Showing 141001 words to 144000 words out of 170683 words
tana jin wani nutsuwa da jinta daban da dacan duk da bawani nisa sukai ba can sosai, dan ma dai ƙwaƙwalwarta mai saurin ɗaukar abu ta taimaka mata matuƙa. Kamar yanda ya faɗa sun kai kusan ƙarfe taran, dan sanda ya fito bayan ya shirya koda yaga kayan data saka kai tsaye yace mata ta sakesu. Taso masa gardama amma sai yace tayi haƙuri gidansu fa zai kaita ta gaida su Ammah kuma can zata yini sai dare. A take yaga farin cikinta ya bayyana, dan ita dai tunda Asma'u suka bata labarin yanda Ammah ke sonta da bibiyar abinda take yi sai take jin ɗokantuwa da sake ganin Ammah ɗin duk da a waccan zaman na kwana ɗaya da aka kaita gidansu bazata ƙarar da fuskar kowa ba. Kanta tsaye ta ce, “To dan ALLAH zoka tayani zaɓen wanda zasuyi”.
Idanu kawai ya zuba mata sai kuma ya saki murmushi zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama. Baiyi zaton zata nuna ɗokin sake zuwa gidansu ba tunda ta kwana a ciki taga yanda yake. Ya fahimci gane wacece ita kai tsaye abunne mai wahalar gaske, dan idan ya gama haddace nan ya buɗe mata sabon shafi sai yaga nan ɗin ma dai akwai abubuwan ban mamaki a cikinsa fiye dana baya daya baro.
Da kansa ya zaɓa mata kayan kamar yanda ta buƙata. Atamfa mai ƙyau da akaima ɗinkin zani da riga, sai hijjab. Anan ne ta ɓata fuska da ɗauke hijjab ɗin gefe ta ajiye ta ɗauka gyale. Zaiyi magana ta marairaice fuska. Shiru yay baice mata komai ba ganin gyalen nada girma. Sai kuma wajen ɗaura zani ma wata sabuwa. Dan Lulu bata iya ba, da tayi-tayi taga ta kasa saita shiga ƙwala masa kira dan sanda zata saka kayan catai sai dai ya fita, shi kuma baiyi musu ba ya fita ya tsaya a ƙofa. Kiran nasa da tai ya sakashi dawowa. Cikin ɓata fuska ta ce, “A canja wasu gaskiya”.
“Saboda mi”.
“Toni na iya ɗaura zani ne”.
Dariya taso ƙwace masa amma ya danne. Ya ƙarasa shigowa ciki yana faɗin, “Kin yarda na ɗaura miki?”.
Shiru tai kamar mai tunani, sai kuma ta ɗan hararesa da faɗin, “To wlhy ka rufe idonka, dan inka kallan ban yafe ba”.
“Oh hakama zaki ce daga taimako?”.
Baki taɗan murguɗa batace komai ba. Shi kuma sai yay murmushi kawai da ƙarasowa inda taken dan bai son ya biye mata Coach nacan na jiransa. Da taimakonsa ta ɗaura zanin duk da anata masa masifar ya rufe ido kuma karya taɓa mata jiki, duk da yana da abubuwan faɗa baice komai ba shi dai. Ɗaurin ɗan kwali ma bata iya ba. Cikin dafe kai ya ce, “Naga takaina, na auri bahaushiya a zahiri amma bata da banbanci da turawa ni Aliyun Ammah”.
Harara ta zuba masa ta figi handbag ɗin ta da mayafi ta fice. Sai wata leda da bai san ko minene a ciki ba hartayi gaba ta dawo ta ɗauki kayarta. Bayanta yabi yana dariya da faɗin, “8-6 kenan”.
Sai da ta hararesa ta ce, “Kama isa. Wlhy 7-6 na sani”.
“K matsalata da ke rinto, garama ki yarda kinyi game over”.
“Never give up wlhy, mai sama da hundred ne yay wining”.
Ta amsa masa nan ma tana hararsa. Ita ta fara fita, shi kuma ya kashe kayan wutar dan an haɗa musu tv yanzu ya kullo ƙofar ya fito. A jikin motarta ya ganta tsaye, sai ya ɗauke kansa ya nufi gate. “Ina kuma zaka je?”. Ta faɗa tana kafesa da idanun ta. Kansa tsaye ya bata amsa batare da ya juyo ba. “Zan sama mana Napep mana”.
Da mamaki ta ce, “Napep kuma? Ita kuma wannan motar fa? Ni malam bana son ƙauyanci kazo mu wuce danni kam bana hawa Napep. Bamma taɓaba”.
“Sai ki fara da ga yau”.
Ya amsa mata yana yin gaba. Tana nan tsaye mamaki da jinjina girman kansa na cimata zuciya, dan ita abinda ta fassara kawai kenan a al'amarin nasa sai gashi ya dawo, baice da ita komai ba ya ɗauka handbag ɗinta da ledar nan ya dubeta da faɗin, “Muje”.
“Aliyu!”.
Ta faɗa cikin kaiwa ƙarshen mamakinsa. Amma sai ya ɗaga mata hannu da nuna ƙofa alamar suje. “Sai dai ka tafi kai ɗaya dan gaskiya bazan shiga Napep ba, kaje zan sameka acan”.
Wani ɗan lumshe idanunsa yay na gundura da maganar a taƙaice ya ce, “Zan ɗauke ki har ƙofar gidan ba ruwana. Dan na faɗa miki ana jirana ko”.
Yanda yay magana a dake babu alamar wasa ya sake sata tsira masa ido. Sai kuma shawarar da zuciyarta ta bata na ta bishin koba komai yau ta ɗan fita tasha iska ya sata ture komai gefe tai gaba yabi bayanta yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Lulu naji na gani a karo na farko na tarihin rayuwarta ta shiga Napep. Sai kuma taji hakan ya sakata a farin ciki batare da tayi zato ba, ga wata iska mai daɗi na rsatsaka tako ina. Sannan kai-kawon mutane da yanda kowa ke sha'aninsa musamman masu tallar abubuwa akan titi yay matuƙar ɗaukar hankalinta da sakata jin tausayinsu. A karon farko zuciyarta ta bata talaka na wahala akan taro da kwabo a ƙasar nan. Wani ɗan yaro da ke tallar papcorn ta yafito da hannu sanda suke tsayawa cikin wani gajeren holdup. Bazai wuce shekara goma sha huɗu ba.
“Hajiya guggurun na nawa kike so?”.
Yaron ya faɗa yana ƙoƙarin yago ledan guggurun a jikin ƴan uwansa. Dakatar da shi tai da faɗin, “No ba shi nake so ba. Miya hanaka zuwa makaranta kake nan kan titi?”.
Ɗan jim yaron yay kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya kalleta ya sake kallon Smart da ke kallonsu kawai batare da ya tanka ba. Muryarsa da alamar damuwa ya ce, “An koroni ne dan Abbana bai biya ba tunda na gama aji uku wai baida kuɗi.”
Idanu ta zaro na mamaki. Sai kuma ta ce, “Kaga yanzu a titi muke ina ne gidanku?”.
“A kwana uku muke”.
Handbag ɗinta ta ɗauka ta ciro jota da pen ta miƙa masa. “Kaga samun Number wayan mamanka anan idan ka sani”.
“Sai dai na yayata, Umman mu wayanta ya faɗa ruwa”.
“Idan ba damuwa sakamun ta yayar taka”. Da murna sauri-sauri yaron ya saka dan an sakesu. Ya miƙa mata. Amsa tai da miƙa masa 2k tana murmushi. Da ga haka suka wuce. Mai Napep da ke kallon komai yay ƴar dariya da faɗin, “Hajjaju idan irin waɗan nan yaran kikace zakiyita amsar lambarsu dan basuje makaranta ba aiko zaki amshi sama da miliyan goma a garin nan. Bayan ƴan gari akwai ƴan cirani kamarsa-kamarsa ba adadi. Su dama sauƙi tunda suna neman na kansu ai, wasu kamarsun rashin karatun kesa abokan banza jan ra'ayinsu su faɗa ƙwacen waya da tare yaran da aka aika a lungu su amshe kuɗin. Ko kiga sun faɗa harkar shaye-shaye yara ƙanana kaga yaro na zuƙar maka tabar wiwi ƴan iskan banza iyayensu sun haifa mana bala'i”.
Wani irin harbawa zuciyar Lulu tai akan zancensa na ƙarshe. Sai taji bakinta yayi nauyi tama gagara cewa komai, sai ɗagowa da tai ta ɗan dubi Smart da yay kicin-kicin da fuska yanzu kam yana ma mai napep ɗin wani shegen kallo. Aiko sai taji mai Napep yay tsitt yana ɗan satar kallon Smart ɗin ta mirror. Har suka iso fagge zantukan na mata juya-juya a zuciya da kartar mata rai. Ba komai ya kawo hakan ba gareta sai tuna itama fa ta fara shaye-shaye ne tana da shekara goma sha uku a duniya. Har ƙofar gida aka kaisu, anguwar da mutane sosai kasancewar Lahadi ne wasu basa fita, ganin yanda akai musu caa da idanu yana biyan mai Napep ɗin yaja hanunta suka shige ciki. Sun samu yaran duk suna nan, basu kai ga wucewa islamiyya ba gidan caka-kai caka-kai. Sai shigowarsa ta sa mafi yawan yaran yin shiru, masu aiki suka maida hankalinsu ga aikin da sukeyi. Asma'u ce dake shanyar kayan Ammah da suke wankewa ita da Maryam ta taho da gudu tana faɗin, “Aunty Oyoyo Oyoyo. Sassanyan murmushi Lulu ta saki ta riƙo hannun Asma'u da ta noƙe gab da zata iso saboda hararar da Smart yay mata ta fasa rungume Lulu da tai niyya, hararsa tai da jawo Asma'un jikjnta dan sarai taga hararar da yayma yarinyar. Maryam ma tasowa tai da fara'arta tana musu sannu da zuwa tare da amsar kayan hanun Yayan nata. Sai suma sauran yaran dake a tsakar gidan duk suka shima musu sannu da zuwa da gaishesu. Suna ganin sun shige falon Ammah kowa ya nufi kaima uwarsa rahoto dan duk suna cikin ɗakunansu aunty Amarya ce kawai a wajen Abba dan yau itace da shi. Sun sami Ammah na sallar walha, sai Nasreen da ke kuka mamanta ta daketa, yayinda ita kuma Hawwahn ke ƙoƙarin saka turaren wuta a rushin da ta ɗibo.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣6️⃣
........Itama cikin farin ciki take musu sannu da zuwa, yayinda Lulu ke amsawa tana nufar Nasreen. “Oh oh mi akaima wannan princess ɗin ne haka take ɓarnar hawayenta masu tsada?”. Ta faɗa tana ɗaga Nasreen, zama tai ta ɗaurata saman cinyarta. Itako ta lafe cike da shagwaɓa da kuka ta ce, “Ba Mommy bace ta daken dan na kira Abbana a wayanta”.
“Ayya Mommy ita bata san mun ɗan ara bane muji muryan Abba. Barta daina kukan bazamu bata chocolate ɗinmu ba”. Tai maganar da share hawayen Nasreen ta ɗauka handbag ɗinta ta ciro chocolate biyu masu daɗi da tsada ta baima Nasreen. Tuni ta fashe da murnar dariya ta kaima kuncinta sumbata cike da farin ciki, sai kuma ta ɗaga musu chocolate ɗin tanai musu gwalo. Hakan ya bama Lulu dariya ta saki murmushi, suma duk sai suka fashe da dariya ƙasa-ƙasa. Dai-dai nan Ammah ta idar da sallanta, batai doguwar Addu'a ba ta juyo fuskarta da murmushi mai ƙyatarwa. Akan Smart da ke zaune kujerar kusa da inda take sallan ta sauke, sai kuma ta maida ga Lulu. Kafin tace wani abu ya saukko a kujerar ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ganin haka yasa itama Lulu sakkowa da ga kujerar ta zauna ƙasan carpet ɗin da ke a share tas ga ƙamshi mai daɗi na tashi a falon ta ce, “Ammah ina kwana”. Da sauri Ammah ta girgiza mata kai da miƙa mata hannu murmushin ɗunbin farin cikinta na sake bayyana ta ce, “A'a zonan ɗiyata kinji, taso maza taso gareni”.
Abin mamaki sai Lulu ta samu kanta dajin kunyar Ammah. Da ƙyar ta iya miƙewa ta nufo inda take, zata zauna ɗan nesa kaɗan nan ma Ammah ta riƙo mata hannu ta zaunar da ita jikinta sosai. Ajiyar zuciya Lulu ta saki hawaye na ciko mata ido, amma sai ta daure kanta a ƙasa ta sake gaida Ammah a karo na biyu. Shi Smart ma da abin ya girmesa kasare kawai yay yana kallonsu. Ammah ta riƙo hanunta cikin nata tana amsawa da kulawa.tare da ɗorawa da faɗin, “Ki saki jikinki ɗiyar albarka nan gidanku ne, ni ɗin ban son ki ɗaukeni mamar mijinki mamaki ce dan yanzu kinfi Hydar matsayi a wajena....”
Cikin waro idanu da ƴar shagwaɓa ya ce, “Ammah! Hakama zaki ce ina babanki ɗin?”.
“Kai tafi can ai photo copy ne ba original ba wake ta taka. Anata sabon ɗa waketa tsohon ɗa”.
Dariya su Hawwah suka saka, Lulu ta ɗago ta masa gwalo da nuna masa 8-6 da hannu. Lips ɗinsa ya cije da ƙaramar harara. A dai-dai nan Mama ta shigo tanama baƙuwa lale marhabun. Itama sai Lulu ta gaidata da girmamawa, Mama ta amsa da fara'a tana sanya mata albarka, dan ita dai barta da rashin mutuncinta idan ya motsa ko Umma ta tunzurata. Amma tanada kirki a lokuta da dama, sannan bata saka ƴaƴa a kishinsu inba taƙure ba.
Yaranne suka shiga shigowa ɗaya bayan ɗaya suna gaidata kamar yanda Mama ta basu umarni, sai dai a ƴaƴan Umma Mubarak ne kawai ya shigo cike da zumuɗi, dan yaso zuwa gaida amaryar yayan tasu Umma ta taka musu birki akan duk wanda yaje koda a bayan idonta saita tsine masa. Wannan girmamawa da Lulu taga an mata ya matuƙar birgeta, (tana son a girmamata a nuna mata ita mutumce mai daraja) koda Umma ta leƙo itama a gatsine wai tana mata sannu da zuwa da ɗan habaicin basu fara shiga ɗakunan su ba Lulu ba fahimtar komai tayi ba. Hasalima kallo ɗaya taima Umman ta duƙar da kanta dan haka kawai take jin Ammah ta mamaye mata ko'ina. Bata taba jin nauyin mutum da kwarjini kamar yanda takeji akan Ammah ba. Ga tsantsar soyayyar ta data hanga a cikin idanun dattijuwar yasata jin wani irin ƙaunarta ta musamman. Smart da shima yake matuƙar jin farin cikin nutsuwar da yaga Lulu tayi a gaban Ammah ya ce, “Da nasan haka za'amun a gidan nan daban zo ba. Amma ba koma a bani shayi nasha nai gaba. Zaku nemeni ne”.
“Wake buƙatarka balle ya nemeka anan”. Cewar Ammah da murmushi. Fuska ya shagwaɓe da faɗin, “Ammah! Ammah gara dai ki tarairayeni dan da tsohuwar zuma ake magani”.
“Ga wanda bai sani ba ba”.
Ammah ta bashi amsa.
“Shike nan na daina magana. Hawwah bani shayi na ƙara gaba, itama fa ku nema mata abinci bamu karyaba muka fito dan zumuɗinta”.
Ammah ta ce, “Kai Hydar dan ganganci. Shine kuma maimakon ka kira waya tunkan ku taho a ɗaura muku”.
“Haba Ammah sai kace wasu baƙi”.
“Baƙine mana. Tunda wannan ne karo na farko data fara marabtarmu dan wancan ba'a sakashi a lissafi. Ɗiyata mi kike son ci”.
Ƙasa Lulu ta ƙara yi da kanta tana girgizawa da faɗin, “Ammah bana jin yunwa ma, abarshi har sai anjima”.
“A'a bazai yiwu ba Mawaddatan'warahmah. Ƙarfe goma harta gota ace sai kuma anjima”.
“Ammah bason cin abinci take ba shiyyasa. Idan kika biye nata ma daga nan har dare zata iya kaiwa”. Smart dake ƙoƙarin kai shayin da Hawwah ta kawo masa bakinsa ya faɗa. Ɗan harararsa Lulu tai ƙasa-ƙasa bata dai ce komai ba. Shi kuma yay mata murmushin da take kira na mugunta.
Yana kammalawa ya miƙe da faɗin shi zaije ya gaida Abba ya wuce, sai anjima zai dawo. Addu'a Ammah tai masa da ta ratsa zuciyar Lulu matuƙa harta tsira musu ido. Karo na biyu yaji wani abu ya tsikarar mata zuciya game da ilimin addini, sai kewar mahaifiya data ratsata, itama fa da Mah-mahn ta nada rai da haka zata dinga mata ko? Sai hawaye suka cika mata idanu. Su Ammah daba lura sukai ba Smart ta ɗan dubeta cikin jin nauyin Ammah ya ce, “Madam na barku lafiya, duk abinda kike buƙata karkiyi fillanci Ammah taki ce.”
Kanta ta jin jina masa tana ƙoƙarin maida hawayenta. Da ga haka ya fice ya barsu....
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shiryama Lulu breakfast, yayinda gidan ya ɗauki shiru su Asma'u ma sun wuce makaranta. Ammah nata janta da taɗi itako tana bata amsa cike da kunya har Hawwah ta kammala tazo ta zauna. Sai Ammah tace suje ɗaki ko zata fi sakewa ta karya kafin suje ta gaida Abba da matan gidan dan yau dai ba fita zaiyi ba. Jin haka yasa Lulu cewa bari taje ta gaida Abban dan bata jin yunwa. Hakan yasa Ammah jin daɗi, dan haka ta miƙe da kanta domin rakata wajen Abban. Hawwah kuma ta shiga tattare kayan tana maidawa ɗakinsu...
Sosai Abbah yayma sabuwar surukar tasa tarbar mutuntawa kamar yanda yake ma sauran. Yayinda Lulu shima ta kasa ko kallonsa dan tsohon ya mata kwarjini sosai. Shima ta gaidashi da girmamawa ya amsa mata da kulawa da sanya albarka. Sannan ya ɗora da addu'a zama lafiya a gare su Ammah na amsawa da Amin cikin murmushi. Basu jima sosai ba dan sunga Lulun dai kunyarsu ta sata kamar takura suka fito bayan ta ajiye masa leda madaidaiciya mai ɗauke da turarruka masu tsada da ƙamshi, sai agogo. Da sauri Abbah yace, “A'a ɗiyata maza zoki ɗauka. Gaidamun ma da kuka zo kawai ya wadatar mun kumayi farin ciki”. Marairaice fuska Lulu da kanta ke a ƙasa tai da faɗin, “Abbah dan ALLAH karkace