Showing 102001 words to 105000 words out of 170683 words

Chapter 35 - FURAR DANKO BOOK 1 by Billyn Abdull.txt

09 Dec 2024

7269

idanunsa sai dai bai rufesu duka ba yana kallon tarin abokan kwallonsa da sukazo da ga gari-gari domin tayashi murnar aure ƙasa-ƙasa.
Suma wasan nasu yayi ƙyau, sai da akai kiran magrib suka tashi sai kuma an haɗu a wajen dinner, dan Coach shi yay ƙoƙarin bama baƙinsu masauki duk da wasu ma sai yau suka iso dai shine kuma mai gayyatar da Ahmad. “Wai ya naga duk jikinka yay wani laƙwasa ne? Ko ciwon kanne bai saukaba still?”.
Cewar Ahmad cikin damuwa. A hankali ya ɗan furzar da iska tare da shafo goshin nasa ya ce, “Ai ciwon kan nan inaga kozai barni sai an gama hayaniyar nan. Harma na saba da shi a kwana biyun nan”.
Sannu Ahmad ɗin yay masa cikin damuwa. A haka suka ƙarasa gidansu Ahmad ɗin dan acan zasu yi shirin tafiya dinner ɗin, kafin su wuce su ɗauki amarya a gidansu.....


*_DINNER HALL_*


Ƙaton waje ne na gaske Alhaji Sufi Ado Garko ya kama domin ya gayyaci manyan abokan kasuwancin sa dana siyasa a ciki da bai ɗin Nigeria. Gashi kuma mafi yawansu sun san Daddy shima tun da babban yaronsa ne na amana da duk wanda yasan Alhaji Sufi Ado Garko to yasan wanene Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi a wajensa. Iya tsaruwa wajefa ya tsaru, ga abinci iri-iri an tanada. Haka ma manyan mawaƙa na Hausa dana turanci duk sun hallaro. MC kansa mashahuri aka ɗakko domin gabatar da komai. Ta gefe ɗaya ƴammata da samarin Garko family da suka haɗe da jiƙamshi family sun haɗa babban show mai ƙayatarwa domin nishaɗantar da jama'a. Duk da girman wajen da alamu ya nuna zai ɗauki mutane masu yawa duk wanda zai shiga sai da i.v ɗin sa ne zai zama masa gate pass. Dan haka su kansu su Smart da ahalinsa suka shirya komai a tsari domin mutunta kansu a wajen. Duk da dai Alhmdllh ALLAH ya riga ya mutuntasu, tunda da har zuwa yanzu babu wata ɓaraka data shiga na raina juna a tsakani, ko Umma daketa neman hanyar baƙanta Smart wajen wani a cikin dangin matar tasa har yanzu ALLAH bai bata damar ba. Kafin takwas waje da ya cika yay hani'an da manyan mutane ƴan siyasa da ƴan kasuwa har ma da ƴan bokon da iyalansu. Kowa ka gani shar da shi, dan duk da ba'ai anko da zai zama komai da komai iri ɗaya ba sun rubuta kalar kayan da ake buƙatar ƴammata da samari duk su saka. Koma wani iri ne ka saka kala kawai ake buƙatar tazo ɗaya. Manya ne dai kowai yay yanda yake so....
Masha ALLAH na faɗa a lokacin da idanuna suka sauka akan ANGON ƙamshi Aliyu Hydar Smart mai masoya da yawa cikin wata dakakkiyar shadda mai tsananin ƙyau da maiƙo taji aiki na musamman. Itace kawai abinda ya yarda ya amsa da ga dangin amaryar tasa dan Baba ya aiko masa da ita matsayin wadda zai saka a yau ɗin, kamar yanda itama amarya ganin nata kawai tayi. Farar shadda ce da akaima wani shegen ƙawataccen aiki da kalar golden mai ɗaukar ido. Takalmar ƙafarsa haif cover suma golden da ratsin fari, haka ma hularsa golden da ratsin fari kaɗan. Sai agogonsa golden shima. Ga gyaran fuska da ya ƙara masa kwarjini da cikar kamala an masa. Sam wannan Smart ɗin ya banbanta da wancan Smart dirver da kuka sani. Ƙamshi har ba'a magana. Tun a gida Ahmad ke jera mar hotuna dan yakai a ɗaukesan. Ya kuma tubure bazai tafi ba sai yaje Ammah da Abba sun gansa. Dole sai da su Ahmad suka kaisa gidan kuwa Ammah da Abban suka gansa da tsaffin da bazasuje dinner ɗin ba. An masa hoto da iyayensa Abba ya rungumesa. Duk kauce-kaucen Ammah sanda za ɗauke su hoto itama sai ya kwanta da kansa a kafaɗarta, hakan yasa ta juyo kamar zata hararesa shi kuma yay murmushi cikin salon shagwaɓe fuska, ga Abba ya kallesu shima yana murmushi. Hoton sai ya zama na musamman........✍️









_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣




......Daga nan gidan Daddy suka ɗunguma ɗaukar amaryar ƙamshi. Lulu lu'u-lu'un Jiƙamshi family, tauraruwa abar buƙatar son ganin kowa.
“Ya arrahaman!” Ango Smart ya ambata a hankali lokacin da Hussaini ke fitowa da ga gidan riƙe da hannun Lulu. Ni kaina masu karatu sai da alƙalamina yay adungure ƙasa da ƙyar na kamosa na cigaba da muku burutun. Amarya da tayi jiƙaƙƙen ƙyau, idan nace muku ƙyau ina nufin ƙyau maƙurar ƙurewa a cikin ƙarshen ƙure. Wani irin shegen material ne golden color da aka ƙawata da adon fararen stones masu walwali da ɗaukar idanu. An masa ɗinkin gown data kama mata jiki, sai aka ɗaura wani ƙawataccen alƙyabba fara da adon golden kuma a sama, ta rufe jikinta gaba ɗaya tana ɗan jan ƙasa kaɗan. Ɗauri iya ɗauri, ga shi kwalliyar da akai mata ƴar dai-dai misali da bata ɓatar da ainahinta ba a yanzu. Kayan yari komai yaji, ƙamshi kam ba'a magana wayyoni ALLAH kai jama'a. Yaufa Lulu ƙamshi a ƙamshin take ɗan gaske. Takalman ƙafarta su kansu abin kallo ne, suma farare ne da kwalliyar golden sai pos ɗin ta itama farace da kwalliyar golden stones. Kamar shock ne ya jasu a lokacin da Hussain ya kamo hannun Smart ya saka masa na Lulu. A tare suka zabura zasu janye amma tsabar muguntar Hussain ya sake riƙewa gam ya hana hakan. Duk sai sukai diri-diri da idanu (kamar an kama suruki a ɗakin ƙawar kakar matarsa😂😜) cikin wani irin malalacin yanayi ta sakar ma Smart kasalalliyar Harara. Sai kawai ya samu kansa da ramawa shima. Shi Hussain ma sai abin ya bashi dariya. Amma sai ya danne daƙyar baiyi ba ya sake matse hannayensu cikin na juna da faɗin, “Yayana Aliyu Hydar Zakin zaki ga amanar ƙanwata na baka, har abada bana son ka saki wannan hannun ya kasance cikin laluben naka dan ALLAH”.
Smart da Adams apple ɗinsa keta kaikawo a maƙoshi ya saki murmushi mai sanyi da faɗin, “In sha ALLAHU Yaya Hussain. Na kuma gode”. Murmushin jin daɗi Hussain ya saki jin Smart ya kirashi da Yaya, duk da kuwa yasan Smart ɗin zai iya girmarsa da kusan shekaru biyar ma. Hannayen nasu ya saki yana kallon fuskar Lulu da tai wani irin yin takwaf-takwaf tana neman zame hanunta dake cikin na Smart shi kuma ya hana faruwar hakan ta hanyar damƙesa da kyau, kansa ya girgiza mata da ɗan lumshe idanu alamar lallashi irin na yaya da ƙanwa. Dole ta haɗiye abubuwan da ke mata kaikawo a zuciya da maƙoshi a tare, Hussain ya buɗe musu motar da Ahmad ke ciki yana jiransu a mazaunin driver. Ita ta fara shiga, sannan shima Smart ɗin ya shiga, sai kawai Hussain ya shiga gaba dan Uncle Yousuf ne duk ya tsara musu hakan saboda dai kar mutuniyar ta bada ƙafa🤣 dan tabbas zata iya maida hall ɗin kudanci da ga gabashin da yake a gine😂. Ganin Hussain ɗin kam ya sake saka mata nutsuwa da ƙwarin gwiwa harda sauke ajiyar zuciya kamar Smart ɗin yazo ɗauketa kenan😂. Bata ƙara yarda ta kallesa ba duk da harga ALLAH ya matuƙar canja mata tamkar bashi ba. Ta kuma saka pos ɗin ta a tsakkiyarsu alamar karma yace zai raɓeta. Shima dai dama baiyi niyyar hakan ba, shiyyasa yay zamansa sosai jikin ƙofa suka bada gaf sosai a tsakkiyar. Da ga Ahmad har Hussain sai da suka ji dariya a zukatansu saboda yanayin zaman amarya da angon. Ga shi kowa ya juya kai ya kalli waje tsabar babu ruwan wani da wani ma kenan. Sai da suka fara tafiya Hussain da Ahmad suka gaisa. Da ga haka sukacigaba da ƴar hirarsu a hankali su biyu har suka iso. Wajen fita ne fa dole dai Lulu ta haƙura Smart ya fara fita, dan shine ya buɗe mata da kansa ya kuma miƙa mata hannunsa alamar ta ɗora nata. Ƙaramar Harara tai masa tana ɗauke kanta, sai kawai ya cije lips ɗinsa tare da ranƙwafowa gaba ɗayansa yana tattare hannun rigarsa bayan ya cire link ɗin, miƙa hannun yay alamar zai ɗauketa. Da wani irin bala'in sauri ta waro duka manyan idanunta waje da faɗin, “Kuttt! Mi zakayi?!”.
“Ɗaukarki mana. Ba haka kike buƙata ba Madam”. Ya faɗa cikin salon ɗage gira ɗaya da kashe ɗayan idon. Tsabar abinda ya tokare maƙoshin Lulu sai taji kamar ta buɗe dukan muryarta ta ƙwala ihun da kowa da ke hall ɗin sai ya fito ma. Ta tsani wannan Madam ɗin da yake kiranta da shi tun daga randa sukaje duba shi. Ganin yanda ta fara cika ya sashi ɗage duka hannayensa (alamar wanda yay surrender) da gyara ranƙwafar da yay yana dungure kansa da faɗin, “Kai Aliyun nan ka nutsu a gaban Madam kake”. Sai kawai ta ƙara watso masa harara da tura baki gaba. Da sauri ya ɗauke idanunsa dan harga ALLAH sai da ƙassan jikinsa suka amsa akan tura bakin nan. Hussain dake dariyar drama ɗin tasu ne ya katsesu da faɗin, “Sorry kinjin Sister bashi hannun kinga su Baba duk suna ciki shigowarku ake jira kawai a fara abinda ya tara mutane”. A hankali ta ɗago yatsunta uku batare data kallesa ba. Shima sai ya saka nasa ukun tsakkiya kamar yanda tayin yana ɗan taɓe baki kamar yanda tayi, sai da ya riƙo hanun nata baki ɗaya sannan ya rumtse cikin nashi. Koda ta fito bai yarda sun bar jikin motar ba sai da yasa ɗayan hannunsa da kansa ya gyagygyara mata rigar alƙyabbar da ƙyau yanda ta sake suturta kuma hakan bai hana fitar ƙyaun da tai ɗin ba. Da ga haka suka ƙarasa inda abokan ango dana amarya ke jira suka tafi a nutse kamar yanda ake raka amarya da ango ƴan gata zuwa ga hi table. Matuƙar birgewa sun burge mutane da yawa, yaro da babba ƴammata da samari. Taro ne da ya haɗa harda manyan mutane da iyaye da kakanni shiyyasa babu wata shiririta ko baɗala a cikinsa. Amarya da ango ma tunda aka kaisu mazauninsu hatta cake a zaunen suka yanka shi. Koda ta ɗibo danta bashi maimakon yin hakan saita lakata masa a hanci. Abin ya burge mutane da basu dariya, dan yanda tayi ɗin sai ka ɗauka duk cikin soyayya ne, itako tayi hakanne danta bashi haushi.
Shima daya ɗibo ya kai mata baki, buɗewa tai tana shiryama ranta muguntar gallara masa cizo a yatsun dake riƙe da cake ɗin, amma sai da yaje gab da bakin nata sai ya juya hannun ya lunƙuma a nashi bakin yana mata gwalo. Ai hall ɗin kamar zai fashe dan dariya saboda yanda ta sakankance zatayi mugunta amma aka rusa mata plan. Pos ɗin hannunta ta ɗan buga masa a damtsen hannu tana hararasa kamar zatayi kuka dan haushi.
“Aliyu abin tausayi wannan harara dai ka banu da ita kai kam. Anya an taɓa angon da yasha harara a ranar aurensa sama da ni?” ya faɗa yana mangare kansa da kansa. Karan farko ya bata dariya amma sai ta gimtse, tama ɗauke kanta gefe tana ɗan taɓe baki, dan yau sam bata da ƙarfin yin masifa kuma. Da ƙyar aka samu hall ɗin ya lafa da dariyar batun cake aka cigaba da abinda ya tara mutane. Ko sau ɗaya Smart bai yarda ya tashi ba hakama Lulu bai bari ta tashi ba. Da an buƙaci ganinta a wajen fili zai riƙe mata hannu ya girgiza kansa, itama ɗin dama bata da sha'awar tashin, saita fisge hanunta tana harararsa dan yau ita kaɗai aketa faman antaya masa buhu-buhu. Har fa dai MC ya fahimci ango bai san amaryarsa ta tashi kamar yanda shima bai tashi ba. Masu musu liƙi ma dai sai dai su samesu anan. Alhamdullah duk wanda ya shigo wajen nan zai tabbatar maka yaci ya ƙoshi har ma da ƙullar takeaway, Smart ya gaisa da mutanen da bai taɓa tunanin ganinsu koda a zahirin rayuwa ba, dan ƴan siyasa sun halarci taron nan matuƙa da manyan ƴan kasuwa. Har akai aka tashi bayan cake ɗin nan da ruwa baici komai ba a wajen, hakama Lulu ita daman cikin nata ya riga ya naɗe abincin ba damunta yay sosai ba. Ganin dare yayi dan sha biyu ta gota sanda aka tashi Uncle Yousuf yace su Smart ɗin suje gida abinsu zai koma da Lulu gida, dan tun a hall ɗin ya ga Smart nata faman dafe kai alamar bayajin daɗi dauriya kawai yake yi. Yako ji daɗin hakan da Uncle Yousuf ɗin yay musu, itama kuma mai gayya mai aikin taji daɗin hakan, dan ko sallama bata tsaya sunyi ba tai gaba tai shigewarta mota tana zare alƙyabba ɗin tata datai mugun damunta ita da ɗaurin ɗan kwalin....


*_WASHE GARI_*


Washe gari safiyar Lahadi aka tashi da shirin kai amarya Lulu. Dan haka da safe Uncle Yousuf ya ɗauketa da kansa ya kaita gidan Baba. Inda yayye da ƙannen mahaifiyarta suka taru domin mata nasiha. Alh. Sulaiman ne kawai babu, sosai zuciyar Lulu tai matuƙar rauni, dan mahaifiyarta ce kawai babu a wajen bayan mahaifin Tajuddeen. Ita kaɗai suka taɓa rasawa a cikinsu........✍️











_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣






........Kuka ne sosai ya kufce mata, dan matuƙa tana so da begen mahaifiyarta. (Dan Lulu ta kasance irin yaran nan ne masu ƙulafucin uwa, sai kuma gashi ALLAH bai ƙaddara zata rayu da ita ba) kukan nata ya sake karya zuciyar iyayen nata, haka ma Baba duk da dauriyarsa sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Hannunta ya kama ya zaunar a kusa da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarsa ta dama yana ɗan bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da suka samu taɗan tsagaita kukan sai ajiyar zuciya da take faman saki sannan baba ya fara mata nasiha. Bayan ya gama kowa a falon yay tasa. Kakarta da suke kira Dada ma dai ta danne abinda ke ƙasan ranta na ƙiyayyar auren tai mata nasiha sama-sama, dan ta ɗauki alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen raba wannan auren ƙaddarar. Komai da suke faɗa yana shiga kunnen Lulu, sai dai zuciyarta na fassara komai da gargajiyanci da kuma tsauri da yawa saboda ita tunaninta daban da nasu kasancewar babu ilimin addini a tare da ita. Kuka ma da sukaga tanayi na tuna mahaifiyarta ne kawai babu na aure dan a wawtarta auren nan dai na wata ɗaya ne kacal. Duk wata ƙyauta da iyayen nata suka shirya bata anan wajen suka bata ita kamar yanda tsarin family ɗin yake. Bayan an gama Uncle Khamil da Uncle Shu'aib suka ɗauke ta suka maida gidan Daddy dan Uncle Yousuf yana ajiyeta ya juya. Acan ɗin ma dai bayan sallar azhar Daddy da Uncle Yousuf, Mommy aunty Saliha da gayyar iyaye ƴan jiƙamshi suka zagayeta da tasu nasihar, duk da dai Daddy baice komai ba, sakamakon gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, jikinsa duk a sanyaye yake alamar damuwar rabuwa da ƴar tashi. Sai dai yana ƙoƙarin dannewa amma hakan ya gagara. Bayan tashi da ga wannan zaman aka cigaba da kimtse-kimtsen tafiya da amarya, yayinda Aunty Saliha ta sake ɗaukar Lulu ta kaima matan nan masu gyarata suka sake murjeta tas da kayan gyaransu na musamman da tarin ƙamshi kala-kala. Ba kuma a maidata gidan Daddy ba sai huɗu na yamma cikin shirin miƙata gidan iyayen mijinta. Tayi ƙyau matuƙa cikin atamfar da Aunty Saliha ta bata ta saka. Aka kuma ɗora mata alƙyabba ƴar ubansu baƙa mai kwalliyar golden da fari kaɗan, sai stones da suka sake ƙawatata. Shara-shara alƙyabbar take. Takalmanta yau ma flat ne baƙaƙe. Babu kwalliya ko ɗis a fuskarta dan tace bata so. Sai dai hakan bai hanata zama mai cika ido da kwarjini irin na amare ba, ga gyara tasha na fitar hankali dama fatar nan ta sake wani irin ƙyau kamar madara a sabuwar ƙwarya (Dangin Smart ban son jealous 🥱😉) Hankalin Lulu bai tashi ba sai da taga Daddy na hawaye sanda aka fito da ita yana riƙe da hannunta zai sakata a motar da Hassan zai ja, dan sune zasu mata rakkiya shi da Hussain da Mubeen. Sai motar ƴan rakkiyar amaryar su biyosu a baya. Duk da abokan ango sunzo kasancewar amaryar ƴar dangi ce akwai zugar motoci da ga family ɗin biyu na Jiƙamshi da Garko da zasu bisu da nasu motocin. Ba Daddy kawai ba Uncle Yousuf kansa yana can falon Daddyn yana sharce hawaye yamaƙi fitowa shi. Lulu da duk taji karaya tamkar ba ita ɗin nan ba ta rungume Daddy ta saki kuka mai ban tausayi. Itafa auren nan baisa taji komai, amma wasu abubuwa da ga zuri'ar tata kansa zuciyarta ta motsu. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu a jikin Daddy aka sanyata a mota, Hussain da Mubeen suka sata a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login