Showing 30001 words to 33000 words out of 47716 words
Chapter 11 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
bakinta yana motsi. Bilkisu ta rarrafo ta kwanta a jikin mahaifiyarta, inda saurayi yake tsaye a kansu, duk da shima a jigace yake, ya tausaya musu matuka.
Budar bakinsa, ya ce, “yanzu me ye mafita?”
Sajida ta kalleshi, gaba daya hawaye sun jika fadaddar fuskarta, idanuwanta sun yi ja sun kumbura kan masifar kuka, gashin kanta gaba daya ya yi taushi kan azaba da zufa da ta jika shi, kafafuwanta kuwa burum-burum kan masifar kura. Ta ce, “kaga wannan? Kadan ke nan daga musibu da muka shiga cikin wannan *GUDUN HIJARA* da muka tsinci kawunanmu a ciki, yanzu zamu ci gaba da gudu ne, har ya zuwa inda ubangiji ya sada mu da mafita ko wata sabuwar jarabawar.”
Suka mike suka ci gaba da tafiya, har dare ya fara yi, ganin haka suka tsaya suka yi salloli da ake biyarsu, saidai suna tsakiyar rama sallolin sai ga ruwa un fara sauka, da suka kammala sallar sai suka nemi wuri domin su buya, kasancewar fallau jejin yake, dole suka hakura a karkashin sabara, ruwan a dukansu, sai cirar sanyi suke, amma a yada suka iya, suka sha kashin ruwan a sama da awa biyar kuma masu tsananin karfi. Da ruwan suka tsaya, duk da da barci a idanuwansu, haka suka cigaba da tafiya, da yake sun galabaita kuma sun jigata, ba sa iya gudu.
Ba tareda sanin ina za su nufa ba, sai tafiya suke ba abinda ke zukatansu irin yau su gan su sunn tarar da wani gari, amma kamar su debe tsammani, domin har safiyar Allah ta waye, ba gari ba alamrsa, dole suka ci gaba da tafiya a haka, suna tsoron su tsaya wadannan azzaluman su tarar da su, ga shi kuma yunwa sai dibarsu take, ita gajiya ba a ma maganarta domin yaddda suke jan kaffuwansu kadai a yayin tafiyarsu ya isa ya bayyana maka hakan. Ganin sun gaji sosai, kuma ga rana ta fara, zafi, ta kuma lura da yaran yunwa suke ji, sai suka ratse kan hanya, suka nemi wani katon dutse, suka zauna cikin kadarkonshi, suka nemi wuri suka gyara, yadda zasu sami kariya daga zafin rana ko saukar ruwan sama, ta hanyar amfani da itace da ciyawu. Sai ta umarce su da su zauna su huta, ita kuwa ta shiga jeji domin ta nemo musu abida za su ci.
Ba ta sami dawowa ba sai zuwa maraice, inda ta zo musu da bushiya kwara hudu, wadanda ta yi amfani da baki ta yanka, kasancewar ba abin yanka. Dama kafin ta dawo sun shiga jeji su debo itace, da idan Allah ya sa ta dawo da abin farauta sai a gasa.
Haka suka gyara inda za a gasa naman, suka tara itace masu girma guda hudu sai ciyawa mai dan yawa, suka kafa wasu itace masu dan tsayi guda biyu sai suka gilma wani ice kwaya daya, wanda a jikinsa suka dora duka bushiyar da suka gyara guda hudu. Aka samo duwatsu na kankara guda biyu, suka dinga bugasu har suka fitar da wuta, wacce ta kama ciyawar, suka ci gaba da hurawa har wutar ta kama sosai. Suka ci gaba da gyara wutar har naman ya gasu gaba daya, suna yi suna fira. Aka saukar da nama suka ci. Ganin dare ya fara, kuma ga shi suna jin kishi na ruwa, Sajida ta ci gaba da tafiya cikin kadarkon har ta tarar da inda ruwa suka taru sosai, ta sha, ta wanke jikinta, daga bisani, ta zo ta kai su suma suka sha, suka wanke jikinsu, ganin haka sai suka nemi wuri kusa da ruwan suka kafa ‘yar bukka.
Haka Sajida ta ci gaba da kulawa da su, tana kuma amfani da damar tana jan kunnuwansu musamman domin su fahimci juriya da yadda da kai su ne sinadarin kowacce rayuwa. Haka suka dauki sati daya a wurin, ganin ruwan sun fara raguwa, sai suka tattara nasu ya nasu suka ci gaba da wannan makauniyar tafiya, da basusan ina suka fuskanta ba.
A garin ‘yan boko Haram din kuwa, da awa 48 suka shude, shugaban ya ga wadanda ya tura basu dawo da Sajida ba, sai ya tura wasu, ya ce, ya basu umarnin su zo masa da su Sajida da kuma wadanda ya turan su biyar gaba daya, wannan karon ko a raye ko a mace.
*GARIN MAI DUGURI*
Aisha kuwa hankalinsu a tashe tun lokacin da suka ji cewa unguwar su Sajida sun kwana cikin tashin hankalin harin ‘yan boko Haram, hakan ya sa ta ajiye a ranta cewa za ta je domin ta ga wanne hali suke ciki. Safiya na wayewa, ta shiryawa Fateema kamar kullum, driver ya dauketa har zuwa unguwar su Bilkisu kamar yada aka saba, amma sai suka tarar da taro a unguwar, mutane sun rufe hanya kama daga masu zowa duba halin ‘yan’uwansu sai masu zowa ganin me ya faru, tun da uwar safiya. Ganin za ta iya makara zuwa makaranta, ta umarci driver da ya kaita makaranata, ta tabbata Bilkisu ba za ta yi fashin zuwa makaranta ba, suka isa makaranta, ana tsakiyar assembly amma hankalinta na kan gate na shigowa makaranta ko Allah zai sa ta kyalla ido ta hango Bilkisu, amma har aka gama aka sallamesu ba Bilkisu ba alamunta. Ana koyar da su a aji, amma sa hankalinta ba ya gun har malamai suka fahimta suka tambayeta, da tambayar ta yi yawa sai ta gaya musu damuwarta, su tausayamata ainun musamman da yake lbari ne da kusan kowa ya ji abinda ya faru.
Da aka tashi makaranta, ta zo ta sanarda mahaifiyarta cewa Bilkisu ba ta je makaranta ba, kuma ta tabbatar da lafiyarta kalau, ba za ta yi fashin zuwa makaranta ba. Dalili ke nan da ya kara tada hankalin mahaifiyarta. Suka shirya suka nufi unguwar su Bilkisu.
Da rana ne, hakan ta sa taro da suka tarar da safe bai kai wannan ba, domin wannan har yara kanani da mata kake gani, dalili da ya sa suka ajiye motarsu kenan nesa, suka taka ya zuwa gidan a kafa, sai kutsa jama’a suke yi su shiga wannan kutsu su fita wancen har suka karaso ta kofar gidan, suka samu suka shiga, abin mamaki, suka tarar ba kowa a gidan, suka fito suka tambayi wadanda suka tarar a bakin kofa labarin su Sajida, wani saurayi ya basu amsa da “ba wanda ya gansu tun jiya, illa dai shi Qasimu munsami gawarsa da aka yi wa kisan gilla ta hanyar yanka shi”. Nan take hawaye suka zubo mata, Fatima kuma ta kamkame mahaifiyarta a jiki, kamar wacce ake shirin kwacewa.
Cikin sanyin jiki suka dawo gida. Sai zullumi Aisha ke yi tana tuno irin wahala da Sajida ke sha da kuma irin jajircewarta, ta tabbata mace ce da za a amfana da ita, gashi yanzu ba wanda yasan duniyar da ta fada, ko boko haram sun tafi da ita, ta sake zubowa da sababbin hawaye a lokacin da ta tuna basira da hazakar Bilkisu da kuma burinta a rayuwa.
Kullum sai sun je unguwar suna neman wanda ya ji labarin su Sajida, amma shiru babu.
*JEJI*
Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina zasu ba, tun safe har zuwa dare, suka dan huta na wasu awanni kana suka ci gaba da tafiya cikin surkukin jeji mai dauke da hadaruruka da musibu.
DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣5⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_it a rayuwa tamkar alawa ce, dadinta ba ya dorewa_
*Shafin Masoya*
Kyautar Allah fans
***CI GABA***
Sai kara nutsawa suke yi cikin surkukin jeji, tun saurayi na nuna alamun kasawa, har shima tafiyar ta bi jikinsa, ba ya bukatar su tsaya hutawa. Wasu lokuta su sha kashin ruwa, wasu lokuta kuma zafin rana ya gasa su, su shiga wannan kwararon su fita wancen, a haka har suka dauki wajen kwanaki biyar suna kitar wannan jejin.
A bangaren ‘yan boko haram, wadanda aka turo su bi bayan wadanda aka aiko domin su kama su Sajida kuwa, suka ci gaba da dubawa har Allah ya sa suka tarar da ragowar hudun zaune a karkashin wani katon ice, suna tattaunawa kan yadda zasu bullowa wannan lamarin lura da lokacin da aka diba musu ya rigaya ya kare, kuma ga shi basu sami kamo su Sajida ba. Hango motoci da Babura, suka fahimci me ke faruwa, tabbas farautarsu aka turo. Sun rigaya sun san da cewa ba tausya musu za a yi ba, saboda haka suka yo cikinsu da zinmmar su yi fada da su, sukaa shiga dukansu. Ganin haka, wadanda suka zo a mota da Babura, suma suka mayar da farmakin, fada mai tsanani ya kaure tsakaninsu, inda suke kokarin kawowa juna sara da suka, idan wannan ya saro wannan sai wannan ya goce shima ya kai masa duka ko wawa ko sara har suka dauki lokaci mai tsawo suna fafatawa, sun jima juna rauni sosai, daga karshe suka sami kashe mutane hudun bayan suma sun kashe musu mutum uku.
Suka dauki gawarwakinsu suka bai wa wasu daga cikinsu, suka saka a mota suka umarce su da su kai wa shugabansu, inda su kuma sauran suka ci gaba da farautar su Sajida.
Daga isar su a garin nasu, suka jibge gawarwakinsu a tsakiyar filin da ake taruwa, nan take aka sanar da shugaban cewa wadanda ya tura sun dawo. Ya zo ya shaida aikin da suka gabatar. Ya jinjina musu, ya kuma kara jaddadawa mutanen da aka tara cewa, ba wanda y isa ya kubuta a hannunsa, kuma wannan shi ne karshen duk wanda zai saba umarninsa ko ya nemi ya ha’ince sa kamar yadda yake fada. Ya kara da cewa tabbas su Sajida ma za su shigo hannu, kuma zasu dandana daga mafi munin azaba kafin a raba su da rayukansu. Jawabansa, suka sanyaya jikin duk wanda ya halarci wurin, kama daga ma’aikatansa har su wadanda aka tsare a garin. A fusace ya koma tantinsa domin ya ci gaba da tsara wurare da zasu kai hari. Sauran jama’a suka ci gaba da sabgogin rayukansu.
Su Sajida kuwa suka ci gaba da tafiya, har kafafuwansu suka kumbura jikinsu ya jigata gabadaya yanayin jikinsu ya canja, amma sai tafiya suke hakan, ga masifar yunwa ga kishi na ruwa, wanda ta kai sai su dauki kwana biyu ba tareda sun hadu da abinda za su ci ba, ruwa ma sai idan sun yi sa’a ne an yi ruwan sama sai su samu su sha daga garesu, abinci kuma da kyar suke samun zomo ko bushiya su kama, wani lokacin kan rashin wuta danye suke cin nama gudun kar rayuwarsu ta salwanta.
Wata rana suna tafiya, da maraice, sai wani iska mai karfi ya taso, dalili kenan da ya sa suka nemi wurin fakewa karkashin wani katon ice, mai dauke da wani katon kogo, iskan sai kara karfi yake yi, kuma ga duhu na kara shigowa abinda ya yi sanadiyyar tashin hankalin Sajida ke nan, musamman ganin Bilkisu ta gaji sosai, kasancewar yau kwana biyu kenan suna tafiya ba tareda sun huta ba.
Suna zaune a gindin icen, duk da icen kato ne, amma a haka iskan ke wujijjiga shi kamar zai fado, suna zaune, sai suka ga hayaki na fitowa daga cikin kogon, sun lura da hakan ne a lokacin da suka fara jin wani masifaffen zafi na fitowa ta daga kawunansu, dubawa da zasu yi sai suka hango hayaki na fitowa daga kogon. Cikin tsoro suka tashi suka ja daga baya, amma kamar wadanda aka ba wa umarni sai suka tsaya suna kallon yadda hayakin ke fita, zafin sai karuwa yake yi, abinda ya fi basu mamaki shi ne, yadda wannan iskan bai shafi fitowar hayakin ba, sun yi zaton wuta ce ke kokarin fitowa ko kamawa a jikin icen.
Suna tsaye nesa da icen, sai suka ga wani katon maciji da girmansa ya ninka Sajida sau biyar ya fito daga kogon, ai ko fitowarsa zafin ya karu, a jikinsa launuka ne na shudi da ruwan dorawa da ja, ya wuce da sauri a saman iska. Wannan ne ya haddasa su duka suka fadi, kamar tunkudasu aka yi, kowannensu ya kasa magana ko motsi kan tashin hankali na ganin wannan shirgegen maciji da ko a mafarki ba wanda ya taba ganin irinsa a cikinsu.
Ya jima yana wucewa kan masifar tsawo, duk da ya wuce, zaka ga alamun launukan ta wurin, haka hayakin ya jima kafin ya bar fitowa.
Ai ko kuzarinsu na dawowa, suka ce kafa me naci bambaki ba, suka ranta a na kare, sai gudu suke suna kokarin waigowa domin su tabbatar da cewa ba biyar su yake yi ba, duk da gajiyar Bilkisu, ita ce gaba a gudu sai Sajida a bayanta. Sun dauki lokaci mai tsawo suna gudu, domin sune basu tsaya ba har sai da sanyin asuba ya fara sauka, suka sami wani kogo a jikin wani dutse suka shiga, sai haki suke yi kamar rayukansu zasu fita.
Sun jima suna zantawa kan wannan abin al’ajabi da suka gani. Kana suka rama salloli da ke kan su, suka sami wuri suka kwanta domin su rage gajiya da ke tattarre da su, tun da subahi suke barci har rana ta fadi ba su farka ba, kamar hadin baki, sai cen cikin dare, Sajida ta farka, ta fito daga kogon ta duba yanayinsa a waje, ta dan zagaya, inda ta ci karo da ramun wasu tsuntsaye, nan take ta ja daga baya, ta dawo ta tad yaranta, da suka wartsake, ta shaida musu abinda ta gani, cikin farin ciki suka biyo ta bayanta, ta nuna musu ramin, ta yi amfani da kara ta saka a ramin, fir! Tsuntsayen suka farka, jin motsin farkawarsu, su Bilkisu suka karaso ta kusan su, suka dinga kama duk tsuntsun da ya yi yunkurin guduwa, a haka har suka kama adadi mai yawa, suka dawo makwancinsu, suka fige, inda lokacin da suke aikin fiigar ita da mahaifiyarta, shi kuwa saurayin yana cen yana kokrin nemo itace da za a gasa wadannan tsuntsayen.
Da ya kawo suka hura wutar kamar kullum ta hanyar amfani da duwatsu, musamman da yake daren ranar ya zo da sanyi, sun ji dadin hura wutar sosai, dalili da ya sa kenan duk da sun kammala gashin sai da suka dade suna karo itace domin su duma jikinsu da wutar, har zuwa tsakiyar dare. Suna so su yi barci amma sun rigaya sun yi barci mai tsawo sosai, shi ne dalili da ya sa suka buge da fira mai tsawo. Inda idan wannan ya bayar da labari, wannan sai ya bayar da nasa, sai raha suke yi sun dariya tsakaninsu
Nan Sajida ta ce, “ku bari na baku labarin KARSHEN ZALUNCI labarin kawo karshen ta’addancin sarki RUSKINANU na littafin ARTABON SARAKAI mai KARAGAR TSAFI wanda ya mallaki maganin mutuwa KUWWATUL KITAAL.”
“Maganin mutuwa fa Inna? Hala akwai maganin mutuwa ne?”
“ba ki ji na ce mulkinsa ya zo karshe ba, shi ke nunamaki ita mutuwa ba ta da magani, wata hanya ce da duk ratsen mutum dole sai ya bi ta wurin, gata ba ruwanta da sarki ko talaka, batasan yaro ko babba ba, batasan namiji ko mace ba, batasan nagari ko dan banza ba, idan ta kira ka kuma ba wanda ya isa ya hanaka zuwa”
“shi wannan sarkin kuma waye shi?”
“kina nufin baki karanta labarin ARTABON SARAKAI ba, na ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN?”
“ban taba jin littafin ba”
“taff! Ashe kuwa jirgi ya bar ki tasha”
“inna tau me zai hana ki bamu labarin daga farko?”
“inda nake da niyyar baku, yafi dacewa da halin da muke ciki, zai kara muku karfin guiwa na sanin cewa uangiji bai manta da mu ba, yana sane da halin da muke ciki”
Nan saurayi ya kara gyara zama, sai ya nisa ya ce, “amma ba a wannan zamani aka yi wanann sarkin ba, tun daga sunansa da kuma aikin da naji ya yi, na mallakar maganin mutuwa?”
“sosai an yi shi ne sama da shekaru dubu goma, ya yi mulki na zalunci fiye da tunanin mutum, ga shi jarumi mai masifar karfi, ga tsafi ga mulki ga shi da ‘ya ZABZABATU mummuna amma ga masifar karfi da dabarun yaki, da bokansa AJAMALU da kaf a lokacin duniya ba kamar shi a tsafi. Ga rashin imani da rashin tausayi”
“zan so ko naji karshen wannan sarkin, RUSKINANU ne kika ce sunasa ko?” saurayi ya fada.
Sajida ta gyara zama sai ta fara.
DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣6⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_yanzu suka dora tasu tukunyar, tuni tamu ta tafasa_
*Shafin Masoya*
*YAN GUDUN HIJIRA FANS*
***CI GABA***
Dandano daga littafin *KARSHEN ZALUNCI*
Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah makadancin sarki, wanda ya bai wa musulunci girma da martaba a sama da duk wani addini, shi ya halicci komai da kowa kuma shi kadai ya dace a bautawa, gagara misali ne a lamuransa wanda buwayarsa ta zarce misali. Ina kara gode masa kan baiwa da ya bani, har na tsintsi kaina cikin dandazon marubuta masu rubuta abin da al’umma za ta amfana ko ta nishadantu, ina rokonsa da ya datar da ni da gidan aljannarsa Firdausi ameeen.
Salati nayo gun Muhammad (SAW) Bakuraishe jikan Abdul-Muddalibi dan Aminatu manzon gaskiya wanda kaunarsa ta mamaye zuciya, kuma tafiyarsa ba za mu ki binta ba, muna rokon ubangiji da ya sadamu da tozali da shi a yinin gobe kiyama a gun shan ruwan Alkhausara ya bamu mu sha da lallausan fararen hannayensa ameeen.
Tsira da aminci ubangiji ka dada gun iyalan gidansa, wadanda suke masoya a gare shi, tare da zaratan sahabbansa wadanda farin cikinsa shi ne nasu, wadanda suka bayar da rayukansu fansa gare shi, tare da duk wanda ya bi turbarsu ya zuwa ranar tsayuwa.
Ina mika godiya ga mahaifiyata wacce ko da wasa ba zan buda shafin godiya ba ba tare da na bata nata sakin layi ba, ita ce jigo da silar duk wani ci gaba nawu, ina