Showing 18001 words to 21000 words out of 47716 words
Chapter 7 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
da ta ce, “ubangiji kana kallon halin da muke ciki ka agaza ka fiddamu wannan masifar”
Ruwan haka suka ci gaba da sauka ba tsaiko har gari ya waye.
Da safe duk inda ka duba idan har wurin yanada rami ko kadan ne, to ya cika da ruwa, ba inda za ka yi taku biyu ba tareda ka saka kafarka cikin ruwa ba, wasu wuraren ma ruwan har a kugu suke kawowa mutum.
Ganin yadda wurin ya koma ta yadda zai yi wuya sui ya zama a wurin, sai suka fara tafiya domin neman wani wuri da za su sauka kuuma, bayan sun dauki lokaci suna shawara a tsakaninsu.
Sai a a lokacin suka lura da cewa wata yarinya kankanuwa ta rasa rayuwarta a sanadiyyar wannan babban hadari da ya dauki lokaci mai tsawo yana zubar ruwa.
Aka yi sauri aka kawar da ita kamar yadda musuluci ya tanadar, suka nusa cikin jeji, domin neman inda za a yada zango. Sai tafiya suke cikin tabo da kuma ruwa da suka kwanta a jikin kasa, daidaiku ne cikinsu ke sanye da takalmi, gaba daya kayan jikinsu a jike sharkaf, suna tafiya har hakoransu ke gwaruwa da juna tsakanin na kasa da na sama kan masifar sanyi da ke ratsa su.
Jikin Amisha ya yi zafi kamar garwashi sai cira take kamar rayuwarta za ta fita, dalilin da ya sa, mahaifiyarta biyar taron kawai take yi amma gaba daya hankalinta ba ya wurinsu, tunanin da take, ina za ta samawar wa yarinyarta da magani.
Suka ci gaba da tafiya har tufafin jikinsu suka far bushewa, kasancewar rana ta dauki zafi sosai, kasa ma ta fara shanye ruwan da suka kwanta a kanta, suna tafiya suna duba inda ya dace su yada zango, amma duk inda suka duba sais u ga ba zai yi musu zama ba. Ganin yara sun fara kukan yunwa, wani daga cikinsu ya bada shawarar a dakata ko da a tsakiyar jejijn ne ba lallai sai ansami wuri yalwatacce ba, a nemowa yara abinda zasu ci, in ya so daga baya a nemi inda za a sauka din. Nan take aka yi na’am da shawararsa, aka sami wurii aka zauna. Maza suka runtuma cikin jeji neman abinda yara za su ci. Matan kuwa suka shiga rarrasar yara da ke kuka. Sajida ta nemi wuri ta shimfidar da Amisha ta dora kanta a cinyarta bayan ta zauna kusa da ita, Bilkisu kuwa zaune kawai ta yi, tana kallon mahaifiyarta tareda mayar da kallo ga sauran mutanen da ke zagaye da su. Duk wacce ta kalla, sai ta nutse da tausayi, a ranta tana tuno irin wahala da suke sha a hannun mahaifinsu, tana cewa “wai ko dai munzo duniya ne domin mu wahala..?”
Bayan wani lokaci, sai ga wadanda suka je fararuta sun dawo dauke da namun zomaye da damo da zabbi jeji, nan take matan suka fara gyarawa, duk da ba ruwa awurin, a haka suka gyara sai aka hura wuta ta hanyar amfani da duwatsu guda biyu aka bugasu suka fitar da wuta, aka dinga dora naman daya bayan daya ana gasawa jan wutar, da aka gasa wani adadi, sai aka bai wa yaran domin su ci, inda daga baya aka gasawa sauran mutane ragowar, ahaka dai aka ci domin a gusar da yunwa.
Suka dugunzuma gaba daya, cikin jeji suna tafiya neman wurin da za a yi masauki.
Tafiya ta yi tafiya, har rana ta fara sanyi, cen suna tsakiyar tafiya sai suka jiwo sauti na kafafuwa a guje tafe ta bayansu, waigowa da za suyi, sai suka hango wasu majiya karfi dauke da makamai, ba mai alamar imani ko tausayi a fuskarsa daga cikinsu, sun tinkaro su a guje. Ganin haka, suka ari na kare suka fara gudu, su kuwa wadannann mutanen suka biyo su a guje da niyyar kama su. Wurin guduwa suka rarrabu, inda Sajida ta mayar da Amisa a bayanta ta goya, ta kama hannun Bilkisu kamar an ba wa yaro alawa ana kokarin kwacewa, suka dubi inda ya musu cikin jeji suka fara gudun ceton rayukansu.
Me zai faru da su?
Ina za su je kuma?
Za su tsira?
Za a kamasu ne?
Kashe su za a yi?
Za ta rabu da yaranta ne?
Duka amsoshinku na cikin feji na gaba.
DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
1⃣7⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Don't waste your time with people who seek attention they are just bored with there life._
*Shafin Masoya*
Her Excellency Hajiya Aisha Atiku Bagudu the wife of the governor of Kebbi State
***CI GABA***
Sai gudu suke yi gaba daya kaya da ciyawu da ke shimfide cikin jejin suka dinga fasa kafafuwansu, amma ko da wasa hakan bai raunana su ba, hasalima basusan ma cewa kafafuwansu sun fashe ba, sai kaimi suke karawa hadi da gudu na ganin cewa sun tserata da rayukansu daga wadannan azzalumai da suka dafo masu. Kara da sauti na wadanda ake kamawa daga bayansu, ita ta hadddasa Karin kaiminsu wurin gudun ceton rai, Amisha duk da jiki ba lafiya kuka kawai take sakarwa, lamari da ya kara saka Sajida a halin na shiga uku, ina zan saka kaina kenan, har ta sa sai hawaye ke kokarin kwarara da idanuwanta, ta rasa me ke mata dadi. Bilkisu kuwa ba babinda take yi sai kokarin taimakawa mahaifiyarta wurin ganin cewa ta dage sosai wurin wannan gudu na ceton rai, sai waigowa take yi tana sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki, idan sun yi kusa da su, ta sanar da ita, idan maan kama wata ko wani ta sanar da ita. A haka har aka kama da yawa daga cikinsu. Su kuwa sai gudu suke. Inda ubangiji ya cece su shi ne, da suka sami wani babban dutse suka haye. Ganin sun haye wannan babban dutsen sai ‘yan book haram din suka dakata da biyarsu din, suka fara zagayar dutsen domin su ga ko ba sojoji kan sa kafin su yi shawarar me kuma za su yi.
Sun jima suna zagayar dutsen, kafin babba daga cikinsu ya bayar da umarnin cewa su koma ainahin masaukinsu domin su ajiye wadannan da suka kama, su kuwa wadannan da ke kan dutse a zauna a tattauna a san yadda za a fatattke su har a kama su su shiga hannu. Nan take suka wakilta wasu daga cikinsu, suka kwashi wdanda aka kama din ya zuwa masauki. Saura suka tsaya suna shawara da karatun ta yadda za su bullowa wannan dutsen har su sami nasarar kama wadanda suka dare samansa.
Wadanda suka sami damar dare dutsen sun hada da Sajida da yaranta, sai mutuminnann mai bayar da labarin Nusaiba, da wasu mata guda biyu.
Dutsen akwai fadi a samansa sosai, yanada tayi kuma akwai wuyar hawa, sai dai idan ka sami hayewa gabadaya, za ka ga filinsa tamkar a kasa kake. Yana dauke da itace wadanda suka hada da Geza, Sabara, Anza da da sauran otace da galibi kan fito kan dutse. Iya kallonka ba abinda za ka iya hangowa face fili fallau har sai abin ya firgitar da kai.
Ba wani kyakkyawan shiri, duk da zazzabin Amisha ya tsananta, a haka ta shimfideta karkashin wani babban icen Kalgo, ta barta nan tareda Bilkisu da matannan guda biyu, ta kalli wannan mutumin, ta ce, “bawan Allah ya kamata ni da kai mu shiga wannan jeji mu gani ko za mu iya samun wuri mai saukin sauka kafin wadannan azzaluman su hawo, domin idan suka hawo tabbas kashinmu ya bushe, kan dutsenannan bana tunanin za mu iya tsira daga sharrinsu.” Gyada kai kawai ya yi, alamar gamsuwa, duk da cewa a ransa ba haka ya so ba. Dole ya bi ta suka fara zagayawa suna neman ta inda za su sauka kafin wadannan azzaluman su hawo ta kan dutsen. Aka bar su Bilkisu da fako, zuciyoyinsu kuwa kan bugawa kamar wadanda za su fito daga kirjinsu.
Sai tafiya suke, har suka dauki lokaci mai tsawo, ba inda suka ga dutsen ya kare ko alamar wurin da za a sauka, lamarin da ya kara tayar musu da hankali kenan, ganin sai kara nutsawa suke cikin jeji kuma kan dutse, sai mutumin ya bada shawarar cewa ya fi dacewa su koma, su dauko mutanensu ayi wannan tafiyar ta neman wurin sauka tare, musamman ganin duhu ya fara shigowa. Da farko ta so ta ki aminta da shawarar, sai daga baya ta aminta, suka juyo. Inda suka bar su, a nan suka tarar da su kuwa, hankulansu a tashe, Amisha kuwa kamar wacce ake karawa wutar zazzabi, jikinnnata ya kara zafi, ko motsi na dole kadai take iya yi, Bilkisu kuwa aikin kuka kadai take. Sai da suka yi mamaki ganin nama a kusa da sun a zomaye da bushiyoyi. Dalilin da ya sa Sajida ta tambaye su kenan, “wa ya kawo wannan?” cikin sanyin jiki, Bilkisu ta karba, “mu muka je muka nemo, ni da wannan” ta nuna daya daga cikinsu. Nan take suka gyara naman, suka hasa wuta suka ci. Bataayi mamakin hakan ba, saboda ta san yarinyarta tanada karfin zuciya, kuma tasan komai za ata iya aikatawa domin ta taimaki wasu, bare da yake ga kanwarta na neman taimako.
Bayan sun kammala cin naman, cen dare ya fara shigowa, suna tsakiyar taimama domin su sauke sallolin da ke kawunansu, sai suka fara jiwo sauti cikin Amsa Amo (loudspeaker) kamar haka; “kun nuna bajinta da har kuka iya tserewa mayakanmu, amma munaso ku san da cewa, wannan gudu naku, ba zai tseratar da ku daga hannunmu ba, saboda mun fi ku sanin jejinnan sosai, zai fi muku idan kuka sallama kawunanku, ba zamu cutar da ku ba, dama mu manufarmu mu dora kowa kan turbar Islama, a ajiye karantarwar yahudawa da nasara a rungumi sunna da Qur’ani, kar ku tsorata mu ba azzalumai ba ne, ba ma kisa, jihadi ne muke yi. Ku mika wuya, ba zaku cutu ba.”
Cike da mamaki suke kallon juna, inda zantukan sun ratsa daya daga cikin matn da ke wurin, har da cewa da su, “ya kamata mu gaggauta mika wuya tun da sun tabbatar muna da xewa ba za su cutar da mu ba, ya fi mu ci gaba da wannan gudun da sam ba tsira ko alamu tsira a cikinsa, ku kalla fa ku gani, wuni daya kenan ba wanda ya saka ruwa a cikinsa a cikinmu, mu kalla fa muga, wanka ba a ma zancensa, abinci a jiye zancensa shima, inaga mika wuya ne kawai mafita a garemu, kunji da kunnuwanku cewa ba za su cutar da mu ba, kuma kan daular musulunci suke gudanar da lamuransu”
Ta jima tana yi wa wannan matar kallon takaici, da jin kamar ta shara mata mari ko ta jefo mata asshar, amma sai ta hadiye, wasu hawaye masu zafi suka fara fito mata, muryarta na rawa ta kalle ta ta soma. “ke yanzu har za ki dauki zancen wadannan azzaluman? Idan da gaske suke yi ke da kike talaka kila ma bakida ilimin book, me ye hadinsu da ke da har za su shigo su dagulamaki rayuwa ta hanyar raba ki danginki da yaranki da mijinki, hakan ne taimako, kuma a naki tunni haka musulunci ya tanadar ko ya koyar? Wannan amsa amo da suka yi amfani da ita, in ce itama yahudawa da nasara suka kawo ta, domin a tarihi bamu taba jin cewa kakanninmu sun yi amfani da irinta ba wurin isar da sako, bindigogi da ke hannunsu, gaba daya na yahudawa da nasara ne. tau su da ke fada da abinda yahudawa da Nasara suka zo da shi, me ye kuma na amfani da kayan Yahudawa da nasara? Tabbas akwai lauje cikin nadi. Ba sa kisa suka ce, kinga tun nan sun nuna maki makaryata ne, domin shakka banayi, ba za su rasa yin kisa a gaban idanuwanki ba, kuma kisa na wadanda basu ji ba su gani ba, ga talaka mai kokarin neman abinda zai sakawa cikinsa, ya nemi inda zai dora awazarsa. Kada kdimewa da neman mafita ya sa ki manta zaluncin wadannan azzaluman ‘yar’uwa, ubangiji da ya je fo mu a wannan halin ba shakka bai manta da mu ba kuma zai nema muna mafita, ko nan kusa komai dadewa ko a duniya ko mu ji dadin mafitar a gobe kiyama. Wannan ita ce jarabawarmu, mu kafe kafafuwanmu, mu dage damtse, ba shakka mafita na kusa, ai duk abinda ya zamo daya, to kamar ya kare ne”
Ta yi ajiyar zuciya har kunya ta kamata, tareda fitar da hawaye. Suka gabata, suka yi sallah har da Bilkisu, sai suka ci gaba d tafiya domin neman inda za su sauka, su kuma ga ko za su sami fita daga wannan jeji, da kubuta daga hannun wadannna makiya Allah da ke biyarsu.
Ganin an dauki lokaci mai tsawo har dare ya fara rabawa, ba tareda ko daya daga cikinsu ya zo ya mika wuya ba, sai suka fara hawo dutsen da niyyar kama su ko su aikasu lahira, musamman saboda sun gindaya musu sharuda da basu damar sallama kawunansu, amma suka ki. Suka biyo su a fusace. Sun jima tsaye suna kokarin neman hanyar da suka bi, kasancewar duhu ya mamaye dutsen sosai, sai sanyi da ke dukan jikin mutum dauke da wani iska mai dadi. Suna tafiya har suka karaso inda suka ci abinci suka kuma yi sallah. Kallon wutar wurin ya tabbatar musu da tabbas sun jima da barin wurin, dalili da ya sa suka kara kaimi kenan wurin ganin sun cinmusu sun tsayar da su.
Su kuwa sai tafiya suke yi, duk inda suka ga alamunsaukar dutse sais u nufaci cen, amma har yanzu ba alamun ta inda z sui ya sauka, dole suka ci gaba da tafiya, har safiya ta waye. Tun fara tafiyarsu take goye da Amisha, inda sauran suke a gaba ita kuma tana ta baya. Dayar matar da suke tareda ita ce, ta nuna musu gaskiya ita ta gaji, kuma ba za tai ya ci gaba da tafiya ba. Jin haka suka yi tsaye suka yi rarrasarta ta nuna gaskiya ita ta gaji sai dai a yada zango a nan. Mutumin da ke tare da su ne, ya ce, “idan muka tsaya a nan, duk gudu da muka yi cikin wannan jejin za tashi a banza ne, domin inada tabbacin cewa yanzu haka suna biye da mu, zamnmu a nan kuwa dole za su riske mu, ina amfanin badi ba rai ke nan? An yi ba a yi ba kenan. Ki daure ki tashi, ki duba har da karamar yarinya da daure, muyi hakuri, su dai da ke son su zlunce mu suka jure wuya, sai mu da ke kokrin kubuta daga rayukanmu….”
Suka yi juyin duniyarnan da ita, ta ki aminta da ta tashi, suka ajiye akan za su bar tan an, suka wuce. Tafiya ta yi tafiya, ga zafin raina sai kara dukansu yake, ga yunwa na cinsu ta ciki, ga gajiya a tattare da su, amma ba mai alamun tsayawa ko nuna karaya.
Azzaluman kuwa sai tafiya suke kamar wadanda ake karawa karfi, kowannensu da mummunar niyya a zuciyarsa, yana hango irin kisa da wulakanci da z su yi wa wadannan da ke kokarin sakaa su wahala, a cikin wannan sunkurun jejin. Suka ci gaba da tafiya, suna yi suna fira da yin ba’a a tsakaninsu, har suka tarar da wannan da ta kasa tafiya, kwance a karkashin wani ice da ta kare kanta daga zafin rana.
Ganin sun zagaye ta, cikinta ya fara rura, gaba daya yawun bakinta ya kafe ta kasa motsi numfashi ma ba ta san ta ya yake fita daga huhunta ya zuwa karan hancinta ba, cikin kidimewa ta ce, “wallahi sun ganni..”
Suka zagaye ta, sai dariya suke yi, ita kuwa sai kuka take rusawa, tana so ta gudu, amma sai take ji kamar kunkunceta aka yi cikin manyan kacoci.
Me za su yi mata?
Mu hadu a shafi na gaba.
DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
1⃣8⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
Never trust someone who lied to you more than twice bcz he won' change at all and will pass for a stupid girl.
*Shafin Masoya*
MATAR YAEESH FANS
***CI GABA***
Sai zagayar ta suke yi, suna yin wata dariya wacce ke kara jefata cikin tsoro da tashin hankali, ganin ta kidime sai shugabansu ya yi alama da hannu, cewar a kashe ta kawai, ya bayar da umarnin ne ganin cewa, idan suka ce su tafi da ita, za ta rage saurin da suke yi na kokarin cinma sauran, haka ba za su iya barinta da rayuwarta ba.
Nan wani ya gabata, ya caka mata wuka da ya zaro daga kugunsa, ya sake daga wukar ya caka mata, har sau uku, duk lokacin da ya caka mata wuka, sai ya juya wukar a cikinta domin ya katse hanjinta, karshe ya tunkudeta ta fadi a mace. Suka ci gaba da tafiya domin su tarar da sauran.
Su Sajida kuwa sai tafiya suke yi cikin matsananciyar zafin rana, ga yunwa ga jikinsu na wari, ga shi ba mai takalmi a kafa, kafafuwansu sun fashe, amma kamar ba su fashe ba, domin ba sa jin zafi ko zafin rana. Suka ci gaba da nutsawa cikin jeji har suka hango inda za a iya takawa a sauka daga kan wannan babban dutse, da suka share awanni suna tafiya a kai. Sai dai matsala daya, wurin da masifar hadari, wanda da zarar ka kalli wurin saukar za ka fara ganin jiri, musamman da za ka zaci wata rijiya ce za ka shiga mai gaba dubu, duk ba wannan ne tashin hankalin wurin saukar ba, irin yadda acen kasan yake da ciyawu da itace manya masu dauke da kaya, kamar su gumbi da sauransu. Wannan ya tayar musu da hankali.
Gaba daya suka tsaya bakin wurin suna kallon ikon Allah. Komai jarumtar mutum dole zuciyarsa ta karaya, dole ya firgita, saboda