Showing 126001 words to 129000 words out of 170683 words

Chapter 43 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7220

ƙasan ranta. Ruwa da lemo ta ɗibo da kayan cin-cin, babu jimawa sai gata ta dawo ta ajiye gabansu. Yanzu kam Smart ya zauna, sai dai kansa a duƙe yana latsa waya. Komawa tai ta zauna itama tana ɗan murmushin santin da su Ahmad keyi na dubulan. Shi dai gogan kamar ruwa ya cinyesa a falon. Sai da ƙyar yay controlling kansa kodan Faisal dan ta Ahmad mai sauƙi ne zai iya fahimtarsa. Sai dai murmushin Lulu sukar masa zuciya yake kishi na sake riƙe masa maƙoshi. Haka dai ya danne har suka miƙe, kayayyakinta suka shigo mata da su sannan sukai mata sallama ita kuma ta basu kayan garar data juye musu a leda kowa da nasa ta ƙaro ma sannan ta zuba wanda za'a kaima Aunty Khadijah matar Abdull-Hameed (Coach) dan suna ɗasawa sosai itama kasancewar akwai ƙawance mai ƙarfi tsakaninta da Aunty Saliha. Suna fita ta koma ta zauna tana dariyar jin daɗin ƙular da Smart da tayi. Jinta take rai fess ita kam. A haka ya dawo ya sameta. Zama kawai yay baice mata komai ba dan a yanzu idan har yay magana ɓacin ransa ne zai bayyana a fili, dan haka yafi zaɓar zama shiru har zuciyarsa ta ɗan sassauta masa sannan ya tura mata ledar da wayoyinta ke ciki ya miƙe yabar wajen. Nanma da kallo ta bisa cikin taɓe baki kafin taja ledar ta buɗe. Sosai taji farin cikin ganin wayoyinta da laptop, cike da jin daɗi ta ɗauka tai bedroom domin saka caji dan duk sun mutu ba caji. Ga cajojin duk suna hanunta.....

Kiran sallar magrib ya fiddosa a ɗakinsa, ya ɗan zubama kayan da su Ahmad suka shigo da shi ido dan suna nan a inda suka ajiye, iska ya furzar batare da yace komai ba ya kwashe su ya fara shiga da su bedroom ɗin nata. Zaune take da laptop data jona a caji gabanta, tun ɗagowar farko da tai suka haɗa ido ta maida bata sake ɗagowa ba har ya kammala shigowa da kayan. Babu alamar wasa tattare da shi ya ce, “Bakiji an kira salla bane?”.
Tsayawa tai da ga danna laptop ɗin sai dai bata ɗago ta kallesa ba. Amma ta tsuke fuska alamar jira take yace kule tace cass. Takowa yay gabanta a hankali ya rufe laptop ɗin ya tura gefe. Dole ta ɗago yanzun kam ta dubesa da iyakar duk wani ƙarfi dan nuna masa yana shiga mata hanci fa. Kallon tsakkiyar ido sukema juna kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, dan ta gagara faɗar abinda tai niyyar da farko. Ita ta fara janyewa cikin taɓe baki. Sai kuma ta miƙe batare data tanka masa ba ta nufi toilet. Bayanta yabi dan yanzun ma yana son tai al'ala a gabansa kamar ɗazun, kasancewar shi yana da ita sai ya tsaya yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ganin tayi kamar yanda ya nuna matan ɗazun, sai yaji kuma nauyin da zuciyarsa yayi ya ragu, dan har cikin ransa yaji ta burgesa, in dai har haka take da saurin fahimta da ɗaukar abu komai zai zo da sauƙi kenan, kafin dai tayin ne yake ganin zasu dinga kai ruwa rana.
A karan farko ya ja musu jam'i yau, abi mafi sakata sake nutsuwa a wannan jam'i yanda Smart ke raira karatun Alkur'ani a nutse da fitar sauti nagartacce. Bayan sun idar cikin fuskewa tai yunƙurin miƙewa domin bar masa wajen amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo mata hannu. Hannun ta kalla sannan ta ɗago fararen idanunta ta zuba masa. Shima ɗin dai ita yake kallo dan haka suka zubama juna ido kowanne najin idon ɗan uwansa na ratsashi har tsakkiyar ruhinsa. Da ƙyar Smart ya iya aro jarumta da ga cikin ɗunbin ƙwarin gwiwar sa cikin fitar sauti ƙasa-ƙasa ya furta, “Inada kishi! Inada kishi mai zafi! Inada kishi mai tsanani Mawaddat. Wannan gaskiya ce da nake gaya miki ita danki haddace a cikin muhimman abubuwanki ki kuma kiyaye saboda gudun randa zaki iya tabbatar da ainahina akan wannan kalmar. Komai zan iya ɗauka, idan nace komai ina nufin komai amma banda kasa riƙe kanki ko killace kanki ga wanina koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suka haifemu da shi. Ki cigaba da sanin *_SMART_* kawai, idan kika ce *_ALIYU HYDAR_* ki ke son gani a zahirance, to fa tabbas wasan zai iya canjawa da ga duk yanda kike iya tunanin ko kwallonsa a tsarin zuciyarki. Duk abinda kikaji nace bana so to da gaske bana sonsa, idan kuma bana son abu bana iya dogon kawaici a kansa game da ɗaukar hukunci mai tsauri. Idan har kina son cigaba da gudanar da duk abinda kika fara da ga gidanku cikin salama to ki kiyaye....”
Rikitaccen abinda ta hango a tsakkiyar idanunsa mai kama da guguwar hayaƙin turnuƙun yaƙi ya sata kasa iya maida murtani. Ba wai ta fahimci ainahin curarrun kalamansa bane ba a yanda shi yake son ta fahimta ɗin, a salon da yay maganar ne kawai ke son tilasta fassara mata su. Ba'a komai take garaje ba musamman maida murtani, dan haka ta shanye kamar komai bai mata zafi ba dan tana buƙatar fashin baƙi kafin ta maida raddi, dan haka kanta tsaye batare data janye idanunta da ga cikin nasa ba duk da hakan na cutar da ita ta ce, “Ka gama?”.......✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣8️⃣






......Ba ita kaɗai ba, hatta shi ma kallon da sukema junan na ƙarshen ƙwal uwar daka na matuƙar zafafa masa garkuwar jiki, amma ya zaɓi nuna jarumtar nan da duk aka san Aliyu Zakin fama da ita ta taurin zuciya da tsaurin shanyewa ya ƙi janyewa. “Gamawata na nufin karɓar umarni na, saɓanin hakan kuma.. hummmm!” yaƙi ƙarasawa sai danne lips ɗinsa da yay da haƙori cikin tabbatar da gargaɗi. Itama saita danne natan da salon muzuba mu gani tana mai ɗaura ɗayan hanunta saman nasa da ke akan natan ta turesa masa. Komai baice mata ba, sai lumshe idanun nasa yay kawai. Saman gadon ta koma ta zauna tare da ɗaukar laptop ɗinta ta cigaba da abinda take yi batare data sake ko satar kallon inda yake ba. Sai dai zuciyarta taƙi samun nutsuwa dan kalamansa ne ke faman mata kai da kawo. Ba wannan ne karo na farko daya mata irin waɗan nan kalaman a cirkuɗe ba, na baya ma kuma sun cimata rai da zafafa ta harta ƙagautu da son jin fasararsu, amma na yau sai batajin suna mata raɗaɗi ƙagautuwar ce kawai ke zaburar da zuciyarta akan hasashen mai iya fassara mata su. Karan farko da taji tana ɗan kewar Nadiya, amma kuma hakan bazai sa tai kiranta ba. Duk da kuwa ta turo mata tarin sakwanni na ban haƙuri amma tai biris, hatta taron bikin nan Nadiya tata roƙon son zuwa, anan ne ta mata reply da cewar (ba'a buƙatar ki) da ga haka kuma bata sake bi takanta ba. Su Afrah kam bata ganin sunada hankalin da zata iya sakasu a sabgarta. (Mubeen ko su Hussain) zuciyarta ta ayyana mata. Mubeen ai ƙaninta ne, ita kuma bata son raini gara ma su twins ɗin, gamsuwa da hakan ya sata ɗaukar wayarta ta shiga WhatsApp, abinda bai dameta ba sai abu mai muhimmanci ya taso mata. Dubawa tai dan ganin wanene online, sai taci sa'ar ganin Hassan dan haka tai masa sallama sannan ta rubuta masa kalaman da Smart ya faɗa mata, (dan Lulu fa irin mutanen nan ne masu ƙwanya matuƙa, tanada saurin ɗaukar abu da haddacesa, ko'a makaranta ƙuruwace ta gaske da kaifin brain yasa zama popular ga malamai da ɗalibai, dan ma abubuwa da yawa sun faru da suka so taɓa mata karatun musamman ma harkar shaye-shaye ALLAH dai ne ya ƙaddara da rabon zata haye da amsa suna lawyer a yanzun). Sai dai anyi rashin sa'a tana turawa Hassan na komawa upline, sai kawai ta ajiye wayar da tunanin bari ta bashi mintuna tasan zai dawo, idan ma bai dawo ba zatai kiransa. Ta cigaba da aikinta sama-sama har akai kiran isha'i, har lokacin kuma Smart na'a ɗakin yana karatu ne shiyyasa shima hankalinsa ba'a kanta yake ba har sai da akai kiran sallar sannan. Yanzu ma koda yace tazo suyi jam'i bata musa masa ba, bayan sun idar ne ya dakatar da ita daga yunƙurin tashi ta hanyar tura mata littatafan da malam Nasirudden ya bashi. Littatafan ta zubama idanu, kafin ta ɗago ta kallesa fuska a tsuke.
Kafin ma tace komai ya bata amsa da “Naki ne, zamu fara karatu sai ki shirya. Dan ya kamata kisan addininki. Hakan ne zai sake tabbatar miki da ke wacece, ki kuma san yanda zaki bautaba UBANGIJI, ki yima mahaifiyarki da ƙasa ta rufema idanu addu'a, ta haka ne kawai zatai alfahari da ke dajin farin cikin barin baya da tayi, zaki san yanda zaki roƙa UBANGIJI da miƙa masa kukanki akan bukatunki ya amsa miki”.
Yana gama faɗa ya miƙe batare da jiran cewarta ba. Tayi niyyar maida raddi akan maganar farko, sai dai ta ƙarshe tai mata takunkumi da hakan, tana son mahaifiyarta matuƙa, tana tsananin begenta kuma. Duk abinda zaka jingina mata da ita yana saurin sanyayata koda batai niyya ba tayi, balle ma ita in dai akan neman abinda duk za'ace ilimi ne da zai amfaneta bataga dalilin dazai hanata amsa ba, a ganinta hakan ribarta ce, ta ƙara koyon abinda bata sani ba....




*_WASHE GARI_* kamar jiya kowa a ɗakinsa ya kwana, garama shi yaɗan leƙata kusan ƙarfe uku na dare daya idar da sallar daya tashi yayi. Samun ɗakin a buɗe ya bashi damar shiga, sai ya sameta tana barcinta a cikin lallausan duvet ɗin gadon, ta rage hasken tabar mai pink. Wayoyinta ya ɗiba duka biyu ya fita da su, kusan akansu ya ƙarasa daren sai gabannin asuba ya kwanta, ana kiran salla kuma ya tashi. Yau ma ya tadata yin sallar, sai dai yana fita ta koma tai kwanciyarta har sai da ya dawo yay mata jan ido sannan ta tashi. A lokacinne ya ajiye mata wayoyinta ya koma can ɗakin ya kwanta sai barci.....


Kusan takwas da wasu mintuna ta kammala shirinta tsaf, tayi matuƙar ƙyau cikin skert da riga na atamfa da suka fiddata tsaf, kamar kullum babu kwalliya, ɗan kwali ma bata ɗaura ba dan bata iya zaman wahalar ɗaure-ɗauren nan dama a gida Afrah ke mata. Sosai ta baza ƙamshi aka toshe ido da glass bayan ta yana ƙaramin veil a kanta ta naɗesa a kafaɗunta. Dan ƙyau kam tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Cikin takun nan nata na yanga da gayu ta fito ɗauke da tarkacenta, sai key ɗin motarta da aka kawota da ita kaɗaice a nan ɗin sauran ba'a kawo mata ba. Kanta tsaye ta doshi hanyar fita, sai dai me tana taɓa ƙofar ta jita a rufe. Ƙaramin tsaki taja da duban agogon dake a tsintsiyar hanunta. Sam bata son makara, dan haka ta nufi kitchen da nufi fita ta ƙofar baya, sai dai nan ɗin ma ɓam. Cikin ɗan jin takaici ta rumtse idonta da komawa falon, kayan hanunta ta zube a saman kujera ta nufi ɗakin Smart. Yana tsaka da barcinsa ya ji ana bubbuga masa gefen filon daya tada kai, da ƙyar ya buɗe idanunsa da ke jingim da nauyin barci ya sauke a kanta. Kauda natan tayi da ga kansa a gadarance ta ce, “Malam bani key zan wuce. Ka wani bi ka rurrufe ƙofofi kamar a prison”.
Kallonta yake shi dai da ga sama har ƙasa har takai ƙarshen maganarta. Ƙoƙarin tashi yay zaune ya jingina da gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji rabin ƙafafunsa zuwa ƙugu lulluɓe cikin bargo.”
“Malam ka tsaya kana kallona kamar wata hoto, bayan kuma kaji na faɗa maka bana son na makara ko? Inada important abubuwa a office”.
Wani ɗan jan idanunsa yay kamar zai lumshe sai dai kafin ya rufe ɗin ya sake buɗesu a kanta. Cikin yanayin muryar wanda barci bai isa ba da ɗan taɓe fuska ya ce, “Ban fahimceki ba, sake maimaitawa”.
Kallon takaici ta watsa masa. Dan ta fara hasala. Amma sai ta danne da ƙyar a ɗan zafafen dai ta ce, “Wai kai miyasa komai a wajenka abin wasa ne. Kasan ko mi kake yi? Ka bani key ni ba neman jidali nake ba”.
“Humm ke idan ance miki ki fita a yau a kuma haka yanda kiken nan sai ki fitan?”.
Harara ta watsa masa cikin gatsali da faɗin, “Sai ka hanani fitar idan na tashi”.
“Okay haka kika ce? To ko zan tabbatar miki ko ƙofar gate bazaki fita ba, idan kema kin shiga duniyar mafarkinne sai ki farka, dan idan har kinga kin fita a gidan nan da sunan aiki sai next week ma. Sannan bada wannan shigar ba idan har kina son aikin naki kenan. Dan bazan hanaki yi ba saboda wasu dalilai na, amma ba'a yanda ranki ya raya miki ba. Yanzu a ƙarƙashin ikon Aliyu Mika'il Idris Mawashi kike ba su Daddy ba. Abinda ya tsara a gidansa dole shi za'ayi ko ana so ko ba'a so. Garama ki nufi kitchen haɗa mana break fast”. Da ga haka ya juya yay kwanciyarsa. Wani irin ƙarajin kiran sunansa ta ƙwala a matuƙar zafafe. Sai kawai yaja filo ya ɗaurama kansa ya toshe kunnuwansa ma ya maida idanunsa ya lumshe. Masifa ta fara zazzaga masa zuciyarta na raɗaɗi kamar zata fito ta baki, amma bawan ALLAHn nan yay biris da ita, da ya ga ma filon bazai masa ba sai ya ɗauki bluetooth ɗin sa da ke a bed side drawer ya manna a kunne ya saka ƙira'a abinsa. Fita tayi a ɗakin dan ta fahimci sai ta haɗashi da Daddy. Wayarta ta cira a handbag ta shiga dannama Daddy kira. Bugu biyu kuwa ya ɗaga dan fitowarsa a wanka kenan shima zai yi shirin office. Kafin ma yace wani abu ta sakar masa kuka da faɗin, “Daddy kaga mutumin nan ko? ALLAH ina raga masa ne saboda abinda Baba da Uncle You suka cemin, amma idan ya ce muyi ta inda ya ɓullo zan hargitsa masa rayuwa, nifa babu lallai babu dole zan dawo gida Daddy, garama komi Baban zaiyi yayi....”
Duk da abinda Daddy keji na yunƙuro masa shima sai ya danne da ƙyar, cikin tausasa harshe ya ce, “Baby kinga relax mi yake faruwa? Mi yay miki?”.
“Daddy Office fa zanje yabi ya kulle ƙofofin, naje ya bani key amma yay min banza yama saka bluetooth a kunne wai babu inda zanje sai next week, irin like kamar wata baiwarsa da ya saya a kasuwar bayi”.
Ƙololuwar ɓaci ran Daddy ya kai, a taƙaice ya ce “Ina zuwa”. Ya yanke kiran, number Smart ya lalubo a karo na farko ya danna masa kira. Kasancewar bluetooth a kunnensa ya sashi jin shigowar kiran a bazata, hannu ya kai ya zare guda ɗaya yana kai hannu kan wayar tasa ya ɗauka dan ganin wanene mai kiransa haka. Bai san number ɗin ba, dan baida Number Daddy, kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga gudun kar yay mistake.
“To sannu isashshe”.
Kalmar data fara dukan kunnensa kenan a maimakon sallama.........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣9️⃣






........Cikin sa'a kuma ya gane muryar Daddy. Amma sai ya danne bai nuna ba, cikin dai nutsuwarsa ya ce, “Assalamu alaikum”.
“Da sallamar nake da buƙata da ita zan maka ai. Miye dalilinka na hana Mawaddat fita office ka kuma kulleta?”.
Shiru Smart yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya furzar da numfashi kaɗan yana gyara kwanciyarsa. Sake tausasa muryarsa yay fiye da ɗazun ya ce, “Kayi haƙuri Daddy sallama wajibi ne ga musulmi, haka ma amsata ga wanda akaimawa. Kai ya kamata ka tunatar da ni hakan a matsayinka na mahaifi. Dan haka kayi haƙuri ka amsa min sallamata kafin muyi maganar da kake son. Assalamu'alaikum!”.
A cinkushe Daddyn ya amsa masa, Smart ya ɗan girgiza kansa sannan ya tashi zaune sosai. Cikin sake tsantsan da kai na girmamawa ya ce, “Daddy ina kwana”. Bai amsa masa ba nan kam. Shima sai bai damuba ya ɗora da faɗin, “Zan sake baka haƙuri a karo na biyu Daddy, dan ALLAH karka saka baki a wannan zancen dan a yanzu Mawaddat tana ƙarƙashin na ne. Inada damar zartar mata da hukunci akan abinda ya dace da kuma banbance mata wanda bai dace ba. Kai mana fatan alkairi kawai shi mukafi buƙata da sanya albarkar ku, na riga na gama yanke hukunci akan hakan babu kuma tunanin canjawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login