Showing 12001 words to 15000 words out of 47716 words

Chapter 5 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt

jikinsu, da suka kammala suka dugunzuma su duka ya zuwa masaukinsu, inda suke tafiya suna fira da kokarin kwatatnta rayuwakansu na gida da na nan wurin. Har suka karaso masauki. Bayan sun ajiye ruwan, mutane suka shiga shirin yin sallah kasancewar lokacin rana saura kiris ta fadi. Da suka kammala sallah, gaba dayansu suka taru, maza a gefe daya mata a gefe daya, aka gabatar musu da wani katon akushi cike da abinci da gasassun zomaye da namun jeji daban, kowa ya zagaye akushin suka fara ci, sai ci ake yi ana fira, mazan da ba za su haura uku ba, sai matan da suke su bakwai har gami da tsohuwa, yara kuwa su tara hadi da su Amisha. Su ne ba su kmmala cin abincin ba har sai da loakci isha ya gabato.






Aka taru gaba daya wuri daya, dattijo ya ja su a sallah. Da suka idar, kamar kullum, ya gabata ya ja hankulansu ya kuma yi musu nasiha da rarrasar zukatansu kan ibtila’I da suke ciki.






Bayan ya kammala, suka taru su duka gaban wuta da aka hura domin yin fira, bangaren maza daban inda yara suke cakushe tareda mata, sai fira ake yi tsakanin juna cen sai tsoho ya gabata, ya ce yanada kyau idan da wani cikinku da yake da labari da zai fadakar da mu, ya gabata ya bayar, amma kafin mutum ya bayar da labarin da yake tafe da shi ba shakka, ya gabatar muna da kansa ko da kuwa mun sanshi, lura da a tattare a mu akwai baki.






Nan take kowa ya yi na’am da wannan shawarar.






Nan wani daga taron ya mike tsaye, shekarunsa ba za su haura, arba’in ba, duk da gemunsa yana dauke da furfura, gashin kansa ya yawaita kuma ga shi a hautsine, fari ne a jiki, amma farin ya garwayu da tsawon lokacin rashin ganin ruwa wanka, har fatar jikinsa ta rina ta fara baki, gajere ne, ba ya da kauri sosai,amma muryarsa tanada nauyi. Sai ya gabata.






Sunana Shu’aibu, an haife ni a garin Maiduguri, a nan na girma duka karatuna tun daga primary har secondary a nan na yi, haka ni ma’aikacin gwannati ne, inda nake aiki da Nitel. Inada yara biyu da matata daya.






Wata rana ce da ba zan taba mantawa ba, naje dauko yarana daga makarantar da suke karatu, yaran sun fito har sun fara murmushi da murnar sun hango mahaifinsu ya zo makaranta daukar su kamar kullum. Kawai sai sauti da karar bindiga suka fara tashi, gaba daya mu da ke wurin muka rude, muka rasa sanin ta ina ne wannan sautuikan ke fitowa, ko da hankalina ya dawo, kawai hango karamin dana nayi, mayakan boko haram sun dauke shi tare da wasu yara, sai kuka yake yana kiran sunana, ni kuwa ba abinda zanmasa sai kuka nake yi, suka ci gaba da yin harbi ta gefenmu, mutane sai zubewa suke yi a mace, ganin haka, muka ranci na kare muka fara gudu, su kuwa suka biyo mu da mashunansu, mune bamu tsaya ba sai da muka tabbatar da cewa mun bace musu a cikin latsetsen jeji.






Kwana da kwanaki muna yawo cikin jeji, mu hadu da wannan bala’in yau gobe mu hadu da wancen masifar, duk wadanda nake tare da su su hudu suka mutu, ni kadai na rayu ya zuwa wannan ranar, har zuwa lokacin da ubangiji ya hada ni da wannan dattijon mai nagarta. (ya nuna mafaraucin da ya kawo su SAJIDA). Shi ya kawo ni nan ya bani kulawa da tsaro.




Gaba daya mutane da ke wurin suka yi tsit, kamar wadanda aka dorawa wuka a wuya.






Cen sai wata tace, “saura ka bamu labarin da ka ce zai amfane mu kamar yadda aka sanar cewa, duk wanda ya gabatar da kansa ya kuma bamu labari ko kadan ne.”






Ya girgiza kansa, ya ce “ba damuwa, zan baku labarin NUSAIBA littafin *Zainuddeen Zain dr. zain*, mai suna SAKACI”








DR. ZAIN
[2/3, 4:53 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾








1⃣3⃣








Na








*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_








dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_








® *PEN WRITERS ASSOCIATION*








```QUOTE OF THE DAY```








_Some people are just so FAKE that if you look properly at the_


_back of their neck, you’ll find a tag saying “MADE IN CHINA”_


















*Shafin Masoya*




*Online Hausa Writers*












***CI GABA***








*DANDANO DAGA LITTAFIN SAKACI*
Na *ZAINUDDEEN ZAIN DR. ZAIN*








Mota kirar camry ce yake cikinta, , mai kalar siminti,duk da cewa sauti ke tashi a motar na wakar 2pac a dai dai gabar: A FUGITIVE MY OCCUPATION IS UNDER QUESTION WANTED FOR INVESTIGATION, EVEN THOUGH AM MARKED FOR DEATH AMA SMOKED TILL I LOOSE MY BREATH MOTHERFU…… ANY TIME I SEE THE PAPER I SEE MY PICTURE, WHEN THEY NIGGAZ GETTING RICHER THEY TRYNA GET CHA, ITS LIKE A MOTHERFUC…..TRAP, AND THEY WONDER WHY ITS HARD BEING BLACK, DEAR LORD CAN YOU FEEL ME? STRESSED GETTING MAJOR UH…………a wakar HELL RAZOR sam hankalinsa ba ya kan wakar saboda unguwar da yake kokarin kutsawa unguwa ce da tafi shahara da rango, unguwa ce da ke makale a jikin dutsi, sai wata ‘yar karamar hanya da iya mota zata iya wucewa, a bangaren hagu da damar hanyar kwazazzabai ne guda biyu wadanda a duk lokacin damina zakayi zaton wani babban kogi ne da har kamun kifi za a iya yi a ciki saboda tsananin cika da ruwa da sukeyi. A hankali ya dinga taka motar har ya karaso daf da wani gida wanda yake a cikin rango ta bangaren hagu da yake ya dauko hanyar ne daga gabas zuwa yamma. Ganin ya kusa isa daf da kofar gidan kuma ga shi ko kusa bai hango alamun yara da zai iya turawa ba su kira masa SAKEENA saboda ya yi ta kiran wayarta bata daga ba, sai rabon idanu yake yi ko Allah zai sa ya hango wani ko wata yarinya da zai aika su kira masa ita, cen idanuwansa suka hango masa wata yarinya, ba shakka yarinyar tanada kananan shekaru sai dai cike yake da mamaki ganin yanzu iyaka sha daya da mintutuka ita kuma wannan yarinyar da UNIFORM a jikinta na makarantar gaba da PRIMARY. Ba tareda wani inda inda ba ya daga mata hannu alamar tazo, cikin sauri ta ajiye Jakarta ta taso, tun kafin ya ci birki ya soma magana, “don Allah kinsan SAKINAR gidannan”?




“Eh” ta fada cikin sanyin jiki.




“Don Allah shiga kice ana kiranta”




“tau” kawai ta fada a daidai lokacin da take juyawa.




Cikin rabin minti sai gata ta fito, “wai ance bata nan”




“nagode” ya fada a dai dai lokacin da yake kara yi mata kallo, wannan karon ba irin kallon da yayi mata a farko ba, yarinya ce karama sosai domin shekarunta ba zasu haura sha hudu ba, da ka kalleta kasan irin shiru shirun yarannan ne da sam basa son hayaniya sai harkar gabansu, a fuskarta akwai kwale har biyu, dark ce in complexion, gata ba tsawo, ko kusa bazaka kirata da mummuna ba haka ba kyakkyawar da za’a kira da mahaukacin kyawu ba, tufafin jikinta duk sunyi dauda har idan ka matso kusa da ita hancinka zai shaidama hakan, tanada idanu da ake kira SEXY EYES, ga muryarta sirariya da laushi, UNIFORM din jikinta kirar siminti ne wando da jacket sai farar riga da hijabi fari da sucks farare takalmi kuwa bakake rufaffu, kayan sosai sun mata kyawu sai dai cike suke da dauda. Ko kusa batada SHAPE, amma irin yarannan ne da mama ya cikawa kirji tun suna a kankanun shekaru.






Daga gayamasa cewa bata nan kai tsaye sai ta nufi wurin da ya daga mata hannu ta taso, ganin haka sai SALEEM ya sake daga mata hannu alamar ta tsaya, cikin murmushi ta tsaya, sai ya fito daga cikin mota yazo har daf da ita, amma shi yana kan hanya ita kuma tana cikin rango, sai yace da ita “me kikeyi a nan”? ba tareda ta furta komai ba ta soke kanta a kasa tana wasa da kasa ta hanyar amfani da sirarun kafafunta.






Sai ya ce “kodai hutawa kike yi” murmushi kawai ta sake sakar masa






Sai ya Ce “okay ki je inda kike hutawar bari in gyara PARKING mota sai inzo in taya ki fira” har yanzu dai da murmushi kawai take biyarsa.






A ransa yake cewa tabbas na sami bagas bari in yi sauri in yi SUBMITTING FILE din wannan kasan ni kamar RONALDO ne bana zubar da chance






A dai dai inda ya gyara PARKING sai ga wani mai gida yazo da tashi motar, saboda haka kokari kawai yayi ya sami wuri yayi PARKING, sai sauri yakeyi yana kokarin ya tarar da ‘yar shila, sunan da yayi mata kenan a ransa, yana iyar da gangarewa a rangon sai ya ganta tana kokarin fitowa har ta rigaya ta dauko Jakarta rataye a kafadarta ta dama.







“ya akayi”? ya fada ba tareda ya tsaya ba ko nuna alamar ita yake yiwa magana ba, ganin a kan hanya akwai wata budurwa da ke kokarin wucewa, yana gudun ta gane cewa wannan karamar yarinyar yake kokarin tsaidawa ta raina shi. Kamar shirin littafi ita ma yarinyar ba tareda ta tsaya ba ta ce da shi “akwai mutum ne a wurin”






Sai ya ida gangarewa, har sai da ya tabbatar hankalin budurwar ba ya kansa sai ya dawo. Koda ya dawo har ta fita rangon ta fara nisa, amma sai waigowa take yi ga alama shi takeso taji me yake tafe da shi






Cikin sauri ya bude motar ya yi STATER, sai ya fiddo da kansa ta tagar motar yayi mata alamar ta zo ta shigo.








Cikin nuna wayau tayi sauri ta shige, har yanzu da Jakarta rataye a kafadarta ta dama.






Budar bakinsa sai ya ce “yanzu ina zamu je?”






Bayan ta saki murmushi wanda a duk lokacin da tayi shi DIMPLES sukan bayyana a kumatunta, sai ta ce “gaskiya bansani ba”






Ganin yara sun fara angaje ya tabbatar cewa dare ya raba sosai, sai ya dakata da bayar da labarin NUSAIBA wato SAKACI. Aka sallami kowa, inda kowa ya nufi makwancinsa.










DR. ZAIN
[2/3, 4:53 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾








1⃣4⃣






Na






*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_








dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_








® *PEN WRITERS ASSOCIATION*








```QUOTE OF THE DAY```








_Don't let the world change your smile , let your smile change the world ヅ_




















*Shafin Masoya*








ASTUU
ZEE BABY
MISS UMMI
INDABAWA




***CI GABA***










Shigarsu yar bukka da aka nuna mata tun zowarsu a mfatsayin inda za su zauna, ta fara duban inda za su kwanta, ko da alama babu tabarma ko abninda zasu shimfida domin dora bayansu, ta fara kawar da ciyawu da datti da suka baibaye bukkar, kana ta cire hijabin da ke wuyanta ta shimfida ta fara kwantar da Amisha, sai ta yi wa Bilkisu ishara da ta je ta kwanta. Tsaye kawai ta yi tana kallon mahaifiyarta, har ta sami wuri cen labin bukka da jingina banta, ta mike kafafuwanta duka biyun, tana kallon inda ta shimfide yaranta. Ganin har yanzu Bilkisu a tsaye take yasa ta kada baki ta ce; “me kike yi a tsaye, ba kya jin barci ne?” “inna inajin barci, amma ai ba yadda zan yi barci na barki a zaune, kina wahala da mu sosai, gamu munzo tsakiyar jeji, inda nake tunanin ba zamu iya kubuta ba, bare ki ci gajiyar wannan wahala da dawainiya da kika sha da mu”.








Murmushi kawai ta saka, sai ta ce; “haba mamanne ya kike zance kamar wata aljihun baya, kin manta ubangiji ya fada da kansa cewa ‘inna ma’al usri usran’ ai babu wani tsanani face ubangiji ya tanadi sauki a karshensa, bature ma ai yana fadar ‘there is always a light at the end of a tunnel’ kada ki biyewa hudubar shaidan har kiyi tunanin wai a wannan jejin rayuwarmu zata kare, ina shinshino zaki zama wata abu gobe wacce kasa gabadaya zata yi alfahari da ita.” “hmm! Inna kenan, ni fa ba yarinya ba ce yanzu” “har gobe ke yarinya ce, akwai abubuwa da bazaki iya hangowa ba yadda ni nake hangensu je ki kwanta” “banajin kwana inna. Shi wancen labari na Nusaiba da alama zai fadakar musamman wurin iyaye da kuma malamai dama yan gari masu halin sakaci ga yaaransu”






Nan suka dauke da fira har barci ya sharesu, cen zuwa ukun dare, Sajida ta tashi domin ta yi nafila kamar yadda ta saba yi a gida. Ta fito a wajen bukkar, ba abinda ke shawagi a kunnuwanta sai kuka da sautuka na tsuntsaye da kuma kwari wadanda wasunsu suna cikin ramukansu, fitowarta ta nufi randuna inda ake ajiyar ruwa, ta suri moda ta nebo ruwa ta koma cen wurin da suka yi fira, ta fara alwala, bayan ta dan kewaya. Daga kammala alwalarta, juyowa da zata yi sai ta hango dattijo mafarauci tsaye yana kallonta. Da alama tun fitowarta daga bukka yake tsaye wurin. Ba tareda ta ce da shi komai ba ta nufi bukkar da suke ita da yaranta. Ta fara sallah. Ta yi nisa cikin sallah sai Bilikisu ta farka, itama kamar yadda take yi kullum a gida ta tashi ta nufi waje, ta yi alwala ta zo ta fara tata sallar. A haka har lokacin sallar subahin ya yi, sun fahimci haka ne da suka fara jiwo kiran farko na assalatu.






Da aka kammala salla cikin jam’I, wani ya gabata ya yi nasiha ya wa’azantar ya kuma ja hankulan mutane kan cewa ita fa kaddara takan zo ne yadda ubangiji ya tsara, kuma wajibi ne kowa ya yi imani da ita ya kuma karbi duk abinda ubangiji ya zo da shi karkashinta. A haka har rana ta fara fitowa. Dai dai lokacin su kuwa mata tuni sun fara shirin abinda za a karya da shi, bayan sun wanke tukwana, yar kuwa suka shiga jeji suka debo itace a yanga, aka hura wuta aka dora tukwane. Da aka kammala abinci, aka saka shi cikin babban akushi, na maza daban na mata daban, a haka aka ci sai raha da ba’a ake da juna, gwanin sha’awa.






Haka matan suka taru wuri daya, suka wanke akussai da aka ci abinci da su, inda ya yara suka shiga gyaran wuri, su kuwa mazan suka fara gyaran wurin da ake zama, fira, cen zuwa wani lokaci sai suka taru gaba daya inda ake firar, wani saurayi ya gabata, ya fara koyar da su karatu bayan ya kammala karantar da su tauhidi suka shiga fikihu da hadisi. Da aka kammala, kowa ya kama gabansa, inda mafarauci ya shiga jeji domin nemo musu abinda zasu ci. Suma wasu daga mazajen suka bazama cikin jeji neman abinci. Yara kuwa suka shiga jeji debo itace, inda mata suka yi rafi domin debo ruwa.






Sai tafiya suke suna fira kamar wadanda ba damuwa a tare da su, har suka karaso rafin, suka debi ruwa suka juya domin kowa mmasaukinsu, suna ciki tafiya suka jiwo motsi a gefen hanya, da farko basu kula ba saboda ganin jeji ne ba mamaki ba ne a ji motsi a surkukin ciyawo, amma jin motsin ya yi yawa, sai Sajida ta gabata domin ta shaida me ye, inda sauran matan suka tsaya cirko-cirko suna kallon me zai faru kuma mme ye ke motsi haka.






Ai ko isarta wurin, batasan lokacin da ta ce, “maciji ne” ba. Jin haka matan suka firgita suka ranta a na kare, wasu da ke dauke da ruwan suka wurgar da abin diban ruwa, wasu kuwa suka fara gudu da ruwa a kansu, gaba daya jikinsu ya jike sharkaf da ruwa. Wasu suka nufi hanyar masaukinsu, wasu kuwa suka arta a jeji ba tareda sanin ina zasu nufa ba. Sajida tana daga ciki wadnnada suka dauki hanyyar masaukinsu.






Amisha kuwa ita da Bilkisu suka bi yaran da suka tafi debo itace, idan suka debi a nan su je cen su diba, har kowa ya tara adadin da yake tunanin zai iya dauka, aka nemo bawan kalgo da wasu ciyawu kamar yodo da gijen kurciya aka rubanya sai suka daure itacen da su, wadanda basa iya azawa da kansu aka dora musu, inda sauran suka dauka, aka nufato masauki, su Amisha kuwa ‘yan rakaya kawai suka koma, saboda basuda kwarin daukar itace. Sai fira suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login