Showing 36001 words to 39000 words out of 47716 words
Chapter 13 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
ko mu ratse hanya, ni fa na tsorata, ji wadannan adduna da sanduna da suke dauke da su.”
“mamanne kenan, akwai makami da zai daga maki hankali ne yanzu, ke da kika ga bindiga, kikaga takobi da gariyo da adda da hargi, wadannan makaman zasu daga maki da hankali? Harbi a wutsiya ai ya fi kuskure, kuma kwai a baka, ai ya fi kaza a akurki. Su muka gani, kuma tabbas su dole gari Zasu nufa, idan ma bazamu bi su ba, ai ya kamata muje su doramu hanya”
Suka mike suma suka bi bayanta, suna tafiya a tsorace, ita kuwa hankalinta a kwance, har suka karaso daf da taron. Ganinsu, sai makadin ya dakata da kidan nasa, hankalin kowa ya koma kansu, lura da shi makadin da ya dakata da kidan, kallonsu ya dinga yi. Kai tsaye Sajida ta shiga tsakiyar filin saurayi da Bilkisu kuwa suka riketa gam. Ta fara magana da murya mai karfi.
“Assalamu Alaikum ya ku taron wadannan mafarauta,ku yi sani yau ba farautar namun jeji kuka yi nasara ba, kun yi nasarar farautar wadanda ke bukace da neman agaji ne, kunyi farautar marayun Allah ne wadanda suka shiga musiba da ibtila’in rayuwa. Mun kwashe kwanaki muna gudu cikin wannan jejin muna neman tsira sai yau ubangiji ya sadamu da ku. Mu ‘YAN GUDUN HIJIRA ne, da mayakan boko haram ke farauta ruwa a jallo, ku taimaka, ku tafi damu a garin da zaku isa ko ku nunamana hanya inda zamu isa kowanne gari ne cikin sauki. Aikin lada ba ya kadan, ku taimaka, ku ceci rayukan marayunnan”
Ta fada cikin kuka, tana nuna su Bilkisu.
Gaba daya mafarautan da ke wurin suka yi shiru, tausayi ya kamasu ya kuma dabaibaye zuciyoyinsu. Nan wani daga cikinsu ya gabata ya soma “mun ji zamu taimaka muku, amma ba zamu iya tafiya tareda ku ba, saboda jiya muka shigo jejinnan farauta, ko zamu koma gida kuwa ba yanzu ba, zamu bar ku ku kwana, tun da safe sai mu doraku kan hanya da za ta sadaku da gari mafi kusa, ai ba nisa, ba zai kai tafiyar wuni daya ba ma.”
Kan murna kamar su zuba ruwa a kasa su sha, nan Sajida ta dinga yi musu godiya, inda hawaye suka rinjayeta kan murna sai kuka take. Nan aka kawo musu abinci, da yake mafarautan basu kafa tantuna ba, dole a kasa suka kwana a fili, sanyi kuwa kamar zai kashe su bayan sauro da ke yayyakar naman jikinsu.
Allah sarki, haka suka kwana, har safiyar Allah ta waye, bayan sun yi salla suka ci abinci, da rana ta fara fitowa, aka nuna musu hanyar da za ta sadasu da gari mafi kusa, suka kama hanya, bayan sun yi godiya kamar su rusuna.
Shikenan wahalrsu ta kare, ko da saura?
Wanne gari ne wannan da zasu nufa?
Me zsu tarar?
Idan sunje garin, ina kuma zasu nufa?
Duka amsoshinku suna cikin shafi na gaba. Yanzu labarin ya fara hawa hanya.
08034840276 call
09039951083 whatsapp
DR. ZAIN
[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣9⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_namu allaxiy da amanu yake tafiya, budurwa kuma anfi so a Santa ne da junta_
*Shafin Masoya*
AMYRAN MD
ASTUU
***CI GABA***
Haka suka cigaba da tafiya sai fira suke yi cike da farin ciki kasancewar an sanar da su cewa ba za su dauki lokaci suna tafiya ba kafin su isa gari mafi kusa.
Sai a lokacin suka sami damar kallon yanayi na jikinsu. Ita dai Sajida a jikinta riga ce da aka bata ta saka a daren amarcinta na aurenta da shugaban boko haram na garin da suka fito, sai hijabi shima duka a garin aka bata shi, hijabin dark blue ne ga tsawo har yana ja a kasa, shi ke hana a hango kalar atamfar da ke jikinta, atamfar ruwan shudi ce, amma tanada ratsi da aka mata na kwalliya ta kaloli irinsu ruwan dorawa da baki da surkin fari. Itama rigar doguwa ce amma iyakarta guiwa, bata matse jikinta ba, sai zani da aka yi da sifa irin ta skirt. Sosai kayan sun yi mata kyau. A kafafuwanta ba takalmi, domin a wurin gudun ceton rai, ta wurgar da su. Gaba daya kafafuwanta sun bice da kura haka jikinta burun-burun kamar wacce ta yi wanka da Hafdi (toka ta wutar murhu) haka gaba daya jikinta ya yi datti sosai, wasu wurare kafarta duk ta fashe da jini kan ratsa ciyawu da kuma gauruwa a duwrwatsu.
Bilkisu kuwa a jikinta wata riga ce da aka bata itama kasancewar auren mahaifiyarta ne, rigar irin dinkinnnan ne na kasar Parkistan, rigar amba colour ce amma tanada ratsi kwalliya na fari a gaba da shudi, sai wando mai fadi da ya tsuke a karshen kafarta. Sai wani dankwali da ta rufe kanta da shi, shudi. Ba ta da hijabi a jiki, haka a kafarta ba takalmi. Ita ma duk ta yi datti ga kafafuwanta duk sun yi dauda a gefen jikinta rigaarta ta yage kan matsifar keta jeji a lokacin da suke gudun ceton rayukansu.
Saurayinda ke tare da su kuwa. Wata polor shirt ce a jikinsa, ruwan siminti, wacce a wuyan rigar, aka kawata shi da bakar kwala, a kugunsa kuwa jeans ne baki, wana da zarar ka kalle shi, za ka san ya dade a jikinsa ba tareda ya ga ruwa ba, duk da bakin da yake da shi. Shima dai ya wurgar da takalminsa kan masifar gudu. Haka wasu wurare a jikinsa, sai jini ke fita saboda raunuka da ya samu wurin kokarin ya kubutar da rayuwarsa.
Haka suka cigaba da tafiya. Sajida ta ce a dan saurayin da suke tareda shi, “sai tafiya muke yi, bawan Allah amma har yanzu bamusan waye kai ba, bamusan daga inda ka fito ba, haka bamusan ya aka yi ka fado hannun wadannan azzaluman ba.”
“haka ne” ya fada bayan ya yi murmushi tareda juyowa, da yake shi ne gaba, “nima ai bansan labarin komai game da ku ba”
“hmm! Labarinmu ba wani abu ba ne mai birgewa ko sha’awa ba, labari ne da tun farkonsa har karshe yake dauke da bakin ciki, kunci, takaici, nadama, tashin hankali da fadi tashi. Labari ne da ba wanda zai so ya ji an ce wani wanda ya sani ya afka cikinsa.”
Ya girgiza kansa, ya ce, “duk wannan labarin a kanku ya kare? Ikon Allah, zan ko so naji wannan labari naku”
“kar ka damu, za ka ji labarinmu, insha Allah, yanzu dai ka fara bamu naka labarin muji, ko ba komai domin musan da wa muke tafiya.”
“da farko dai sunana Mustapha, ni haifaffen garin Borno ne, a unguwar GRA, lafiya lau muke zaune da mahaifiyata da mahaifina suna nunamin kauna fiye da komai, kasancewar ni kadai suka mallaka, ni din ma sun jima da aure kafin ubangiji ya basu ni, inada kaka daya, ita ce wacce ta zo ta tada ni daga barci, ta hada ni da ku, ina matukar kaunarta ta yadda hatta rayuwata zan iya badawa domin na fansheta. Ina karatu a jami’ar Maiduguri, inda nake karanta biology a 300level. Wata rana nazo ziyarar kakata a unguwar da take nan bayan TH, shigata gidanta ke da wuya, sai muka jiyo sauti na bindigogi da tashin bamabamai, da kuma kara da kuwwar jama’a, hakan tasa muka rufe ko’ina na gidan, muka kasance cikin tsoro. Mun jima a wannan yanayin, da muka ji sautin ya lafa sai na bude kofa domin mu ga ko sun tafi, budewa da za mu yi, sai muka ga gaba daya kan titin mayakan boko haram ne dauke da mugayen makamai, muka yi yunkurin juyowa cikin gida, daga nesa wani yace, idan kuka kuskura kuka juya sai na watse muku kwanya da wannan bindigarar, dole muka tsaya, cike da tsoro, suka zo suka kama mu. Tun ranar muke hannunsu, mun sha wahala iri-iri da sunan wai horo ne suke bamu na zama sojojin boko haram. Kullum babu abinda suke koyar da mu fiye da falalar jahadi da kuma lada da ke kunshe cikin kashe makiya addini. A wurinsu duk wanda bai koma jeji ba ya jaddada jahadi ko ya kafa daular musulunci, tau shima kafiri ne da jininsa ya halatta. Sun sha koyar da mu, falala da yadda ake kunar bakin wake da sauransu. Abu daya ke dauremin kai game da su, wasu lokuta sai kiga turawa ne ke kawo musu abinci da makamai, wasu lokuta kuma sai kiga bakaken fata ke kawowa amma kuma daga gani kasan ba kudinsu ne ba, domin wanda yake zaune a jeji, ina yaje ya nemo kudi da zai sayi bindigar da kwaya daya zata haura dubu dari biyu. Nayi tunani naga daga cikin masu wannan ikirarin na boko haram, zaki ga talaucin kansu kadai ya ishe su, ya za ayi wanda yake da talauci, ya iya samun kudin sayen bindiga mai masifar tsada, kuma ya sayeta, kuma ya dawo jeji ya tare, wa zai ciyar da shi?”
“Mustapha ke nan, ai duk mai hankali yasan wadannan yan boko haram din, daukar nauyinsu ake yi, matsalar da yawa daga cikinsu jahilai ne kan addinin, wasu ma sai ka tarar ba musulmi ba ne, ana amfani da su ne kawai domin a lalatawa musulunci suna. Akwai labari na wani bawan Allah da ya ce, su biyar aka taba turawa a kasar Misra wato Egypt domin su nemo ilimin addinnin musulunci su zo su dinga bayar da fatawowi domin su rikita addinin musulunci, hakan ta faru har ga Mai Tatsine, wanda turawa ke daukar nauyinsa, da asirinsa ya tashi tonuwa aka fahimta, kuma ashe ba musulmi ba ne, hakan takan faru, saboda kafurai sun fahimci cewa musulunci shi ne addinin gaskiya, basuda wata hanya da za su dakushe addinin sai ta hanyar kirkirowa da irin wadannan abubuwa na rudani da zasu dinga shafe hasken musulunci su dinga jingina su ga addinin musulunci”
“Allah dai ya kyauta”
Suka ci gaba da tafiya. Su ne basu iso gari mafi kusa ba sai da maraice. Tun daga nesa suke hango hayakin girki na tashi, ga kamshin kauye da ke kokarin dumfaro hancinsu, sai kuka na jakai da shanu. Daga nesa suke iya hango kalar bukkoki da dakuna da wannan kauyen yake da , duk da tun daga nesa za ka iya fahimtar cewa kauyen ba ya da girma amma akwai ruhegu (wurin ajiyar abinci kamar su damma da sauransu ko buhuhuwa) sosai a garin, wanda zai tabbatarwa mutum da cewa, wannan garin tabbas na manoma ne. ganin sun fara hango gari, suka kara sauri, kamar zasu ruga aguje. Amma da suka karaso daf da garin, sai Sajida ta umarce su da su tsaya. Da suka tsaya cike da mamaki suna kallonta, sai ta umarce su da suyi addu’ah da ake yi kafin a shiga gari. Suka yi addu’ah suka shiga garin da kafar dama. Duk wannan abin da ke faruwa, kusan magariba ne, domin saura kiris rana ta fadi.
Shigarsu garin duk inda suka biya sai kallonsu ake yi, irin kallon tabbacin cewa wadannan baki ne, da suka ga abin ya ki ci ya ki cinyewa, sai Sajida ta nufi wasu da ta gani zaune a gindin wani ice, ta yi musu sallama, suka amsa, sai take tambayarsu ko za su iya nunamata gidan maigari ko mai unguwar garin, ganin yadda suke kallon ta ya tabbatar mata da basa jin Hausa, ta yi musu fulatanci, nan ma ba wanda ya iya mayarwa. Ta gwada yin turanci, shima ba wanda ya amsa. Nan idanuwanta suka raina fata, taji gaba daya murnar da take yi ta koma ciki. A ranta tana mai cewa, yanzu duk wahalar da muka sha ta tafiya ba mai jin yarenmu. Ta kalli Mustapha da Bilkisu, taga dukkaninsu suna cikin damuwa ne. ta yi ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya, suka nemi wuri suka zauna, domin su yi shawarar me kuma zasu yi, ya zasu yi da wadannan da basajin Hausa.
Suna zaune karkasin ice da suka zauna, sai suka jiwo an fara kiran sallar magariba, dalili ke nan da ya sa suka sauya shawara, Sajida ta nuna su tafi masallaci, idan suka tafi, dole dayan biyu ta faru, kodai su sami wanda ya iya yarensu ko kuma su tarar da mai gari a masallacin.
Suka dugunzuma su duka uku, zuwa inda suke jiwo sautin kiran sallah na fitowa,da suka karaso masallaci, suka debi ruwa suka yi alwala, Mustapha ya shiga masallaci aka yi jam’I da shi, inda su kuwa suka tsaya daga waje suka bi jam’i. daga kammala sallah mustpha ya mike ya fara jawabi da kokarin yin bayanin ko su waye. Amma har ya kammala bayaninsa, ba alamun ko da mutum daya ne ya fahimci me yake so ya fada, ganin haka, sai ya fara yin yaren kanuri, amma ba alamun an fahimce shi. Ganin haka ya fashe da kuka su Sajida ma da ke wajen, sai kuka suke yi. Dole ya fito ya tarar da su. Suka nemi wuri cen nesa da masallacin suka zauna.
Aka kira sallar isha, suka zo aka yi salla da su. Aka sallame, suka koma wurin da suke zaune, suka zauna. Har mutane suka fara watsewa daga masallaci suna zaune. Wasu ma idan suka biyo za su wuce, sai su dinga basu sadaka, inda Sajida ke nuna su ba sadaka suke so ba. Har dare ya fara kamawa suna zaune garin da ba wanda ke jin yarensu, ga su ba sa jin yaren ‘yan garin su kuma.
Me zai faru?
Ya za su karata a wannan garin?
Amsoshinku na shafi na gaba
DR. ZAIN
[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
3⃣0⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
Duk laifi na kura ne, bacin satar zare
*Shafin Masoya*
Duk mabiyi wannan labarin
***CI GABA***
Suna zaune suna zullumi, ba tareda sanin me za su barkata ba, kasancewar gaba daya hankalinsu a tashe yake. Cen sai Mustapha ya ce da su, “tun da lamarinnan ga yadda ya zo, ya kamata ace tun da safe munkama hanya ya zuwa gari na gaba ko ubangiji zai sa mu dace da wadanda zasu fahimci me mukeso mu fada. Wannan abin ya yi yawa, ace gaba daya kazo garin da ba mai jin yarenka.”
“haka ne” Sajida ta fada. “wannan zai nuna muna buwaya da gagara ta ubangiji, ya kuma kara nunamuna kudurarsa kan komai. Mu kalli kwanaki da muka share muna gudu a cikin jeji kadai, kuma ga shi muka tarar da wasu suna rayuwa a wani wuri da sam ma ko yarenmu basaji, tabbas ubangiji girmansa ya zarce tunani”
Suka yi ajiyar zuciya, suka ci gaba da tattaunawa. Suna cikin fira sai Bilkisu ta ce, “Inna ya kamata mu shiga garinnan ba zai yi wu ace ba wanda zamu samu da zai fahimci abinda muke so mu fada ba, ace duk garinnan ba wanda ya yi yaki da jahilci na boko ko wanda ya dan yi karatun addini da zai dan fahimci larabci”
“haka ne” inji Sajida. “amma kinsan da cewa karatu na kauyuka a fannin boko basu yi karfi ba, ki kalla gaba daya fadin garinnan ba zai yi wu a gina musu makaranta ba saboda yaransu ba zasu haura nawa ba, malamai nawa za’a kawo musu, bacin ga wurare cen da ya dace a tura malamai anki, kan karatun addini, a kauye fa akwai matsala, zaki tarar da liman ko ahdwari ba ya iya karantawa, fatiha ma da kyar yake iya karantawa saboda karancin ilimi, ta ya kike tsammanin irin wannan ya iya larabci ko waninsa? Birni ne fa ilimi ya yawaita har kike ganin da yawa an iya turanci an iya larabci, kauye tuni an manta da su, su suke da bukatar a bawa kulawa ta fannin addini da karatun zamani, amma ina shuwagabanninmu sun yada su. Wallahi idan za ki je wasu kauyuka sai kinyi kwalla, wasu ma da ke da makarantu, azuzuwansu ba sa zaunuwa saboda gabadaya rufin azuzuwan sun tashi, ba kujeru ga allon rubutu ya lalace, a takaice dai azuzuwan ba sa zaunuwa, tau ya kike tunanin a iya karatu a cikin su, bangaren malami kuwa, sai kiga makaranta wacce kusan kauyuka shida ke kawo yaransu karatu, amma malami daya ke karantar da su, gayamin injimi ne da zai iya ba su ilimi yadda ya kamata? Ko kiga malami yana zaune yana jiran wai sai yara sun dawo daga jeji kafin su zo makaranta, haka har lokaci ya kure. Ko kiga malami shi karn kansa yana bukatar a ilmantar da shi, amma shi ne wai headmaster. Gayamin yadda zasu iya samun ilimi? Bangaren addini kuwa sai dai mu dora hannu a ka muce ‘innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ domin yadda kauyuka ke tura yaransu almajiranci kana dubawa kasan da lauje cikin nadi.”
“lauje cikin nadi fa?” Mustapha ya fada yana mai kallonta cike da daukin jin me za ta fada.
“Eh! Lauje cikin nadi kuwa” ta fada tana mai kara gyara zama. “ ka duba ka ga, galibi lokutan da ake tura yara almajiranci, lokaci ne da aka girbe albarkar abinci bayan damina, sai su tura yaran da sunan karatu saboda kar yaran su ci abincin da suka noma, idan lokacin noma kuma ya yi, sai kaga yaran sun koma gida wasu domin taya iyayen aikin jeji. Ka kalli yara da ake turowa, wasu shekaru uku wasu hudu, haba gayamin yadda yaro da ba ya da kwanciyar hankali abinci ma ba ya da tun tashinsa da safe hankalinsa na wurin me zai ci yau, ina zai sami abinda zai sakawa cikinsa. Yaro kankani da wurin barci ma ba ya da sukuni saboda zasu haura su dari suna kwance a wuri daya, ga rashin wanka, cututuka su biyo baya, ga haduwa da marasa tarbiyya tun suna kanani. Gayamin yadda malami kwaya daya zai iya ba wa yara sama da dari biyu tarbiyya. Duk ba nan gizo ke sakan ba, wasu ta nan ne ake lalata su, wasu su koyi shaye-shaye wasu su koyi fashi da sauran ta’addanci.