Showing 9001 words to 12000 words out of 47716 words
Chapter 4 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
rarrasarta da kuma kokarin dafe bakinta domin ta daina fidda sauti, SAJIDA kuwa sai faman kallon yaranta take yi, inda gogannaka ya fara fitsare wandonsa, cen sautin bindiga ya fara tashi, sai Taa! Taa! Kake ji ta ko’ina har sai ka rasa sanin daga ina sautin ke fitowa.
Cen suka jiwo an shigo gidansu, ai ko suka kara narkewa a juna, shi QASIMU tuni ya mutu daga inda yake a kwance, idanuwansa kadai ke motsi sai zuciyarsa da ke bugawa, amma sam hankalinsa ya fita daga gare shi kan tsoro da firgici. Suka shigo dakin nasu kai tsaye. ‘yan boko haram din su biyu ne, kowanne rike da bindiga AK47 rataye a wuya da wani mariki mai tsayi, a jikinsu duka kakin sojoji ne sai dai sun rufe kawunansu da rawani, haka sun rufe bakinsu, dalilin da ya sa ba zaka iya fayyace su ba ko da kuwa ka san su karti ne majiya karfi ainun, sai a kugun kowanne daga cikinsu, Bam ne sai wukake manya guda biyu, a kafadarsu kuwa harsashi ne a ake yi wa hadi da bindigar da suka dauko. Kallonsu kadai ya isa ya sakaa mutum ya kidime ya rasa ina zai dosa ya rasa me ke masa dadi.
Cikin murya ta firgitarwa suke tambayarsu, ina maigidanta, sai a lokacin suka lura ashe QASIMU tun shigowar wadannan ‘yan boko haram din ya shige cikin kwamacala ya rufe kansa da kayan da ke kusa, makyarkyata da yake yi kan tsoro ita ta ankarar da ‘yan boko haram din cewa fa da mutum a cikin kayan, wanda ya sa daya daga cikinsu ya shuri kayan, sai ga QASIMU ya fado tim har da kuwwa cikin rauni, ya kalle shi ya ce “shege maza na a jeji kai kana nan sai sharholiya kake yi da mata ko” ya fada dai dai lokacin da ya kai wa SAJIDA Kallo. “tuba nake ranka ya dade..” ya share shi da mari, ya ce “dan shegiya” ya iza keyarsa ya sake kai masa shuri da mari duk a lokaci daya. Nan SAJIDA ta kara matse yaranta a jikinta, sai zubar hawaye take yi.
Dan boko haram din ya juwo, ya ce “lallai yau dole mu dandana dadin da kake sha kai ma, matar nan taka za ka bamu muji dadi da ita, idan mun gama kuma za mu tafi da ita inda muke zama mu ci gaba daga inda muka tsaya. “haba yallabai, ai ba sai ka gayamin ba, wallahi ku tafi da ita na baku halak, ga diyarta nan ma idan ita bata ishe ku ba duka ku hada ku tafi da su, nidai ku yimin rai, kar ku taba lafiyata ko rayuwata”
Jin haka dan boko haram din ya juyo cike da mamaki ya kalli QASIMU ya sake kallon SAJIDA, sai ya ce da shi; “kai wanne irin lusari ne da ba ya kishin iyalinsa, duk inda muka je sai munsami mazaje na kokarin kare iyalansu daga fyade ko muzgunawa amma kai da kanka kake bayarda matarka, ba ka da kishi ne?” yallabai ai banga amfani yin jayayya inda baka da karfi ba, a ganina ai wauta ce” “ko kuma wauta ce ka kiyin yunkurin ceton matarka ba”
“don Allah kar ku ketamin da mutunci, ku tafi da ni na aminta, amma ku barmin yara na don Allah, kun fa ce musulunci kuke yi wa aiki,amma wannan aikin naku sam bai yi kama da na musulmi ba, ba aikin musulmi ba ne yin fyade ko satar matan mutane ba, hasali ma musulunci ya yi fada da wannan mummunar halayyar. Don Allah ku ceci rayuwar yara na”
Nan dan boko haram din ya shareta da mari ya ce “ke! Lallai wuyanki ya yi kauri”
Suka janyo QASIMU a gabansu suka dora wuka a wuyansa suka yanka, inda su kuwa suke kuka kamar rayukansu za su fita. Daga yanka shi suka nufato su SAJIDA, ganin sun banbare AMISHA daga jikinta, wani sabon karfi ya shigo ta, ta mike tsaye idanuwanta suka rufe, ta suri dayan dan boko haram din da tandara a kasa kaji Kumm! Kansa ya fado a kasa, sai jini ke fita ko motsawa bai yi ba ya mutu, ganin haka dayan ya yo cikinta, kafin ya karaso shima ta yi cikinsa suka fara kokawa, ya dauke ta ya buga a kasa, ganin haka BILKISU ta fita a guje ta dauko tabarya, ko da ta dawo yana kan mahaifiyarta yana kokarin cire mata tufafi, ta saita da kansa ta maka masa tabarya, kafin hankalinsa ya dawo ta sake maka masa, ya fadi, mahaifiyarta ta mike, ganin yana motsi ta amshi tabaryar ta ci gaba da maka masa, har sai da ya daina motsi. Ba shiri ta goya AMISHA ta ja hannun BILKISU suka fito a guje daga gidan, fitowarsu suka hango an tara jama’a nesa da su sai harba bindiga ake yi kowa ya kwakkwanta a kasa, dalilin da yasa suka sudada kenan a hankali suka hau hanyar jeji suka fara gudu ba kama hannun yaro.
Labarin zai fara a shafi na gaba
08034840276
DR. ZAIN
[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
1⃣1⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Do not think about the past_
_Accept the Present._
Think for the Future, and _face tomorrow with a sweet and beautiful smile._
*Shafin Masoya*
*YAN GUDUN HIJIRA FANS*
***CI GABA***
Sai gudu suke faman zubawa kamar wadanda kafafuwansu za su cire, a bayanta Amisha ce ta goyo, inda ta rike hannun Bilkisu da hannunta daya, sai faman zabga gudu suke yi, duk inda suka yi nisa da gudu sai su waigo suga ko ana biyar su ta baya. Sautin bamabamai kuwa da na bindiga su suke kara musu kaimi wurin gudu da ganin sun tserata da rayukansu. Sai gudu suke wani sa’in su fada rami kasancewar ba wuta kuma ba hasken wata, wani sa’in su gwaru da kafafuwansu da manyan duwarwatsu da ke kafe a cikin kasa. Amisha kuwa kuka ne kadai nata, gaba daya Sajida ta jike da zufa sharkaf kamar wacce aka zubawa ruwa a jiki, gashi kaffuwanta duka sun fashe sai zubar jini suke, amma a jikinta ba ko alamar gajiya ko nuna kasawa a haka ta ci gaba da gudun ceton rayukan yaranta da tata rayuwar. Bilkisu dole ta jure duk da ta gaji, amma gajiyar ba ta nuna a jikinta ba.
Su ne ba su tsaya ba, har sai da suka tabbatar da cewa sun daina jiyo sautuka da karar bamabamai da harbin bindiga. Sai haki suke kamar wadanda zuciyoyinsu za su fito daga makwancinsu. Suka tsaya cak a tsakiyar jeji, ta duba gabas da yamma kudu da arewa ba mutane ba alamun mutane, ta tada kanta sama, ta ga ko taurari babu, a kunnuwansu kuwa sautuka ne na kwarin jeji da ke fitowa daga nahiyoyi daban-daban da ramuka da suka cika jejin, danye batak ciyawa da ta kawata kasar jejin.
Ta kalli yaranta, kawai ta fashe da kuka, ganin haka sai Bilkisu ta rungumeta Amisha dai har yanzu faman kukan take, tun mahaifiyar na rarrasarta har ta gaji ta bar ta. Sai ta tada kanta ta ce; “ya ubangiji kana kallon hali da yanayi da muke ciki, munsan da cewa ba mantawa da mu ka yi ba, ya ubangiji ka kawo muna dauki, ka kalli yanayin wadannan marayu da nake tareda su ka yi jinkai gare mu” ta sake fashewa da kuka.
Nan suka ci gaba da tafiya cikin sunkurun jeji ba tare da sanin ina za su nufa ba. Sai ketan ciyawa suke, saboda tun shigowarsu jejin ba kan hanya suke ba, sun shigo ne a guje su kawai abinda ke gabansu shi ne su tserata da rayukansu. sai da suka tabbatar hankalinsu ya kwanta kafin suka sami karkashin wata itaciya ta dorawa suka zauna, dole ta cire hijabin da ke jikinta da tun lokacin da suka fara gudu yake a wuyanta, ta shimfidawa yaranta, bayan ta laluba ta tabbatar ba mugayen kwari a wurin, ita kuwa ta kishingida a jikin icen. A haka ta zama maigadin yaran, inda su kuwa suka bige da barci. A rayuwarta sai sake-sake kala-kala take yi.
A cikin gari kuwa, da ‘yan boko haram suka ga wadanda suka tura a gidan su Sajida ba su fito ba, sai aka tura wasu su uku domin su gaya musu cewa su fito an kammala operation za a wuce ne masauki, shigar su gidan, suka tarar da gawarwakin mutanensu biyu da gawar Qasimu, cike da mamaki suka tsaya kan gawarwakin, daga bisani suka tura dayansu ya sanar da shugaban tawagar, ya hadashi da wasu masu aikin daukar gawarwakin wadanda aka kashe, suka zo suka kwashi mutanensu suka fita. Da za su bar garin wasu saman motoci Hilux wasu kuwa kan Babura sai harba bindiga suke a sama suna kabbara wasu kuwa suna ihu. A haka har suka fita daga garin.
Haka jama’ar gari suka wayi gari cike da bakin ciki da zullumin abinda ya faru cikin dare, in da kowa idanuwansa sun yi jawur kamar wuta sanadiyyar rashin barci da kusan duk mazauna unguwannin da abin ya shafa ba su sami runtsawa ba.
Malamai kuwa tun kammala sallar subahin suka shiga yin nasihohi domin kokarin kwantarwa wadanda aka dauki yara ko mutanensu da hankali. Sai jiyo kara ka ke yi ta amsa kuwwa daga masallatai daban-daban.
‘yan jaridu kuwa sai kokarin neman labarai suke daga jama’ar da abin ya shafa.
Sajida kuwa har safiya ta waye ba ta rumtsa ba, sai gadin yaranta take yi, ko motsi ta ji sai ta tashi ta duba ko me ye tafe. Kasancewar ba ruwa, dole taimama ta yi, ta yi sallah. Duk da gajiyar gudu da rashin kwanciyar hankali, Bilkisu da Amisha suka farka a lokacin sallar subahin, kasancewar mahaifiyarsu ta saba musu da tashi a lokacin. Bayan sun iyar da sallah, suka tashi suka ci gaba da tafiya cikin jeji, da ba su san ina za su nufa ba. Kuma iya inda kallonsu ya tsaya, ba abinda suke hangowa sai shirgegen jeji da dimbin ciyawa kore kuma danye shar.
Ita ce a tsakiya, inda ta riko Amisha a hannun dama, ita kuwa Bilkisu tana daga gefenta na hagu. Sai tafiya suke ba mai cewa kowa uffan, tun suna tafiya cikin dungun safiya har rana ta fara ketowa har ta fara zafi duk tafiya suke yi, ba abinda suke haduwa da shi face, dimbin ciyawa sai yashi da manyan duwarwatsu da ke jibge cikin jejin. Cen da rana ta haura sosai kusa da tsakiya, sai Amisha ta fara neman abinci, cikin matsanancin kuka mai dauke da sauti mai karfi. Dalilin da ya sa dole mahaifiyarsu ta tsaya da tafiyar da suke yi. Ta duba gabas da yamma kudu da arewa, sama da kasa, ta ga ba abinci kuma ba mafitarsa a kusa da su, ta sunkuyar da kai hawaye suka fara rigangar fitowa suka jika gefen kumatunta. Ta tada kanta ta kalli yaranta duka biyun, nan take hawayen suka kara karfi wurin gangarowa. Ta fara dube-duben ina za ta sami wurin da ke da inuwa domin ta ajiye su. Cen ta hango icen kalgo ya yi girma sosai, sai ta ja hannun Amisha ta kaisu karkashin icen, ta cire hijabinta ta shimfida musu, ita kuwa ta shiga jeji domin ta nemo masu abinda za su ci. Bayan ta gaya musu cewar kar su kuskura su daga daga wurin.
Tana tafiya tana zubda hawaye na tunanin yanayi da ta baro yaranta a ciki, ta tsunduma cikin jeji tana neman abinda za ta kawowa yaranta, duk inda taga zugu na surkukin itace, sai ta je gun ta bincika ko za ta sami abinda za ta yanka ta kawowa yaranta. Amma har rana ta karkata daga tsakiya ba abinda ta samo.
Su Bilkisu kuwa sai faman hamma suke yi, Amisha tun tafiyar mahaifiyarta take kuka, shimfide a kirjin yayarta, inda take kokarin rarrasarta, amma abin ya ci tura. Hakan ya sa ita ma ta fara kukan saboda tausayaw kanwarta. Cen sun yi nisa cikin kukan da ba mai rarrasar wani, suka jiyo motsi da sautukan tafiya, kuma sautin sai kokarin dumfaro su yake yi. Cikin tashin hankali Bilkisu ta mike zumbur, tashin da za ta yi sai ta ga wani mutum da a shekaru zai haura arba’in, rike da kwari da baka, gaba daya jikinsa a hargitse, da alama ya kwashe kwanaki ba tareda ya yi wanka ba. Cikin rudewa ta suri kanwarta domin su gudu, sai ya yi mata alama da hannu cewa shi ba zai cutar da su ba. Sai ta tsaya. Ya karaso daf da su ya zauna. Ya yi numfashi mai tsayi bayan itama ta zauna sai ya ce; “Bauyar Allah ga ku yara kanani, me ya kawo ku wannan jejin mai matukar hadari?” Nan ta kwashe labarinsu ta gaya masa. Bayan ya sake ajiyar zuciya ya soma; “gaskiya ku tashi, akwai wani masauki da na killacewa irinku, muna tareda mutane sama da ashirin ni nake fita ina samo mana abinda za mu ci, kuma kunga idan kuna cikin jama’a hankalinku zai fi kwanciya, kai ga kuna a nan ku kadai” “ban ki ta taka ba, amma, mahaifiyarmu ta bamu umarni kan kar mu yarda mubar wurinnan har sai ta dawo” ya yi murmushi, ya ce tau shi kenan, bari na zauna na jira dawowar mahaifiyar taku” “su mutanen da za ka nemowa abinci fa?” “kar ki damu” ya fada cikin sakin fuska. Ya cire kayan farautarsa ya ajiye a gabansa, suka ci gaba da tattaunawa.
Cen sai ga Sajida ta dawo, gaba daya a jiggace, kafafuwanta burum-burum, hawaye kuwa kamar a yanzu suka fara zubowa, kasancewar duk yawon da ta yi, ba abinda ta samo, kuma ga shi lokacin har rana ta fara sanyi. Ganin yaranta tareda wani, hankalinta ya tashi, ta karaso wurin a guje, daga zowanta ta ce; “wa ye wannan kuma mamanne?” “wani bawan Allah ne Umma…” ta kwashe labarinsa ta gaya mata. Bayan ta yi ajiyar zuciya, suka gaisa. Sai ya nuna musu su tashi su karasa masaukinsu. Suka dugunzuma gaba daya ya zuwa masaukin, inda su duka ba abninda suka saka a cikunansu, sai rurin yunwa suke.
Ina za su je?
Me za su tarar?
Duka ku biyo ni a shafi na gaba.
DR. ZAIN
[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
1⃣2⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Don’t walk as if you rule the world…Walk as if you don’t care who the hell rules the world._
*Shafin Masoya*
MATA TUBALIN AL'UMMA
GIDAN BUKI
***CI GABA***
Tun daga nesa za ka fara jiwo sauti da wasannin yara kanani, inda hayaki ke kokarin tashi ya zuwa sararin samaniya. Filin wurin an gyara shi sosai duk da cewa a kewaye da shi ciyawu ne da manyan itace, tsakiyar a share yake kuma a tsabtace. Manyan mata su ne ke kokarin gyara wuta domin gasa abinda aka kamo ko dafa abinda aka samo na abinci, inda yara kanani maza da mata ke ta zagayar filin a guje da wasanni kala-kala. Duk da Amisha na dauke da yunwa kuma ga masifaffiyar gajiya, sai da ta murmusa, alamun ta ji ndain zowa wannan wurin. Ganin isowarsu, gaba daya jama’ar wurin suka yo cincirindo suka nufato su da sannu da zuwa, inda wata tsohuwa ta gabata ta ja hannun Sajida suka wuce ta kai ta wani daki da aka zagaye da itace, sai ciyawu da aka rufe itacen da su ta yadda za su ba da kariya daga dukan rana ko saukar ruwan sama. A cikin dakin kuwa ba komai face fako, alamun a kasa ake kwanciya. A ranta tana kwatanta rayuwarta ta gida da wannan dakin, sai ta yi murmushi ta kara godiya ga ubangiji ta ce a ranta; tabbas duk halin da mutum yake ciki idan ya kasa ya yi godiya ga ubangiji ya yi butulci. Nan ta tunanmin da wakar wani mawaki wai shi ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN wakar mai suna brighter star, inda yake cewa; _‘ko a bakin kura dole ne mu gode Allah, a gunsa kadai muke nema idan muka yi salla_…..” sai ta fito domin ta janyo yaranta. Cen ta hango su zaune cikin yara suna cin abinci, ita kuwa sai ga tsohuwa ta kawo mata nata abinci. Ta koma cikin dakin domin ta ci nata, da ta kammala ta fito aka bata ruwa ta sha. Sai ta hango wasu za su tafi debo ruwa. Budar bakinta ta ce; “dama da ruwa ne nan kusa da mu?” tsohuwa ta kalleta firgigi, ta ce; “ruwa akwai su amma ba kusa ba, ko za ki bi wadancen ne?” “e saosai, domin munada bukata da ruwan gaskiya”. Ta kira yaranta suka bi wadanda za su tafi diban ruwa a rafi.
Mata uku ne a gabansu kowacce rike da abin diban ruwa, wanda aka sassaka daga ice, sai ita da ta sako yaranta a gaba tsakaninta da matan uku, sai tafiya suke yi, matan na fira inda ita kuwa hankalinta gaba daya ba ya nan, ta shiege duniyar tunani tuni.
A ranta tana cewa; dama mutane zasu iya rayuwa a kungurumin jeji haka? Tabbas na yarada duk bakin da ubangijin ya tsaga ba zai hana shi abninci ba.
Haka suka ci gaba daa tafiya har suka karaso rafin, bayan sun dauki lokaci suna tafiya. Wuri ne da ya kawatu sosai da ruwa da ke gudanawa a guje, sai ‘yan duwarwatsu da ke kafe daga ciki ruwan wadanda mutum zai iya takawa domin ya zauna ya yi wasa da ruwan ko ya diba, ba wasu ciyawu a kusa da ruwan kasancewar a bakin kogin yashi ne mai dimbin yawa wanda shuka ba za ta iya rayuwa a kai ba. Kuma abinka da jejin Maiduguri mai masifar zafin rana (lol).
Ta koma daga gefe ita da yaranta domin su wanke jikinsu, kasancewar sun jima ba su sakawa jikinsun ruwa ba. Inda sauran matan ke kokarin dibar ruwa da za su koma da su domin amfanin jama’a.
Suka kammala dibar ruwa sai suka jira su domin su karasa wanke