Showing 33001 words to 36000 words out of 170683 words

Chapter 12 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7244

kuma bai nuna ya damu ba. Abokan karatun kuwa akan jima ma ba'a haɗu ba sai ta waya ko wani taro mai muhimmanci ya haɗa. Shiru ya kwanta kamar mai barci, da gani kasan duniyar tunani ya faɗa, dan babu abinda yake sai furzar da huci akai-akai da ga bakinsa, hakan kamar ɗabi'a ce data zame masa jiki in dai yana cikin damuwa.. Abubuwa ne masu yawa ke ci masa rai, ciki harda batun bauɗaɗɗiyar yarinyar can, shi mutum ne da baya shiga sabgar da ba tashi ba koda kuwa a cikin gidansu ne sai idan yaso, amma sai yake ji zuciyarsa na ingizashi akan taimakon ubangidan nasa da yarinyar, badan komai ba sai dan ƙannensa mata da bazai taɓa fatan su tsinta kansu a irin wannan rayuwar ba. Yasan idan har ya tsamota da ga wannan musifar yayi jihadi, sai dai bai san ta ina zai farama taro wannan al'amari nata ba. Karan farko yaja sirrin tsaki, sai kuma ya tashi zaune yana ɗan furzar da huci tare da kai hannunsa saman goshinsa yana ɗan murzawa. Ganin yaƙi samun nutsuwar hutawar da yake buƙata ya sashi tashi ya fito a ɗakin, nan ƙofar gidansu ya zauna yana ɗan gaisawa da mutane masu wucewa har akai kiran sallar magrib. Bai fito da ga massalacin ba sai da akai isha'i, yana kwaɗayin shiga gidan suyi hira da Ammah dan wannan ɗan lokacin kawai yake da damar haka gareta, amma zuciyarsa nata masa tuni akan Lulu da abinda yaji suna magana ita da ƙawarta zasuyi a daren na yau da sunan wai murnar samun lafiyarta. duk yanda yaso yaƙar zuciyarsa abin ya gagara, saboda yana ji a ransa ba alkairi za'a shuka ba wajen, dan haka ya fito da ga layinsu ya samu Napep zuwa hotoro gra. bai damu da kuɗin da suka tsuga masa ba. Ɗan nesa da gidan ya sauka, amma ya tsayar da mai napep ɗin, ya samu jikin wata bishiyar dabino kusa da katangarsu ya tsaya, ya kai mintuna talatin da wani abu a wajen yaji motsin an buɗe gate ɗin gidan, ido ya zuba na son ganin wanda zai fito. Ilai kuwa Lulu ce, dan a kanta idanunsa suka sauka saboda haske dake tako ina a street ɗin, gashi ta sauke glass ɗin motar sosai har kana iya hango kalar kayan da take sanye da su. Tayi ƙyau matuƙa ga uban ƙamshinta na isowa har inda yake tsaye saboda yanda ta gumbuɗashi kamar ba mace ba. A ɗan kasancewarsu na kwanaki ya fahimci sam bata tausayawa ƙamshi, haka kawai sai yaji tanan ɓangaren ta ɗan samu sassauci a garesa, duk da tana saka nata ƙamshi ne ba bisa ƙa'idar da ya kamata ace mace ta saka ba. Da sauri ya ƙarasa ga mai napep da ke zaman jiransa. “Kabi wannan motar Please, amma karka bari ta fahimci muna biye da ita”. Ya faɗa yana nuna ma mai napep ɗin motar Lulu da ke tafiya a hankali kamar bata son tuƙin yau. Yanda take tafiyar ya bama mai napep ɗin damar binta cikin hikima har zuwa wata sabuwar anguwa, dai-dai wani gida da alamu suka nuna shima ba'a daɗe da kammalashi ba ta tsaya, da ga inda suke yana hangen yanda ta kai waya a kunnenta alamar kira take ko an kirata, tana ajiye wayar ana buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ya fita tare da miƙama mai napep kuɗi yana faɗin, “Abokina nagode ko”. Bai jira amsarsa ba ya nufi gidan, kasancewar akwai ƙarancin haske a anguwar dan kamar ma basu da wuta sai ƙarar gen... Ɗin gidan data shiga yake jiyowa ya samu damar bin motar tata ta gefe suka shiga tare batare da mai-gadin ya lura ba. Motoci ne kusan bakwai a gidan duk an parker a babban compound ɗin kamar wasu masu biki, tun kafin ta fito a motar ƙawayen nata suka baibayeta da ihun faɗin, “Sai Lu ɗin mu!!!, sai ƙamshin mu!!!”.
Fuskarta ƙawace da wani shegen murmushi ta fito. Wani shegen gown ne a jikin nata ta lafe mata kamar babyn roba. Da sauri ya kauda idanunsa yana mai jan sirrin tsaki da taune lips ɗinsa da ƙarfi. Bai sake kallon inda suke ba har suka shige ƙofar da yake ƙyautata zaton ta cikin gidan ce. Huci mai zafin gaske ya furzar tare da gyara tsaiwarsa. A ɓangaren su Lulu kam suna can cikin ƙaton falon gidan da ya sha kayan alatu. Abinda zai baka mamaki bawai iyakar su kaɗai bane ƴammatan ashe, akwai dattijan maza a shekaru bawai a cikar kamala ba har su huɗu, tun shigowar su Lulu kusan su duka suka zubo mata idanu fuska a washe, yayinda ita kuma nata murmushin ya ɗauke ta wani yamutse fuska tana kallon Nadiya, sai kuma ta juya ta fito a fusace. Da sauri Nadiya tabi bayanta tana faɗin, “Please Lu ki saurare ni.”
“Anƙi a saurareki ɗin, Nadiya kin san dai na tsani irin wannan ko...?”
“Na sani, amma bamu da wani zaɓi ne wlhy Lu.., dan ALLAH ki fahimce ni, kin san dai bazanyi abinda zai ɓata miki rai da gangan ba....”
“In ba kinyi da gangan ɗin ba miya kawo waɗan nan tsoffin banzar nan? Ni ban hanaki huɗɗa da su ba, amma ki sani duk randa suka zubar da ke bayan gama lalata miki ƙuruciya kiyi kukanki ke kaɗai kar ki tunkareni. Amma ki daina sakamin su a sabgogin rayuwata”.
Ɗan murmushi Nadiya tayi cikin rashin ɗaukar zancen na Lulu da muhimmanci ta ce, “Naji, ni dai yanzu kiyi haƙuri mu koma ciki dan ALLAH. Dan wannan fa zaman naki ne, dan ke akayisa, mun riga mun gama tara mutane, su Shony fa tun daga ktn suka taho a yammacin nan domin wannan shagali kawai. Abinda yasa ki ka ga su Alh. Baita anan ma saboda su Shony ne, dan sun riga sun kirasu cewar zasu shigo Kano, amma wlhy badan ke bane ba”.
A hankali ta furzar da iska, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. “Shike nan amma ki kiyaye gaba, dan in har kika sake sakamin sabgar waɗan nan mutanen a tawa wlhy sai mun rabu. Suma su Shonyn idan suna buƙatar haɗuwa da su ne suje can su haɗu bai shafeni ba”.
“Naji na yarda baza'a sake ba. Suma kuma zan musu bayani yanda zasu gane Muje to dan ALLAH suna jiranmu”.
“Bani details ɗin mai kayan nan na tura masa kuɗinsa karna shiga wata sabgar. Sannan wannan gidan na waye uwar kwashe-kwashe kika kawo mu kuma?”.
Gidan Nadiya ta kalla tana ƴar dariya tare da faɗin, “Gidan wanda ya sayar mana da kayan ne, wlhy Guy ɗin akwai kirki gashi so handsome kuma, ya bamu shawara ne muzo nan musha shagalinmu dan zaifi mana sirri kasancewar kinga dare ne, ke kuma ba cika son shiga clubs na nan Kano kikai ba kin ce ƴan hayaniya da ƴan iska sun cika yawa”.
Cikin rashin damuwa ta ɗage kafaɗa kawai, batare da ta sake tofa komai ba ta bar wajen. Binta Nadiya tai suka shige tare.... Gaba ɗaya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiɗa ya fara tashi kaɗan-kaɗan saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiɗan ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya ɗan dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba ɗaya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan ɗinne da burin ganin abokan sheɗanar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana ƙullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen.... Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaɗan-kaɗan da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa ƙofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daɗa karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar ƙarar sautin kiɗan da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura ƙofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na ɗurama wani hamshaƙin Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da ɗan yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko'ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huɗu da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan ƙusoshin attajirai kuma ƴan siyasa masu faɗa aji a garin na kano ɗaya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma ƙawace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na ƙarshe-ƙarshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa.........✍️








_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣






........Cikin kuka da dafe kanta tana ɗan layi alamar ta fara shiga maye ta ke faɗin, “Wlhy! Idan baka fita sabgata ba sai na keta maka rigar mutuncin tufafi da mutanen gari ke kallonka da shi, dan dama shi kaɗai ya saura gareka. Nace banayi! Banayi wai na minene wannan takura duk inda na saka ƙafa kana biye dani, shine yau harda bani wine saboda kai tsinanne ne, ka taɓa ganin na sha wine ne duk rashin ji na azzalumi!! Shin wai ku kuna ɗaukar duk macen da ke shan wannan abubuwan dan bama kanta farin ciki ita ɗin ƴar iska ce ko me? Manyan banza manyan kawai, ku gama hura hanci ga al'umma ku dawo bayan fage kuna lalata musu tarbiyyar yaransu. Ka sani har gaban abada bazaka taɓa samun wannan jikin ba, bama kai ba duk wani maye sai gani sai hange dan ni ba mazinaciya bace, bar ganin ina wannan rashin jin nasan ciwon kai na wawa kawai da ƙi ƙ.....” ta kasa ƙara sawa saboda shuuu da tai zata faɗi. Da sauri Nadiya ta tarota. Fisge jikinta tai tare da ɗagowa gaba ɗayanta kan ƙafafunta ta ɗauke fuskar Nadiya da mari haggu da dama.. A fusace Alhajin nan da ke tsaye tun ɗazun cikin ɓacin ran zagin da Lulu kema abokin nasa yayo kanta. Hannu ya ɗaga zai kwasheta da mari shima, sai dai cak ya tsaya jin an riƙe masa hannu ta baya. A karo na farko duk wanda ke'a falon ya farga da shi. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Alhajin da ke faman huci. Idanu ya lumshe cikin girgiza kansa da faɗin, “Haba kai kuwa ai babba babba ne, ba'asan namiji kuma da faɗa da mace ba. Bakaga abokinka yanda ya nuna mazantaka ba? Tunda kun gama zubar da kimarku garesu banga abin tada jijiyar wuya ba idan irin haka ta taso a tsakaninku ai......”
“Kai kuma a matsayinka na ubanwa anan?”.
Maimakon amsa sai ya ƙara tsaresa da idanunsan nan masu kwarjini da suka gama ƙwarewa a kallo mai girgiza zuciya cikin nuna gargaɗi (Na macizai inji Lulu😂). Sakin hannun Alhajin yayi, kafin cikin yanayin nan nasa a daƙile da kowa ke ɗauka girman kai ya ɗage kafaɗunsa da ɗan taɓe lips ɗinsa. “Sanin ɗan waye ni bazai maka amfani ba, idan dani kake son sani sai na baka amsa da cewar drivern ta ne”.
“What?! Driver fa?!!. Ubanwa to ya baka damar shigo mana nan har da tsoma baki a cikin abinda bai shafeka ba?”.
Shi ba mai yawan magana bane, dan haka maimakon amsa masa a yanzun ma sai kawai ya zuba masa ido. Hon. HD Nakowa sai ya sake fusata. Magana zai sakeyi cikin fusata Alhaji Ɗan-kande Baita ya dakatar da shi.
“Kaga HD please it's ok mana. Kai ɗan saurayi jeka kawai waje ka jirata nan ba huruminka bane ba”.
Wani banzan kallo Smart ya watsa musu su dukan, sai dai baice komai ba ya juya ga Lulu da ke zaune a kujera sharɓe tanata surutai da zagi har yanzu. Hanunta kawai ya fisga ta miƙe, batare da wani binta a hankali ba ya jata tana turjewa sukai waje. Da ƙyar ya iya kaita har motarta, dan haka ta maido da zagin da take ma Hon. Babale Misau kansa. Hakan bai damesa ba, sai ma rufeta da yay a motar ya koma falon ɗaukar handbag ɗin ta dan key ɗin motar na ciki....
“Ban yarda da wannan yaron driver bane ba, dan haka ina son a binciko min ɗan uban wanene shi a faɗin garin nan na kano”. Hon. HD Nakowa ne ke faɗa dai-dai Smart na sake shigowa falon ɗaukar tarkacen Lulu. Nunawa yay kamar baiji mi Hon. Nakowan ya faɗa ba, ya nufi handbag ɗin da ya gani ɗazun a hanunta da takalmanta masu azabar tsini ya kwashe ya sake juyawa ya bar falon ko kallo basu ishesa ba.....


Gotawarsu kaɗan da gidan wata dalleliyar mota ta iso ƙofar ita kuma. Horn yay aka buɗe masa. Yanda sautin kiɗa ke tashi a cikin motar zai baka tabbacin yana cikin nishaɗi matuƙa. Duk da yasan taro ake a gidan nasa hakan bai hanashi jin mamakin ganin wasu manya-manyan motoci guda uku ba, bawai ƴammatan bazasu iya zuwa da motocin bane, a'a kawai dai yasan sun musu girman da bazai yiwu ace sune suke hawansu ba. Cikin kai-kawo zuciya ya fito yana ƙara ƙarema motocin kallo, cikin ɗan basarwa irin na masu akwai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki yay ciki abinsa ransa fal nishaɗi yau zai haɗu da mafarkinsa. Yayi alƙawarin sai ya ɗanɗani yarinyar nan dan ta tsare masa ko'ina na zuciya tun a randa ya ganta. Da wani irin sauri yaja birki ya tsaya yana ƙarema falon nasa da ya hargitse kallo, bawai na tarkacen da suka zube bane kawai dan yasan wannan ne ya kawosu ai. Iya shegen da ake aikatawa a falon duk da shima yasan yana aikatawa ya sashi zama turus, dan shi dai Nadiya batace masa zasu gayyato namiji ko ɗaya ba. Amma sai ga har mutum huɗu manyan mutane sa'ar Daddynsa, kai abinma tashin hankalin shine harda abokan Daddyn nasa ma da suka sanshi ya sansu. Da baya-baya ya koma ganin hankalinsu su bai kai kansa ba saboda shagala a ɓarnar da suke aikatawa da yaran mutane. Duk cikinsu baiga Lulu ba, gashi kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba'a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, “Ranka ya daɗe barka da dare”. Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da “Ta iso ne?”. Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha'a ta amsa masa da “Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi”.
“What!!” MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan......


★★
Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi.....
Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, “Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye”.
Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login