Showing 33001 words to 36000 words out of 47716 words
Chapter 12 - 'YAN GUDUN HIJIRA Complete BY Dr. Zain.txt
rokon ubangiji da ya kare ta daga sharrin masharranta ya kuma datar da ita da gidan aljanna.
Masoyana na nesa da na kusa, banida baki da zan gode maku, musamman a dan karamin littafi irin wannan, amma naso ace zan iya bude zuciyata, da na nuna muku yadda soyayyarku ke shimfide a huhu da ruhi da kahon zuciyata, irin kun dai ganennan ana tare.
*TSOKACI*
Wannan season din, wato *KARSHEN ZALUNCI* ci gaba ne na _KUWWATUL KITAAL_, idan maikaratu bai manta ba, mun karanto season one _(KARAGAR TSAFI)_ season two _(KUWWATUL KITAAL)_ wannan shi ne season three *(KARSHEN ZALUNCI)*. Kar maikaratu ya damu ko da wanne season ka fara za ka iya fahimtar ina labarin ya dosa, amma idan baka karanta season one ba kafin ka fara wannan season na uku yanada kyau ka nema a shawarce, akwai lambata a jikin littafin, idan aka nema zan turo.
Idan maikaratu bai manta ba a karshen season one, su _JAUHARANU_ da _WALKINANU_ sun shiga hannun dakarun _SARKI SAMAKATUL BAHAR_ har aka killace su a cikin keji, domin yara su zo su dinga kallonsu a matsayin tsuntsaye, sun yi yunkurin su kubutar da kawunansu amma, a banza domin duk wani tsafi da suka sani sun yi amfani da shi amma abin ya ci tura, dole suka hakura suka ci gaba da zama a keji, abinci ma sau daya suke gani a wuni, hakan ta sa suka rame sosai har sai sun ba ka tausayi idan ka kalle su, labarinsu kuwa, dole aka rufe aka ki sanar da _SAMAKATUL BAHAR_ gudun hukunci da zai dauka kan mazauna garin kafin su _JAUHARANU_.
A karshen season two kuma mun ji yadda _GIMBIYA ZABZABATU_ da mahaifin _WALKINANU_ wato _WASHMANU_ suka sha alwashin karbo su tareda dauko ita _KARAGAR TSAFI_, tambaya a nan ita ce, _BAHARUL MAUTI_, gari ne da ke a karkashin ruwa kuma yana dauke da hadarurruka bila adadin, me zai faru da su _ZABZABATU_? Za su sami damar dauko _KARAGAR TSAFI_ kuwa? Za su kwato mutanensu kuwa? Cikin labarin komai zai warware.
Wannan season zai fi karkata ne gun fassarar mafarkin da _ZABZABATU_ ta yi har sau shida a season two, wanda zai dauke mu ya zuwa tarihin wani jarumin gaske, wanda sam baisan tsoro ba, kuma ga shi addininsa ya bambaanta da na su, sunan jarumin _AMJAD_, yana zaune ne a kasar _HERA_ da ke nesa sosai da kasar _FARETU_.
Ta yaya fassarar mafarkin zai alakanta da wannan jarumin? Ya halin su _RUSKINANU_ wanda ya mallaki *KUWWATUL KITAAL* maganin mutuwa? Duk za mu ji a wannan littafin da ikon Allah.
Wanne addini ne ake yi a kasar _HERA_? Duk za mu ji a cikin labarin.
*FARKON LABARIN*
Kasar _HERA_ kasa ce da ke dauke da wasu al’adu wadanda suka sabawa mafi yawa daga cikin kasashe, kasa ce wacce ta tara jarumai da manyan masana a fannoni daban-daban, kasa ce wacce ta hada da mafarauta da masu ilimin likitanci, amma duk wadannan a kan koyamaka ne gwargwadon inda matsayinka ya fada, misali wadanda za su zama jarumai dole ne su fito daga gidan jarumai, ko gidan sarauta, dan matsafi duk yadda ya kai ba za a bari ya koyi yaki ba, haka wanda za a koyawa tsafi dole ya fito daga gidan bokaye, haka sauran, doka ce diyan talakawa su koyi wani abu a kasar idan ba sana’a ce ba, kamar kera makamai ko wani abu da ya danganci aikin kwadago. Wannan dokoki da ke shimfide a kundin kasar, shi yasa kasar ake kallonta da tsaurin ra’ayi inda talakawan ke kallon gaba daya ba a masu adalci, duk da haka kasar tana kula da bai wa na gaba girmansa, duk da tana cike da zalunci suna nuna soyayya tsakanin junansu.
Kasar suna bautar duk sarkin da ke kan mulki, duk wanda ya ki sai ya biya da kansa. A haka abubuwa suka ci gaba da tafiya a kasar, har aka haifi jarumi _AMJAD_, sai dai aka yi rashin sa’a, domin mahaifinsa _SUMAIRU_ talaka ne sosai wanda ke sana’ar kera makamai.
Tun haihuwarsa, mahaifinsa ya ga abubuwan al’abi dangane da shi, mahaifiyarsa ta rasu ne sanadiyyar haihuwarsa, amma tun haihuwar ta sa, abubuwa suka fara canjawa mahaifin, idan da naira dubu yake samu a wuni, sai ya dawo samun dubu goma, wannan shi ya bashi damar kulawa da dansa ta hanyar siya masa duk abinda yaro ke bukata, a haka har ya kai shekaru takwas, a makaranta kuwa idan ana koyar da shi sai kayi zaton ya ma fi malamansu sanin abun, bayan kaifin basira da rikon abu ba mantuwa akwai shi da zuciyar jarumai, wanda kan haka har ake ganin ko ba ya da tausayi ne, karami ne amma akwai matsanancin karfi, wannan jarumta ta shi ita ta sa gaba daya sa’anninsa shayinsa suke yi, kai har na gaba da shi na tsoronsa duk da kananan shekarunsa.
*Note:* _duk seasons da nake kawowa online, ina katse su ne daga asalin yadda na rubuta su, saboda haka ba komai ne nake sakawa online ba, ainahin labarin, idan zan fitar a kasuwa zan sanar sai a nema, domin ko kashi talatin na labarin ban sake ba._
DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣7⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_kyawun budurwa asanta da kunya_
*Shafin Masoya*
Jega Village
***CI GABA***
*Cigaban labarin ‘yan gudun hijira.*
Tana kawowa nan da labarinta, suka yi shiru gaba daya, sai kallon juna suke yi cike da alamun tambayoyi a fuskokinsu, da ta fahimci tambayoyi suke so su mata kan labarin KARSHEN ZALUNCI ta ce, “kar wanda ya min tambaya cikinku, idan labari ne zan ci gaba da baku shi a duk lokacin da muka sami lokaci, a halin yanzu mu mayar da hankalinmu kan yadda zamu sami fita daga wannan jejin mai dauke da hadaruruka”
Suka girgiza kawunansu alamar gamsuwa da zancenta. Kana suka shiga shirin daukar hanya na wannan tafiya da ba a san ina za a dosa ba, kawai dai titi ne mafarkinsu.
Haka suka cigaba da tafiya shiga wannan ramin fita wancen, shiga wannan hadarin fita wancen, har rana ta yi zafi sosai, ganin haka suka sami wuri suka labe cen cikin wani katon rango da ya samu ta sanadiyyar ruwa da ke saukowa daga kan falalen dutsi. Nan suka yi sallah, suka dan sami abinda suka sakawa cikinsu, kana suka ci gaba da tafiya.
Har zuwa faduwar rana suna tafiya, ba gari ba alamunsa, da rana ta fadi, suka tsaya suka yi salla, sai suka hura wuta domin su duma jikinsu. Cikinsu sai kiran ciroma yake, kaancewar sun dauki lokaci ba tareda sun ci komai ba. Duk da haka cikin walwalaa suke firarsu, duk da ana cewa wai yunwa ba ta da sabo.
Ganin sun nutsu, sai ta ci gaba da basu labarin KARSHEN ZALUNCI.
*DANDANO DAGA LITTAFIN KARSHEN ZALUNCI.*
Kamar yadda muka sanar jarumi Amjad ya taso ne hannun mahaifinsa wanda yake sana’ar kere-kere, hakan ta bashi damar sanin makamai sosai da amfaninsu da kuma sanin yadda ake sarrafa su, da yake kasar Hera kasa ce da ta haramtawa duk wani dan talaka koyon dabarun yaki, Amjad bai samu damar shiga makarantar koyon yaki ba, amma a haka yake labewa yana kallon yadda ake koyar da fada azuzuwan da ake koyar da jarumai, idan dare ya raba tsakiya sai ya dinga bitar abinda ya koya, hakan ta bashi damar zama gwani wurin iya sarrafa takobi, da iya harba baka, domin zai iya harba baka, har tayi tafiya tsawon kwanaki uku. A karfi kuwa sai ya dauki giwa komai girmanata ba tareda wahala ba, duk wannan abin da ke faruwa da Amjad, masarauta ba ta sani ba, amma mahaifinsa ya san komai, duk da da farko yana masa fada daga baya ya dinga karfafamasa ta hanyar kera masa makamai nashi na kansa musamman.
Jarumi Amjad da ya girma sai ya zama wani saurayi mai kyau sosai mai kwarjini a idanun mutane haka a zuciyoyin ‘yan mata.
Wata rana suna tafiya da abokaninsa cikin jeji suna yawon farauta, kwatsam sai wasu dakaru na makociyar kasarsu suka tare su da niyyar illata su, dakarun za su haura dari, su kuwa su biyar ne kadai, ganin mutum dari sun zagaye su, gaba daya hankalinsu ya tashi, sai rawar jiki suke yi, Amjad ne kadai tsaye a kafafuwansa, su duka dauke suke da makamai banda Amjad domin shi kadai ne daga gidan talakawa, kuma a dokar kasar ba a bari talaka ya koyi fada, a cewarsu bai dace da shi ba. Ganin abokaninsa sun tsorata, ya zare takobi daga hannun daya daga cikin abokanin nashi, ya tinkari wadannan dakarun, ya fara saransu yana sukarsu, su kuwa sukai masa kawanya. Suka fita batun abokaninsa suka yi wo kansa da niyyar illata shi, suka zagaye shi sai kawo mashi sara da suka suke yi, yana gocewa shima yana kokarin kai musu sarar, cikin kankanin lokaci ya illata su gaba daya. Cike da mamaki abokaninsa suka fara kallonsa. A kan hanya suke tambayarsa, ina ya koyo irin wadannan salallai na fada, yaki ya sanar da su.
Da suka dawo gida, ya tafi bakin aiki a kasuwa domin komai ba su kamo ba ranar, ya je wurin mahaifinsa domin ya gani ko da aikin da zai taya shi, su kuwa abokanin nashi suka wuce makaranta, domin an umarce su da su zo karatun maraice, shigarsu ajin da dan wani lokaci aka fara masu darasi. Daya bayan daya suke fitowa domin su fafata da malamin nasu, kasancewar yana so ne ya gwada hazakarsu, har ya zo kan wanda Amjad ya yi amfani da takobinsa, wurin tarwatsa dakaru dari. Daga zare takobinsa, sai malaminsu ya fara kallon takobin cikin mamaki, bayan sun kammala darasi, sai ya kira shi ya ce da shi, “me ya faru da takobinka, na ganshi da jini na mutane, kuma da alama ka fafata ne da mutune da dama?” nan ya fara rabon idanu, yasan idan ya yi karya, fille masa kai za a yi domin shi ne dokar kasar. Dole ya kwashe labarin gaba daya ya sanar da malaminsu, sai da malamin ya dade yana tunani kafin ya nisa ya sallameshi.
Amjad na kan hurawa mahaifinsa wuta shi kuwa yana kokarin narke darma da zai kera wani takobi, kusan faduwar rana, sai ga dakarun sarki sunzo cikin sauri, suka jajibi Amjad, mahaifinsa ya yi yunkurin shiga tsakani, suka tunkude shi, ya fadi, shi kuwa Amjad ya rigaya yasan laifin da ya yi, kuma yasan idan ya yi yunkurin fada da su, gaba daya zuri’arsu za’a shafe daga doron kasa. Ya bi su har fada. Suka gurfanar da shi gaban sarki.
Wani da ke gefen daman sarki ya matso ya fara magana, “Amjad dan Sumairu, an kamaka da laifin taka dokar kasa, ta hanyar nuna salon fada, wanda ‘ya’yan masu mulki kadai keda wannan damar, me za ka ce?”
“ba shakka hakan ta faru, amma ranka ya dade, da ban aikata haka ba, da yanzu diyan manyan dagatai a wannan kasar sun rasa rayukansu, mumfita farauta ne, dakarun kasar Jaiha suka zagaye mu da niyyar illata mu, ganin abokanina duka sun shiga tashin hankali, shi ne na karbi takobin daya daga cikinsu na ceci rayukanmu”
“ba shi ne bayani da nake so kayi muna ba, muna so musan wa ya koyar da kai salon fada?”
“ba wanda ya koyar da ni fada ranka ya dade”
“ina aka taba yin fada, har illata mutum dari kuma kace ba koyar da kai aka yi ba, idan ka batamuna lokacin kaa san hukuncinka”
Nan ya kwashe duk yadda aka yi ya iya fada ya sanar da su. Bayan fada ta dan yi nazarin zantukansa, suka kuma auna maganganun sai suka yanke masa hukuncin kora ta har abada daga garin, domin hukuncinsa kisa ne, amma ganin taimako ne ya yi, kuma ba koyar da shi aka yi ba shi ne aka sassauta masa aka kore shi kawai daga garin. Mahaifinsa yana kuka, dole ya bar shi ya tafi.
Wadanda suka raka shi, ba su rabu da shi ba har sai da suka fita da shi iyakar kasar. Ya duba hagu da dama gabas da yamma ba a binda idanunsa ke gani illa faifan jeji wanda ke cike da sunkuru da falalaen duwatsu manya. Nan ya ci gaba da tafiya har ya kawo inda hankalinsa ya kwanta, ya tsaya a nan ya shiga jeji ya saro manyan itace, ya kafa ‘yar rumfa da sunan daki, inda zai dinga kwana.
DR. ZAIN
[2/3, 5:04 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾
2⃣8⃣
Na
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_
® *PEN WRITERS ASSOCIATION*
```QUOTE OF THE DAY```
_sammako ake bugawa idan ana so a Kama fara_
*Shafin Masoya*
MRS. ISMA'IL
SISTER NAJA'AT
AMEESHAH
MARYAM HAMZA FUNTUA
***CI GABA***
*Cigaban labarin ‘yangudun hijira*
Su duka suka yi shiru, sai kallon juna suke yi. Bilkisu ta nisa ta kalli mahaifiyarta ta ce, “lallai wadannan sunada tsattsauran ra’ayi, wane irin dokoki ne a wannan kasar da ke kokarin haramtawa talaka motsawa da taka tasa rawa wajen nuna gwannta ko hazakarsa, talakawa ai mutane ne, kuma da yawansu zaka tarar sunada baiwa wacce ma ta fit a ‘ya’yan masu kudin, amma duk sai a kange su a hanasu shiga inda zasu nuna baiwar tasu, sai kiga kasa ta kasa cigaba”
A duk lokacin da Bilkisu ke magana, sai kaga mahaifiyarta ta kashe kunne tana saurara, saboda hikima da ke kunshe cikin zantukanta. “haka ne mamanne, amma ai ko a wannan zamanin idan kika duba kusan duk daya ne da kasar HERA”
“haba Inna, daya fa?” ta fada cikin zazzaro idanu.
“eh! Sosai, ba bambanci. Ki duba kiga yanzu ko aiki za ka je nema, idan ba dan masu hannu da shuni ba ne kai da wuya ka samu, sai kiga talaka da kwalinsa mai kyawu amma ‘ya’yan masu mulki za a dauki mukamin da ya dace da na talakan a basu, sai su dare kujerar su kasa tabuka komai, kullum sai a ga kasa na ci baya. Idan kika dawo bangaren damar karatu, wato daukar nauyin karatun dalibai, sai kiga dan talaka ya cancanci a fita da shi kasashen waje ya je ya yi karatu, amma sai a dauki wannan damar a baiwa yaran masu mulki, su je cen su yi ta aikata masha’a karshenta su dawo ba karatun su kawo wata mummunar akida. Kinga kuwa ba bambanci, gara ma su kasar HERA sun nuna doka ce, da wadannan da ke aikatawa a dunkule.”
Saurayi ya yi ajiyar zuciya, yanaso ya furta zance, amma zantukan Sajida sun rigaya sun gamsar dole ya yi shiru. Ganin sun fara gyara zama da niyyar su kara hutawa, ta dube su ta ce, “me kuke nufi? Babu amfanin badi fa ba rai, da muguwar rawa, kuma gara kin tashi. Zaman baya ba ya yi wa tafiyar da ba fashi. Kar mu bata rawarmu da tsalle, kada mu yi jifar gafiyar Baidu, kada wahalarmu ta tashi a iska, idan muka sake jiki muka zauna, su fa masu biyar mu, ba sakewa za su yi ba, ba za su tsaya ba har sai sun tabbatar da mun shiga hannunsu, idan har su da ke yunkurin kama mu, basu huta ba, babu dalilin mu mu tsaya hutu. Mun fa dade muna tafiya, inada yakinin inda zamu nufa dole kusa da fita hanya ne.”
Suka tashi cikin tsalelen dare, suka dauki hanya, duk da yunwa a taredasu, jikinsu da kwarinsa. Sajida ce a baya inda saurayi ke gaba, ita kuwa Bilkisu a tsakiyarsu.
Suka ci gaba da tafiya cikin jeji, ga sanyi ga duhun dare ga sunkurmin jeji, ba abinda ke shiga kunnuwan mutum irin kuka da sautuka na tsuntsaye da kwari da ke kwance a ramukansu. Cen suna cikin tafiya suka hango haske na wuta a dokar jejin, alamun akwai mutane kusa da gun, suka ci gaba da tafiya, duk da sun dauki lokaci mai tsawo suna tattaunawa kan su is da gun ko su ratse daga kan hanyar, gudun su fadawa zago bayan gara suke gudarwa. Jiwo sautukan na mutane ya sa Sajida ta umrce su da su bi ta gun, amma idan sun kusa kai sai su labe, domin su shaida abinda ke faruwa, idan ‘yan boko haram ne, sai su canja hanya, domin ta yiwu ba su ba ne, sai su nemi taimako. Duka suka amince da hakan.
Haka suke jan jiki a kasa, da suka karaso daf da taron gudun hango su, suka sami wuri suka labe, amma suna gani da jin duk abinda ke faruwa.
A tsakiyar filin wani ne tsaye kyam, zaka gan shi wani dan fyarat da shi, duk tsananin sanyinnan da ake yi shi ba riga a jikinsa, hakan zata baka damar ganin layu da karhuna da ke zagaye a wuyansa da hannayensa da kugunsa. A cen gefensa wasu ne a zugunne kowannensu sai bari yake yana rawar kafa, kamar wanda ake tunzurawa. Shi kuwa sai kirari yake yi wa kansa. A cen dayan gefe kuwa makadi ne da ke buga ganga yana zuga wannan dan taurin, shi kuwa yana ririta hadi da dada kansa.
“ni ne kafiri da ba ya sallar safe, ni ne na Salima duk wanda ya ji haushina zai mutu. Ni ne kafirkafir da ba kafiri ba amma nafi kafiri kafirci. Yau ina wanda yace ba ni ba ne na aikashi lahira nan take. Ni ne dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna daidai. Ni ne murucin kan dutsi ban fita ba sai da na shirya, ni kuturwar uwa ce, zama da ni ya zama dole. Ni ne lange-lange mai ramar keta, ni ne…tsufa da ni ya zama dole, Allah ya kashe mijin kyaklkyawa, ana jana’iza muna kai kaya. Yaro ka ja da mu, mu ja da iyayenka…….”
Sai kalamai yake wadanda ke kunshe da shirka da kuma habaici.
Bilkisu ta kalli mahaifiyarta, ta ce “wadannan kuma su waye? Amma dai Inna kafirai ne, naji yana fadar ba ya sallar safe”
“Wadannan ‘yan tauri ne da ke fitowa farauta” ta fada a lokacin da take kokarin mikewa tsaye
“inna ya ke nan, yanzu wurinsu za mu je