Showing 144001 words to 147000 words out of 170683 words

Chapter 49 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7227

haka. Mu albarkanku muke nema, indai bazan sayama Daddy abu dan neman albarka ya dawo min da shi ba kaima haka nake fata daga gareka”. Abba dake murmushi sai ya jinjina kansa da nisawa. Ya ce, “ALLAH yay miki albarka. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki....” ya dinga jera mata addu'oi masu ratsa zuciya Ammah na tayashi kafin suka fito.
Anan kam saita kira Hawwah akan tazo ta raka Lulu kowane ɗaki. Hawwah ce tai mata rakkiya, inda suka iske Umma cike fam, amma saboda shawarar da Hajiya Naqiba data kira ta labartama mata zuwan su Lulun yasata dannewa ta tarbeta da fara'ar yaƙe, ita kuma Lulun sai ta kasa sakin jiki da ita dan ita kam dai haka kawai taji Ummah batai mata ba, basu wani jimaba Lulu ta ajiye mata ƙaramar leda ta miƙe, sai hakan kuma ya sake zafar Umma. Ɗakin Mama ma an mata tarba ta mutuntawa, nan ma sai sukafi ɗakin Umma daɗewa, dan duk da Mama taji hassadar kasancewar wannan zukeƙiyar yarinya ƴar masu kuɗi ba wani acikin ƴaƴanta ya samu ba ta danne a ranta ko a fuska bata nuna ba, sai godiyar ledar da Lulun ta ajiye mata ya shiga jerawa. Ɗakin aunty amarya kam tarba suka samu kamar wata ƙawa. Dan tsokanarta ma taitayi suna dariya. Sunfi jimawa anan fiye da ko'ina kafin su koma ɗakin Ammah bayan itama ta ajiye mata ledar, bakuma komai bane aciki sai kayan turaren wuta data ɗiba musu da su cin-cin. Itama Ammah ta kawo mata harda turmin zani biyu su Asma'u kuwa kayan kwalliya ta basu jiya da sukaje. Basu zauna a falo ba suka nufi bedroom ɗin su Hawwah ɗin inda ta maida break fast. Duk da Hawwah zata iya ɗan girmar Lulu da ko shekara biyu ne jikinta ta saki da matar yayan nasu, hakan sai ya saka Lulu sakewa abunta dan wayayyace dama kai babu duhu. Duk da ba son cin abincin take ba sai gashi ta saki jiki sunci tare da Hawwah suna hira cikin mutuntawa, anan ne ma Lulu ta samu damar sake jin matsalar Hawwah ɗin sosai, a ranta kuma ta ɗauki ƙudirin taimaka mata, dan haka ta amshi address ɗin gidan nata a cikin hikima batare da Hawwahn ta fahimta ba. Bayan sunyi sallar azhar falo suka dawo wajen Ammah, cikin hikima taita jan Lulu a jiki ganin bata sakewa idan suna tare, da yake abune daga cikin abinda take ƙishirwar samu sai gashi ta saki jikin nata fiye da yanda sukai zato, dan hirar tasu ne ta karkata akan yanda matsalolin fyaɗe ke ƙara yawaita da yanda wasu ma yaran kan rasa ransu a take ko a cutar da su ta hanyar saka musu cuta, da yanda wasu iyayen kan rasa ransu adalilin hakan kosan ɓoyewa saboda kar duniya taji ƴaƴan su tozarta da su kansu. Lulu ta ce, “Wlhy Ammah nakanji kamar na dinga kashe irin waɗan nan aladun da hannuna, akwai case ɗin wata yarinya da har yanzu yake cimun rai duk da shegen na prison kusan shekara uku kenan, danni duk wanda nasan na samu nasarar alƙali ya turashi prison akan wannan laifin cigaba nake da bibiyasu a prison ɗin dan karma ayi amfani da wata dama a sakesu ina nan baki buɗe. Yarinyar tana nan ta zama mahaukaciya kamar yanda Nanny ɗina ta kasance kafin mutuwarta....”
Wasu irin hawaye suka zubo mata masu azabar zafi saboda tuna mata da abinda ya shuɗe kuma yake sosa mata zuciya da zama sanadin komai da ake kallon zagaye da rayuwarta a yanzu.........✍️







_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣7️⃣






........Yanda take kuma ya tadama Ammah hankali matuƙa, ta dawo kusa da ita da jawota jikinta ta rungume tana jin itama hawayen na cika mata idanu. Yanda Lulu ke kukan nan zai tabbatar maka al'amarin na matuƙar taɓa mata zuciya, dan har Hawwah sai da tai hawaye. Sosai Ammah taji ƙarin ƙaunar Lulu a zuciyarta. Sai da tai shiru sannan ta fara mata nasiha da bata addu'oi akan ta dage ta dingayi da yawaita karatun Alkur'ani hakan zai dinga rage mata nauyin zuciya, dan masu irin ayyukansu saboda yanda suke tara abubuwan ɓacin rai da damuwar al'umma daga ƙarshe sai kiga sun kamu da hawan jini dana ciwon zuciya. Sosai yanda Ammah ke jero addu'oi a bakinta taji ta sake birgeta da kwaɗayin akan samun ilimin addini. A haka su Asma'u suka shigo ƙarfe biyu. Da mamaki Ammah ke dubansu dan tasan dai sai biyar suke dawowa daga islamiyya duk ranar weekend. Hawwah ta ce, “Kukuma fa naga kun dawo?”. Kallon juna sukayi kafin Maryam tace, “Adda haddace bamu iya ba shine muka gudo, kin san dai malam Jabeer ba sauƙi wlhy”.
Ammah data tsira musu ido tace, “Duk karatun da kukai ɗazun da asuba. Kudai faɗi wani ba wannan ɗin ba. Wai Maryam yaushe ma kika fara ƙarya?”.
Ƙasa Maryam tai da kanta tana shafa ƙeya, Asma'u dake ƙara rakuɓewa jikin kujera ta ce, “Ammah gaskiya da gaskiya dai saboda Aunty muka gudo, kinga fa yini zatayi amma mu banda mu. ALLAH muna son muma mu yini tare da ita shine mukai shiri tare da Adda Maryam idan akai salla muyima Malam Jabeer ƙaryar zamu rakaki asibiti”.
Hawwah dake dariya tace, “ALLAH ya shiryeku Ammahn kukai ma sharrin ciwo kenan?”.
“A'a wlhy mu bamuce kowa ba, kawai dai munce zamu rakata asibiti”.
“Kuma ya yarda? Bayan nasan Malam Jabeer da shegen bin ƙwanƙwanto”.
Dariya Asma'u tai tana kallon Maryam, ita kuma ta harareta alamar dai akwai wata a ƙasa. “Munafukai mi kuke ɓoyewa?”. Cewar Hawwah tana kallonsu cikin waro ido. Alamar zip Asma'u taima bakinta da faɗin “Ba ruwana ba'a bakina ba”. Lulu da ke murmushi ta ce, “Haba Auta bamu musha mana”.
“Aunty ba faɗar bane matsalar, sai kun gudu gidajenku ta jibgan a ɗaki ko Ammah bazata bari ta sani ba”. Ranƙwashi kuwa Maryam takai mata. Da gudu tabar wajen tana dariya. “Sonta yake ya kasa gaya mata, gashi kuma ya tsaya kallon ruwa kwaɗo yay masa ƙafa. Dan ga wani tauraro mai babban haske ya faso kai da ƙarfinsa”. Binta Maryan tayi suka shige ɗaki da gudu. Kai kawai Ammah ta girgiza da faɗin, “ALLAH ya shiryeku”. Yayinda Hawwah da ke dariya ta ce, “A gama ɓoye-ɓoyen intai wari maji ai”. Lulu dai murmushi takeyi dan komansu burgeta yake yi. Bakomai ya jawo hakan ba kuwa sai yanayin rayuwar data tashi a ciki ita da nata ƴan uwan. Bayan su Maryam sun cire Uniform suma falon suka dawo aka ɗora hira, anan sukaci abincin da aunty Amarya ta gama, bayan sallar la'asar Maryam tai zaman yima Lulu kitso. Dan nakan Hawwah ta gani ya burgeta ta tambaya duk da ba son kitso take ba. Jin Maryam ce tayi sai tace itama aimata ko kaɗan. Shine sukai zamanyi suna cigaba da hira harda Ammah. Nasreen da suka dawo daga makaranta tana zaune a cinyar Lulu suna shan chocolate dan itama shazumamun ce kamar Lulun. Sallamar Smart ta sakasu tsagaita dariyar da sukeyi dan Asma'u ce ke kwaikwayon Muryar malaminsu Jabeer dake son Maryam wai idan ya ganta har ƙara maƙewa yake yi. Akan Lulu ya fara sauke idanunsa kafin yabi sauran da kallo, ya ƙarasa takowa cikin falon yana kaiwa zaune da faɗin, “Miyay muku daɗi haka kuke kwasar dariya har tsakar gida kun cikama mutane kunne? Ammah duk sun zagayeki sun dameki”.
Cikin murmushi ta ce, “A'a basu damen ba Hydar, ai ko kurama da ƴaƴanta take wasa a jeji. Sai yanzu muke ganin ka”.
“Wllhy ki bari dai Ammah. Da ga wani waje mai nisa muke fa, kin san Ahmad da shegen kutse-kutse can wani ƙauye ya samo gona zai gyara yay gidan gona a wajen shine fa mukaje dubawa”.
“Kai masha ALLAH, ai haka mukeso mu kuyita shiga irin hakan dan nan gaba kaɗan kune manyan goben.”
Murmushi yay cikin jinjina kansa. Kafin ya maida hankali ga ƙannensa da ke gaishesa. Idon Ammah ya sa Lulu faɗin, “Sannu da dawowa”. Sai da ya maimaita kalmomin guda uku a zuciyarsa yana mai ɗan kafeta da kallo, sai kuma ya janye shima cikin basarwa ya ce, “Yauwa ya gidan”.
Abinci Asma'u taje ta kawo masa, sai cewa yay ta maida baya jin yunwa, garama in sunada fura dan yasan dai Ammah bata rabo da ita. Asma'u tace masa akwai, taje ta ɗibo masa a fridge ta kawo masa. Daga haka suka cigaba da hirarsu Lokaci-lokaci yana satar kallon Lulu da akema kitso masu ƙyau. Wajen shida ya kalla agogo da faɗin, “Ku wannan kitson yaushe zaku gama shi har mu wuce? Gashi ina son mu biya ta wani wajen”.
“Ina? Ai ni nan zan kwana yi tafiyarka”. Cewar Lulu da iya gaskiyarta. Murmushi Ammah tayi, yayinda Smart dake mata kallon mamaki ya ce, “Kwana fa? Kin manta gobe Monday zakiyi resuming office?”.
“Ba damuwa jibi naje”.
Murna su Asma'u suka fara yi zata kwana. Ya hararesu duk sai suka nutsu. Ammah dai bata ce komai ba har sai bayan sallar magrib da ya shigo ya sameta a ɗaki, lokacin su suna can ɗakin suna tasu sallar. Zama yay kusa da Ammah, hakan yasata yin addu'a ta rufe Alkur'anin. “Ba dai tafiyarba ko?”.
“Da haka nake so dai ta shirya, da anyi isha'i sai mu wuce dan ina son mu biya ta gaida Kakanta ɗazun Uncle Yousuf ke faɗamin baya jin daɗi ya dawo daga Legos ɗazun, gashi kuma tana batun kwana anan”.
“Karka damu zan mata magana. Amma Aliyu sai nake ganin akwai wani ɓoyayyen al'amari a rayuwar yarinyar nan dake damunta, na fahimci hakanne a ɗan firarmu da ita ta ɗazun. Sannan bata son kaɗaici, dan ta roƙeni na baku Asma'u ta koma can da zama. Danace mata Abbanku bazai yarda ba ina kula da ita sai da idonta ya cika da hawaye. Mizai hana a ɗan samo mata ko tsohuwa haka da zasu zauna tare, sannan kai kuma ka ƙara ƙaimi wajen janta a jiki dan ka fahimci minene damuwarta. Ko yaya ta sanar maka itama zataji nauyin ya ragu mata a zuciya. Ashe mahaifiyarta bata raye kuma?”.
“Ta rasu, tana haihuwarta. Inasha ALLAH zan yi iya ƙoƙarina”.
“ALLAHU akbar. ALLAH ya gafarta mata. Wlhy duk sai yarinyar ta sake bani tausayi. Gata da sauƙin kai da sanin darajar mutane. Sai kuma yanda na fahimta akan aikin nan nata kamar zafinta akan al'amarin fyaɗe nada alaƙa da wani abu daya sosa ranta gaskiya. Ya kamata dai ka zama mai haƙuri da dinga ƙarfafata”.
“Insha ALLAHU Ammah zan yi iya ƙoƙarina. Batun Asma'u kuma haƙuri zakuyi ta koma can ɗin tunda tana son hakan. Kodan ma tafiyar nan dake tunkarowa.”
“To bazance A'a ba, amma ka samu Abbanku da maganar kadai sanshi. In akan tafiyane kuwa bazai yiwu dama a barta ita ɗaya ba. Ko ita da Asma'u kawai dole cikin samarin nan wani ya koma can ya dinga kwana da su”.
“Hakan ma yayi Ammah. Duk yanda kikace haka za'yin”.
Sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha'i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaɓa Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah ɗin shagwaɓa sai Smart ya zama ɗan kallo. Dan mamakin yanda tai bala'in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a ƙanƙanin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin ƙyautukan data raba musu ɗazun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baƙin wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron ƴaƴanta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba'a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo ɗaya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart ɗin suka shigo da tace yaje ita zata je ɗakin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko'ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai ɗakin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daɗi tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haɗa Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daɗin wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep ɗin ɗan anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep ɗin suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke ɗakin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake ɗan murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daɗi mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.
A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep...”
Yanda Dadan ke maganar a zafafe da ɗaga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin ɓata fuska amma ta dakatar da ita........✍️







_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣8️⃣






.......Itama dakatar da itan abinda tai niyyar sake faɗan da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai ɓace. “Wai miye haka kuma ban son ƙaranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”
Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama'ar ɗakin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taɓe baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin daɗin jiki Baba ya balbale Dada da faɗa, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki.....


Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buɗe musu suka shiga, gaba ɗaya kayan na'a hannunsa har handbag ɗinta ma. Har ɗaki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daɗin abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login