Showing 27001 words to 30000 words out of 37818 words

Chapter 10 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

kada na rasata bazan iya jurar rashintaba Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni kairan minha shine abunda yaketa maimaitawa a bakinsa jin kukanta yake har cikin ransa ji yake kamar zuciyarsa zata tarwatse don bakin ciki, zamewa yayi kasa tare da dafe kansa, jin kirar sallahr la'asar da ake Kira shiyasa ya rarrafa dakyar yayi alwala yayi masallaci.






Bangaren HAFSA kuwa kuka kawai take sharbawa ga wani kululun abu da yayi mata tsaye a zuciya hannuwanta duk jini duksun fashe, jin fitar HAFEEZ yasa ta mike da sauri tana juye juye, bude dakin tayi cikin sauri tayi waje kai tsaye bakin titi ta nufa ta tsaida mai napeep gida ya kaita, ko daidai tsaiyuwa beyiba tayo waje ta bashi kudi masu yawa ba tare data dubaba, iya karfinta take dukan gate din gidan da sauri mai gadi ya bude don ganin waye, bata jira tambayar da yake mataba ta kutsa kai ciki da sauri fuskarta na tsiyayar hawaye, Ummu dake zaune parlor cikin sauri ta juyo jin muryar HAFSA da kuka tana fadin"ke lafiyarki kuwa?, meya samu Hafeezun? ".


Fadawa tayi jikin Ummu ta kuma fashewa da matsanancin kuka tana fadin"Ummu HAFEEZ ya cuceni, Ashe shine yayimin fyade, Ummu wallahi bazan iya ci gaba da zama dashi ba"ta kuma rushewa da kuka.


"Ke saurara mana kikemin wani bayani a baibai ki nitsu kimin bayani kafin Abbunki yaji hargowarki ya fito". Cewar Ummu.




Cikin muryar kuka ta fadawa Ummu komai hada yadda akai HAFEEZ yasa aka daukota dacin amanar da Abban little (HAFEEZ) ya mata.


Jinjina kai Ummu tayi tace"kunyi kuskure sosai na rufe wannan sirrin Ashe HAFEEZ guduwa yayi, to amma abun yazo da sauki rungumar kaddara zakiyi ki rufe sirrin mijinki ku zauna lafiya".






"Saima kin bata shawara akan haka, ae aekin gama ya gama tunda Wanda tsautsayi ya fadawa shiya aureki, donko HAFEEZ mutumin kirkine, maza fitarmin na daina ganinki ki baro gidan ALHAJI Muhammad kizo nawa to me zamu baki, ina gargadinki amincinmu ba wasa bane"cewar Abbui.


Mikewa tsaye Ummu tayi tare da rike HAFSA jikinta na kyarma ta dora hannu aka ta kuma fashewa da kuka tace"Abbui kuyimin rai, bazan iya zama da HAFEEZ ba koda na second na tsaneshi, wallahi Abbui mutuwa zanyi idan na koma wurinshi".




"Shut up, saidai ki mutu fitarmin daga gida kuma kada na kuma ganin kin nunamin fuskarki". Abbui ya fada a zafafe cikin matukar bacin rai.


HAFSA tasan Abbui tunda yayi fushi bazai taba bari ta zauna mishi gidaba, juyawa tayi tana toshe bakinta tayi hanyar fita, cikin sauri Ummu ta rikota.


"Koki saketa, ko ki bita kema auran naki ya kare"yana fadan haka ya koma sama.




HAFSA ko cire hannunta daga na Ummu tayi, tayi waje abunta.




Bangaren HAFEEZ kuwa yana dawowa masallaci yaga kofar dakinta a bude da sauri ya kutsa kai, saidai bata ciki duk inda ya dace ya duba ya duba babu ita a gidan, cikin sauri ya safko yana tambayar mai gadi koyaga fitarta, ya bashi amsa da ta fita tun dazu, garin daukar key yaci karo da farar takarda, cikin sauri ya buda ya soma karantawa
Lallai ka ansa sunanka namiji, na gode kwarai, na dade ina nemanka a rayuwata Ashe ina tare dakai, nikam na tafi sai wata rana in kaga sakona tokayi gaggawar sakina donna rabu dakai har abada
Daga tsohuwar matarka HAFSA.


Wani uban ihu ya kurma Wanda ya karade gidan da sauri ya figi key yayiwa motarsa key ya fice da wani azabban gudu, ikon Allah ne kawai ya kaishi gidansu HAFSA a waje yabar motar, ya shiga gidan da sallama.


Ummuce ta amsa bayan sun gaisa HAFEEZ yace"Ummu ina HAFSA nasan na mata laifi saidai bazan iya jure rashinta ba".


Murmushin karfin hali tayi tace"ka natsu Hafsa zata dawo gareka tazo dazu, saidai mahaifinta ya koreta".


A razane yake kallon Ummu, beyi mata sallama ba ya fito daga gidan, kokarin daidaita natsuwarsa yayi ya kira, Ummy tace batazoba, haka ya kira maryam itama tace batazoba, haka zalika gidan Amma ma, cikin tashin hankali ya Kira Momy bugu daya ta dauka da sallama.


Fashewa yayi da kuka kamar karamin yaro yace"Momy ta tafi, tace bazata dawoba, Momy bazan iya rayuwa ba HAFSA ba".


Hankalin Momy tashe tace"son ka daina kuka kamin bayani pls".


Nan ya fadawa Momy sabani suka samu ya boye gaskiyar yace kuma tazo gida Abbui ya koreta, kuma ya tambaya ko ina ance batazo ba.


Kwantar masa da hankali tayi tace"ka daina kuka fushi ne tayi, kuma nasan data huce zata dawo gareka, yanzu zanje gidan nasu kayi hakuri".


Kashe wayar yayi ya rufa kansa a mota yana hawaye dana sanin abunda ya aekata yakeyi tare da tsanar hali irin na Adam daya bashi gurguwar shawara, kuma ya dauka a lokacin ya yarda shawarar Abduol wacce itace me kyau.




Dariya Adam da HAFEEZ suka fashe da ita tare da tafawa yayinda Suhailat ke jinjina masu tana fadin"kunyi kokari aeki yazo karshe".


Murmushi HAFEEZ yayi yace"kowa zai cika burinsa, don nima yanzu zan nemi masoyiyata tana haihuwa na aure abuta".


Kara kashewa sukayi sannan sukawa motarsu key sukabar inda suke.




HAFSA kuwa tana fito daga gida titi tabi na bayan gidansu hawayene kebin fuskarta, ga zuciyarta dake radadi kamar zata tarwatse ga mugun ciwan kai, tafiya takeyi kamar marar lakka don kuwa karfinta ya soma karewa ga kishin daya kawo mata ziyara, kallon kafarta tayi lokacin da jini kebin gefan kafarta hakan yayi daidai da murdawar da cikinta ya shigayi kamar ranta zai fita, ga tari da takeyi ya sarketa lokaci daya ta dafe zuciyarta ga wani irin wawan jiri dake dibarta bata kara taku biyuba ta zube a kasan titi a sume.




Ganin kuka ba nasa bane yasa ya share fuskarsa yana tunanin ko wanne hali HAFSA take tabbas ya Santa da muguwar zuciya ga kafiya, kuma yasan ba zata taba zuwa gidansa ba shawarar zuciyarsa yabi na yabi titi koya ganta, kai tsaye mota ya shige yayi mata key ya soma bin titin bayan gidansu yana tafiya a hankali zuciyarsa cike da kunci.




Hango wani abu yayi a gabansa kwance kamar mutum kuma yanata horn yaga abun bai motsa ba, hakan yasa ya fito, "HAFSA "ya fada da karfi yayi kanta da gudu girgizata yakeyi shiru, ruwa ya dauko a motarsa ya zuba mata, wata doguwar ajiyar zuciya taja ta bude idanuwanta da suka lumshe kamar mai bacci turesa ta somayi tana fadin"ka sakeni guduwa zanyi, bazan kuma zama dakaiba"makalkalesa tayi ta saki kara tare da dafe cikinta ta fashe da kuka.


Momy ce ta dafasa tana fadin"subuhanallah daukarta muje Asibiti nakuda nakeyi".


Mikewa yayi rungume da ita ya shiga bayan mota yayinda ya ciro key dinsa ya jefa a motarsa ya Kira Samuel ya sanar dashi inda yabar motar.


Gudu Momy keyi sosai cikin kankanin lokaci suka iso asibiti family Doctor dinsu ta Kira, cikin sauri aka kawo gadon daukar mararsa lafiya, HAFEEZ be kalli gadonba yayi dakin da za'a shiga da ita da gudu ya shinfidar da ita bisa bed, dakyar suka samu ya fito waje, yayinda likitoci sukayi kanta don ceto ranta da abunda ke cikinta.


Rungume Momy yayi ya fashe da kuka lallahinsa tayi sannan ta Kira Amma ta fada mata meke faruwa, ita Ummy ta Kira, kusan a tare suka iso asibinti sai ga maryam itama.


Kai komo kawai suke wasu na addu'a, Ummy kam babu abunda takeyi sai kuka.




Sosai likitoci ke kokarinsu a kanta tasha wahala sosai dakyar suka samu ta haihu da kanta inda aka samu yara biyu namiji da mace, macan na fitowa HAFSA tayi wani irin nishi tare da sandarewa ko motsi batayi, nurses suka karbi yaran don shiryasu, ita kuma suka dora duk wata kwarewarsu akanta amma abun yaci tura result daya suke samu, a matukar kidime Dr Ahmad ke furta innalillahi wa'inna ilaihir raju'un HAFSA ta rasu, sosai jikinsa yayi sanyi karbar yaran yayi ya rungume ya fito, cikin sauri HAFEEZ yasha gabansa ya jefo masa tambaya"Dr ina matata".


Mika masu Momy yaran yayi yace "ina zuwa ka kara mana lokaci"hakan yayi daidai da shigowar Daddy da Abbui da Abba musabaha sukayi da Dr sannan yace"yallabai ko zaku bini ciki amma HAFEEZ yadan jiramu".


Gyada kai sukayi Daddy yace"ka jiramu muna zuwa".


Sannan yaja hannun Abbui Wanda saida suka kai ruwa rana sannan ya yarda ya biyoshi sukazo asibitin.


Bayan sun shiga Dr Ahmad yace"kuyi hakuri kullu nafsin za'ikatul maut, HAFSA ta ansa kiran mahaliccinta sai ayi gaggawar kaudata".


A razane suke dubansa sannan suka maida kallonsu ga bed din da HAFSA ke kwance an lullubeta da farin zani, innalillahi wa'inna ilaihir raju'un suke furta jan kafafu sukayi suka isa wurin, hannun Abbui na kyarma ya yaye malillibin daga fuskarta, a take fuskar tata ta bayyana ta kara wani irin haske idanuwanta a rufe, kaman ka Kira sunanta ta ansa, hawaye Abbui ya soma zubarwa ya duka akan gwaiwowinsa yana shafa kanta yace"Ashe ganin karshe zan miki, Allah ya karbi bakuncinki Hafsatu lallai nayi rashi babba". Yasa babbar riga yana goge fuskarsa.




Su Momy da Daddy ya sanar masu jan hannun HAFEEZ da Ummy kawai sukayi zuwa cikin dakin.




Sororo HAFEEZ yayi yana binsu da kallo kunnuwansa sun kasa fahimtar kalaman da yakeji wai HAFSA ta mutu donshi wai yake gani, isa yayi gabanta ya soma girgizata yana fadin"Hafsa ki tashi, ki fada masu baki mutuba, kin tuna alkawarin da kikamin na zamu rayu tare bazan jure rashinki ba pls pls ki tashi".


Ko gezau bare tayi motsi, kowa kuka yake a dakin wani irin ihu HAFEEZ ya kurma ya fadi wurin a sume, hakan yayi daidai da sumewar Ummy itama, cikin gaggawa aka daukesu aka kaisu emergency, yayinda kowa na dakin ke kuka hankali tashe, Abbui ya rungume gawar HAFSA har gida, ya shinfidar da ita tsakiyar parlonshi yayinda Ummu ke gefe guda hawaye masu dumi sunabin fuskarta.


*innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Hafsa ta rasu😭😭😭Lallai nayi kuka sosai*


*banason korafi ku biyoni donjin Karashen labarin*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻




Emm Iyy luv


*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


By
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat(ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


31
Tunda aka sallamesu suka shirya komai na tafiya, donko HAFSA tace kwana daya ba zata sake a garinba, sai yamma likis jirginsu ya tashi zuwa Nigeria, sun sanar da zuwansu don haka sun iske su Samuel sunzo daukarsu lokacin 8 na dare kowa gidansa ya wuce da nufin gobe za'a hadu, HAFSA kuwa fir takibin HAFEEZ tabi Amma suka wuce gida, ummy Muhammad yazo daukarta.


Koda Ummu taji y'arta ta koma ras sai murna tahauyi da godewa Allah.


Suna zuwa gidan Amma, cike da murna ta gaeshe da Abba, kafin tabar yaran Amma ta masu wanka ta shiryasu ita kuwa ta fada dakinsu na da, tana shiga ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta hada ruwa masu zafi ta fara gasa kanta kamar yadda Amma ke mata a London, sosai take tuna abubuwan da suka faru, kafin ta fito fuskarta tayi sharkab da hawaye shiryawa tayi cikin blue dogon riga ta saka black hula ta feshe jikinta da turare ta fito parlor, saida Amma ta tsareta sannan taci abinci ta shayar da yaranta ta koma daki ta kwanta, itama Amma daukar yaran tayi ta wuce dakinta.




HAFEEZ kuwa zuciyar sa cunkushe ya isa gidansu wanka yayi yasha jallabiya ya kabbara sallah saida dare ya raba tsaka sannan bacci yayi awan gaba dashi akan sallaya.




A cikin daren Adam ke fadawa Hafeezu cewar captain fa ya shigo gari, dariya Hafeezu ya kwashe da ita, Wanda saida Adam ya raba wayan daga kunnensa,sannan Adam ya kara da cewa"kuma labari mai kyau HAFSA na raye kuma ta shigo garin nan".


Murmushi ya kumayi yace"ae nasan bazata mutu tabar masoyinta ba, tasan ina sonta, amma tunda da auran wannan karfan a kanta dole zansa a kawar man dashi daga doron kasa kona samu damar mallakarta".




"No bazai yuwuba kadaiyi abunda zaisa ya saketa, cos idan HAFEEZ ya mutu ya zanyi da Suhailat bazata iya jurar rashinshi ba"cewar Adam.


"Ok gobe ka fito da wuri ma tsara komai"cewar HAFEEZ yana kuma kashe wayar.


Dubansa kabir yayi yace"wallahi HAFEEZ baka da imani, ya kasan abunda kayiwa yarinya da sannan yanzu ka yaudari kanka da cewa wai zaka aureta, kuma wai har kayi iki rarin kashe rai saboda son duniya, meya shiga kankane, ya kama ta ka sauya tunani tun kafin dare yayi maka haba kanayin abu kamar marar ilimi".


"no kabir ni kake Kira marar ilimi, abota fa ba hauka bace, dahar zaka kalli cikin idona kana fadamun magana wlh yau daba kai bane da tuni ka bakunci lahira". Cewar HAFEEZ a fusace.


"Kai har kanada bakin magana, haka kuma soyayya ba hauka bace, me ilimi zai aekata abunda kakeyi ne, ae bazan hanaka ba kaikasan wacece HAFSA tunba yanzuba nasan tana zuwa kanka ne kuma ba zata bari ka cutar da uban yayanta ba, dahar kake yaudarar kanka wai zaka aureta, dir da wannan furuci naka, kuma indai bazaka sauya haliba ina dab da fadawa Mama komai"yana zuwa nan ya ficewarsa yayi wa motarsa key ya tafi gidansa zuciyar sa cike da kuna.




HAFEEZ kuwa dafe kai yayi yana tunanin yau daba kabir bane daya gaggauta daukar mataki a kansa, saidai bacci barawo ya daukesa.




Suhailat duban Fadila tayi tace"husband fa ya shigo garin".


"Lallai lokaci yayi da zaki sanar dashi sirrin zuciyarki kanki tsaye kiyi amfani da kayan da malan ya baki kije gidansa gobe da sassafe"cewar Fadila.


"Eh haka za'ayi kuma ae ita HAFSA din wai tana gidan Amma dazu Adam yake fadamun"Suhailat ta fada.


Haka dai suna fira har suka fada masha'arsu yayinda Mom tazo ta gansu sai tayi baya taja kofar itama ta wuce hotel wurin kortonta.
(Allah kayi mana tsari da irin wannan rayuwar ka kuma shiryemu).


Next day.


Tunda safe Adam ya shirya tsab ya isa gidan HAFEEZ a parlor ya samesu nan suka ci gaba da gudanar da yadda sukeso komai ya kasance.




Amma tuni ta shirya yara tasa HAFSA ta shirya suka wuce gidansu, anan suka samu Momy da Ummy sunzo, Ummu tayi farin cikin ganin y'ar tata, kallonsu kawai HAFSA tayi ta duka ta gaeshe da Abbui da Daddy, ta koma gefe ta rakube kanta cikin gwaiwarta ta lula duniyar tunani.




Horn take aka wangale mata gate din gidan shiga tayi tayi parking ta dade kafin ta fito da kafarta dake cikin dogayan shoe sannan ta fito duka jikinta sanye take da crazy jeans black colour ga wata arniyar riga kusan duk jikinta a bude yake tasha makeup ga kai yasha attachment sai zuba kamshi take kai tsaye murda handle din Kofan tayi ta shiga babu kowa a parlon sai karar TV da Ac bisa chair Suhailat ta zauna tana karewa dakin kallo.


Fitowa yayi tare da rufe dakinsa sanye take cikin shadda ash colour dinkin yayi matukar karbar jikinsa dukda ramar da yayi ga kanshi yasha gyara ya dora dara akansa ga agogon azurfa daure a tsintsiyar hannunsa yayi matukar kyau, a nutse yake safkowa daga stairs zuwa parlon tsaye yayi turus yana kare mata kallo cike da mamakin ganin ta a gidansa.


Murmushi ta sakar masa ta mike ta iso tana niyar rungumarsa, ya daga mata hannu yace"wait meya kawoki kuma? ".


Murmushi ta kumayi tace"alkairi, Wanda duk wani da namiji da ya mace zasuyi burin kullawa a tsakaninsu wato aure".


Dariya maganar taso ta bashi amma ya daure yace"ina jinki".


Kallonsa tayi tace"yaya HAFEEZ na dade ina dakon soyayyarka a zyciyata, tun kafin kayi aure, ina sonka fiye da yadda nikeson kaina, kuma zanyi komai dominka kulllun sonka kara nunkuwa yake a cikin zuciyata pls ka daure ka aureni kayi mani koda rabin son da nake maka ne"ta karashe maganar hawaye nabin kuncinta.




Tuni fuskarsa ta canza ya daure fuska tamau ya fara magana tace"saboda baki da aekinyi ne, yasa kika tsaya har zuciyarki ta kamu dason abunda ba zaki taba samuba, an tun dadewa nasan kina sona, amma ni banga abunso a jikinki ba jikin da kika gama tallarsa a titi kuma har kiyi tunanin waini zan iya auranki, hakan na zama abokinki dahar kike kallona ido cikin ido kike cewa wai kina sona, maganar karshe kada ki kuma tarata da irin wannan maganar marar amfani, idiot kawai"hankadeta yayi yasa kai ya fice, tana kallonsa ya tada mota yabar gidan, hannu ta dora akai ta fasa ihu ta fito ta shiga mota, tana tukin ganganci ikon Allah kadai ya kaita gida.




Shiko gidansu HAFSA ya nufa, ya iske kowa ya hadu cike da ladabi ya gaeshe da kowa dake dakin ya tsurawa HAFSA ido da har yanzu kanta ke cikin kafarta ko motsi batayiba.


Gyaran murya Daddy yayi yace"nasan kowa yasan meya taramu anan, inaso ku fahimceni mu gano gaskiya kafin mu yanke hukuncin daya dace, ke HAFSA ki mana bayani".


Sai a lokacin ta dago rinannun idanuwanta tace"kamar yarda na fada, yara ukku na Haifa, donko hankalina be gusheba, amma bansan ya akayi naga biyu ba, ku bincike Drs din da suka kula dani "kuka ya subuce mata.


"Hakan shine daidai, mu fara bincike daga asibiti nan zamu gano gaskiya"cewar Abba.


"To hukuma zatayi ko ya kuke gani"Abbui ya fada.


Sai sannan HAFEEZ yayi magana yace"ina rokon alfarmarku daku barmin case din a hannuna".


Nandai sukaitayin magana hardai aka samu matsaya anbar HAFEEZ yayi bincike. Da gudu HAFSA tayi dakinta tana kuka, Ummy ta rufa mata baya, tana shiga kan bed ta fada ta rushe da kuka, Ummy ce ta dafata tare da dagota, shima HAFEEZ din rufa masu baya yayi.


Kallonta HAFSA tayi tace"kuncin rayuwa ni na shiga Hafsa dukka na dimauce haddira mai yawa nina shiga amma nayi kaucewa, ya rabbu Allah buwayi kaine kake juya yayi kakanyi zafi da sanyi manufa ta rabbana ya tsareni duka kaidi bazai kashen ba".




Girgiza kai Ummy tayi tace"HAFSA karki damu, kibarwa sarki jalala y'ar uwata HAFSA komai zai wucewa, mu taru muyi murna yan uwan juna ne kin jiya, ba sa'insa ba hamayya babu hayaniya karki damu, ni kaina zuciyata dukta sanyaya".


Ganin HAFEEZ yasa HAFSA mikewa fadawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login