Showing 39001 words to 42000 words out of 170683 words

Chapter 14 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7246

daɗin rayuwar doya da manjan da ke a tsakaninsu. Dan ko gidan su ƴan biyun sukazo basa kulata bata kulasu, saboda sun riƙe abubuwan da mahaifiyarsu ta fuskanta da ga mahaifinsu dalilin mahaifiyarta da ita kanta. Goshinta da yay mata nauyi saboda abinda ta sha jiya bai gama sakinta da ƙyau ba ta ɗan shafo tana furzar da iska. Ba ƴan uwanta kaɗai ba hatta Mommy tana jin ƙaunarta, dan kallon uwa take mata a zahiri da baɗinin rayuwa. Ta sani duk wanda yasan gidansu ma ya sani Mommy bata taɓa cutar da rayuwarta ba koda da harara, idan dai tayi laifi yanda take ma yaranta faɗa itama haka take mata. Shiyyasa duk rashin mutuncinta har abada bazata taɓa kwatantashi ga Mommy ɗin ba. Musamman ma idan ta tuna nasihar da Kakanta Alh. Sufi Garko kanyi mata a duk sanda taje garesa game da Mommy ɗin da halaccinta ga zamantakewarta da mahaifiyarta. Duk da dai itafa har yanzu bata taba jin labarin ainahin zaman da Mamanta tayi da Mommy ɗin ba...... Gaisuwar da ma'aikatan gidan ke mata ce ta katse mata tunani, batare data kalli ko guda a cikinsu ba take wucewarta kawai da takun nan nata na yauƙi da isa. Tana gab da isa motar da take buƙatar hawa idanunta suka sauka akan Smart da ke zaune wajen maigadi kamar kullum hankalinsa a waya yana buga game ɗin ball da yake matuƙar bege. Sake tamke fuska tai da ɗauke kanta, abinda ya faru jiya ne ya shiga mata kaikawo cikin kai. Sosai taji ɓacin rai ya sake baibayeta da takaicin su Nadiya da suke son jamata rainin nan wajen wannan shashashan, ta jima tana shaye-shaye, amma duk wanda yay mata sani na haƙiƙa bai san wannan halayyar tata ba, a koda yaushe cikin ƙoƙarin binne sirrinta take, amma sai gashi a haɗuwarta da mutumin da tafi tsana fiye da kowa a duniya shi ya ganta a yanayin. Ƙwafa tai da balla masa harara, cikin borin kunya ta cilla masa key da sake jan tsaki. Idanunsa da ke nuna alamun barci bai ishesa ba ya ɗan lumshe ya sake buɗewa, batare da ya kalleta ba ya miƙe zuwa gaban Motar data ɗakkoma key ya buɗe mata bayan, sai da ta shiga ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver, motace mai tsadar gaske da ɗaukar hankali, kasancewarta ƴar gatan gidan hatta Daddy tafi yawan motoci. Dan motarta biyar kuma duk ƙosassu, sai ƙarama ɗaya da sha'awa kawai ya sata matsawa Uncle ɗinta Khamil ɗan uwan mahaifiyarta dake Abuja saya mata ita. Dai-dai suna barin kan titin layin nasu ya miƙa mata handbag ɗinta ta jiya da key ɗin mota, a hankali ta ɗago da ga duba takardun da takeyi ta ɗan sake hararsa sannan ta kalla kayan a yamutse. Murya a dake sai dai acan ƙasan maƙoshi ta furta, “Waya gayyaceka inda nake jiya?”.
Sarai ya jita, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita ya haura kan babban titin bayan motar da ya dakatama ta shige layin da ya fito. “Malam da kai nake yi”. Ta sake faɗa cikin zafin rai da borin kunya. Karan farko ya ɗan ɗago idanu ta cikin mirror ya dubeta. Ido suka haɗa, tai saurin kauda nata zuziyarta na tsirgawa. Itafa komi za'ai ayi amma kar ya kalleta da wannan shegun idanun na macizai (kamar yanda ta raɗa musu😂🥱). Yanda tai ɗin sai ya so bashi dariya, amma sai baiyi ba ya ɗan saki murmushin gefen baki da maida hankalinsa ga titi cikin salon lumshe idanun nasa kamar yasan suke razanata, babu alamar zai bata amsar da take buƙatar son ji. Ba ƙaramin takaicinsa bane ya kume Lulu, ga wayarta ta isheta da ruri. Nadiya ce keta faman kiranta tun ɗazun, sai dai taƙi ɗagawa dan tai alƙawarin sai ta koyama ƙawar tata mafi kusanci hankali. Tsaki taja a karo na babu adadi, ta fisgi wayar da ke kan rigarta ta lauyoyi ta kashe tare da sake cillar da ita kan rigar da ke a gefenta. Haushin Nadiyar dana sharetan da yay ta tattaro gaba ɗaya ta nufesa da shi.
“Wai kai mika ɗauki kanka ne da har ina maka magana kana wani cika da batsewa?”.
Yanda tai maganar muryarta har tana zuga kamar wadda kuka ke son yunƙuromawa sai dai ƙarfin halinta na dannesa ya sashi sake dubanta a karo na biyu ta cikin mirrorn. Sake maida kansa yay ga titin sai kuma ya ɗan muskuta zamansa da furzar da iska. Ƙasa-ƙasa na rashin kuzarin da kasala irin na wanda barcin bai ishesa ba cikin deep voice ɗin nan ta shi ya ce, “Mi kike son sani?”.
Wata irin kasala muryar tasa ta nema saukar mata saboda yanda yay maganar cikin sanyi da tausasa lafazi, sai dai cikin yaƙi da kai da nuna juriya irin ta masifaffun mutane ta watsa masa kallon banza da yin ƙwafa tana maida kanta ga takardun da take dubawar. Kamar bazata ce komai ba sai kuma bayan kusan minti ɗaya ta ce.........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣






.........“Waya aike ka inda ka sameni jiya? Miye ma dalilinka na bina?”.
Idanu ya lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Kamar yanda yay magana ɗazun a tausashe yanzu ma haka yayi. “Baki so asan kina aikata abinda na gano ɗin ne?”.
“Kai ɗin banza da zanji ina son ɓoye maka abu. Shiga abinda ban saka ka bane ya sa nake neman ba'asi dan bana son shiga sharo. Idan kuma kace zaka cigaba da shiga min hanci wlhy zan saka ka dana sani kai da duk wanda ma yake maka kallon arziki. Tsabar kai ɗan haɗin masifa ne ka ɗauke ni ka kai gidan Uncle you.., wlhy kasan mima zaka faɗa masa, in ba haka ba sai naje har gidanku kaima na maka ƙullin da har gaban abada baka isa ka kwancesa ba ɗan sa ido kawai. Idan kuma kaji ƙarya mu zuba ni da kai mai shishshigin tsiya, kai a dole sai ka shiga jikin iyayena dan maular tsiya irin ta talaka”.
(Maula! Talaka!) Zuciyarsa ta maimaita cikin jin ƙunar kalmomin. Kamar zai yi magana sai kuma ya haɗiye abinsa dan ya fahimci al'amarinta na buƙatar sai da uzuri, idan yace zai biye mata sai ma su zama ɗaya. Yanda bata sake magana ba tana ta faman duba takardun nata shima bai sake kallon inda take ba, sai dai ƙamshin turaren data bulbula ya addabesa har yana hawar masa kai kamar yanda itama nashi ke cizon can ƙasan zuciyarta. A cikin tsare-tsaren da Uncle Yousuf ya bashi nata ya sashi sanin inda zasu je a yanzu ɗin, dan haka kai tsaye babbar kotun da muke kira da (kotun ALLAH ya isa) dake a jiha ya nufa. Tamkar ba safiya ba harabar court ɗin cike da mutane, hancin motar na kunna kai cikin gate ɗin wasu gungun ƴan jarida suka yomusu caa, isowar securitys da ke son hana ƴan jaridar isowa garesu ya ɗan maido hankalin mutane kan motar suma. Kafin ya gama kashe motar har an buɗe mata. Fuska a yamutse da ɗan jan tsoki ta kalla harabar court ɗin. Wanda ya buɗe matan ta miƙama tarkacen hanunta tare da rigarsu ta lauyoyi. Ita kuma ta ɗauki handbag ɗinta bayan ta toshe fuska da wani shegen gilashi mai tsananin ƙyau ta haɗa da hular, dai-dai tana ficewa ta balla masa harara da faɗin, “Saura nan ma kace zaka biyoni kaga yanda zan baka mamaki”.
Da kallo kawai ya bita, sai kuma ya ɗan furzar da iska ransa fal mamakin yanda bata gajiya da masifa. Da ga can ƙasan ransa kuma yanda ake ta bata wani girma da kariya da ga security ɗin da zallon da ƴan jarida ke faman yi na son isowa gareta ya ƙara ɗaure masa kai da jin takaicin da sun san wacece a zahirinta da ko kallon mutuntawa bata cancanta a garesu ba. Bai iya ɗauke idanunsa garesu ba dan takaici har suka shige wata ƙofa ba ainahin ta Court ɗin ba. A take ya ga gurin ya sake ribcaɓewa, mutane sai faman ɗura kai suke cikin court ɗin. Maganar wasu samari da ke wuce motar cikin ƙaucin shiga kotun ta ɗan ja hankalinsa. Na farko mai riƙe da camara ke faɗin, “Yaufa akwai ƙura, dan na tabbatar barrister Mawaddat Jiƙamshi ba ƙaramin sabon shiri tayo ba duba da yanda Barrister Marafa ya nema zubar da ita a wancan zaman. Kasan fa ita bata taɓa bari a kaita ƙasa musamman a kan irin wannan case ɗin na fyaɗe, ga shi tasan aikinta lawyers ƴan uwanta da yawa har tsoron karawa suke da ita, dan ita ko waye ma ubanka akan fyaɗe sai tayi kutu-kutun turaka jail dan haka kullum ita bata kare mai laifi sai wanda aka zalunta musamman ƴan uwanta mat.......”
Bai ƙarasa jin abinda saurayin ke son faɗa ba dan sun masa nisa. Da farko baiyi niyyar shiga wajen ba, sai dai saboda gargaɗinta ya ƙudiri shigar dan yaga mizata iya masan. Ƙoƙarin fitowa yay a motar kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya cirota da ga aljihu. Ƙanwarsa ce mai bimasa Hawwah dake auren abokinsa. Ɗagawa yay, sai dai yana kaiwa kunnesa yay saurin janye wayar yana mai lumshe idanunsa. Buɗesu yay a hankali zuciyarsa na wani irin zallo. Cikin motar ya koma tare da sake kiranta. Ringing ɗaya ta ɗauka. Cikin matsanancin kuka ta ke faɗin, “Yaya dan ALLAH ka barni na taho gida. Wlhy na gaji da wannan rayuwar bazan iya ba. Inko ba haka ba wataran sai mahaifiyar Abban Nasreen ta kasheni a gidan nan....”
Iska ya ɗan furzar mai ɗaci, tare da faɗin, “Miya kuma faruwa?”. Sake fashe masa tai da kuka, da ƙyar ta iya faɗin, “Mai fa da nake suya airish ma Nasreen da zata wuce school ta kusa kwaramin yau a jiki Yaya. Ban san wane irin rashin ƙauna matar nan take min ba. Wlhy bazata taɓa canja halinta ba nima na gaji da haƙuri da ita.”
“Shi ina Sa'id ɗin yake?”.
“Yaya yana fa a gidan, gashi can ya jata wai yana bata haƙuri saboda ni ba'a san ciwona ba. Yanzu Yaya data sameni da man nan haka zai tsallakeni ya bita ke nan....”
“Kinga ya isa. Ki jirani gani nan zuwa gidan yanzu”. Da ga haka ya yanke wayar batare da ya jira abinda zata ce ba. Fitowa yay a motar ya kulle. Da ƙafa ya fita a habar court ɗin da ta yi tsittt alamar an fara shari'ar ko za'a fara. Yana fitowa a gate ɗin ya samu napep zuwa Daurawa anguwar da gidan ƙanwar tasa take. Kasancewar safiya ce basu wani samu matsala ba, dan haka suka iso da wuri. Bayan ya biya mai napep ɗin maimakon shiga gidan kai tsaye ko yin knocking sai ya ɗaga waya yay kiran abokin nasa Sa'id Ibrahim da sukai karatu a jami'a tare. Yanda Sa'id ɗin ya ɗaga wayar ta isa tabbatar da a rikice yake. Dan duk ya daburce sallamar ma da in ina yayi ta. Sai kuma ya shiga kame-kamen gaisuwa. Katsesa Smart ɗin yay da faɗin, “Gani a ƙofar gidanka ka turo min Hawwah zamu wuce gida”.
“G...g...gida kuma Mawashi? Miya faru ka...k...kake wannan maganar haka? Ko itace ta kira ka ta faɗ......”
“Sa'id!!”.
Ya dakatar da shi a harzuƙe. Sake tsurewa Sa'id ɗin yayi dan yasan halin abokin nasa sarai. Bai da yawan magana ko hayaniya, dan bai taɓa ji ko ganin abokin faɗan Smart Mawashi ba a rayuwa. Amma shi kaifi ɗaya ne akan komai da kowa. Duk yanda yake da kai bai yarda ka latsashi ba ko gasu abokai. Yanda ya rikice ɗin sai ya harzuƙa ran mahaifiyarsa da ta hanashi fita duba matarsa. Dan ta rantse ko bakin ƙofa yaje domin Hawwah ɗin sai ta tsine masa. Cikin masifa ta wafce wayar, kunnenta ta kai da faɗin, “To ɗan mulkin mallaka wai shin nikam ko kai ne ka haifa min Sa'id ne ban sani ba? To bazai zo ɗin ba, nace bazai zo ba idan ka isa kai duk abinda kake jin zaka iyayi, ko ita ƙanwar taka autar mata ce da in ya rabu da ita zai kasa cigaba da rayuwa har ya auro wasu huɗun. Aikin wofi kawai anga kuɗi an nanema yaro na”.
Har tayi ta gama bai ce uffan ba, sai da yaji tayi shiru ya yanke kiran. Yanda yake huci zai baka tabbacin sanin ran ƴan maza ya kai ƙololuwar ɓaci. Number Hawwah yay kira, bugu ɗaya ta ɗaga. Kafin tace komai ya ce, “Ɗakko mayafinki ki sameni waje”. Ya yanke kiran. Minti shida kuwa bata gama cika ba sai ga Hawwah da ƙaton akwati da Nasreen ƴar shekara huɗu biye da ita. Tana ganinsa ta cilla da gudu garesa tana faɗin, “Oyoyo Uncle”. Kaɗan ya saki murmushi, tare da duƙawa ya ɗauketa ita da school bag ɗin da ke goye a bayanta alamar an gama mata shirin makaranta ne. Sau ɗaya ya kalla ƙanwar tasa ya kauda kansa. Batare da yace komai ba ya amshi akwatin hanunta yay gaba tabi bayansa. Napep ya tare musu suka shiga, Nasreen nata zuba masa surutu dan yarinyar ko akku haka ta ganta ta bari kamar ƴar ƙwa-ƙwa akwai wayon jaraba. Dan bakinta ya girmi shekarunta. Sai da ya kaisu har gida sai dai bai shiga ba yace taje ta jirasa zai je ya dawo. Bata musa ba ta fita, shi kuma yace ma mai napep ya juya da shi babban kotun dake jaha. Ya samu har an fito da ga shari'ar, yanda harabar kotun ke'a harmutse da ƙayataccen murmushin da ya hango a fuskar Lulu ya sashi tsira mata idanunsa. Tsaye take a tsakkiyar lauyoyi ƴan uwanta wanda da alama duk ƴan ɓangare ɗaya ne a shari'ar, dan yanda fuskokinsu ke a washe kamar ita saɓanin waɗanda ke gefensu kaɗan zai baka tabbacin hakan. Ƴan jaridar da suka zagayesu ya sashi daina iya hangota, ɗauke kansa yay tare da buɗe motar ya shiga, a kallo ɗaya zaka fahimci damuwar dake zagaye da fuskarsa, dan babu abinda ke faman masa kai kawo sai batun ƙanwarsa Hawwah, shi shaida ne Sa'id na matuƙar son Hawwah, sai dai matsalar mahaifiyarsa da tun farko ta nuna bata son auren saboda ƴar ƙanwarta da taso ya aura shi kuma yaƙi tsayawar mahaifinsa ta sa ta janye ta amince ya auri Hawwah, sai dai tunda take gidan mahaifiyar tasa ke nuna mata hantara da ƙyara musamman idan Alh. Ibrahim mahaifin Sa'id ɗin baya gari. Tasha marin Hawwah ɗin dayi mata abubuwa masu cin zuciya shi yana zuwa ya sasanta bada sanin iyayensu ba. Sai dai a wannan karon ya fahimci dole ne fa a tauna tsakkuwa dan aya taji tsoro. Dan tsohuwar na buƙatar sanin Hawwah nada gatan iyaye da dangi itama, sannan dukiya ba itace rayuwa ba kawai akwai muhimman abubuwa da suka fita a zamantakewar rayuwa. Kai dai kai fatan kawai ALLAH ya rufa maka asiri kafi ƙarfin yau da gobenka. Idan kuma ya azurtaka da dukiyar ka bida ita ta hanyar da kai a karan kanka zakai alfahari da kanka watarana da zaka amsa tambaya akan dukiyar kwabo bayan kwabo........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻






𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣






.........Gigitaccen knocking ɗin da akai ma glass ɗin motar ne ya sashi dawowa hayyacinsa. A hankali ya buɗe idanunsa da sukai mugun kaɗawar ɓacin rai ya sauke a kanta. Harara ta balla masa da juyayyun idanun nan nata da shaye-shaye ya gama canjawa yanayin kallo.
“Kai anya kuwa ka taɓa shiga ajin makaranta? Dan na fahimci baka san aikin ka ba, malalacin banza kawai ka zauna kanama mutane tunanin iska a mota, ko an gaya maka a banza ake mallakar irin motar har ai zaman tunani a cikinta Mtsowww!! Baƙauye”. Ta buɗe motar a fusace ta shige tare da rufe murfin da ƙarfi. Fitowar da yay niyyar yi buɗe mata ya fasa, batare da ya tanka mata ba kamar yanda ya saba yayma motar key. Bata sake bi takansa ba ta maida hankalinta a lap-top itama, yayinda shi kuma yake tafiya a nutsensa. Sunyi nisa sosai batare da ko sau ɗaya ta ɗago taga ina suke nufa ba, dan ita duk zatonta hanyar office ɗinta ya nufa da ita tunda Uncle Yousuf yace mata ya bashi komai nata a rubuce. Jinfa tafiya na neman ƙin ƙarewa ya sata ɗagowa. Da sauri ta ƙara ware Lulu ayes ɗinta tana kallon inda zata iya rantsewa bata taɓa sani ba ma, dan ita dai kusan yawonta wajen Kano a jirgi ne. Gabanta ne ya faɗi, zuciyarta ta shiga mata kai-kawon ko yayi kidnapping ɗinta ne? Amma sai ta dake a masife ta ce, “Kai malam mi kake ƙullawa ne? ina ne kake shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login