Showing 42001 words to 45000 words out of 47716 words
Chapter 15 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
a guje domin mu dauko yaranmu guda biyu,dayan shekarunsa biyar”, ta fada a dai-dai lokacin da take dafa dayan yaro da ke kan cinyarta daya, “sunansa Sani, sai dayan yaronmu da shekarunsa biyu, sunansa Ahmad” ta fada a dai-dai lokacin da take kara rungumashi a jikinta, hawaye kuwa suka ci gaba da ganagarowa daga idanunta ya zuwa kumatunta. “Ba shiri muka fito, Ahmad na goye a bayana, in da Sani na rike shi a hannuna, shi kuwa Jamilu yana ta bayanmu sai gudu muke yi, a haka a gabanmu muke ganin yadda ake kama mutane ana yankawa dalili da yasa muka kara kaimi kenan wurin gudu domin mu tserata da rayukanmu. Wurin gudu kasancewar akwai dandazon masu so su tserata da rayukansu, muka rasa Jamilu, na so na koma na nemashi, amma na kasa, domin ina tsoron na koma, rayuwar yarana ta salwanta, dole muka ci gaba da gudu na neman tserata da rayukanmu, har muka fado cikin jeji. Fadi nan tashi cen tsawon kwanaki tara muna yawo cikin jeji, ba ruwa isassu, ba isasshen abinci ba tsaftar jiki bugu da kari gani dauke da ciki na wata har shida. Ga yara sai kuka suke yimin kan yunwa, wasu tsofaffi da muke tareda su, suka rasa rayukansu kan wahala, haka wasu yara da muke da su suka mutu. Wata rana muna cikin tafiya, Allah ya nufa muka karaso wani kauye, kamar hadin baki mu shida ne har yarana, ko sunan garin bamu fara tambaya ba, sai ga jirgin sama ya fara yimuna aman ruwan alburusai da bama bamai, ai kuwa nan hankalina ya tashi, na fara kallon yarana zasu mutu, ga shi bamusan wanne hali mahaifinsu yake ciki ba, nan muka runtuma cikin jeji gudu ya dawo sabo” ta fyace majina da ke kokarin fitowa daga hancinta, ta hanyar amfani da gefen zaninta, ta ci gaba. “wurin gudu, Ahmad ya bata, dole na ci gaba da gudu da goyon Sani ni kadai cikin uwa jeji ga tsohon ciki. Fadi tashi har na kawo wani kauye inda ake saka mutane a tsallake da su a jirgin ruwa, musamman wadanda irin ibtila’inmu ya far musu. Cikin ikon Allah a nan naga Ahmad, a hannun wani bawan Allah, na karbi abina bayan na yi masa godiya. Aka saka mu a jirgin ruwa aka tsallaka da mu, a haka har Allah ya kawo ni garin Yola. Zuciyata bata mutu ba, kan haka ban tsaya kada girmana ko mutunci na ba wurin yin bara, sai na nemi aikin wanke-wanke wurin wata mai sayar da abinci a unguwar Demsawo, na dauki kwanaki ina yi mata aiki, na tara ‘yan kudi, sai na dawo a unguwar Jambutu na ci gaba da kamawa wata mata dahuwar abinci a nan, kwana biyu da na tara kudi masu dan tsoka, sai na ce bari na nufi garin Kebbi, ko ba komai, munada ‘yan’uwa a cen kuma gari ne da ke da zaman lafiya sosai. Kunji labarin rayuwata a takaice.”
Tana kawowa nan, hatta driver sai da ya yi kwalla, Sajida kuwa ajiyar numfashi kawai take yi.
Wata a cikin motar, sai ta kada baki ta ce, “wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwar? Gaskiya kun ga ibtila’in rayuwa, Allah dai yasa kaffara ce a gareku, shi yasa bahaushe ke cewa, ‘ko a bakin kura, ya kamata mutum ya godewa ubangiji’, domin duk musiba da ka shiga, idan ka ji halin da wani yake ciki,sai ka tausaya masa dole.”
Juyowa kawai Sajida ta yi domin ta kalli, mai magana, ba taredaa ta furta ko kalma daya ba ta sake mayaar da fuskarta kan titi ta ci gaba da tuno abubuwa a suka faru da ita a lokacin da take karkashin kasimu.
Da suka kammala tattauna matsalar matar, sai wani da ke zaune a kujerar tsakiya, ya ce, “idan da wanda ke dauke da labari irin wannan ya bamu, ko ba komai zamu kara jin tsoron Allah mu kuma godemasa kan ni’ima da ya bamu komai kanakantanta kuwa.”
Gaba daya suka ce haka ne kuwa. Ganin haka, sai wani matashi da iyakarsa shekaru ashirin da uku ya gayara murya ya soma.
DR. ZAIN
[2/3, 5:06 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
3⃣3⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_Allah ne kadai ya san karatun kurma_
*Shafin Masoya*
Wannan shafin naku ne masoya a duk in da kuke a fadin duniyarnan ina godiya da irin addu'o'i da fatan alkhairi da nakesamu daga gareku. Haka ina godiya da shawarwari da kuke bani Allah ya bar mu tare.
***CI GABA***
*LABARIN SHU’AIBU*
“Sunana Shu’aibu, ni haifaffen garin Bunza ne da ke karkashin jihar Kebbi, a unguwar Fulani aka haife ni nan garin Bunza, a nan na tashi na yi wayau har na girma, lura da ban mayar da hankalina kan kiwo ba duk da cewa ni Fulani ne gaba da baya, ya sa mahaifina ya tura ni karatu a garin gashwa da ke karkashin jihar Borno. Nan na yi karatu har na sauke alqur’ani, ina karatun litattafai, kafin na mallaki karfi da hankalin kaina, na kasance ina yin bara gida-gida domin na sami abin da zan ci domin in rayu. Da na mallaki karfin kaina, sai na dinga yin sana’ar dako a kasuwa, a lokutan da ba ma yin karatu a makaranta, nakan je kasuwa domin na sami abin da zan tallafawa kaina. Bangaren iyayena kuwa, tun lokacin da suka kawo ni karatu, bansake ji daga garesu ba, hasali ma su da kan su ko sau daya basu sake komawa ta kaina ba, tun abin yana damuwata, har ya bi jikina, yanzu banajin komai kan hakan. A in da muke kwanciya kuwa, zamu haura mu dari, kuma ga wurin matsattse wan da dole wasu sai dai su gwamu da wasu kan rashin yalwar wurin kwanciya, bayan wari na daudar jikinmu, numfashi ma kadai a gauraye yake, wanda shi karan kansa wata mabuda ce ta shigowar cututuka daban-daban. Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, muna aiki da maraice a kasuwa, kusan lokacin magariba, na daukowa wata mata kaya da ta siyo tana gaba ina biyar ta daga baya, muna karasowa bakin kofar kasuwa, sai muka fara jiwo kara ta bindiga, mutane sai guduwa suke yi suna kokarin tserata da rayukansu, hakan ta sa mutane sai gwauruwa suke da junansu a halin fita daga kasuwar, sai faduwa mutane suke yi, ana take wasu, wasu a nan wurin suka rasa rayukansu. Ganin haka, na yada kayan matar da ke dauke a wuyana, na bi jama’a aguje da ke kokarin ficewa daga kasuwar domin su ceci rayukansu. Sai gudu muke yi, irin gudunnan na idan ba ka yi ka bani wuri, bugu da kari ga duhu sai kara shigowa yake yi, mune bamu tsaya ba har sai da muka kai tsakiyar jeji, kuma ga masifar duhu, saboda mun dauki awa biyar muna gudu, ba tsaiko. Muka tsaya tsakiyar jeji mu hudu ne, wata mata na tareda mu, sai wasu tsofaffi maza gudu biyu. Matar kuma gata dauke da tsohon ciki. Amma a haka take gudu kamar ba ciki a tattare da ita. Nan muka yada zango cikin jejin da bamusan sunansa ba, bamusan a ina yake ba, bamusan ina zamu nufa ba. Muna tsakiyar hutawa aka fara ruwa masu masifar karfi, dama tun da maraice munga alamun hadari, ba alamun ruwan zasu sauka, saukarsu kawai muka ji,dalili kenan da yasa muka fara sassarfa muna neman in da zamu labe domin mu buya daga shan kashin ruwan sama. Da kyar muka sami wani kwazazzabo mai zurfi muka shiga, duk da bai bamu cikakkiyar kariya daga shan kashin ruwan ba, ya taimaka wurin rage karfin ruwan daga dukan jikinmu kai tsaye. A lokacin ni ba ta kaina nake yi ba, na fi tausayawa matar da ke tare da mu, musamman yadda naga tana cira tana rawar sanyi, a duk lokacin da na kalleta na kuma kalli tsohon cikinta, sai kawai naji hawaye na kwaranyowa daga idanuwana. A haka ina tsaye har ruwan suka kammala sauka gaba daya, kallon da nake wa matar ya sa gaba daya banajin dukan ruwan. Wani abin tausayi, shi ne, wadannan tsofaffin da muke tareda su, a kalla kowannensu zai haura shekara saba’in, wannan shi ne dalili da ya kara tsayar da mu cikin jeji tsawon makwanni muna shan azaba da ganin bone. Domin kamar hadin baki, su duka biyu, suka kamu da rashin lafiya mai tsanani, ban yi zaton zasu rayu ba. Haka ni da wannan matar muke shan wahala wurin kulawa da su, musamman da yake tsofaffi da suke da bukatar kulawa ko ba ciwo bare ga dalili. A rayuwata, ban taba haduwa da mace mai dakakkar zuciya mai karfin hali irin matar da muke tareda ita ba. Duk da cikinta tsoho ne, bazaka gane hakan ba, yadda take tafiyar da lamura gata da sanin ya kamata. Haka nake fita farauta na nemomana abin da zamu ci, in da ita kuma take kokari wurin ganin ta gyara duk abin da na kawo ta sarrafa shi ya zama abinci, tsawon makwanni a jeji. In da muka tashi tukuru domin ganin mun nemawa wadannan tsofaffin magani. Da muka lura cewa sun sami sauki sosai, sai muka tashi daga masaukinmu in da muka mayar da shan kashin ruwa tamkar yin wanka.”
Gaba daya wadanda ke cikin motar hankulansu suka dawo kansa, wasu sai sharan hawaye suke yi, in da wasu ke ajiyar zuciya. Wasu kuwa suka bige da mamakin, wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwa a duniya. Shi kuwa mai tukin motar sai ya kunna musu wakar ZAINUDDEEN ZAIN mai taken ALAMJIRI wacce suka yi da wani mawaki dan Katsina da kuma Ranking Boy dai-dai in da yake cewa;
_ya baro uwa ya baro uba duk a kauye_
_Fadi-nan-tashi-cen burinsa safiya ta waye_
_Ina za ya dora kansa, ba sukuni a barci_
_Ba sutura mai kyawu, walla ba abinci_
_lafiya ta kaurace daga garesa_
_Babu kwanciyar hankali babu walwalarsa_
_sama da su dari suke kwanciya a daki_
_Malami guda daya ba ya dora su tafarki_
_iyaye da gwannati ya kamata duk mu lura_
_su ne fa suke girma su zamemna lalura_
_tun suna kanani tarbiyya sun kasa samu_
_mu duba abinda ke faruwa a makotanmu_
_kula da yaranmu wajibi ne ai a kanmu_
_Idan muka kula kuma lada ai zamu samu_
…………………………………………..
Haka dai wakar ta ci gaba da tafiya, sautin na tashi a hankali, ta yadda ba ya hana kowa ya ji zancen wani. Shu’aibu ya ci gaba da labarinsa.
“muka ci gaba da tafiya, tsawon kwana daya muna tafiya cikin jeji tun da muka baro in da masaukinmu yake har Allah ya kawo mu wani kauye, munsami kulawa sosai daga mutanen kauyen, kwana daya muka yi a garin sai ga mayakan boko haram sun yi wa garin kawanya. Suka zagaye mu, sai suka yi magana da wata amsa amo, cewar, idan mu mazajen mun aminta mu shiga yakin da suke yi su kuwa matan su bi su su tafi da su, da suka ga alamun ba za a amsa musu ba, suka shigo garin, haka suka dinga kama mutane suna yankawa ba imani, ba kokkotawa. Su kuwa matan suka dinga kama su, da sunan wai ganimar yaki. Ganin haka, na kaikaici idanuwansu na ranta a na kare, in da wasu mutum biyu suka biyo ni, da suka tabbatar da cewa ko shekara aka yi bazasu iya kama bahillace a jeji ba da gudu dole suka sallama suka koma wurin jama’arasu. Kun ji rabuwa ta da tawagar da muke tareda su. Nasan ba shakka ba jinina ba ne, amma naji rabuwa da su tamkar rasa wani bangare na rayuwata. Wanda har yanzu mikin yana tare da ni, musamman na matarnan mai ciki. Yanzu Allah kadai yasan halin da take ciki. Ni kuwa da na tabbatar na tsere musu a gudu na nemi wuri na zauna domin in sami karfin tafiya da ci gaba da neman hanya domin in koma asalin garina wato Bunza a jihar Kebbi.”
Gaba daya motar kowa ya yi shiru ya sha jinin jikinsa. Shi kuwa shu’aibu ya ci gaba da labarin ibtila’in da ya same shi sanadiyyar Boko Haram.
Kwanci-tashi har na fado garin Mubi, in da a nan ma harin Boko Haram ya tarar da mu, dalili kenan da yasa dole na yi kaura, na yi amfani da ‘yan kudi da na tara ta hanyar dako na shigo mota ya zuwa garin Yola. A Yola na sauka a wata unguwa da ake kira Anguwan Tana, a nan ne na hadu da wasu samari masu kirki, duk da talakawa ne, sun bani kulawa sosai yaddda ya kamata. Nan na dinga zama, duk da safiya nakan fita neman kudi, idan na sami aikin lebaranci ko dako nakan yi, a hankali ina tara kudi, har na sami guzuri da na tabbatar zai kai ni garina na Bunza a jihar Kebbi. Shi ne na shiga mota domin na koma gida.”
Yana kawowa nan ya yi shiru, suma dai wadanda suke cikin motar shiru suka yi kamar wadanda aka umurta. Cen wani tsoho da ke zaune daga tsakiya ya kada baki ya ce; “wasu lokuta mutane na bani mamaki musamman wadanda suke tura yaransu yawon almajiranci, sai ka ga an tura yaro almajiranci tun bai ma mallaki hankalin kansa ba, wani ko wando bai iya dorawa ba, baisan hagu bare damarsa ba amma a haka za a tura shi almajiranci, abin takaici sai a kaiwa malami shi, ba abincin da zai ci, ba kudin kula da lafiyarsa ba ko sutura a tatter da shi, mafi mamaki sai kaga lokcin da ake tura su almajiranci sai bayan an kammala girbe abinci ne. idan muka kalli garuruwa da suke dauke da ‘yan ta’adda galibi zaka ga sun fi yawan masu yawon bara ne da sunan almajiranci, yaro tun yana kankani zuciyarsa ta mutu da bara, ta ya zai girma ya nemi na kansa ko ya tsaya da kafafuwansa? Allah dai ya kyauta”
Ya fada bayan ya ja dogon tsaki. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa, driver kuwa sai sharar gudunsa yake yi, idan ya canja wannan wakar ya saka wannan.
DR. ZAIN
[2/4, 7:52 PM] Dr. Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
3⃣4⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_People will stare..._
_Make it worth their while._
*Shafin Masoya*
_Sis Naja'at_
_Aisha_
_Fatima_
_Zainab_
Kawayena na kaina
***CI GABA***
Haka suka ci gaba da tafiya cikin motar idan wannan ya bayar da nasa labarin, wancen ya bayar. Kwanci tashi har suka karaso garin Gusau, dole suka lallaba gudun kar su hadu da masu garkuwa da mutane. Suka karaso Sokoto, suka ci abinci suka karaso Kebbi.
Duk da cewa ta dauki lokaci mai tsawo batazo garin ba, fasali na garin bai rikitata ba. Aka saukar da su a tashar sir Yahayya Memorial Hospital Birnin Kebbi, kasancewar suna tareda wani tsoho da ta yi wa alkawarin cewa zata taimake shi, basu nemi motar zuwa garin kalgo ba, sai ta tsayar da wasu jama’a ta tambaye su in da sansanin *‘YAN GUDUN HIJIRA* yake. Aka sanar da ita cewa sansanin guda biyu ne, akwai daya da yake a bayan Oando bye-pass kenan, sai daya da ke unguwar malala quarters hannun riga da sabuwar makabarta. Ganin na malala quarters ya fi zama kusa da su sai suka nufaci cen. Ita da Bilkisu da dan tsoho, suka gangara gangaren malala cikin keke napep, duk in da suka ga taron jama’a sai su tsaya su tambaya, a haka har suka kawo daf da kofar gidan.
Gida ne da ba shafar siminti a bulon ginin haka ba fenti ba kyaure kai kofa ma babu, akwai fadi da gidan ta ciki amma duka kofofin dakunan ba wacce ke da gambu duka labulayya ne aka rufe kofofin da su. Gida ne da cikinsa akwai mutane sama da dari biyu, kama tun daga kananan yara ya zuwa manya maza da mata.
Da maraice suka isa gidan wurin karfe biyar da minti arba’in da wani abu, suka yi sallama da masu gidan, sai wata mata da ake kira Hauwa’u ta fito. Sajida ta yi mata bayanin daga in da suka fito. Bayan matar ta nisa, sai ta ce da su, gaskiya ita ba ta da damar karbar shi tsohon a gidan, amma tana zuwa, fitowa da zata yi bayan ta shiga cikin gidan, sai ta fito da wani saurayi dogo baki da shi mai suna Sani. Ta bar shi da su nan tsaye ta koma cikin gida.
Sajida ta sake kwashe labarinsu da ya dace ya sani ta gayamasa, ta kuma nuna abin da ya zo da su nan shi ne domin su taimakawa wannan tsohon ya sami wurin da zai fake. Sai da ya dauki lokci mai tawo kafin ya fara magana. “gaskiya ba za mu iya barin shi ya zauna nan ba” “saboda me ke nan?” Sajida ta fada cikin mamaki da son jin me zai fito daga bakinsa. “saboda nan da kike gani, duka iyalinmu ne kadai, ba wani wanda ba ya da alaka da mu duk yawanmu da kika gani kuwa, eh! A halin yanzu gwamnati ke biya muna kudin hayar wurinnan, amma asali mu muka saka kudin jikinmu, na matsananciyar shan wuya muka biya hayar gidan, kinga wani wanda ba muharramin matanmu ba bai dace ya zauna a cikin gidanmu ba. Kinssan duniya kumaa ta wuce tunaninmu, yanzu bamuda tabbasa cewa ku ‘*YAN GUDUN HIJIRA* ne da gaske, domin ba rubuce yake a fuskokinku ba, haka bamusan halin shi wannan dattijon ba. ‘yar’uwa naji labarin da kika bayar, amma ki sani muma mun shiga musiba da irin wannan hali da kuma kuka shiga, saboda haka nasan ‘yan boko haram ba zasu yi kasa a guiwa ba har sai sun cinma burinsu, hakan kuma zasu iya yi ta kowacce hanya. Kuyi hakuri”
Ta yi ajiyar zuciya mai tsawo a ranta tana kokarin neman mafita, amma ina duk abinda ta yi yunkurin tunawa, sai ya tafi kamar kura da ke kan taga. Kawai sai hawaye suka fara fitowa daga idanuwanta, ta kalle