Showing 114001 words to 117000 words out of 170683 words
sai ruhinta ya kasance cikin sallama tai alfahari da haihuwarki da jin bata bar bayan a banza ba. Mawaddat babu ruwan mutuwa da yanzu kika fara rayuwa, tana ɗaukar ɗan cikin ciki ma tabar uwa, alokacin da kike jin ke kin fara rayuwa wani ma a ranar aka samar da cikinsa. Ki dawo cikin hankalinki ki koyi darasi a duniya ba sai duniya ta shirya koya miki ba. Dan ita ɗayan biyu ce. Ko ka koya a yayin da take koyar da waninka, kota koyar da kai a lokacin da guri ya ƙure maka. Zaɓi ya rage naki”.
Da ga haka ya tura mata wayar ya miƙe yay wucewarsa toilet. Harara kawai ta bisa da shi ƙasa-ƙasa. Dan gaba ɗaya jitai kamar an danne mata baki a sanda yake maganar. Bakin ta taɓe da matsawa ta ɗauka wayar tasa ta fice abinta. Sai dai tana komawa ɗakin nata ta zauna a bakin gado da nufin kiran Uncle Yousuf hakan ya gagara. Maganganunsa ne suka shiga dawo mata, musamman akan yima mahaifiyarta addu'a kuma zatai farin ciki da ita daya faɗa, samun kanta tai da kiƙewa zumbur ta nufi toilet, babu jimawa sai gata ta fito da alamar alwalar tayi. Wardrobe ta buɗe ta ciro abaya ta saka tare da naɗa gyalenta a kanta ta kabbara sallar.. dai dai nan ya shigo ɗakin shima, dan haka kawai zuciyarsa ta kasa nutsuwa harya fara cire kaya zai yi wanka ya fasa ya biyota dan yaga zatayi sallar. Karo na farko zuciyarsa ta tsarga ganin yanda take salla babu wani bin ƙa'idojinta yanda ya kamata. (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa da ɗunbin takaici. Ashe dole abubuwa suke rikicema yarinyar nan dan babu nutsuwa ko nagarta a cikin al'amarin ibadarta. Tabbas rashin tsaida ibada tamkar wani dafin allura ce a jikin ɗan adam mai karya masa garkuwar nagarta da ɗaurasa akan laifuka. Ashe al'amarin nata ya gawurta da yawa har haka. Zafin rai da takaicin iyayenta ya sake mamaye masa zuciya, domin fa in har ɓera da sata to a bincika itama daddawa nada wari. Shin mi mahaifinta da matar babanta dama Uncle Yousuf keyi haka har balagaggiyar yarinya mai shekaru da yake da tabbacin sun haura ashiri amma bata iya salla ba? Amma a ilimin boko da anyi magana zata iya bugar ƙirji ta kira kanta mai ilimi. Oh ALLAH a wane irin zamani muka tsinta kammu da tarbiyya ke neman kufcewa iyaye saboda soyayyar ƴaƴansu?. Wannan al'amari ya tayar masa da hankali matuƙa, ya tuna lokacin suna yara, idan lokacin salla yay sukaƙi barin wasa suje suyi sai dai kaji saukar tazbahar Ammah a jikinka kawai. Idan ko bakayi ba ranar ko kulaka batayi sai tace ita bazatai magana da wanda yafi son shiga wuta ba. Amma yau sai ga shi wadda ke amsa sunan matarsa bata iya salla ba. A hankali ya jingina da ƙofar yana mai harɗe hannayensa a ƙirji da lumshe idanunsa abubuwa masu yawa na masa kaikawo a zuciya, lallai akwai aiki, dan yaƙine babba garesa akan yarinyar nan, shi duk ma sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi..
A ɓangaren Lulu tunda ta idar idanunta ya sauka akan Smart kamar wani mayan ƙarfe. Sai da taji gabanta ya faɗi musamman da abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata a rai, amma sai ta basar tama miƙe tana naɗe abin sallar. Sam Smart shi bai san da ta idar ba. Dan idanunsa a lumshe suke ya afka duniyar tunani. Samun kanta tai da tsura masa idanu, yayinda kalaman Nadiya na waccan ranar na dawo mata a zuciya. Kamar wadda aka tsawatarwa sai kuma ta ɗauke idanunta cikin yamutsa fuska tana jan tsaki. Duk da bai san mi take jama tsakin ba saukarsa a tsakkiyar kansa ya sashi ɗagowa cikin nutsuwar nan tasa ya buɗe idanunsa a kanta.
“Gadin na miye?”.
Ta faɗa cikin ƙarfin hali dan ba ƙaramin tasiri idanunsa keyi a duk sassan jikinta ba. Maimakon bata amsa ɗauke kansa yay, hakan kuma sai ya tunzura mata zuciya. Ta buɗe baki zata fara masifar tata yay gyaran murya kaɗan, kamar zata share sai kuma dai ta jiyo ta ɗan kallesa cikin harara tana ƙoƙarin warware gashinta. Ido suka haɗa ta mirrorn ta balla masa harara ta ɗauke nata. Shima ɗauke nasan yay ya maida kan gashinta mai tsaho da alamun samun gyara ya sashi yin wani ƙyau na musamman da sheƙi duk da a jiƙe yake a yanzu. Knocking gate da ake da ɗan ƙarfi ya sashi haɗiye maganar da yay yinƙurin yi. Agogon dake a ɗakin ya kalla sai kuma ya buɗe ƙofar ya fita. Ƙaramin tsaki yaja lokacin da ya fito harabar gidan sosai yaji bugun ƙofar babu ƙaƙƙautawa, sai da yasa key ya buɗe sannan ya zare sakatan. Da sauri Huwaila taja baya tana sissine kanta. Sai da ya gama kallonta ita da kwandon hannunta sannan ya matsa mata fuskarsa na ƙara tsukewa, dai-dai nan napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin, dakatawa yay da ga yunƙurin rufewar da yake saboda hango Asma'u na fitowa a Napep ɗin. Fuskarta da murmushi ta ƙaraso garesa tana faɗin, “Yaya ina kwana”.
“Lafiya Lau” ya amsa mata idonsa akan kayan hannunta, itama kallon hannun tayi har sannan fuskarta da murmushi ta ce, “Yaya abincinku n.....” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda hango Huwaila da tai a ƙofar shiga falon ɗauke da kayan abinci itama, da sauri ta kalli Yayan nata kamar zatai magana dan ita bata san da zuwan Huwaila ba. Ganin yay gaba abinsa ya sata bin bayansa batare data faɗi abinda ke bakin nata ba. Kallon juna sukai ita da Huwaila da ke hararta ta ƙasan ido, Asma'u ta ɗan girgiza kanta cikin basarwa ta ce, “Adda ai ban san nan zakizo ba da mun taho tare”.
“Zaku shigo ne ko zaku tsaya surutu”. Smart dake kaiwa zaune cikin kujera ya faɗa. Shiga sukai da sauri, kowa ya ajiye kayan hannunsa suka gaishesa. Amsa musu yay da kulawa, sai kuma Asma'u cikin zumuɗi ta ɗora da faɗin, “Yaya ina auntyn?”. Ɗan jimm yay sai kuma ya nuna mata hanyar bedroom ɗin da Lulu ke ciki.
“Yaya dan ALLAH barci takeyi?”.
Kansa ya sake girgiza mata nan ma. Miƙewa tai, kafin ma yace wani abu harta kusa zuwa ɗakin, ƙoƙarin dakatar da ita yay dan shi dai yasan wacece matar tasa, kuma baya buƙatar ƴan uwansa su fara sanin wacece itan su tun a yanzun, sallamar da Asma'u tai da ɗan knocking ƙofar ya katse masa tunani.
“Asma'u!”.
Ya kira sunanta kamar a kasalance, amsawa tai da “Na'am Yaya”. Tana jiyowa.........✍️
(😂Lulu karki bamu kunya dan ALLAH)
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣2️⃣
.......Dai-dai nan Lulu ta buɗe ƙofar ita kuma waya a kunne ta tana magana da Uncle Yousuf cikin shagwaɓa akan a aiko mata da wayoyinta. Miƙewa Smart yay ya nufosu, sai dai yana isowa Lulu da batama lura da shi ba ta riƙo hannun Asma'u suka shige ciki tana mata murmushi. Turus ya ɗan tsaya yana bin ƙofar da kallo, sai ma ya rasa wane irin tunani zai yi. Sai kawai ya ɗan furzar da isa ya nufi ɗakin daya kwana al'amarinta na ƙara ɗaure masa kai, ya fahimci gane ainahin yarinyar nan sai an shirya.
Huwaila da ke kallon komai ta cika tai fam, dan ita babu abinda zuciyarta ya bata sai wulaƙantata da nuna mata wariya. Wayarta ta ɗauka tai kiran Umma, bugu ɗaya kuwa ta amsa, daga can cike da zumuɗi Umma ta ce, “Ya ya kin ɗebo ko?”. Sosai Huwaila ta tunzura baki gaba, idanunta akan hanyar corridor ɗin nasu kamar zata saki kuka ta ce, “Umma bayan munafukar yarinyar nan itama tazo, gashi can ya jata sun shige ɗaki wajen matar tasa sun barni ni kaɗai a falo, dama tunda ya buɗen ƙofar yake min kallon banza kin san shi dai da baƙin halin tsiya, balle yanzu yana ganin ya auri ƴar masu kuɗi kamar yafi kowa a gidanmu.”
Ƙwafa Umma tai da ƙarfi zuciyarta na sake ƙuntata, cikin fusata da jin haushin lusarancin Huwailar ta ce, “To ke bazaki tashi ki bisu ba. Kije duk ma uwar da akeyi a ɗakin ayi da ke. Ki kuma tabbatar kin kwaso min abinda na sakaki”. Ƙitt ta yanke kiran batare da Huwaila ta sake samun damar cewa wani abu ba. Tasan hanlin Ummar su sarai akan jarabar tsiya, dan haka ta miƙe ta nufi inda taga Asma'u ta shiga. Ba knocking ba komai balle aje batun sallama ta afka musu. Asma'u da ke gyaran gado tai saurin jiyowa, hakama Lulu da ke waya da Sakatariyarta Zainab yanzu idanu ta zubama Huwailar.
“Kai Adda Huwaila ALLAH har kin ban tsoro shigowa haka ba sallama”. Asma'u ta faɗa cikin jin takaici sai dai ta tausasa harshenta. Harara Huwailar ta zuba mata da taɓe baki ta nufi sofa ɗin bedroom ɗin mai azabar ƙyau da ɗaukar ido ta zauna, itama sai Asma'un ta watsar da ita ta cigaba da gyara gadon cikin takaici. Harta kammala ta shiga toilet shima dan ta gyara Huwaila na cigaba da harare-harare, sai dai fa ɗakin ya mata masifar ƙyau, ji take inama a cikin ƴan ɗakinsu ne suka samu wannan duniyar haka.
Lulu kam tun kallo ɗayan datai mata bata sake ba tana cigaba da wayarta da Zainab da kuma gyara gashinta data kammala busarwa, so take sai ta kammala taji wace ita da kuma dalilin shogo mata ɗaki haka ba knocking. Asma'u data fito daga Bathroom alamar ta kammala ta yafito da hannu, koda ta iso batare da tayi magana ba ta miƙa mata ribbons da yimata nuni da gashinta alamar ta ɗaure mata. Amsa Asma'u tai da murmushi akan fuskarta, ta shaƙi fitinannen ƙamshin da gashin keyi ta lumshe idanu tana tattarosa cikin hanunta. Dai-dai nan Smart ya shigo ɗakin da sallama. Yayi masifar ƙyau cikin wani kwantaccen yadi da ya sake fiddo nagartarsa ta cikakken bahaushen arewacin Nigeria nutsatstse, daga ita har Asma'un ya zubama ido, sai kuma ya ɗan kalla Huwaila da ke gefe ta baje cikin couch tana ta wani faman hura hanci, sai dai shigowarsa ta sata ɗan nutsuwa dan tasan halinsa sarai.
“Ku tashi mu wuce ku kuma ko?”.
Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. Asma'u ta ce, “To Yaya can gidan zaka kaima”. Kansa ya ɗaga mata kawai batare da yace komai ba, amma sai Lulu da ke ɗan kwallonsa ta cikin mirror ta juya kujerar tana dubansa da ƙyau tare da janye wayar kunnenta alamar ta kammala. Kallon ido sukaima juna, kowanne ya janye nashi cike da basarwa. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Please ka barmin Auta anan dan su Afrah ma na zuwa kawo min phones ɗina”.
Zuba mata idanu yay sosai da alamar mamakinta, dan shi dai bai san yaushe ta fara son mutane haka ba da har ma tasan ana kiran Asma'u da Auta. Maimakon bata amsa sai ya dubi Huwaila da Asma'u. Da sauri suka fice dan dama Asma'u ita tayi niyyar yin hakan, Huwaila ce dai dake kallonsu ta ƙasan ido bata da wannan niyyar. Lulu da ke kallon yanda yaran ke rige-rigen ficewa ta wani taɓe baki, “Kai kowa ma sai ka nuna masa halinka ne, jibi yanda yara ke fita kamar zasu ci da ka”.
“Oh ni har wani hali ne da ni kuma wanda ban sanshi ba?”. Ya faɗa cikin ɗan ɗage gira ɗaya da ƙanƙance idanunsa. Nata tai saurin ɗaukewa da ƙara taɓe bakin ta koma ta juya ga mirror ɗin batare data bashi amsa ba. Ƙarasa takowa yay jikin mirror ɗin shima ya ɗan jingina tare da ɗaukar wayarsa ya duba dawa-dawa tai kira. Ganin number Uncle Yousuf da dama yana da ita, data Zainab da itama dai yana da itan dan tun randa ya kaita gida ya amsa saboda wataran. Ya ɗan ji nutsuwa dan shikam yanzu ya fahimci sai yayi takan tsantsan, tunda har jiya tai amfani da shi wajen sayo mata ƙwaya batare da ya fahimci komai ba dole ne ya nutsu ya fahimci duk wani dabarun su. Iska ya ɗan furzar kaɗan da gyara tsaiwarsa da ƙyau sai kuma ya fara magana a hankali tare da maida hankalinsa sosai ga kallon yanda take tufke jelar gashin bayan ta sharceta da comb. Yana matuƙar son gashi a jikin mace, dan haka natan ke matuƙar ɗaukar masa hankali.
“Zanje na gaida su Ammah na dawo bazan jimaba, sai dai ki sani kar fita ta ta baki damar aikata wani abu daban, dan shaye-shaye babbar hanyace ta maida ɗan Adam baya akan dukkanin nasarorinsa da kima da mutuncinsa. A duk inda mai wannan ɗabi'ar yake zakaga baida farin jinin al'umma, kowa bai san raɓarsa balle huɗɗa da shi da ga sanda aka fahimci yanayi. Shi a karan kansa kuma yakan rasa damammaki da yawa na cikin burinkansa ko nasararsa ta duniya da lahira. Misali ga barin salla, da wahala a samu mai wannan ɗabi'ar da tsaida salla akan lokacinta, hakan kuma babban naƙasu ne ga rayuwa. Karatun Alkur'ani, ambaton ALLAH da sanin mi rayuwa take ciki kota dosa duk dama ce dake kufcewa a hannunsa. Ga ɗiya mace in har tana wannan ɗabi'ar hanya mai sauƙi ce a samu damar keta mata mutuncinta. Shin mi kika rasa a rayuwa na ni'imomin ALLAH da bai miki ba, miyasa ki ka zaɓi gode masa ta wannan hanyar? Miyasa kika zaɓi sakama iyayenki da wannan tukuycin da duk iyayen da suka fuskanci yaransu nayi basu da sauran nitsuwar zuciya, ki tuna kema uwa ce wataran. Bazance miki ki kiyaye ba, dan ban isa hanaki ba, sai dai ki sani wannan itace ɗabi'a ta biyu da bazan ɗauka ba bayan barin salla. Ki zauna kiyi nazari. Ga break fast can su Asma'u sunzo da shi. Nima yanzu zan dawo sai na karya a nan ɗin, ina son yin abu mai muhimmanci ne acan”. Da ga haka ya nufi hanyar fita abinsa batare da ya ko waiwayo ba balle yaga halin da tasirin da maganganunsa sukayi gareta. Lulu da tun fara maganarsa abu ya tokare mata maƙoshi ta raka bayansa da kallo wani shegen takaicinsa da mamakin gadarar nan tasa da yake son fara bayyana mata a fili. Wai mi wannan mutumin ke nufi da ita ne? To duk abinda ya shirya ita a shirye take da mafiyinsa su zuba ita da shi a gidan nan ɗan halak ka fasa, ina ruwansa da rayuwarta....
Dawowar Asma'u da kayan shara ɗakin ya maidota hayyacinta. Ta kalleta tana ɗan waro idanu waje. “Ya barki ne?”. Cikin zumuɗi Asma'u ta bata amsa da “Eh, amma yace yana dawowa zan wuce. Shiyyasa zanyi sauri na shashshare miki aunty dan shifa Yaya baya magana biyu”. Yanda ta ƙare maganar da ƴar shagwaɓa ya sanya Lulu sakin murmushi. “Uhhm kudai autocin nan ko'a ina sai kun nuna hali. Kinga bar batun sharar nan karki wahal da kanki nace su Amrah su taho da Iya tabawa zatazo duk ta gyara ko'ina”.
“A'a aunty ki kirasu ma kice su barta basai sunzo da ita ba. Zan gyara yanzun nan dan nan ma sharane kawai da gogewa ya rage. Nifa kin san ina son aikin gida sosai, shiyyasa su Aunty Bilkisu idan suna jin lalacinsu har zuwa suke su ɗaukan na musu hutu koda Ammah zataita ƙorafi ne sunta lallaɓata kenan”.
“Uhhmm sannu busy body ke baƙya gajiya ma kenan. To nidai bazakimin aiki ba, amma zanso Ammah ta bari ki dawo mana nan kinga na samu abokiyar hira ko.”
“Tab aunty Ammah bazata bari ba, ba irin nacin da mijin Aunty Bilkisu baiyi ba kan a basu ni amma taƙi ita da Abbah. Amma ke ƙila taji kunyarki ta yarda ko weekend nake zuwa dan tasan dai halin Yaya bai son yin magana sai yaso, kina buƙatar abokiyar hira”.
“Zan gwada na gani to, ALLAH yasa su bani, bari na shirya naci abinci ina ɗan jin yunwa kaɗan-kaɗan, kema ajiye kayan sharar nan Please”.
Magiya Asma'u tai taima Lulu har sai da ta barta tai aikin nan, dan danan kuwa ta tsaftace ko'ina ta baza kayan ƙamshi. Itako tana zaune a falo tana tsakurar abincin da su Asma'u suka kawo, sai dai tana buɗe wanda Huwaila ta kawo ta maida da sauri ta rufe saboda jin ƙamshin korin da aka zambaɗa a miyar fankason ta dakar mata hanci, sam ita bata ƙaunar kori a abinci shiyyasa ma idan har an saka batacin sa komai son da take masa. Sai kuma ma akai rashin sa'a fankasu ba abincinta bane shima, duk randa ma Iya Tabawa tayisa a gidan to ita sai dai ai mata wani abun, hakama idan taje gidan Uncle Yousuf ko gidan Grandpa ta tarar anyi bataci, bata son su shi da tuwo sam musamman miyan yauƙi ko wani taga yanaci sai zuciyarta ya hau tashi. Wanda Asma'u ta kawo ta buɗa, a hankali ta saki ajiyar zuciya ganin lafiyayyen yam balls ne a kular farko, ta