Showing 117001 words to 120000 words out of 170683 words

Chapter 40 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7235

biyu farfesun naman kaza ne yanata tashin ƙamshin attaruhu da albasa. Sai jug irin mai riƙe zafi ɗin nan ɗauke da kunun gyaɗa da yay ƙyau yanata ƙamshi har da su ƙwa-ƙwa a cikinsa. Sai shayi a flaks da yaji kayan ƙamshi shima, anan kam ajiyar zuciya ta sauke harda sakin guntun murmushi ta zuba kunun gyaɗar da farfesu kaɗan ta fara tsakura tana bin Asma'u da keta aikinta a nutse da kallo da sauraren labarin da take bata akan yanda suke matuƙar jin daɗin abinda take yi game da case ɗin fyaɗe. Haka kawai jin ƙaunar yarinyar take a ranta, balle jin abinda take faɗa na yanayin da suke shiga na jin daɗi har itama tana burin zama lawyer kamarta........✍️











_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣






.......A ɓangaren Smart kam suna isa gidan sashen Abba ya nufa domin gaidasa, yayinda Huwaila ta shige ciki fuuu tana ƙunƙuni. A falo ta iske Umma zaune suna karin kumallo da sauran ƴan uwanta da ƴaƴansu da duk ke shirin wucewa gida a yau tunda biki dai ya tashi. Umma ta bita da kallo kamar a firgice, sai dai kasancewar bata son tace wani abu a gaban sauran yaran ya sata ƙyafta mata ido ta cigaba da cin abincinta. Amma Huwaila sai ta dinga ƙunƙuni, da ga ƙarshe dai ta fara bama ƴan uwanta labarin ƙarya da gaskiya akan wai an mata wulaƙanci a gidan Smart, sun shige ɗaki sun barta, yanzu kuma yace Asma'u ta zauna can ita kuma ya taso ƙeyarta sun dawo. Da yawansu sun hau sun zauna. Sai Ismaha ce dai ta ce, “Humm Huwaila gaskiya ban yarda ba. Koda ace hakan da kika faɗa ma ta faru sai dai idan yanada manufarsa, kowa dai yasan Yaya Hydar a gidan nan kan rashin nuna bambanci a tsakaninmu da ƴan ɗakinsu. Da dai Yaya Salim kikace yayi hakan ko musa miki bazanyi ba...” tana gama faɗa ta tashi tai ficewarta. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya kaure da ka-ce-na-ce, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Da wannan damar Umma da hankalinta sam ba'a jikinta yake ba ta miƙe tana kama hannun Huwaila suka shige uwar ɗaka.
“K lafiya? Ina abinda na aikeki yi na ganki hannu rabbana”.
“To Umma ya kike so ki ganni, a gabanki fa na faɗi irin wulaƙanci da akai min a gidan can”.
“Ke tafi can wawuyar banza da wofi, kin ko san muhimmancin abinda na turaki yi da zaki dawo min da wani shirmenki na banza. Wai ke ko Huwaila yaushe ne zakiyi hankali a rayuwarki. Ƙanwar-ƙanwarki Asma'u har ta fiki wayo amma ke gallaƙeƙiyar budurwa da ake shirinma aure baki son ciwon uwarki ba....”
“To wai ni Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Ni Wlhy ko ƙyallin wani kayan da suka saka jiya suka cire ban wani gani ba a gidan. Tunda kina ganin banyi miki ƙoƙari ba sai kije da kanki ai”. Tana gama faɗa tai waje abinta. Duk irin kiran da Umman ke ƙwala mata ko waiwayenta batai ba. Sai ma jiyo muryar Smart da tai alamar ya shigo gaishe ta. Sai dai yanda taji ƴaƴan nata na gaishesa a gatsine ya sata fita wuff dan taga suna neman ɓata mata shiri, saboda Malam Na-zuru ya jaddada mata a waya ɗazun da safe sai fa ta rage nuna abinda ke ranta a garesu, musamman ma matar tasa tai duk yanda zatayi ta shiga jikin yarinyar hakanne zai sakasu cin nasara cikin sauƙi. Cike da fara'a ta amsa gaisuwar da Smart ke mata tana tambayar ya baƙuntar sabon waje da amarya. Kansa a ƙasa cikin jin nauyi da girmamawa ya ce “Lafiya Lau tana gaishe ku”.
“To madalla ALLAH yay muku albarka. Kamayi ƙoƙari ai da ka fito tunda safe haka banyi zaton yau zamuga idonka ba a gidan nan kwata-kwata.”
Shi dai murmushi kawai yay yana miƙewa batare da ya bata amsa ba ya fice abinsa. Sashen Ammah ya shiga dan ya gaisa da mama da Aunty Amarya. Nan ma dai zama yay suna gaisawa da dangin mahaifiyarsa da ke ta jansa da kiransa babansu babansu. Daga haka suka sake ɗora masa da nasiha mai ratsa jiki tare da addu'oin zaman lafiya mai ɗorawa da zuri'a mai albarka. Bai jima ba sosai Adda Suwaiba tace ya tashi yaje yabar matarsa dan ma Asma'u nacan. Daga haka yay musu sallama ya fito bayan sun ɗanyi magana da Ammah a gefe ya kawo kuɗin jikinsa na gudunmawa da ya ɗan sassamu ya bata akan ta basu suyi kuɗin mota. Daga haka ya juya ya tafi akan zuwa anjima zai dawo kafin su tafi gidan su Lulu godiya ta al'ada da ango kanje da abokansa gidan dangin amarya washe garin tashin biki.....


Har lokacin da ya shigo gidan Lulu na zaune tana tsakurar abincin nan, yayinda Asma'u ke ƙarasa saka turaren ruwa a carpet ɗin falon da labuloli. Ɗaga kai kawai tai ta kallesa ta maida kan abincinta batare data amsa masa sallamar ba. Sai Asma'u ce ta amsa tana masa sannu da zuwa cikin girmamawa. Amsa mata yay da kansa kawai. Da yake hankalinta ba'a kansu yake ba ita bama ta lura Lulu bata amsa masa sallama ba. Ta kammala ta maida turaren a inda ta ɗauka Lulun na mata sannu cikin murmushi. Ta gefen ido yake kallonta da mamakin yanda take sakema Asma'un. Baki ya ɗan taɓe batare da ya kalla Asma'un ba ya ce, “K zoki bani abincin nan na karya”. Amsa masa tai da to Yaya, sannan ta nufi kitchen ɗin ɗakko masa plate kamar yanda ta ɗakkoma Lulu ɗazun. Sai lokacin ya dubi Lulun a kaikaice, cikin deep voice ɗin nan tashi a dakensa ya ce, “Ke baki iya amsa sallama ba balle sannu da zuwa ko, amma kin iya tasa abinci kina ci”.
“Sauƙin ma bakai ka bani ba balle kamun gori shishshigi master”. Ta faɗa tana balla masa harara. Lips ɗin ta dake motsawa a hankali yabi da kallo, sai kuma ya ɗan cije nasa da ɗauke kansa yana jin wata irin kasala na sake saukar masa fiye data barcin da yake ji. Bai sake magana ba saboda fitowar Asma'u, ta jawo basket ɗin gabansa tana buɗe kulolin da faɗin, “Yaya mizan zuba maka bayan kunu dan nasan dai shikam ba canji”. Ƙaramar hararar data sata saki siririyar dariya ya sakamar mata, sai kuma ya nuna mata yam balls ɗin da faɗin, “Karki sakama kunun komai”. Da to ta amsa masa, sannan ta zuba komai yanda ya kamata kuma dai-dai adadin da tasan zai cinye dan shima yam balls ɗin ma masoyinsa ne. Lulu da ke satar kallon abincin ta gefen ido ta ce, “Hu'umm kuma duk cinyesa zakayi?”. Yanda tai maganar da ɗan waro Luluu eyes ɗinta waje tana riƙe haɓa ya bama Asma'u dariya, sai dai ta danneta da ƙyar ta tashi ta fice da ga falon gaba ɗaya taje waje tai abarta son rai.
Smart ya ɗan laɓe baki batare da ya kalleta ba ya fara cin abincinsa da faɗin, “Mi kike tsoro ne a cikin cin abincin nawa? Kina gudun kar ki gagara ɗaukata ne?” ya ƙare maganar da ɗago idanunsa da take kira na macizai ya zuba mata su. Baki ta taɓe cikin masa kallo mai kama da harara ta ce, “Kamar ya? Miya shafen da nauyinka?”.
A karan farko ya saki wani makirin murmushin da aduk sanda yayisa yake tunzurata dan tafi kwallonsa a murmushin rainin hankali ya cigaba da cin abincinsa. Siririn tsaki taja da ɗauke kanta itama ta cigaba da shan romon farfesun da yaci ace tama manta ta gama ci. Amma ina gayu da yanayinta yasa anata tsakurarsa, ga shi yamata daɗi matuƙa ta yanda ta gagara ajiyesa. Duk da yaji tsakin nata bai sake yin magana ba ya maida hankalinsa ga cin abincin harya kammala zai tashi, sai lokacinne itama take kammalawar. Asma'u ya ƙwalama kira, ta amsa da ga waje dan ta gama zagaye gidan ne tana jin daɗin kallon flowers ɗin da aka ƙawatashi da su. “Zoki wuce gida” ya faɗa yana miƙa mata ɗari biyu. Lulu Asma'u ta kalla cikin shagwaɓe fuska, itama Lulun shi take kallo, ta ce, “Kamarya tazo ta tafi? Nan fa zata kwana”. Yanda take maganar itama kamar a shagwaɓa-shagwaɓa ya sashi kallonta. Sai kuma ya ce, “A ina ɗin zata kwana? No karma ku fara abinda bazaku iya ƙara sawa ba, common Malama ɗakko hijjab ɗinki ki wuce gida, wannan abincin ki tafi da shi a bama wani dan nan dai bacinsa za'ai ba”. Da ga haka yay wucewarsa hanyar bedroom. Sum-sum Asma'u ta nufi kwanikan da suka kammala cin abincin ta tattara zata kai kitchen sannan tazo ta wuce dan tasan shifa baya magana sau biyu. Takaicin wannan nuna isar tasa ya saka Lulu miƙewa a fusace tabi bayansa. Burumm ta shigo ɗakin dai-dai ya zare rigarsa zai cire wandon, amma sai ya dakata ya tsaya kallonta.
“Malam wai kai miyasa kake son dinga juya mutanene kamar wasu ƴaƴanka?”.
Kallonta kawai yake yi batare da yace komai ba. Aiko sai ta sake fusata da takaicinsa ta ce, “To babu inda zataje”.
“Idan kece sama da ni kenan”.
Ya faɗa yana ƙara tsatstsareta da idanu. Itama a tsiwace ta ce, “Oh da mika ɗauki kanka?”. Karo na biyu ya saki murmushi, dan shi kam ƙarfin halinta tunba yanzu ba dariya ma yake bashi. A hankali ya tako zuwa gabanta daf, ta wani yamutsa fuska tare da matsawa baya tana hararsa, sake matsawa yay shima ta matsa itama, shima ya bitan dai, a masife ta ce, “Miye haka wai?”.
“Ina son nuna miki abinda na ɗauki kaina ɗin ne Madam” yay maganar dai-dai suna danganewa da bango idanunsa cikin nata. Yanda suke daf-daf ga hannunsa da ya tokare a bangon ya bashi damar dabaibaye ta da ƙyau har tanajin numfashi na neman mata wahalar shaƙa dan in ma ta shaƙa ɗin ƙamshinsa ne iskar da kawai take iya zuƙowa ya sata faɗin, “Aliyu bana son iskanci da raini fa. Dalla matsa min”..
“Haba Madam! K bakiji kunyar faɗar sunan ba haka gatsal sunan mijinki ne fa”. Yay maganar da sake ranƙwafowa yay mata rumfa ta yanda jikinta ke neman fara rawa. Amma sai ta dake dan bata yarda itafa yaga gazawarta ba. Hannu tasa ta turashi amma ko gezau, sai ma wani lumshe idanun da yay ya sauke akan hannayen nata da ke a saman jikinsa. Da sauri ta janye tana jan tsaki da faɗin, “In ma abinda banzan zuciyarka ke faɗa maka kenan to ka goge, dan tamkar kana mafarki ne a gaɓar da ake gab da tashinka da ruwan sanyi, wannan auren baida maraba da wasan drama ɗan son banza phone store”.
Idanunsa ya lumshe da buɗewa a lokaci guda yana cafko hanunta dan shirin duƙewa take tabar wajen. “Haba Madam ya kuma zaki wuce ban nuna miki abinda na ɗauki kan nawa ba?”.
“Aliyu!!”.
Ta sake faɗa da ƴar tsawar takaicin kiranta Madam da yake yi dana goga jikinsa a nata.
“Uhmm Madam”.
Ya amsa mata da wata irin kasalalliyar muryar son sake ƙular da ita yana sake kusanta fuskarsa gab-gab.........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣






........Ƙarshen kuma firgita Lulu ta gama kaiwa, sai dai kafin tai wani yunƙuri a matuƙar bazata taji saukar lips ɗinsa masu sanyi akan tausasan nata masu sheƙi da ƙamshin lipgloss ɗin data ɗan saka, cin abinci ma yasa duk ta shanye rabi. Iyakar rikicewa da firgici Lulu ta shiga, gashi ya mata ritsawar da ko iya motsa kanta ta gagara yi balle tace zata iya ƙwacewa. Shi kansa da yayi ne domin kawai tabbatar mata ba drama ɗin data ambata ɗin bane jiyay gaba ɗaya jininsa na yamutsawa, dan karo na farko kenan a rayuwarsa da haka ta faru tsakaninsa da mace. Da ƙyar ya iya juriyar shafe minti guda sannan ya sake mata lips amma bai matsa da ga jikin nata ba, sai ma magana da ya fara cikin kunnenta muryarsa a wani irin sarƙe duk da jarumtar son hana hakan bayyana da yake nunawa. “Waya gaya miki baƙo na kwana gidan sabbin aure ne? Ai sai ya jiyoma kansa abinda zai hanashi barci, bar yarinyar mutane ta tafi gidansu girmanta bai kai ba. Sannan ki rage ɗaukar kanki sama can ƙololuwa, dan a wannan fadar Aliyu Hydar shine ZAKIN KI. Fassara SARKIN KI Mawaddatan'warahmah Isma'il Ibrahim Jiƙamshi”. Ya ƙare maganar da ɗanja baya yana wani kashe mata ido ɗaya ya bar wajen gaba ɗaya.. Suɓul numfashin Lulu ya nema barin jikinta. Takaici ne, baƙin ciki ne. Mamaki ne bata sani ba. Abinda kawai ta sani wannan itace rana mafi abin takaici da koma baya da tazo mata a tarihinta. Bakin illiterate driver ɗinta ne cikin nata, ya zuba mata yawunsa ta sha fa a cikin cikinta. Wayyo ALLAH shike nan tata ta gama ƙarewa....
Kamar Smart ya san mi take tunani, dai-dai yana hawa gadon ya wani lashi lips ɗinsa da faɗin, “1-0 kenan, amma fa yawunki akwai daɗi Madam. Ina fatan nawa ma akwai ɗanɗano na musamman irin wanda iyali zasu so. Dama na faɗa miki jahilin baƙauyen nan fa ɗan takife ne, ki guji masa gatsali dan bajin magana yake ba. kije ki sallami yarinyar mutane inba haka ba na tashi na ganta a gidan nan ita ranta zai ɓaci, ke kuma zakisha yawun baƙauyenki”.
Harara ta watso masa da faɗin, “Shash....” bata ƙarasa ba ya yunƙura zai tashi. Da gudu ta fice kuwa tana nunashi da yatsa da faɗin, “Wlhy sai na koya maka hankali. Maye!”.
Komawa yay ya kwanta yana mai lumshe idanunsa da sakin ƙaramar dariya. A hankali ya furta, “Na samu promotion da ga illiterate velleger zuwa MAYE kenan”. Sai kuma ya kai hannunsa saman lips ɗin nasa ya shafa yana jin wani abu na masa yawo a cikin jini har yanzu. “Ko mima ya kai ni, ni Aliyu Madam ce fa”. Ya sake faɗa yana wani ɓata fuska kamar gaske, sai kuma yaja filo ya ɗaura a saman face ɗin sa da sake faɗin, “ALLAH ya shiryeka Aliyu wannan abun kunyar da ka tafka fa wa ogarka”.


(😂😂Ɗan manni, amma ka kwana da sanin idan muka tashi ramawa sai ka raina kan ka malam🥱 Tom😏🚴).




_________★




A hankali Mommy ta jinjina kanta tare da sakin ajiyar zuciya na ɗunbin mamakin Daddy a karo na babu adadi. Kallonta ta sake maida wa garesa har yanzu yana a yanda yake zaune da tagumi hannu bibbiyu. Abincin data ajiye masa kusan tsawon awa guda har ya ƙandare shayin ko ya koma kamar ruwan sanyi. A tsakanin shekaranjiya zuwa yinin jiya yanayinsa na nuna kewar barin Lulu gidan ne kamar yanda suma duk sunji hakan a ransu, amma da ga daren jiya zuwa safiyar yau yanayin nasa sai ya ninka ko barcin kirki bata tunanin yayi, da farko tayi tunanin ko baya jin daɗin jikinsa ne. Amma koda ta tambayesa amsar da ya bata sai taji ta girmi kunnenta. Tun cikin daren take tunanin anya kuwa mijin nata kuma ɗan uwanta lafiya lau yake? Dan al'amarin nasa kuma ya fara wuce makaɗi da rawa. Ita bama ta fatan ko Yousuf yaji wannan taɓargazar tasa a wannan gaɓar dan abin kunya ne na gaske. Ajiyar zuciyar ta sake saukewa, sai kuma ta miƙe a nutsenta ta koma gefensa ta zauna. Karo na farko akan al'amurin Lulu ta fuskancesa da son tausasawa da nuna masa goyon baya ɗari bisa ɗari. Hannunsa ta kamo cikin nata tana ɗan murmushi da faɗin, “Yaya kayi haƙuri kaci abincin, ka kuma kwantar da hankalinka bari na shirya sai naje gidan na duba mana Mawaddat ɗin, duk da dai inaji a jikina yaron nan bazaiyi abinda zamuce ALLAH wadarai ba. Amma nima zuwa yanzu zuciyata tafi gamsuwa da naje na dubatan tunda babu waya a hannunta balle mu kira, tura yara kuma bazai bamu abinda muke so ba.”
A karo na farko shima Daddy ya dubi Mommy ɗin da tausasawa a akan lamarin Lulun. Murya a sanyaye ya ce, “Kina ganin baza'ace munyi ba daidai ba Kareema, kin san fa masifar Yousuf akan yaron nan daban ce, na rasa wane irin so yake masa da bai son ace yayi ba dai-dai ba. Ni kuma wlhy ina tsoron ya illatamin yarinya a banza tunda dai ba taɓa auren nan yay ba balle muce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login