘yan sanda sai sojoji da kuma civil defence. “me ke tafe da ku?” daya daga cikin masu tsaron kofar ya fada, in da sauran suka kora musu na mujiya, ai kallon su suke yi kasa da sama. Ta kwashe labarinsu ta gaya musu. Cikin yi musu kallon uku saura kwata, daya daga cikin masu tsaron kofar ya ce, “gwamna ba ya nan ku tafi” “tau don Allah ina zamu sami mai kula da walwalar al’umma?” “shima ba ya nan, ku tafi aka ce” “malam ya da haka kake wani korarmu kamar wadanda suka zo bara? Hakkinmu ne fa muka zo mu taimaka su saukar amma kake mana haka?” “bara wa ya sani ko barar kuka zo, ke wallahi ko kubar kofarnan ko rayuwarku ta baci”








Ta yunkura ta yi magana, tsoho ya ja hannunta ya ce “yata zo mu je”






Suka tafi, suna tafiya tana mita da fada, har suka kawo Diamond bank suna tafiya tsoho ke gayamata.






‘yata ai wannan kadan kika gani, halin masu gadi kenan, sai azo neman gwamna da magana mai muhinmanci amma wadannnan su hana, suna zaluntar gwamnati suna zaluntar talakawa suna zaluntar kawunansu.”




Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina zasu nufa ba. Daf da bakin first bank a round about ta central mosque suka hau keke napep. Bilkisu dai bata ce komai ba. Suka nufaci dayan sansanin “*YAN GUDUN HIJIRA* da ke bayan Oando. Nan ma aka gaya musu kamar yadda aka gaya musu a malala, dalili kenan da ya sa suka nemi wuri suka zauna domin ganin ya ya dace su bullowa lamarin. Gata ta iso jaharsu ta dauka komai zai saitu, amma wankin hula na so ya kai ta dare. Suna cikin zantawa suka jiwo kiran sallar magariba.








Suka tafi a massallaci da ke kusa, tsoho ya shiga masallaci ya yi sallah, in da suka tsaya daga waje suka yi sallah. Daga kammala sallah tsoho ya tarar da su a bakin masallacin, suka ci gaba da tafiya, har suka karaso kan titi da ke hannun riga da sabuwar tasha. Suka jira abin hawa, basu samu ba, sai suka ci gaba da tafiya har suka karaso kan babban gate na sabuwar kasuwa ta gaba, in da gobara ta yi barna. Duka suna tafiya ne, suna neman mafita ta hanyar tattauna shawarwari. Daga karshe suka yanke shawarar zasu tafi da shi a unguwar badariya su nema masa in da zai zauna, da suka karaso unguwar badariya a keke napep aka saukar da su dai-dai ‘yar kassuwar badariya, suka nemi gidan mai unguwa aka nuna masu, suka tafi suka yi magana da shi suka kwashe labarinsu suka sanar da shi, ya dauki alkawarin zai kula da tsoho da ikon Allah. Da akayi isha suka yi sallama da maigari ita da Bilkisu suka nufaci garin kalgo, bayna ta kawo kudi har dubu ashirin ta bai wa tsoho, ta ce ya tanka jalli da su ya sami sana’a ya dinga yi da zai dinga kula da kansa.






Badariya gari ne da ke da kafaffen tarihi, amma a halin yanzu unguwa ce a cikin Birnin Kebbi, kasancewar gine-gine sun tarar da su. Mutane ne da a zamanin baya sun fi shahara da farauta da noma, Hausawa ne, amma sune surke da Fulani da Zabarmawa. Wan da ya sa suka zama kamar tanti na kasuwanci da kuma harkar gini saboda hadewarsu da Birnin Kebbi.






Kai tsaye a tashar da ke Haliru Abdu keke napep ta ajiyesu, suka tari mota da zata kai su Kalgo. Cikin mintuna kadan motarsu ta tashi.







08034840276


DR. ZAIN
[2/24, 7:48 PM] Dr. Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾






_last page_






3⃣5⃣














Na








*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_










dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_










® *PEN WRITERS ASSOCIATION*










```QUOTE OF THE DAY```










_Mulki da kasaita ubangijinmu shi ya bada_














*Shafin Masoya*








Yan Gudun Hijira Fans
MATA TUBALIN AL'UMMA




***CI GABA***












Daga saukarsu daga keke napep a farkon titi daga round in da zai sadaka da babban filin wasan kwallo na Haliru Abdu, wanda ya fi shaahara da Haliru Abdu mini stadium Birnin Kebbi, in da ta fuskarsa ne ake samun motoci da zasu dauki mutum ya zuwa bunza, kalgo jega minna kamba da dai sauran gruruwa. Nan wata mota ta tsaya gabanssu tun kafin su karasa in da motoci ke taruwa. Suka yi sauri suka shiga motar, kamar yadda mai motar ya umarta, a cwarsa doka ce daukar mutum kan hanya, amma su aikaatawa suke ba ruwansu. Daga shigarta ta tambaya, nawa ne kudin motar, ya ce da su naira dari-dari zasu biya. Ya buga mota suka ci gaba da tafiya. Daga ita sai Bilkisu a motar, sai wani dan saurayi da ya ce shi a Federal University Birnin Kebbi za a ajiye shi FUBK. A kan hanya ya dauki wasu da zasu tafi kalgo, har dai motarsa ta cika, mutum biyu a gaba sai mutum hudu a baya.




Sai fira ake yi cikin motar, in da Sajida ba abinda ke ranta irin tunanin halin da zata trar da gida, anya kuwa ma zasu shidata? Batasan lokacin da hawaye suka fara kwaranya daga idnuwanta ba, sai ji kwai tayi Bilkisu na kokarin sharemata. Dalili ke nan da ya mayar da hankalin wata mata da ke kusa da su ‘yar kimanain shekar 29, amma zaka yi zaton ta haura shekaru arba’in kan galabaita da shan wahala. Budar bakin wnnan matar ta kalli sajida ta ce, “bauyar Allah, komai fa ya yi zafi, to maganinsa Allah sarki, kin ganni nan, ba musiba da ban fada ba, babu tashin hankali da ban gani ba a rayuwa, amma dole na jingine komai gefe, na kurawa sarautar ubangiji idanu na yi wa kaina fada domin na gina kaina da kaina. Ba abin da kuka zai haifar maki, face mutuwar zuciya” cikin sanyin jiki Sajida ta juyo ta kalli wannan matar da take fara sol duk da ba kyakkyawa ba ce, sai ta kada baki ta ce, “ke kuwa boyar Allah wacce musiba kika shiga haka? Ki sanar da mu wata kila mu amfana muma mu sami izina daga labarinki.”




*LABARIN SHAMSIYYA*




Bayan ta nisa, sai ta soma.




“Sunana Shamsiyya, ni asalin ‘Yar garin Wamakko ce, da ke cikin jahar sokoto, mahaifina da mahaifiyata duka haifaffun sokoto ne, amma yanayin aiki yasa a garin Tambuwal aka haife ni, nan nayi karatu na primary da secondary, haka jami’a a Usman Danfodio University Sokoto nayi karatun diploma. Bansami aiki ba, kasancear yanayi na kasa idan ba wanda ya tsayamaka, kai talaka sai dai ka yi hakuri, duk da kyawun takarduna kuwa, a haka na sha yawun neman aiki ba dare ba rana, har na gaji dole na saduda. Kan haka mahaifina ya sakani a gaba akan tilas sai na fiddo da mijin aure, ni kuwa ba mai tara samari ba ce, wanda nake so kuma na bincike shi bai shirya ba, kan haka na sha tsangwama da barazan daga mahaifana kan lallai zasu aurar da ni ga duk wanda suka ga dama, na sha kuka har idnuwana suka kumbura, har kuka ya zama tamkar wani bangare na rayuwata. Haka na ci gaba da kokartawa na gani ko zan iya taimkawa Jamilu saurayina domin mu samu mu yi aure, amma abin ya ci tura, kasancewar shima kamar ni baisami aiki ba, sai ya yi lebaranci kafin ya sami ya kula da mahaifansa da kannensa guda uku. Wannan ya sa na shiga damuwa matuka. Kwanaki da mahaifana suka dibamin akan lallai na fidda miji, suka cika, hakan ta sa suka sake zaunar da ni suka bincike ni kan zancen, na kasa basu magana da zata gamsar da su, hakan ta kara tunzurar da su, suka ce tabbas zasu hadani da wani wai Alhaji Rabi’u da ke nan Tambuwal, tsoho ne da zai haura shekaru saba’in, amma mai kudi ne sosai, ni kuwa a lokacin shekaruna 25. Na ci kuka sosai, tun da safe na sami Jamilu, na sanar da shi abinda ke faruwa. Ranar kamar ya yi hauka, ya rasa me ke yi masa dadi, a haka ya rarrasheni ya nuna na kwantar da hankalina, bamu isa mu canja kaddarar Allah ba, shi dai yanada tabbaacin cewa yana ji a jikinsa, shi zai aure ni. Zantuknsa sun kwantar mani da hankali, amma sun kasa fahimtar da ni cewa gaskiya yake fada, domin ni sai na dauka cewa nafi son shi ne, hakan ta sa na koma gid sai kuka nake yi ba ko kokotawa. Sai na share kwana biyu ba tareda na sakawa cikina komai ba, duk na yi baki na rame. Kwatsam ina cikin daki ina sharbar kuka kamar kullum, ga mahaifina ya shigo dakin da nake, shigowarsa, ya wurgomin katuka na gayyatar daurin aure ya fice abin sa, na yi maza na dauko, katukan sun kai kimanin dari biyu. Dubawa da zan yi sai nag a anrubuta. ‘Iyalan gidan Malam Kasimu tsoho da na Malam Sani Kahutu na gayyatar mal,malama….zuwa daurin auren ‘ya’yansu…..’”ai sunana da na hango wai za a dura aurena da Alhaji Rabi’u, ya sa cikina ya murda gaba daya yawun bakina ya tsinke, abin mamaki saura kwana uku a daura auren namu. Hakan ta sa na tashi a gigice, na yo garka, na tarar da Jamilu na sanar da shi, cikin kidimewa ya rushe da kuka, ya gayamin ai ya dade da fara ginin da zai sakani, kum ya sayar da dabbobinsa da dama har ya hada da yawa daga lefe da zai aiko gidanmu, duk gudun kar wannan ta faru. Nan muka zanta kan ina zamu sami mafita, na nunamasa mafita daya ce, kawai yazo mu gudu, in da ya nunamin illar aikata hakan, ya nuna kamar bijirewa umarnin iyayenmu ne idan hakan ta faru, ya ce na ajiye hankalina wuri daya mafita bazata gagara ba. Na faufaye, har na fara gayamasa maganganu marasa dadi, ina fadar dama nasan ni ke sonsa ba shi ke sona ba, duk yadda zai kwantarmin da hankali ya yi, amma na ki na saurare shi. Karshen ganina da shi kenan, domin da asubar fari na saci kudin mahaifiyata nayo kudin mota da su na zo garin Jega, na jima a nan Jega ina harkar sayar da abinci ina tara kudi, sai daga baya na dawo nan Kalgo, in da kasuwanci na ya girma, bayan sana’ar abinci har atmafa ina sayarwa da sauran kayayyaki”




*CI GABAN LABARIN ‘YAN GUDUN HIJIRA*






Nan Sajida ta nia, ta ce “kin taba tunanin wanne hali shi Jmilu yake ciki? Ba kya tsoron a yi tuninin shi ya boyeki har a cutar da shi? Kin yafe mahaifiyarki ne da ko sau daya baki koma garinku ba tsawon shekaru hudu? Allah ya kyauta” sajida ta fada, a dai dai lokacin da take cewa driver ya ajiye su a unguwar Tudun Tasha.






Aka ajiye su suka yiwa sauran fatan alkahiri su kuwa suka nufaci wasu mutane da ke zaune gefen titi ta hannun dama, bayan sun yi masu sallama, suka gaisa da su, sai Sajida take tambayarsu ko Allah yasa sun san unguwa da ake kira shiyar Huci. Inda wani saurayi ya nuna ya sani, haka ya yi musu bayani sosai, kyam tayi tana kallonsa, da ya fahimci ba in da suka sani, sai ya ce su biyo shi, haka yana gaba suna bayansa, har suka karaso a shiyar Huci, suka yi masa godiya ya koma, ita kuwa ta sake tambayar wasu bayin Allah kan gidansu, kasancewar garin ba babba ba ne, nan take aka nuna mata.






Gida ne da ba kyaure tare da shi, ginin na laka ne ta gaba, amma sauran katangar gidan duk da darni aka yi amfani aka zagaye shi, ba shakka ta dauki shekaru masu tsawo bata zo ba, amma fasalin gidansu bai canja mata ba, nan kawai ta fashe da kuka, ta rasa kukan me take yi, kukan bakin ciki na abubuwa da suka faru da ita, ko kukan dadi na ga shi ta dawo gida.






Suka kutsa kai sukayi sallama, yara kawai ke guje-guje a farfajiyar gidan da ya sha shara tsaf, a cen gefe kuwa wata tsohuwa ce zaune kan tabarma abinci kusan kala uku a gabanta, sai kokarin kiran jikokinta take kan su zo su ci abinci. Zumbur ta mike duk da jikinta na rawa, a haka ta tako da sauri, tana fadar “muryar wa nake ji haka? Sajida ke ce kuwa?” ta fada a daidai lokacin da ta rungumota tana kuka, ita ma sajidar ta fashe da kuka, ta kara rungume mahaifiyarta. “inna wannan wacece kuma?” “mahaifiyata ce” wannan ya sa kakar Bikisu ta saki sajida ta juwo ta rungume Bilkisu, cikin muryar kuka ta ce aje a kira mahaifinta.






Da ya shigo ta gabatar da Sajida gare shi, nan ya fara fashewa da kuka, yara da mata da ke gidan sunsan Sajida a labari, amma sai yau ubanguji ya nufa suka ganta. Nan ta kwashe duka abinda ya faru da ita ta gaya musu, mahaifanta suka bata hakuri, ta tambayi saurayinta, aka sanar da ita cewa, ya rasu da jimawa. Bayan ta yi kuka na wani lokaci aka nuna mata in da zata zauna ita da diyarta.






Kwana biyu da ta nutsu ta tambayi kalar sana’ar da ta fi ci aka sanar da ita, ta fara a hankali, ta kuma saka yarinyarta karatu a BICE da ke garin Birnin Kebbi domin ta ci gaba da karatunta.






Haka dai Sajida ta zama hamshakiyar ‘yar kasuwa mai kudi sosai cikin shekaru biyu in da da bisani ta auri wani danmajalisa da ke Aliero, bayan ta tura ‘yarta karatu jami’a domin ta karanci law.








Alhamdulillahi, nan wannan labarin ya tsaya. Littafina na gaba sunansa *KANGIN BAUTA* _KAFIRCIN TURAWAN YAMMA_ amma kafin na fara sakinsa zamu sake sakin *ARTABON SARAKAI*




VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.


AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.






We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors






We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.






AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.






Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.




08034840276
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login