Showing 138001 words to 141000 words out of 170683 words

Chapter 47 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7275

ta shiga, bin bayanta sukai da sauri suma duk suka shiga. A guje tabar anguwar damma ba yawan hayaniyar mutane a aria ɗin kasancewar sa babbar anguwa......


__________★


Bayan magrib Smart ya koma gida, ya iske Lulu cike fam da taicin su Nadiya har lokacin. Kasancewar bai san abinda ya faru ba sai ya ɗauka fushi take na daɗewarsa. Dan haka yayta satar kallonta da ga inda yake tsaye dan tunda ya shigo batako ɗaga kai ta kallesa ba balle ya samu sannu da zuwa. Aikinta take tayi a laptop da shan chocolate da su Hussain suka kawo mata lokaci-lokaci. Ice-cream ɗin da ya sayo mata da shawarma ya ajiye gabanta, batare da yayi magana ba shima ya wuce bedroom. Wanka yay har zai kabbara salla sai kuma ta faɗo masa a rai, amma sai ya ture zancenta gefe ya kabbarra sallarsa, sai da ya idar sannan ya miƙe, fitowa yay inda ya sake samunta har yanzu ido a laptop babu alamar ma ko kallon kayan da ya kawo matan tayi. Babu alamar wasa a harshemsa ya ce, “Kinyi sallar magrib da isha'i?”.
Shiru babu alamar zata tanka masa, ya ɗan rumtse idanunsa da sake buɗewa cikin sake kausasa harshe da buɗe deep voice nashi fiye da farko ya sake maimita mata. Yanzu kam dole ta ɗago ta ɗan kallesa, cikin harara ta ce, “Miye naka a ciki idan nayi ko banyi ba? Wai nikam dan ALLAH miyasa kake son shiga min rayuwa da yawa ne haka? Ko gadin rayuwata aka baka ne bani da labari. Bana son damuwa kabar ganin ina ɗaga maka ƙafa ka dinga ganin zaka cigaba da latsani a duk sanda kake so fa, dole ne duk abinda nayi ko baka nan sai na faɗa maka”.
Idanunsa kawai ya zuba mata, sai dai baiyi magana ba sai hannunsa kawai da ya rumtse waje guda alamar ɓacin rai matuƙa tattare da shi amma yana controlling temper ɗinsa. Dan baya son ko sau ɗaya ya ƙwace wajen bayyana mata ɗayan side ɗinsa a yanzu. Tsaye kawai ta gansa a gabanta, batare da yay magana ba ya ɗauke lap-top ɗin gefe gaba ɗayamta ya ɗauka kamar ɗazun. Yanzu kam ba duka ba har da su cizo takai masa amma ko gezau, bai direta ko ina ba sai bathroom ɗin ɗakinsa, dama a farce take, sai hakan ya ƙara tunzurata, sai dai kafin furucin bakinta ya ida fita ya taka mata birki da faɗin, “Shiiiiii!! Idan ki ka sake cewa tak wlhy sai kin sha mamaki yau.” da ga haka ya juya yay ficewarsa ya barta a toilet ɗin. Tsabar rasa abinyi sai kawai ta saki kuka, hawaye sosai tayi kafin tayi alwalar, koda ta fito batako kalla inda yake ba tai ficewarta, shima sai bai ce da ita komai ba dan ya riga ya kai waya ɗakin nata ya ajiye ta yanda in ma batai ba zai gani. Sai dai kuma Alhamdullah, koda ta shiga can ɗin sallar tayi dan da gaske dama batayi magrib ɗin ba, Azhar da la'asar dai da yake aunty Saliha na gidan tare ma sukayi. Bayan ta idar ta jima zaune a wajen tana tunani akan nasihar da Aunty Saliha ta sake mata musamman akan ibada. Da ga baya ta sake fitowa falon, anan ta sameshi kwance. Inda lap-top ɗinta ta ke ta koma ta zauna ta cigaba da harkar gabanta batare data kulashi ba, shima kuma baice mata komai ba yay shiru ne ma a kwancen kamar mai barci yana tunanin abinda ya faru a yinin yau ɗin gaba ɗaya. Sai da ta shagala a abinda take yi yaje ya ɗakko wayarsa, koda ya duba ya ga tayi sallar sai ya sake samun nutsuwa..........✍️







_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣4️⃣






.........Haka abubuwa suka cigaba da tafiya a gidan Smart da ɓangaren kwallonsa. Dan matuƙa ya dage da training da kuma kiyaye cin abubuwa tare da miƙama UBANGIJI al'amuransa, harda azumin kwana uku yayi da sadaka. Maganar shaƙuwa ko hirar arziƙi kam tsakaninsa da Lulu babu. Babu mai shiga sabgar wani ta ɓangaren lalama, garama shi wani lokacin yakan ɗan tsokaleta ita kuma tai masifa. Idan lokacin salla yayi kuma ko baya gidan zai tura mata text message akan tayi dan ALLAH, tai ma mahaifiyarta kuma addu'a. Sosai yake karya lagonta da hakan shiyyasa a yanzu kam Alhamdullah da wahala kaga lokacin sallar ma ya shige bata tashi tayi ba, daya turo saƙon ko batai niyya ba zata tashi taje tayi. Idan kuma yana gidan zai mata magana nan ma tayi. Girki ma dai kullum da rigima ake yinsa na safe dana rana idan har yana gidan, idan kuma ya fita na safen kawai akeyi ita dama ba damuwa tai da abincin ba, da dare kuma shi dama ba damuwa yay da cin abinci ba balle yanzu da yake sake ƙoƙarin daidaita jikinsa. Kayan shaye-shaye dai duk da ya toshe ko'ina da samunsu hakan baisa zuciyarsa ta samu nutsuwa ba, a duk motsinta kaffa-kaffa yake yi, ita kuma duk da ta daure kwana biyu a cikar kwana na biyar sai da yanayinta ya canja saboda matuƙa take buƙatar su, ta rage kulashi suyi faɗa, ta zama shiru-shiru, wani lokacin ma yakan shigo gidan ko ɗakinta ya ganta zaune a lungu ta takure kanta cikin damuwa koma tana kuka, sosai take bashi tausayi, dan haka a duk sanda ya ganta a yanayin sai ya zauna yayta mata nasiha ne cikin tausasawa, yana kuma ƙoƙarin bata ruwan addu'oin da malam ya basa a ɓoye batare da ta sani ba, magani ma na nan zuwa da malam ɗin yace zai haɗa mata inasha ALLAH akan shaye-shayen dai. A ɓangaren karatu da suka fara duk da dai suna ɗan kai ruwa rana wasu lokutan kafin ayi, Alhamdullah ya fahimci tana ganewa, dan a ɗan tsukun kwanakin a ɓangaren salla abubuwa da yawa Lulu ta gyara, tana kuma ƙoƙarin riƙe addu'oi. Nacin fita aiki kuma bata daina ba, shi kuma bai kulata ba. Washe garin da suka cika kwana biyar ranar asabar Aunty Bilkisu da Hawwah da Maryam da Asma'u sukazo gidan, ranar yana gida bai fita ba, dan dama fitar tasa dai ba ko yaushe bace ba, ba kuma ta wuce zuwa gidansu, stadium training, sai ɗan kaikawo akan case ɗintan nan na yarinyar nan da yake mata bincike tunda su Uncle Yousuf sun shigar da ƙara court da mahaifiyar yarinyar da kuma taimakon ƴan sanda. Duk sanda ya fita kuma baya yarda ya daɗe idan yayi tunanin ya barta ita kaɗai dan a ɗan zaman sun nan ya fahimci bata son kaɗaici, sai kuma sauran kai kawon da suke da su Coach akan batunsa na abubuwan da suka saura dole da kansa zaiyi. Tarba suka samu ta muntunawa ga Lulu irin wadda su kansu basuyi zato ba, sai suka ji ƙaunar matar ɗan uwan nasu ta ƙara mamayesu. Fargabar da suke ta wataran zai iya aure matarsa ta rabasu da shi ta fita fit a zuciyarsu. Yana ɗaki yana barci hayaniyarsu ta tada shi, bai san kosu waye ba dan haka ya tashi badan barcin ya ishesa ba ya fito, turus yay yana kallonsu, sai bin Lulu daketa faman murmushin yake da kallo, a zuciyarsa kuma yana wani tunani, musamman akan maganar malam da yace tana da ɓoyayyun halaye masu ƙyau, to amma miyasa masu aikin gidansu su take musu duk yanda taso? Kodan su suna a ƙarƙashin ta ne take gani, na biyu ya fahimci bata son kaɗaici sam, dan koshi idan zai fita gidan sai ya ga yanayinta ya canja zuwa damuwa koda bazatace komai ba. Maryam ce ta fara hangosa, cike da jin daɗi ta ce, “Yaya Hydar sannu da fitowa”. Da kai ya amsa mata, yayinda sauran ma duk suka juyo harda Lulu, sai dai kallo ɗaya ta masa ita ta ɗauke nata idon. Falon ya ƙaraso ya zauna, cikin girmamawa ya gaida Aunty Bilkisu, su Hawwah ma suka gaida shi. Daga haka aka ɗan cigaba da hira sai dai basu yarda sunyi wani abinda Lulu zataji a ranta kamar ita barece a cikinsu ba. Wannan abu yayi matuƙar tasiri a zuciyarta, sannan yanda suke girmama juna da shaƙuwarsu da soyayya mai ƙarfi ya matuƙar sata jin kewa da jin inama itama haka take da nata ƴan uwan. Ta kasance cikin farin ciki a wannan yinin, dan ko abinci Maryam da Hawwah ne sukayi basu barta tai komai ba sai Asma'u data gyara gidan, dan wannan shine kema Lulu wahala kuma duk da bata ƙaunar ƙazanta. Ta masa maganar mai aiki yaƙi ce mata komai, shi kuma ba mai aikin ce baiso ba duk da yasan kuɗin biyanta ma a garesa wani abu ne daban, tsoron kar mai aikin ta zame mata ƴar aikar sayo ƙwaya yake shiyyasa yay mata shiru. A lokacin da su Hawwah ke kitchen suna girki Aunty Bilkisu kece masa. “Hydar baka ganin ya kamata kayi haƙuri Hawwah ta koma ɗakinta, mijinta na sonta sannan yana ƙoƙarin sa a kanta, mahaifiyarsa kuma shima tafi ƙarfinsa ne. Tunda su Abba sun bar komai a hannunka ya kamata ayi haƙuri ta koma haka nan ai anja masa kunne, ALLAH tausayi yake ban kullum yana cikin zaryar zuwa gidan nan, ga Nasreen dake damunta kullum ita Abbanta Abbanta, ita kanta Hawwah dauriya kawai takeyi da kuma bazata iya ƙetare maganarka ba, kayi haƙuri ka duba ta koma gidan mijinta kodan halin Umma da bata gajiya da abin faɗa kullum ta ALLAH a gidan nan kan Hawwah, haƙurin shi yafi komai ko ya kikace Mawaddat?”. Ta ƙare maganar tana duban Lulu da ke saurarensu. Jin jina kai Lulu tai da faɗin, “Hakane Aunty, to amma miya kawo matsalar har haka? Sa'id ɗin bashine na gani a wajen bikin nan ba anata kai da kawo da shi?”.
“Shine fa.....” nan ta kwashe komai ta sanarma mata. Sosai Lulu tai mamaki, sai dai kuma hakan baizo mata baƙoba dan sun sha cin karo da irin waɗan nan case ɗin wasu ma sai iyayen mijin sun illata yaran saboda ƙiyayya, wasu ko yaranne fitsararru, sannan kakarsu Dada ita kanta fitinanniyar mace ce da tasan tana ƙuntatama matan kawun nanta matuƙa. Duban Smart tai da faɗin, “To amma shi miyasa bazai zauna yay magana ta fahimta da mahaifiyarsa ba, ko kuma yabar gidan nake ganin hakan zai basu masalaha idan basa ganin juna ai Aunty, ko za'a dinga samun matsalolin ba kamar suna zaune waje ɗaya ba”.
“Kowama haka yake faɗa Mawaddat, to amma maman ce taƙi yarda wai zasu barta a kaɗaici. Shi dai mijinki shi ya kamata yay haƙuri a duba kodan Sa'id ɗin” ta ƙare maganar da kallon Smart.
Shiru kamar bazaice komai ba sai kuma ya ɗan nisa. Cikin ɗage kafaɗa ya ce, “Aunty Bilkisu bawai zaman nata nima namin daɗi bane, sai dai kuma bazan barta ta koma ba haka salin alin, inada shiri nima dan dolene sai mahaifiyar Sa'id ta fahimci kuskurenta ko kuma ya raba musu gidan, inada hikimata na tsaiwa akan hakan dan har mahaifinsa ya dawo sannan”.
Cikin gamsuwa Lulu ta ce, “Hakan da yayi ɗin shine dai-dai, inba hakaba komawar tata haka nan babu wani mataki zai cigaba da bada damar faruwar fiye da haka a tsakaninsu......”
Haka suka cigaba da tattaunawa har su Hawwah suka kammala girki. Wani abu daya saka Lulu farin ciki lokacin da su Aunty Bilkisu sukai zaman cin abincin da suka zuba a tray ɗaya sai ta tsaya kallonsu musamman da Smart ya ɗakko nasa spoon yazo tsakkiyarsu ya zauna yana faɗin “Ni sai a ware ni”. Abune da bata taɓa gani a gidansu ba, itama saita tura baki gaba tace, “Ni baku so naci da ku saboda ba Ammah ta haifoni ba”.
Da sauri aunty Bilkisu ta kamo hanunta ta zaunar kusa da ita kusa da Smart kuma ɗan shine a gefenta, har suna haɗa baki ita da su Hawwah wajen faɗin, “Karkisa Ammah ta dafamu a tukunyarta da jin wannan kalamai”. Murmushi tayi kamar yanda shima Smart ke kallonta ta ƙasan ido yana yi, sai tana mai jinta kamar sabuwar halitta a yau. Lulu da bata damu da abinci ba yau kam saita saki jiki ta ɗan ci. Da son neman magana Smart ya ɗauki naman gabanta, hararsa tayi da tura baki itama ta ɗauki na gabansa batare da tace komai ba, kallonta yay yana ɗan zaro ido ya ce, “Miye kuma na ɗauka min nama Madam?”.
“Nawa daka fara ɗauka naka ne”.
Itama ta faɗa cikin ɗam murguɗa baki kaɗan. Kai kawai ya jinjina alamar zan rama, su dai su Hawwah sai gimtse dariya suke. Can Lulu ta sake ɗaukar naman gaban nasa ta rufe da abinci, sarai ya ganta sai baiyi magana ba sai da ya shammaceta ta ɗakko zata kai baki caraf ya ɗauke sa daga spoon ɗin nata ya lunƙuma baki. “What!” ta faɗa tana kallonsa, miƙewa yay da mata gwalo yabar wajen dan ya ƙoshi daman. Da gudu su Maryam suka tashi suna dariya. Lulu ta dubi Aunty Bilkisu kamar zatayi kuka ta ce, “Aunty kin ganshi ko? Shi baiso a zauna lafiya kullum sai anyi faɗa yake jin daɗi”.
Aunty Bilkisu dake danne dariya da ƙyar ta harari Smart da dafa Lulu da itama ke hararsa ta ce, “Kinga ƙanwata barsa zamu rama. Tsarabar dana kawo takine ke kaɗai nama fasa bashi”. Murmushi tai da sake hararar Smart itama ta masa gwalo da faɗin, “7-6”. Ƙwaɓe fuska ya ɗan yi shima da yin ƙwafa ya ce, “Ki jira game over. Aunty kuma gaskiya ba haka akeyi ba”.
“To ni haka zanyi”. Cewar Aunty Bilkisu tana hararsa. Sai kuma ta kalla Lulu, “Kin san wani abu shi fa dama Hydar akwai zura tun yana yaro, idan aka zuba abinci aka bashi sai yace shi bashi yake so ba na Ammah yake so, idan aka bashi sai kuma yace (Ni wannan ina co) ya sake nuna namu, nan ma a bashi sai ya sake nuna wani nanma yace shi wannan yana co, hankalinsa bazai sake kwanciya ba sai yaga kaf abincin an tara masa gabansa zai bar kunnen kowa ya huta kuma fa ba ci zaiba.
“Kai aunty miye na faɗa mata kuma” Smart ya faɗa cikin shagwaɓa. Aiko mi Lulu zatai inba dariya ba. Sai ta kallesa tace “Ni wannan ina co” ta ƙyalƙyale da dariya. Sai da takai ya kwashi filos ya fara jefa mata ta tashi da gudu tana cigaba da faɗa. Dole aunty Bilkisu ta dara itama tana sake jin ƙaunar Lulun a ranta. Waɗan nan abubuwan sun matuƙar ɗauke ma Lulu kewa da sakata a farin ciki a wannan yinin, yayinda gefe ɗaya ta takurama Smart da faɗin ‘Ni wannan ina co’ har bayan tafiyarsu. Shima sai abun ya koma bashi dariya dan ya fahimci ta samu abin yi.........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣5️⃣








........Washe gari bayan ya dawo motsa jikin safe da yake fita yace ta shirya zasu fita, da mamaki ta dubi agogo da faɗin, “Da sassafen nan? Ko 8 fa batai ba”.
Shima agogon ya kalla sai kuma ya dubeta. “Ina ganin kafin mu kammala shiryawan tara ma zata iyayi, dan inada abune mai muhimmanci shiyyasa nake son mu fita da wuri”.
“Wai ina to zamuje?”.
“Idan mun fita ai zaki gani, ke dai ki shirya”. Ya faɗa yana ficewa, kitchen ya nufa ya sake ɗaukar ruwa ya sha sannan ya nufi bedroom ɗinsa ya cire kayan motsa jikin dake jikinsa ya faɗa wanka. Itama a ɓangaren Lulun wankan ta tashi ta shiga, dan dama dai tana duba karatun da ya ƙara mata ne kafin fitarsa training. Harga ALLAH tana jin daɗi da farin cikin karatun da sukeyi na addini, abinda kuma ke sake zaburar da ita akan hakan watarana akan wani case an gayyaceta hira a gidan wani tv tare da wani lawyer da basa shiri sam saboda duk karon da tai da shi a shari'a sai ta kaisa ƙasa. A cikin hirar kawai ɗan jaridar sai ya sakko wata magana data shafi addini, amma sai ta kasa amsa masa dan bata sani ba, sai shi lawyer ɗin ya amsa da karsashi da son nuna isa har yana mata shaguɓe akan bata da ilimin addini. Abin ya mata ciwo, tun a lokacin kuma tayi ƙudirin fara neman ilimin sai dai bata san tayaya zatai hakan ba, sannan bata da shaƙuwa da wani a ƴan uwanta da zata iya kawo zancen ta yanda za'a fahimceta, na biyu rashin barin abu a rai da take da shi ya sata tattara abin ta ajiye gefe ta cigaba da sabgoginta. To bayan fara karatun nan da Smart ke koya matan sai ta fara fahimtar abubuwa da dama, sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login