Showing 36001 words to 37818 words out of 37818 words

Chapter 13 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

shigar da karar Adam ga shuwagabanninsu kuma daya gama zai wuce London.


Sosai shugabansu Wanda suke kasanshi ya jinjina lamarin cin amanar da Adam yayi, gyada kai yayi yace"ka barshi zamu dauki mataki a ranar da kuka dawo daga cos dinku".


Kamewa Abduol yayi yai saluting ogan nasa yace"thank u sir".


Alamar tafiya ogan ya masa, sannan ya juya ya fice cike da farin cikin samun nasara, sannan ya wuce Airport jirginsu ya tashi zuwa London.


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karsheπŸ‘πŸ»


Emm Iyyyy luv


*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


By
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
*duk wani masoyin Wannan book din ina yinku sosai da sosai*


Gaesuwa ta a gareku
Aunty fauza
Neeshar jay
Hauwa'u salisu HAUPHA
Ummy ontop
Sis feenarh
My ladingo
Ummu HAFEEZ
Ummu yusuf
Real maryam
Maryam Abdul
Ummu nabil
Maryam obam
Amnoor
Nafisa Anka
Billyn Abdul
Real mai dambu
Xahra farooq
Nabilancy luv
Nabiya
Mrs Sardauna
Aysha aiche
Maryam paki
Rashidat usman
Aunty Hauwa
Amaryar july(khady)
*kai dadai duk Wanda ban ambatoba don nasan bazaku kareba inayinku duka Wanda ban Kira sunanku ba, kuyi hakuri kuna raina*




πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š




Yau ta kama Monday yaune zaman kotu na farko tun sassafe suka shirya, HAFSA kam gida tabar yaranta ta kama hanya, sosai kotun ta cika can ta hango Suhailat fuska tayi luhu luhu alamun kuka tasha, ga HAFEEZ gefanta suna zaune Adam ne dayan side din sai kabir, anan ta samu Ummy da Momy da Muhammad sosai sukayi masu fatan nasara sannan suka shiga ciki, basu wani jimaba alkali ya shigo kowa ya mike don girmamasa, saida ya zauna sannan ya masu izinin zama, kafin aka gabatar da kara, sannan aka mika masa file din.


Yan rubuce rubuce yayi sannan ya dago yace "zan iya ganin wadanda ake kara? ".


Cikin girmamawa Suhailat da HAFEEZ suka mike zuwa cikin abun tambayar mai bada sheda.


"Suhailat, HAFSA tana kararki akan kashe mata y'a kuma gudan jininta me zaki iya fadi"Alkali yayi tambayar


Sunkuyar da kanta tayi kasa hawayen bakin ciki na ziraro mata cike da dakiya tace"na amsa laifina ya mai shari'a".


"To meyasa kika kasheta? "Ya kuma jefo mata tambaya.


Murya na rawa tace"saboda son zuciya, na nemi mahaifin yarinyar daya aureni ne yaki, nayi duk wani abu da zan jawo hankalinsa amma yaki, shine naje wurin wani malami yace aeki bazai yiwuba harsai matarsa ta haihu an kawo jinin jaririnta".




Dam gaban HAFSA ya fadi wasu hawaye masu dumi suka soma gangarowa a kyakyawar fuskarta tana kuma jin tsanar Suhailat a ranta.


Goge hawaye Suhailat tayi taci gaba da cewa"a lokacin komai zan iyayi domin na samu mijin HAFSA, shine nasaka ido harna samu labarin tana nakuda da asibitin da aka kaita, shine naje na hada kai da Dr Anas na bashi miliyoyin kudi sannan ta amince zai taimakeni, lokacin data haifi yaranta ukku biyu mata data namiji duka lafiyayyu shine na dauke mace daya kuma Dr Anas yayiwa HAFSA allurar guba donta mutu, Amma Allah beyiba likitoci sukayi nasarar ceto ranta, duka abunnan munyishi a boye ba tare da sanin Dr Ahmad ba wato shugaban Asibitin Wanda ake zargi, bacin na gudu da yarinyar tun kafin na isa ta fara sandarewa a bayana alamun bata motsi na tabbatar wahala ta saka ta mutu, shine na dawowa Dr Anas da gawan don a lokacin ji nayi bazan iya bada gawar ta ayi tsafi da itaba"kukane yaci karfinta sosai har tana niyar shudewa.




HAFSA kuwa don bakin ciki idonta sun firfito waje kanta ke wani mugun sarawa saboda tsananin tashin hankali hawayene kance akan fuskarta tanata faman jawa su Suhailat Allah ya isa.


Nanma Alkali rubuce rubuce yadanyi sannan ya dago yace"idan Dr Anas yana kusa ya fito".




Dama tunda Suhailat ta fara magana yayi zufa sharkab hankalinshi yayi mumunan tashi sai dana sani yakeyi, kafarsa na kyarma ya fito yana goge gumi.




"Kaji abunda Suhailat ta fada, kana da ja ko wani Karin bayani "Alkali ya tambaya.


Da kyar Dr Anas ya hadiye yawu yace"bana daja ya mai shari'a duk abunda ta fada gaskiya ne, saidai yarinyar data maidomin ta dade da mutuwa, shine na rufeta kamar yadda addini ya tanada".




Alkali maida kallonsa yayi ga HAFEEZ yace"malam HAFEEZ kai kuma ana kararka akan cin amanar daka aekata da siyar da mutuncin HAFSA, dason raba auranta da kakeyi shin kanada ja ko wani karin bayani".




Nisawa HAFEEZ yayi sannan yace"na amsa laifina ya mai shari'a nayi hakanne duka bisa son zuciya da son kai, saidai ina rokon kotu ta yankeman hukunci daidai da abunda na aekata".


Gyada kai Alkali yayi ya kuma rubuce rubuce sannan ya dago ya gyara zaman gilashinshi yace"abisa la'akari da kotu tayi, na masu laifi sun ansa laifinsu batare dasun batawa kotu lokaci ba don haka kotu ta yankewa HAFEEZ kamal zama gidan kaso na tsawan shekara biyar sakamakon cin amana da ciyar da mutuncin HAFSA, sannan kotu ta yankewa Suhailat da Dr Anas hukuncin zama gidan kaso na tsawan shekara goma tare da horo mai tsanani sakamakon jiyar kashe rai da sukayi"buga tebur Alkali yayi sannan aka mike don girmamashi ya wuce.




Wasu zafafan hawayene suka zubowa HAFEEZ sakamakon kallon little da yayi sai wasanta take batasan wainar da ake toyawa ba, kai tsaye yan sanda wurinsu suka iso tare da saka masu ankwa a hannuwa, fashewa da kuka suhailat tayi tana dana sanin abunda ta aekata, cak HAFEEZ ya tsaya gaban HAFSA daketa rizgar kuka anata faman lallahi.


Isa yayi ya duka akan gwaiwowinsa ya hada hannuwansa waje daya yace"hakika na cutar dake, kin zauna da bakin cikina na na tsawan shekaru, don Allah ki yafe mini duka son zuciyane da sharrin shaidan Amma nayi dana sani, ki yafemun kodon na isa gaban uban gijina ranar gobe da tsarki".




Tunda HAFEEZ ya yaudari HAFSA wannanne karo na farko da tausayinsa ya darsu a zuciyar ta zuciyarta ta soma bugawa murya na cracking tace"na yafe maka".




Little ce ta matzo tana goge masa hawaye tace"Daddy ka daina kuka kaji, zaka siyamun ice cream ko Daddy kuma muje wurin Mama tunda bata dawowa".


Hawayene suka kara yawan gudu a fuskarshi ya rike hannunta yace"Daddy kabir zai siya maki, amma ki yafewa Daddynki Wanda yayi silan tarwatsewar rayuwarki zan tafi bansan wani hali zaki fadaba, Allah ya albarkaci rayuwarki"rungumeta yayi sosai.




Hannu HAFSA taja ta jawo little tace"inka yarda zan kula da ita harka fito rayuwarta bazata taba tarwatsewa ba.


Cikin kuka ya gyada mata kai, hannun yake dagawa kabir dake kwaranyar hawaye, turasu ake shirin yi mota, wani mumunan labari ya iso, da guda Momyn fadila ta iso wurin tana fadin"pls ku barta ko kallon karshe tayiwa gawar mahaifiyar ta da Aminiyar ta".


Cikin razana Suhailat ta juyo tace"meya samesu? "


Gawawakin da aka shimfide a gabanta yasa tayi shiru, hannunta na kyarma ta bude ta farko momce sai kayi da gaske kake gane kamanninta, ta biyun ta bude Fadila ce itama tayi daga daga.


Ihu ta kurma, da gudu Adam ya tsere yana tsoran shima ta iso kansa(nace hmm kaima tana zuwa gareka ne).


Dafata maman Fadila tayi tace"wurin sauri suzo su karbi belinkine trailer ta bigesu saida hakuri".




Mikewa Suhailat tayi kamar zautacciya tana fadin"kun gani ko, duniya ba komai bace sun tafi sun barni na shiga ukku na"hannu ta dora akai tayi titi da gudu, binta sukayi su kamota kafin su isa mota tabi ta kanta ta fado kasa kai ya fashe shure shure ta soma na mutuwa tanason yin magana abu ya gagara anan ta mace kafin ayi yunkurin kaita Asibiti.


(Allah sarki dama haka duniyar take)


Dafe kai HAFSA tayi tashin hankali ya kuma mata yawa a take ta fadi wurin a sume, before takai kasa HAFEEZ ya rungume ta Wanda isowarsa kasar kenan, iskan bakinshi yake hura mata a bakinta da gudu yabi bayan Abduol sukayi asibiti da ita, ummy ce ta karbi little daga hannun kabir suma sukayi asibiti, yayinda aka wuce dasu HAFEEZ gidan kaso, da taimakon kabir aka kai su Suhailat makwancinsu saidai muce Allah yaji kansu.




Asibiti taimakon gaggawa suka shiga ba HAFSA harta farfado dama firgita tayi, tas ta tako kafarta ta fito, jikin HAFEEZ ta fada suka rungume juna, kafin suka runguda zuwa gida, sosai su Daddy suka masu fada da nasiha kuma sun dauka, zumudin HAFEEZ yayi yawa ba arziki Ammi ta tattarasu bayan ta gyara HAFSA ta tarkatasu gida, soyayya takin kari sukewa juna kullun suna jone, little harta saba da gida ga yaransu na wayau.


Yau satinsu daya da dawowa daga London kuma yaune za'a kara masu girma, wanka HAFEEZ yayi cikin uniform na soji yayi matukar kyau yayinda HAFSA ta hade cikin tsaddan less ga yaransu sunsha kyau in baka saniba ba zakace ba ita ta haifi little ba, yan uwa duk ansha shiri an fito das sannan suka dunguma zuwa wurin taron, sosai aka yaba kokarin su HAFEEZ sannan aka kara masu rank harda Abduol sai a sannan aka Kira Adam, ya fito cikin uniform da isa, gabatar da laifinsa sukayi sannan aka cire masa uniform a wurin, basu jira cewar kowaba suka badashi ga gidan horaswarsu, taro ya tashi lafiya kowa ya koma gida.




"A gaskiya nayi farin cikin zamuki a matsayin mata ina sonki har abada ina tare dake"HAFEEZ ya fada.


"Ni ya kamata na fadi haka, nayi sa'ar miji mai kula dani, fatana ka rikeni har abada"cewar HAFSA rungume juna sukayi cike da tsantsar soyayya.


Time to time kabir na zuwa duba little kuma yayi aure abunsa, kuma suma suna kai little taga mahaifin ta.


A gurguje pls


Rana bata karya yaune HAFEEZ ya cika shekar biyar gidan yari kuma ya fito, sosai yakewa HAFSA godiya kan rike little, a ranar ta mayar masa da duk wata dukiya data karba wurinsa, ansha daga kafin ya ansa, anma ta rikesa dayabar mata little ba musu yace aetafi karkin Wannan wurunsa,watanshi biyu da fitowa yayi aure abunsa, komai ya koma normal sunajin dadin rayuwa.






Some years




Yanzu little na ss2, zaune take tana karatu Amira ta rugo bayanta ta buya tanawa Amir gwalo ball rike a hannunta tana fadin"wallahi ni bazan bakaba"


Amir da Amira zasukai shekara 12 suna tsananin kama da juna komai nasu iri daya da mahaifunsu.




Kallon ta little tayi tace"ni Wannan rigimar taku tafi karfina Allah".




Bata fuska Amir yayi yace"Allah ki bani kayaba".


Jawad dan 6yearsa shike bi masu ya taho yana masu dariya da tsokanarsu tuni suka hade kai suka bisa da gudu yayi hanyar fita, Cak HAFEEZ ya da gashi sama yana masa oyoyo, ihun murna dukansu suka saka suna kiran"Daddy oyoyo"little kam rungume mahaifin ta tayi, zama sukayi kafin suka gaeshe da Auntynsu sannan little ta karbi meena yarda auntynsu ta Haifa.




Hafsa da HAFEEZ ne suka safko daga stairs tana dauke da katon tsohwan ciki, fira sukeyi sosai.


Yanzu yaran Ummy 3,Abduol yanada ukku mata sai Ahmad babbansu.


Sukan kaiwa Adam ziyara dukda shima shekarunsa sun kusa karewa.




*Alhmdllh na godewa Allah daya nunamin karshen Wannan novel, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mamu, ya bamu ikon fahimtar sakon dake ciki, maryam luv u all*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login