Showing 24001 words to 27000 words out of 37818 words

Chapter 9 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

cike da farin ciki.


Wurin mamar tasa ya shiga da murmushi dauke a fuskarsa ya gaesheta yace"Mama Sannu da hutawa".


"Yauwa dan albarka ka ganni inata fama da Hafsatu dakyar tayi bacci".


Shafa kan HAFSA yayi yana murmushi.


"Ya kamata kayi aure hafeezu zaman bamai yiwuwa hakanan bane".


Murmushi kawai yayi yace"Mama muna hanya ae".


Haka dai sukaitayin fira kafin ya wuce dakinsa ya kwanta donya huta.




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻


Emmm Iyyyy luv




TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}.


🌈kainuwa writer's association
By
maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat (ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


27
Cike daso da kauna suke zaune zamansu lafiya yayinda shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu sunata soyewa hankalinsu kwance hakanne ya kara kwantar da hankalin iyayennasu suna karajin soyayyar juna.


Zaune yake a parlor fuskarsa cike da damuwa ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu kwata kwata bayajin dadin zuciyarsa.


Fitowa tayi parlon sanye da dogon riga maroon colour ga cikinta ya fito das daya kara mata kyau white hijabce a hannunta ta iso gabansa cike dason sanin meke damun mijin nata, zama tayi kusa dashi, dora kansa yayi a cinyarta tare da dafe gefan zuciyarsa dake mugun bugawa, shafa kansa tayi tace"zama dayin tunani basa bada mafita saidai kara tura mutum a rudani da bata lokaci, ka natsu ka fuskanci komai da zuciya daya kayi abu da yakini domin kunne aekinsa jini zuciya kuwa itace mai sakawa kafin ta aekata, damuwa bata jarumin gwarzon namiji irin mijina bace".


Sosai hankalinsa ya kwanta yana kara godewa Allah daya bashi Hafsa a matsayin mata, zama yayi yana fuskantarta ya riko duka hannuwanta biyu yace"wife don Allah karki barni duk rintsi ki kasance dani, wallahi rashinki a wurina tamkar tarwatsewar rayuwata ne".


Rufe masa baki tayi tace"ya isa haka, kasan ina tare dakai nima, tashi muje".


Rungume juna sukayi sannan ya saka mata hijabinta ya kama hannunta har bakin mota, yau shiyake driving kai tsaye super market suka nufa inda HAFSA zatayi siyayyan kayan zaki donyau rigima takeji, suna zuwa suka shiga ciki kai tsaye fannin sweet sukayi nanta fara bibar wanda takeso, kallonta HAFEEZ yayi yace"wify kiyi sauri inaso muje na siyi turaruka".


"Kada ka damu kaje, zan iskeka saimu gama a tare ko"HAFSA ta fada.


"Ban yardana a kalleminke kuma wazai daukar miki kaya"cewar HAFEEZ


Murmushi tayi tace"zan rike kaje kawai pls my love"


Shafa fuskarta yayi ya wuce zuwa wurin Sweet.


"Daddy ni muje sweet nakeso fa"cewar little tana dira kafa kaman zatayi kuka, rugawa tayi wurin sweet din ba yadda HAFEEZ ya iya a dole yabi bayan little din.


Ita kuwa tana isa ta soma eban sweet kawai da gudu ta nufi HAFSA tana fadin"Aunty ki dauki wannan da dadi Allah "little ta fada tana mikawa HAFSA ledan sweet din.


Sosai yarinyar ta burge HAFSA dukawa tayi tace"tona gode my baby, ya na ganki ke kadai ina mamanki? ".


Shagwabe fuska little tayi tace"Aunty bana da mama daga granny sai Daddy na tare dashi nazo"


Lokaci daya tausayin yarinyar ya ratsa zuciyar HAFSA, nan take suka rungume jina, "la Aunty Daddy na yazo"maganar little ta katse mata tunani, lokaci daya kuma taji zuciyarta na zafi da azazzalarta a sanyaye ta juyo daga dukiyan da take, a firgice yake kallon fuskarta ta kara masa kyau ga kwarjini data masa baki na rawa ya furta"HAFSA ".
Jin ya ambaci sunanta muryar da ba zata taba mantawa a rayuwarta ba ta daki dodon kunnenta ta kwammace a narka darma a zuba mata a kunne dajin wannan mumunan muryar, tun daga kasa take kallonsa tare da mikewa tsaye har I zuwa fuskarsa, kara daure fuska tayi duk wani farin ciki nata ya gushe cikin kakkausar murya tace"ko kayi mamaki ne, ko kuma kaso na mutu lokacin da kazamo bakin azzalimi".


Murmushin gefan baki HAFEEZ yayi yace"akwai azzalumi banda mijinki maci amana mayaudari".


A tsawace HAFSA tace"Dallah rufemun baki, bazan taba iya daukar munanan kalamai ga mijina ba, a wannan kaskantartar muryar taka me karamin zuciya wacce batasan hallici ba".




Dariya ya tuntsire da ita ya soma zagaye HAFSA sannan ya dawo gabanta yace"soyayya ruwan Zuma, HAFSA Ashe har yanzu ke yarinyace neman abu kike kuma kina tare dashi, to bari na baki sani, babu azazzali mai kaskantartar zuciya sama da mijinki wanda besan halacciba mayaudari, to inaso ki sani mijin da kike tutiya dashi shiya lalata rayuwarki ya dasa maki TABON da bazai taba warkewaba kinaso ki cemin bakisan shine wanda yasa na kawoki ya miki fyade ba, amma kin yaudari kanki".




Kamar saukar aradu haka takejin maganganun HAFEEZ lokaci daya tunaninta ya kulle ta dago ido tana jefarsa da mugun kallo cike da tsantsar tsana tace"ae ka fishi tunda kai soyayya ka siyar don kwadayin abun duniya, kuma ka sani dukiyar haram tacin amana tanan zata koma zan iso kanka"tana zuwa nan tayi gaba abunta zuciyarta na dukan ukku ukku, saurin ficewa tayi daga wurin, cikin sauri HAFEEZ ke kwala mata Kira dayaga fitar tata a rude, shiko saba little yayi yabar wajen, da sauri HAFEEZ yayiwa mota key yabi bayan napeep din data shiga, amma ta rigashi zuwa gida kudi kawai ta mika masa ta shige gidan dinhar jiri take gani, tsaye tayi a parlon sororo dabin caset din da aka kunna a TV tabbas itace lokacin da aka mata fyade har sanda aka fitar da ita, HAFEEZ da Adam suka yaye max din fuskarsu wani irin mugun faduwar gaba taji ga pictures din sake watse tsakiyar dakin ga littafi aje, dauka tayi tana dubawa hakan ya kara tabbatar mata da abunda ta gani, innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shine kalamin dake fitowa a bakinta yayinda hawaye masu dumi kebin fuskarta, lokaci daya kuma ta maida kallonta ga HAFEEZ daya kame kaman gunki yana kallonta da alamar tsoro karara a fuskarsa, magana tajesonyi amma ta saka lokaci daya ta saki kuka mai sauti tayi dakinta da gudu tasa key. Jikin kofan ya nufa yana kiran sunanta a matukar kidime dukan kofan yakeyi amma kamar bata jinsa, sai sautin kukanta yakeji da karar fashe fashe.




*tofa yau ake yinta, kudai ku biyoni donjin ya abun zai kasance*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻






Emm Iyy luv




*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


By
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat (ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


30
London
Tunda sassafe HAFEEZ ya tashi ya shirya tsab cikin black shadda yayi matukar kyau sosai sai zuba kamshi yake komai nasa black abunka da farin mutum saiya fito ras dashi, da sassarfa ya fito parlor Momy da Amma ya samu a zaune suna shirya yaransa, har kasa ya duka ya gaeshesu, suka amsa cike da fara'a tsurawa yaran ido yayi cike da tausayinsu gasu da uwa amma an illata masu ita, maimakon su bude baki da nonon mahaifiyarsu saidai suka buda baki da madara amma duk Wanda yamin haka ya cuceni, Amma ce ta katse masa tunani tace"HAFEEZ kaje kayi breakfast kaji".


"Amma bazan iyaba, Asibiti zanje yanzu"yana idasa maganan ya mike yana goge hawayen dake shirin zubo masa yayi waje.




Cike da tausayinsa Amma tace"Allah ya bamu mafita, duniya ba yarda"


Da Ameen Momy ta ansa cike da jinjina al-amarin, "gaskiya rayuwar HAFSA tana cike da rudu da ban al-ajabi y'ar karama da ita amma taga kalubale na rayuwa iri iri"cewar Momy


Murmushi Amma tayi tace"gaskiya kam da bata da karfin jini da bata kawo yanzu ba, ita kuma tata kaddarar kenan".
Haka dai sukaitayin fira kafin suka fara shirin tafiya asibiti.


Shikam nasa bangaren yana zuwa ya tura kofar dakin da take ciki ya shiga, tananan yacce take a kwance, cike da natsuwa ya isa inda take ya shafa fuskarta yace"ina fatan ki tashi my wife, donko nida yaranki muna tsananin bukatarki a kusa damu"murmushi yayi ya zauna yana wasa da yatsun hannunta har bacci yayi nasarar daukesa a wurin.


Koda su Amma suka shigo ganinsu a haka yasa suka kara jin tausayinsu, suka fita tare da ja masu dakin, don Momy ta tabbatar jiya beyi bacci ba.




Next day Ummy tazo ita da iyalan Abduol, driver yaje daukarsu kai tsaye asibitin ya nufa dasu, sosai suka tausayawa Hafsa inda ummy ta share hawayenta tace"kwanciyar me kikeyi, rashinki babbar matsala ne, be kamata kibar Adam da HAFEEZ da Suhailat ba tare da daukar fansa ba, sun cutar dake , da duk Wanda yayi silan kwanciyarki ko zafin nakuda baki gama ba ina bukatarki a raye swtheart "ta karashe maganar cikin kuka, da kyar aka kaita gida.


Yau ta kama ranar sunar yaran HAFSA su kadai a gida yanka aka masu inda Namijin yaci Ameer macen kuma Amira, HAFEEZ yasa sunanan saboda Shi HAFSA take burin sawa inta haifi yan biyu, su kadai sukayi sunansu yayinda uwar jego ke asibiti.




Washe gari sukaje asibiti, a wajen dakin suka zauna suna fira, HAFEEZ ne kadai a dakin rike da hannunta, idonta a rufe take karanto addu'ar tashi daga bacci, zabura yayi ya kura mata ido yana ambaton Alhmdllh ga wani irin dadi dake ziyartar zuciyarsa ya soma sakin murmushi, a hankali takebin dakin da kallo hawaye nabin fuskarta, idanuwanta ta sauke akan HAFEEZ "bari na Kira Dr"ya mike, amma saita kara rike hannunsa tana fashewa da kuka tare da runtse idanuwanta, rarrashinta yayi tayi shiru ba tare data fadi komai ba, cikin hanzari ya fadawa su Amma ta farfado Ummy harda sujadar godiya tayi, yayinda Dr geb yazo ya dubata babu abunda ke damuwarta saidai rashin karfin jiki Wanda ya tabbatar zata warware cikin kwanaki, murna sosai ya tayasu kafin ya fita, cikin sassarfa suka shigo kowa na jera mata Sannu, a lokacin Abduol da Faty suka shigo, suna murna suke da Sannu kallonsu kawai take har lokacin.


Cikin murna Ummy ta mika mata danta namijin tace"gashi taci suna Ameer, wannan kuma taci suna Ameera"Ummy ta fada tana mika mata su.




Karbar yaran tayi ta rungumesu a kirjinta tana jin soyayyarsu na ratsata ta fashe da kuka, dakyar Momy ta lallashe sai a sannan ta mikawa HAFEEZ yaran ta mike tsaye tadanyi taku biyu sai a sannan tayi magana cikin dashewar murya tace"ina dayan yarinya ta? "


Cike da mamaki suke kallonta a tare sukace"yara biyu kika Haifa ae"


Murmushin takaici tayi tace"yara ukku na Haifa biyu mata, nice uwar da ina cikin zafin nakuda aka kashemin y'a a gabana, akamin allurar mutuwa, mena aekata haka, inaso ku sani rai befi raiba, kuma jini befi jini ba, rai daya kashe rai shizai biya ran y'ata bazan taba hakura ba, aka rabani da yarana na tsawan kwanaki ".


A rude suke kallonta cikin tashin hankali HAFEEZ ya rike hannunta yace"waye ya kashemin y'a na tabbatar kin gani".


"Karka damu sunyi hakane don bukatar kansu, inaso mu koma Nigeria cikin satin nan".


A rude suka sanarwa su Daddy, sukace a bari su dawo sai ayi case din.




Kwananta ukku Asibiti aka sallameta donta warke ras Tana shayar da yaranta.




Tofa ana wata ga wata readers kudai ku biyoni.




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻




Emm Iyy luv


*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


Na
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat(ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


*naji korafinku, kowa da abunda yake fada, saidai inaso ku sani na riga na tsara littafinnan tun kafin na fara to pls ku biyoni kuji meye karshen lvrn baku tari numfashina ba, ninasan meye hikimar yin hakan*


29
Kafin Kace me tuni gari ya zagaye da mutuwar HAFSA lallai naga dinbun jama'a, mutuwarta ta ratsa mutane sosai, yayinda ake shirin yi mata wanka a kaita makwancinta.


A matukar razane HAFEEZ yake kallon Adam yace"ta mutufa Kace, wannan bamai yiwuwa bane".


Murmushi Adam yayi yace"while yadda ka dauka Abban little but HAFSA ta mutu yanzu haka ana shirin kawar da gawar ta ne"yana zuwa nan ya juya ya fita ranshi yayi fari kal.


Wani uban ihu HAFEEZ ya kurma tare da fadin"no kada kimin haka".
Saban salo 😄😄


Bangaren goga HAFEEZ kuwa a hankali ya soma bude idonsa yana zagaye dakin da yake da kallo idonsa ne ya safka akan fuskar Abduol yayinda hawaye kebin gefan fuskarsa, goge masa hawayen Abduol yayi yace"kayi hakuri haka Allah ya tsara, kaddararka kenan, kada kayi jayayya da hukuncin ubangiji bayan kanada iliminka ka daure ka cije yanzu kam HAFSA bata bukatar komai sai addu'ar ka shine zai nunawa duniya cewa ka sota sona gaskiya".


Balle drip din jannunsa yayi yace"Abduol muje gida, inaso naga gawar matata".


Kamasa Abduol yazoyi, ya dakatar dashi cike da kwarin gwaiwa ya mike ya soma tafiya a hankali, Abduol yaja motar har kofar gidansu HAFSA, kallon kofar gidan yake yadda ya tare yan Adam wainan duk masu son salatar matarsa ne da kumayi mata rakiya, hawayen da yake makalewa suka fara ambaliya a fuskarsa juyar da fuska yayi ya shige cikin gidan da sauri Abduol na rike dashi, ko kadan be kula matan dake cike da gidanba saidai su ke nunasa suna kukansu, kai tsaye part din Abbui ya nufa inda ake shirin yi mata wanka, Ummu na ganinsa ta tashi tabar dakin don wani irin tausayi ya bata lokaci daya ya rude ya fiffige ya fita hayyacinsa, kallon kuskarta dake a bude yake ya shafa gefan fuskarta yace"kicemin mafarki nake wife, kin tafi kin barni ga yara, tabbas naji rashi babba, ki jirani ina hanya donko rashin zai iya matso da ajalina kusa". Momy dake kuka bayansa ta kamasa, rushewa yayi da kuka ya rungumeta tsam kamar karamin yaro.


"Kuna ganin abunda nake gani kuwa, ku duna, wallahi motsi idonta da hannunta keyi"makociyarsu ta fada.


A razane HAFEEZ ya juyo yayo kanta, duka mutanan dakin sukayo kanta, tabbas idonta motsi yake ga dan yatsanta dake juyawa, cikin gaggawa aka sanar dasu Daddy tare dasu Abbui suka shigo suma tabbas sun ganewa idonsu HAFSA bata mutuba ga idonta nan yana motsi but a rufe yake, Alhmdllh HAFEEZ ya furta ya rungume HAFSA yana zubar da kwallar dadi.


"Maza mu tafi asibiti yanzu"cewar Daddy.


"A ganina a fitar da ita waje kawai zaifi"Momy ta fada.


Waya Abba ya dauko ya kirawo Dr dinsa, ya shaida masa ya iskesa gidan aminin nasa, sannan ya dubesu yace"wannan likita nane, a waje yayi karatu, ya fara duba mana ita a gida sannan muyi visa zuwa wata kasar".


Kowa ya aminta da shawarar Shi sai lokacin HAFEEZ yayi maga yace"Abba, London zamu wuce da ita, inada likita kwararre acan, kuma shike dubata tunda mukaje can din"


Momy ta san Dr geb shiyasa bata musaba tasan ya kware a aekinsa, nanda nan Abduol yayi masa waya cewar zasu zo gobe.


Dr lawal na shigowa dakin Abbui aka kawosa, I yanzukam mutane duksun watse suna addu'ar Allah yasa bata mutuba, saida ya gaesa da kowa sannan ya bukaci su bashi wuri, ba yadda basuyi da HAFEEZ ba yaki fita, a dole Dr ya fara aekinsa tana a jikinshi, kwaje kwaje yayi yadai tabbatar bata mutuba, sannan ya fito wurinsu ya zauna yace"bata mutuba, amma anyi mata allurar guba ne, itace ta haifar mata da suman da tayi, amma Alhmdllh nayi mata allurar da zata tsayar da gubar har zuwa gobe, kafin nan an samu visa fitar da ita daga kasar".


A kidime suke maimaita allurar guba kuma, cikin tashin hankali HAFEEZ yace"yanzu kam ba yarda kowa yana cikin zargina, dole nayi bincike duk Wanda na kama dasa hannu saiya fuskanci hukunci"sai a sannan ya karbi yaransa yana kallonsu ga wata soyayyarsu da tausayinsu ya mamayeshi sai tsotsar hannu suke, sai a sannan Amma ta hada masu madara tana basu.


HAFEEZ kam shida kansa yakai HAFSA asibitin Dr lawal, kuma ya tsareta, Abduol kuwa yanacan cuku cukun visa.


Karfe 9 na dare motar asibiti ta danno kai cikin airport tare da wasu ukku a bayansu, cikin gaggawa aka turo bed din daukar mararsa lafiya aka dora HAFSA akayi da ita cikin jirgin, HAFEEZ, Momy, Amma, Abduol sune zasuyi wannan tafiyar, acewarsu komai ake ciki zasuzo dubasu, ba jimawa jirginsu ya lula cikin sararin sama niya.




Da motar asibitin Dr geb akazo daukar HAFSA, emergency aka wuce da ita ya shiga bata taimakon gaggawa, cikin ikon Allah ta farfado tare da tari da nishi mai karfi, allurar bacci yayi mata sannan ya daura mata drip sannan aka kaita daki na musamman yanzu kam lafiya lau take fitar da numfashi.


Office ya kirawo HAFEEZ da Abduol yace"komai lafiya lau yanzu, gara da kuka hanzarta tsaida gubar anyi sa'a bata game jikinta ba, amma sai kunsa ka ga masu shiga wurinta gudun samun matsala, dukdadai ba'a kwana anan, zamuci gaba da kula da ita, yanzu na mata allurar bacci donta samu natsuwa"dukda turanci yake wannan bayanin.


Hamdala sukayi ga sarki Allah, sannan suka masa godiya suka fito, saida suka ganta sannan suka wuce gida, Abduol ma ya wuce gudansa, a parlor sukayi masauki sai a sannan yayiwa yaran huduba da addu'o'i ya mikawa Amma ya wuce dakinsa, wanka yayi ya saka jallabiya ya zauna gefan bed yana tuno rayuwarsu ta gidan, da kyar Momy tazo ya lallabashi yasha fresh milk, suko tuni masu aeki suka girka masu abinci sukaci sannan suka shirya yaran suna suka kwanta donsu huta.




Da kuka Ummy ta farfado ta mike zaune tana bin dakin da kallo, da sauri Ummu ta zo wurinta tana mata Sannu. Kuka ta kuma fashewa dashi, rungumeta Ummu tayi tace"kiyi hakuri Ummy, HAFSA bata mutuba".


Sororo takebin Ummu da kallo sannan tace cikin muryar kuka"dama ana mutuwa a dawo ko wasa da ita".


"Gaskiya Ummu ta fada kaki, HAFSA bata mutuba"cewar Muhammad nan ya labarta mata abunda ya faru.


Sosai tayi farin ciki saidai tace saita gano Wanda yayi wannan aeka aeka, amma kuma ba jira jibi zata wuce London.




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻




Emm iyy lov


*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


Na
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat(ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


*wannan page din nakine y'artulluwa Andija ta KAINUWA fans 6,na gode kwarai da kulawarki, aradu kodon tsoron da kikaji dole HAFEEZ ya gaesheki kyauta*




28
Wani mumunan tashin hankali ke ziyartar kwakwalwarsa ya rasa meke masa dadi yana zancen zuci yanzu nan HAFSA tasan sirrin da nake boyewa don gudun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login