Showing 6001 words to 9000 words out of 47716 words
Chapter 3 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
ya kina harkar yawa, wannan ba yi ba ne..” suna fada cikin maagagin maye. Ta ce “idan kai jahilin mahaukaci ne, bari na nunamaka ni mahaukaciya ce da ko lasisi banida, in ba jahilci ba, iyalinka wai za ka ce wani katon banza ya zo ya kwanta su hada jiki a shimfida daya, shaye-shaye hauka ne hala? Ku kuma imbanda jahilci da hauka da rainin hankali wai har ku biye wa wannan tsarin saboda tsabar lalacewa, ai ko a yahudawa ba za a sami masu irin wannan aikin ba…” su duka hudu sai dukansu ruwan sama ke yi, ita kuwa sai faman zuba take yi, tana fadan tana kara jin haushin abin, cen QASIMU ya kada baki yace, har yanzu dai cikin mayen yake, “ke nan gidana ne ni keda ikon in tsara duk yadda na so ba wata shegiya da ta isa ta hana ni, da zan gina gidan, Naira nawa kika bani?” Ya fara zarar belt daga kugunsa. Wasu hawaye suka fara kwaranyomata, ta rasa hawayen me ye, na zama mijinta jahili, mahaukaci, marar kishi, lusari, wawa, dakiki ko me? Ta kalle shi ido cikin ido ta ce “QASIMU wallahi bari in gaya maka, kalle ni da kyau, zan iya daukar irinka biyu ba tareda na gaji ba” ya kalleta ya tabbatar ko a jeji suka hadu ba abinda zai iya yi mata. “ko ka dawo cikin hayyacinka ko in illtaka da wannan tabaryar, ku kuma ku fita gidannan tun kuna kalluwa ko in muku raunin da har makiyanku sai sun tausaya maku” jin haka suka kwashi kunyarsu sumu-sumu suka nufi waje cikin ruwan sama da iska, sa’arsu daya iskan ba karfi. Ya juyo ya kalleta sai haki take kamar wacce ake yi wa kidan tauri a ka, gaba daya ya tsorata domin bai taba ganin ta shiga yanayi irin wannan ba, ta kalle shi ta ce. “idan ka ga dama ka iya shigowa, idan kuma abokaninka za ka bi ga hanya cen” ya dubi ruwannan kara karfi kawai suke yi, ya nufi daki, sai makyrakyatar sanyi yake yi, ta ajiye tabarayar ita ma ta nufi dakin a fusace.
Ta tarar da yaranta suna cikin damuwa, ta gyara musu inda za su kwanta, inda ta shimfida dayan tabarmar domin su kwanta ita da mijinta.
Su ASHCO kuwa, daga fitarsu sai sabbatu suke suna fadan, kai wannan matar akwai masifa, ita ko irin wayewarnan ta zamni ba tada, amma fa gaskiya ta iya girki kawai dai ’yar masifa ce. A haka har suka karaso inda za su kwana, gaba daya tufafin jikinsu sun jike su kuwa sun sha kashin ruwa sosai har da makyarkyatar sanyi su ke yi.
Har yanzu dai QASIMU kallonta kawai yake yi, ya kuma tabbata a buge ba abin da zai iya a jikinta, sai kawai ya ci gaba da mitarsa, ita kuwa ta ci gaba da rarrashin yaranta, musamman BILKISU da ta lura hankalinta ya tashi.
Washe gari bayan sun iyar da sallah suka dauko kur’ani suna karantawa kamar kullum, har zuwa wani dan lokaci suka dora Karin kumallo, ba da jimawa da kammala Karin nasu ba sai ga driver ya iso, sun fahimci hakan ne, sanadiyyar har cikin gidansu FATIMA ta shigo, bayan sun kammala gaisawa da mahaifiyarta, ta suri littfanta da dan kwandonta wanda ke dauke da abincin da za ta ci dama ta jima da shiryawa suka fice.
Kamar kullum; yau ma ita ce zakara a bayar da amsoshin da malamansu ke tambayarsu a cikin aji, wanda shi ne dalilin kara tunzurar da mahassadanta.
Da suka tafi cin abincin tara, haka suke nuna kyama gareta a fili, dalilin da ya yi sanadiyyar FATIMA ta shigar mata fada, har suka bata da abokaninta. Sai fada suke; yanzu kan ‘yar talakawa kike fada da mu? Hala kin manta inda muka fito, kin manta shakuwa da muka yi da ke? Ta amsa musu , “idan dai haka ne zaman tare, ba shakka ba inda wannan tafiya za ta kaimu sai ga halaka, shin mun manta cewa da mai kudi da talaka duka bayin Allah ne? ku dakata nai muku tambaya, shin mu da iyayenmu suka mallaki dukiya, wata gwaninta suka yi wa ubangiji ne ta sanadiyyarta ya basu dukiya? Shi talaka daga sama ya fado ne ko kuwa an gayamuna cewa ubangiji bai san da zamansa ba? Kar mu manta, shi fa ubangiji a ko da yaushe kan aiki yake haka mutum ba wanda aka kammala halittarsa, ta yi wu, mu iyayenmu masu kudi ne, amma mu a talakawa ubangiji ya rubuta za mu kasance, ba wanda ya isa ya canja hakan, ta yi wu ita da take diyar talaka dama cen mai arziki ubangiji ya halicceta. Duk yadda muka ga mutum mu daina wulakantashi.”
Wasu daga cikinsu jikinsu ya yi sanyi, inda wasu suka buge da tsaki suka suri jakunkunansu suka wuce aji duk da cewa da sauran lokaci, a cewarsu, su ba za su saurari wa’azinta ba, bayan wasunsu sun rafke da Kabbara.
BILKISU kuwa hawaye sai faman kwarara suke daga kumatunta, ta kalli FATIMA ta ce, “bai dace ki bata da abokaninki ba a kaina, abinda suke fada gaskiya ne, ni diyar talakawa ce, su kuma diyan masu kudi ne, sun fi dacewa da ke ba ni ba da kika sani a kankanin lokaci…”
“kada ki kara furta komai, ashe dama za ki iya juyamin baya tun tafiya ba ta yi nisa ba? Duka zama ko mu’amala da ba ta ubangiji ba ba ta da amfani ko wacce iri ce kuwa, da suke da kudi, a aji ai kin fisu kokari, kinga kuwa ba ko’ina ba ne kudi suke abin azo a gani.”
Suka rungume juna suna faman kuka wanda sam ba ka jin sautukansu.
Zuw wani lokaci, suka wuce aji domin daukar darasi. A cikin aji sai harararta abokaninta suke yi, inda ita kuwa BILKISU ta sha jinin jikinta kamar wacce aka dorawa kan bindiga a ka, dalili da yasa malamai da dama suke tambayrta ko lafiya kuwa.
Da aka tashi daga makaranta suka nufi gida kowa ya shiga sabgar rayuwarsa.
Da misalin karfe shida na yamma bayan tasowarta daga Islamiyya ta tarar da taro a unguwarsu, da kyar ta samu ta kutsa tsakankanin jama’a ta shiga gida. In da ta tarar da mahaifiyarta sai kokarin izar wuta take da kokarin dubawa ko abincin da ta dora ya kusa ya nuna. “me ke faruwa Inna naga taro a unguwa, har da masu waka maza da mata”? “’yan siyasa ne suka zo wai campaign, nima saurin da kika ga ina yi domin na halarci wurin ne, na ji me suke tafe da shi”. “Hmm! Inna kenan; wadannan mutanen fa ko kusa ba sa tausayin talaka, ba abin da ke gabansu face su yi amfani da kuri’ummu su jefa mu rana, ki duba duk rana da yunwa da muke sha a layin zabe da barazana da muke fuskanta daga makuwwata siyasa, karshenta sai kiga sun zo sun manta da mu ko su dinga wawasar dukiyoyinmu, ba za su sake dawowa ta kanmu ba, sai lokacin da siyasa ta gabato, amma saboda wautarmu mun kasa mu fahimta” wani ajiyar zuciya SAJIDA ta yi tare da kallon ‘yarta wacce kullum take yi wa kallon mamaki, saboda fasaha da masifar zurfin tunani da ya yi katutu a kwakwalwarta. “ba shakka haka ne, amma ai yanada kyawu mu halarci wurin, ko ba komai za mu ji alkawaruka da za su yi, idan ma ba su cika ba ohonmusu” “Allah dai ya kyauta”. Ta shige daki ta shirya ta fito taya mahaifiyarta aiki. Da suka kammala, suka fita tare domin saurarar me ‘yan siyasa suka zo m,asu da shi na alkawari.
Har yanzu labarin bai fara ba
08034840276
DR. ZAIN
[2/3, 4:47 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
🅾9⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Life is 10 percent what happens to you and ninety percent how you respond to it._
*Shafin Masoya*
Zainab Idris Makawa
Fiddausi Sodangi
Menu gee
Chuchu
Queen Mermu
Nafee Anka
Asy Khaleel
Aunty Baraka
Hauw Auta
***CI GABA***
Haka unguwar ta cika makil da dimbin jama’a kama tun daga maza tsofaffi zuwa mata, ga samari ga yara kanani, a cen dayan bangaren kuma motoci ne da aka cika bayansu makil da na’urori masu amsawa da fitar da amo, sai wakoki ke tashi na ‘yan takara, har wasu wakokin ba ka ma jin me ake fada sanadiyyar wasu wakokin na shiga ta cikinsu.
A bangare daya kuwa, wani minbari ne aka kafa wanda ke da fadin daukar mutum uku kacal, inda nan duka wanda zai yi wa mutane magana yake takawa ya tsaya.
Fitowar SAJIDA da BILKISU suka yi dai-dai da wanda ke magana a lokacin, shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyya mai adawa
Nan ya shiga zayyano musu alkawaruruka na abubuwan da zai yi musu idan suka zabe shi a matsayin gwamnansu. Wannan shi ne dalili da yasa sai kuwwa mashaya ke yi suna fadar “sai ka yi” duk da ana amfani da amsa amo mai karfin gaske, a sama-sama kake iya jiyo zantukan masu magana kan mimbari saboda wurin ya cika makil da jama’a kuma suka kasa yin shiru.
Kusan magariba, aka fara watsin kudi, wanda shi ne dalili da ya hautsina wurin gaba daya, aka fara sare-sare fada kazami ya kaure wurin nan aka fara aika wasu barzahu kan ‘yan kudi kalilan, ganin haka SAJIDA ta suri ‘yarta suka fada wani gida, su kuwa ‘yan kuwwar siyasa sai faman daga takubba sama suke yi suna kokarin kai wa juna sara ko suka.
‘yan takaran kuwa tun da suka watsa musu kudin suka bar wurin, wasunsu ma har sun jima da fita unguwar.
Kai talakan Nigeria, yaushe za ka san ciwon kanka?
Zuwa lokaci mai tsawo, ana dauki ba dadi tsakanin wadannan jama’a da mafi yawansu abokai ne, tuni wurin ya cika da jini, haka kasar wurin ta fara rufewa da gawarwakin baraden siyasa, cen sai ka fara jiwo jiniya ta motar ‘yan sanda, wanda ya yi sanadiyyar wasu suka ranta a na kare, wasu kuwa suka tsaya. Isowar motar, ba su yi wata-wata ba suka fito cikin sauri, suka fara duka da kama duk wanda suka gani, inda su kuma baraden siyasar suka fara mayar da martini na dukan da saran.
Har bayan isha ana wannan dauki ba dadin
Gaba daya unguwar ta rude, wasu da dama a gidajensu ko abinci ba a daura ba.
SAJIDA kuwa ba ta sami damar fitowa daga inda suka labe ba sai da misalin sha dayan dare har da mintuka, gaba daya hankalinta a tashe kasancewar ta baro AMEESHA ita kadai a gida, sai faman zubar hawaye take. Cikin sauri har da hadawa da gudu take tafiya inda take janye da hannun BILKISU sai faman tuntube take, amma ko ta tsaya ta duba, kasancewar hankalinta ba ya kanta. Daga shigowarta gida sai faman duba take inda za ta ga AMISHA, shigowa da za ta yi a daki sai ta tarar da ita tana barci, ashe tun da ta bar ta tana barci ko farkawa ba ta yi ba, dalili da ya sa ta yi ajiyar zuciya kenan tareda karasawa cikin dakin. Saukar mari kawai ta ji a kumatunta har sai da ta fadi cikin firgita da razana, waigowa da za ta yi sai ta ga QASIMU tsaye tuni ya zare belt dinsa daga tsugaggen kugunsa, kafin ta motsa daga faduwar da ta yi, ya fara shauda mata belt din, ya bugamata a ka ya buga a bai ya buga a jiki, ta rasa ta ina za ta kare duka. BILKISU kuwa sai faman kuka take tana fadar “ka yi hakuri” nan ya jawo ta ya maka a kasa ita ma ya shiga dukanta, kukan da ta ke yi mai dauke da sauti mai kara, ya farakar da AMISHA.
“don ubanki ina kika fito? Wato halayyar nan taki ba za ki taba sauya ta ba ko? Da zarar na fita sai ki suri kafafuwanki la’antattu ki fita? Babbar matsalar ma ko sisi ba kya kawowa, yanzu da a ce fitar nan da kike yi kina dawowa da wani abu ai da ba matsala. Dakata ma don uwarki ni da abokanina za ki yi wa Bura uba ranar ko?” yana fada yana zabga mata belt a wuya, BILKISU sai kokarin karemata take yi.
Ya dake su son ransa, kana ya fita wurin yawonsa na dare.
BILKISU ce ke rarrashin mahaifiyarta tana kokarin share mata jini da ke tsiyaya daga jikinta. Cen AMISHA ta fara ihun yunwa take ji, dalilin da yasa mahaifiyar ta tuna tun kammala girki da ta yi fa kafin magariba suka fita, sallar magarib da isha duka suna a kansu. Cikin sauri ta tafi inda ta ajiye abinci ta debo mata suka suri buta ita da BILKISU suka yi alwala suka yi sallah bayan sun kammala Sallah ne suka ci nasu abincin, da misalin sha biyun dare.
Haka suka ci gaba da jinyar juna, barci ya kasa zo musu. Cen kusan biyun dare ta jiwo shigowar maigidanta, duk da ba abin mamaki ba ne a wurinta amma dai yau abin ya taba ta, ya shigo sai mashalo yake yana tangadi na masahaya, tun daga nesa za ka jiwo shi yana warin giya sai faduwa yake yana tashi, da kyar ya samu ya dafa kofar shigowa gidan, kasancewar gidan ba kyaure ya shigo kai tsaye. Ya zube a bakin kofa sai faman zuba amai yake yi, da ya kammala amansa ya fadi nan sai barci, ga shi ane-ane cikin amai jikinsa duk kasa ce ga wasu uban takalmi a kafafuwansa.
SAJIDA kuwa kuka ya dawo mata sabo, ta tada kai sama, ta ma kasa furta addu’ah, ta kalli yaranta da gaba daya sun yi barci, ta sake kallon inda QASIMU ya bige da barci, wani bakin ciki ya sake dasuwa a zuciyarta hawaye kuwa suna rigangar sauka daga kumatunta, kawai ta ci gaba da karatun kur’ani da dama shi ne ya hanata barci.
Tun da asubar fari ta tashe shi ya je ya yi sallah, ama kamar kullum ya hauta da masifa. “wai shin rami daya ne za a saka mu? Ince kowa da nasa ramin? To me ye na damuwa da lamurrana? Wai ke ustaz, wa ya san mugun ta’adin da kike yi, mu za a ci da burga? Mu za a nunawa tsoron Allah, mu da muka ga manyan malamai irinsu…” kawai ya sake bigewa da barci, har da minsharinsa. Ta tada yaranta suka tafi yin alwala ita kuwa ta ci gab da lazumi.
Har yanzu labarin bai fara ba, amma saura kiris mu shiga labarin
[2/3, 4:52 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
1⃣0⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_A musician must make music, an artist must paint, a poet must write, if he is to be ultimately at peace with himself. What a man can be, he must be_
*Shafin Masoya*
'YAR BABA
FATIMA SANI IDI
MINISTAN MATA
***CI GABA***
Da misalin karfe uku ne na rana, amma za ka dauka tsakiyar dare ne yadda gaba daya sama ta canja, haske ya kaura daga garin Maiduguri, wani iska mai dauke da sautin ban tsoro kawai ke tashi kuma yana dauke da kura wacce ta yi sanadiyyar kwashe duk wani mai tafiya kan titi ya nemi wurin fakewa.
Cen ruwa masu tsananin karfi suka fara sauka na tsawon lokaci, sai zuwa bayan isha ruwan suka dauke. Daga nan sanyi ya gauraye garin gaba daya, sai daidaiko kake hango mutane masu wucewa kan titi, inda ruwa suke kwararnya a indaruruka kamar a bakin kwarya.
Tun lokacin gaban SAJIDA yake yankewa yana faduwa, gaba daya hankalinta ya tashi, sai faman taslima take yi da kokarin karanto ayoyin kur’ani domin ta kwantar da hankalinta, amma abin ya ci tura. Dalilin da ya sa ta saka a jikinta cewa ba shakka a wannan daren akwai mummunan abu da zai faru.
Kan tabarma suke zaune ita da yaranta, inda take kokarin koyar da su karatuka da suka koyo daga aji a Islamiyya. Shigowar QASIMU ba ko sallama cikin dakin ya mayar da hankulansu ya zuwa bakin kofa, sai haki yake yi, idanuwansa kuwa kamar wanda aka bai wa gashi aka kwace, ba ko takalmi a jikinsa, gaba daya hankalins a tashe, wannan yanayi ne da ko matarsa ba ta taba ganinsa ciki ba bare yaransa.
Ganin haka ta mike tsaye cikin kidimewa da tsananin tsoro, a fuskarta kuwa alamomin tambaya ne a shimfide wadanda ke bukatar sharhi da fashin baki. “me ke faruwa” ta fada muryarta na rawa, yawun bakinta suna kokarin subucewa makogwaronta.. ya kasa furta komai, sai kokarin nuna bakin kofa yake yi, yana so ya yi magana amma kamar wanda aka sakawa rodi a makoshi. Ganin haka sai ta nufi bakin kofar domin ta ga ko wasu ne suka biyo shi. Abin mamaki, har ta fito a tsakiyar gida ba kowa, kuma gaba daya unguwar tsit ba hayaniyar cewa biyo sa aka yi, hakan ta sa ta ci gaba da tafiya har ta karaso kofar waje, ta leka garka. Amma sai ta fara shinshinar ba lafiya, ksancewar a lokacin ba zai kai karfe goma na dare ba, amma gaba daya ba kowa kan titin, illa sai wani sanyayayyen iska da ke kokarin ratsa mutum, wanda ya yi sanadiyyar kara fitowarta da kyawu domin ta ga me ke faruwa. Fitowar da za ta yi, sai ta jiwo karar bindiga Taaa! Ai ko nan ta fadi dirsham, da rarrafe ta fada cikin gida, gabanta sai dukan uku-uku yake yi kamar zauciyarta za ta fito daga makwancinta. A rikice ta fado daki, ta janyo yaranta ta rungume a jiki. Bakinta na rawa ta ce “’yan…b..b..ko haram..ne” ai ko nan BILKISU ta kara shigewa a jikin mahaifiyarta. QASIMU kuwa ya koma cen gefe cike da tsoro sai kallon matarsa yake yi ya kasa furta komai.
Cen sauti mai masifar firgitarwa ya tashi, wanda yayi sanadiyyar hatta ginin gidansu sai da ya fara girgizawa yana zuba, cikinsu kuwa sai kugi da rura yake kamar wadanda ake yamutsawa, AMISHA ta fashe da kuka mai tsananin sauti, inda BILKISU ke kokarin